spon

Showing posts with label HAUSA NOVEL. Show all posts
Showing posts with label HAUSA NOVEL. Show all posts

Monday, September 10, 2018

SANADIN GATA (HAUSA NOVEL) PART 1

~Kanta dauke yake da farantin talla wanda aka kasa mata dafaffen rogo da gyada kulli kulli, taci damara sai kace wadda za tayi dambe tana tafe tana rera wakar ta"iye nanaye ayye yaraye nanaye carmama, ina tafiya ta jirgin goro zaya kade ni, jirgin goro kar ka kadeni, jirgin goro zan maka sako, sakon goro ko na turare in kaje kace da uwata, in kaje kace da ubana jirgi yai bari, jirgi yai bari da madaurin aurena, iye nanaye ayye ya raye nanaye carmama, da inna da baba an kawo kudin toshina cacas cas suna kirgawa, sun ganni suna boyewa in kun so kubar boyewa, auren fari sai na zaba sai na zabi wanda na ke so koda soja ko dan sanda, koda kuku koda boyi, koda jinjiri sha mama sai yaci tuwon kwanona sai yasha ruwan kwanona sai na kai ruwa sai nakai ruwa ban daki yai wanka, iye nanaye ayye yaraye nanaye carma....kuluwa, kuluwa kawo rogon, muryar wasu maza masu sai da ruwa ne ya hana kuluwa karasa baitin wakar da take rerawa, cikin sauri ta nufi wurin da suke, tana zuwa ta sauke farantin da ke kanta ta fara kukkulla musu kamar yadda suka saba siya, nan da nan aka warwashe ta dauki farantin ta cikin hanzari bayan ta kirga kudinta ta hada Kansu naira dari biyu cif cif, sauri take sosai dan tasan yanzu iyatu tana nan tana jiran zuwanta.

Tafiya take gudu gudu sauri sauri kamar zata bar garin har ta karasa gidan nasu wanda yake ginin kasa ne wato jar kasa, ciki ta karasa can ta hango iyatu kwance a tsakar dakin ta kamar yadda ta saba a kullum. Ta maza tayi ta tunkari cikin dakin ta shiga bakinta dauke da sallama agwasale iyatu ta amsa sallamar tata ta kara gyara kwanciyarta kafin ta wurga mata harara, tsugunnawa kuluwa tayi tace gashi iyatu na sayar na dawo, baki iyatun ta taba sannan tace miko min kudin na gani, mika mata kuluwa tayi ta karba ta kirga kudi sun cika cif cif ko kwandala bata bata ba, ungo wannan ki tashi ki tafi kasuwa kije ki iyo cefanen tuwon dare da zakiyi saura kuma ki tsaya a yawon da kika saba ki ga yanda zan rugurguje ki a gidan nan, yar masu da bakar zuciyar tsiya, tashi kuluwa tayi ta fita daga cikin gidan ta nufi kasuwa inda za ta iyo cefanen.

Wata azababbiyar yunwa take ji saboda rabonta da taci abinci ta koshi har ta manta yunwa take ji sosai, haka ta samu ta shiga kasuwar ta yi cefanen ta nufo gida, akan hanyarta na dawowa ne taci karo da mairo kawarta, kallon mairo tayi cike da sha'awa saboda sanye take cikin uniform din makarantar islamiya duk da cewa ita ma mairon tana talle to amma ita tana zuwa makarantar boko da islamiya sabanin ita da babu abinda take yi sai talle, daga talle sai aike sai aikin tsakar gida komai na gidan ita ke yinsa ita iyatu bata da abin yi sai kwanciya sai ko idan tayi wani abun na laifi ta jibgeta, cikeda tausayawa mairo tace kuluwa daga ina haka? Hmm mairo kenan ai kema kin san daga inda nake domin daga talle sai aika sune ayyukana ina son makarantar boko da arabi amma iyatu ta hanani karfi da yaji, gashi iyatu bata tausaya min ko kadan hatta baba bata daga masa kafa, dafa kafadar ta mairo tayi kiyi hakuri kuluwa kuma dan Allah kici gaba da hakuri da halayen iyatu saboda wata rana sai labari komai na duniya da kika ganshi mai wucewa ne, daga kai kuluwa tayi idonta duk ya cicciko da kwalla naira goma mairo ta mika mata gashi inji shamsu yace idan na ganki na baki, karba tayi tace nagode nagode mairo hakika shamsu ya cika masoyi cikakke saboda komai runtsi yana tare dani, murmushi mairo tayi hakane sai dai Allah yasa soyayyar taku takai ga aure, murmushi kuluwa tayi tare da juyawa ta fara tafiya tana murmushi wa ya ganni nida shamsu a matsayin ma'aurata? Ni kaina nasan za a zuba love ba dan kadan ba.

Gida ta tunkara tana shiga tun daga cikin soro ta fara jiyo hargowar iyatu wannan shegiyar yarinya tana kona min rai, wannan yarinyar kwai marar albarka, tun da dadewa na aike ta amma saboda bata ganina da mutunci shine taje tayi zamanta to wlhi bara ta dawo yau mai rabani da ita sai Allah, jikin kuluwa ne ya fara rawa saboda jin kalaman iyatu saboda tasan bata iya duka ba duk abinda ta samu kwada mata za tayi, da makyarkyata ta shiga cikin gidan bakinta yana rawa tayi sallama, ai iyatu na ganinta ta fara ruwan bala'i sai yanzu kika dawo? Nace sai yanzu kika dawo min? Saboda ke shashasha ce mai bakin hali shine kika je kika yi zamanki ko? Cikin in ina kuluwa tace wlh iyatu babu a inda na tsaya, zaki fada min a inda kika je kika zauna yanzu yanzun nan iyatu ta fada tare da daukar wani faskare ta nufe ta tana cewa kar ki kuskura ki gudu idan kika fita daga gidan nan sai na lahanta ki, kuka kuluwa ta fara yi ita kuwa iyatu ta nufeta gadan gadan, da gudu mahifinta ya fito daga cikin turakar sa yazo ya rike faskaren hannun iyatu yana cewa haba tsahare me yasa kike haka ne? Yarinyar nan kina gallaza mata, kina cutar da ita ki kiyayi ranar da sakayya za tazo wlh kiji tsoron Allah tsahare domin yawancin yaron da ka cutar shine yake zama wani abu a rayuwa,kuma irin su Allah yake daukaka wa, rufe min baki tsohon banza tsohon wofi, kai in banda ma hudubar shaidan ta yaya zaka zauna kana yabon wannan yarinyar har kana tunanin zata zama wata nan gaba, to ai ba irin wadannan Allah yake daukakawa ba saboda yarinyar nan ba yar arziki bace yar tsiya ce kuma wlhi in dai ta iyo cikin shege babu ruwa na sannan sai dai ta nemi wani gidan amma ba dai wannan ba, in sha Allahu hawwa'u ba zata yi cikin shege ba saboda ni nasan irin tarbiyar da na bawa yata, dakyau malam muhammadu, nace da kyau Malam muhammdu lallai yayi maka kyau wato saboda ban taba haihuwa ba shiyasa zaka yi min gorin haihuwa? Yayi maka dai dai babu shakka kanka ya fito daga kuttu kuma ka samu lafiya, nagode da ka daurewa yarka kugu tayi min rashin kunya a gidan nan sannan kuma ka nuna mata ban isa da ita ba dan bani ce na haifeta ba,to wlhi sai na dau mataki a kanku, ba dai da ni kake magana ba, yayi maka kyau, juyowa ga kuluwa tayi ke kuma idan kin ga dama kije ki dauko ruwa kizo ki dora abincin idan kuma baki ga dama ba ki barshi shashasha mai mugun yancin tsiya, bokiti kuluwa ta dauka ta fita daga cikin gidan ta tafi tuka tukar dake girke a filin gidan sarki, nan taje ta saka bokitin ta akan layi ta koma gefe ta zauna ta fara tunanin rayuwarta.

Ita kadai ce a wurin mahaifin ta, bayan ita bai sake haihuwa ba, Allah ya karbi ran mahaifiyar ta tun lokacin da ta haifeta domin a wurin haihuwar ta ta rasa rayuwar ta, tun lokacin da mahaifiyar ta ta rasu babanta ya auro iyatu domin ta riketa amma sai abin ya canja salo domin iyatu babu abinda take mata sai zalunci sam ba ta kaunar ta ko kadan asalima duk wanda ya nuna yana kaunar kuluwa to sai ta dau karan tsana ta dora masa, ayanda mahaifin ta ya bata labari mahaifiyar ta salaha ce mutuniyar kirki mai son jama'a sam duniya bata dame ta ba gata da rikon addini she is pious, religious, gata kamila tunda ta samu cikin kuluwa take fatan Allah yasa ta haifi yarinya Mace domin ta rada mata suna hawwa'u amma sai Allah bai yi zata zauna da yar tata ba. Iya babanta da iyatu kawai ta sani saboda bayan su ba tasan dangin mahaifiyar ta ba balle na mahaifin ta sai dai ako da yaushe mahaifin ta yana bata labarin cewar yana da yan uwa guda 2 a birni daya mace daya namiji, namijin yayan sa ne yayin da macen ita ce take binsa sunanta Salma amma ita bata taba ganin yan uwan nasa sun zo ba kuma yasha fada mata cewar yasan iyatu ce tayi surkullen ta irin nasu na mata ta raba shi da yan uwansa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga idanuwan ta suka gangaro kan kumatunta saboda tausayin mahaifin ta da taji ya mamaye ta a hakikanin gaskiya mutum ne mai hakuri baya son fitina amma iyatu ta sako shi gaba da masifa har kuka ta ke sashi shiyasa itama taji iyatun ta fita daga ranta saboda tsanar da take nuna mata ga mugun bakin da take binta dashi kullum tsine mata take tana yi mata fatan cikin shege ga zagin mahaifiyar ta da take yawan yi alhalin ko zama ba su yi ba tare tunda sai da mahaifiyar ta ta rasu sannan aka auro iyatun. 
Pg 11-20
~~Ganin layi yazo kanta ne ya sata katse tunanin da ta keyi ta tafi bakin tuka tukar ta tara bokitin ta,ta debi ruwan ta kama hanyar gida tana zuwa ta tsinkayo iyatu tana  ta kai komo a tsakar gida sai yi take da bakinta me za ayi da dan riko? Ai dan riko jaraba ne kuma masifa ne saboda idan ka zuba masa ido ya lalace laifinka za a gani ace ka bar da ya lalace, idan kuma ka na yi masa fada nan ma baka tsira ba sai ace dan ba kai ka haife shi ba shiyasa kake takura masa, ai sharrin dan riko yawa ne dashi, sai dai kawai fatan samun sauki a wurin Allah, ni dai duk wanda yasa duniya ta zageni bazan yafe masa ba, karasawa ciki kuluwa tayi ta sauke ruwan ta fara hada wuta a murhu domin ta dora tuwon sayarwa yayin da ita kuma iyatu har yanzu ba ta bar bakinta ya huta ba sai masifa take ta yi, yo dama waye zai rungumi dan kishiya ai sai wawa shashasha saboda dan ma ko ka rike shi ba fita za kayi ba wani dan ma in mai bakin hali ne Allah Allah yake ya samu duniya domin ya wulakanta ka, sallamar maryama ce ta katse iyatu daga babatun da ta ke yi ita dai kuluwa iyatu har mamaki take bata saboda kwata kwata bata gajiya da surutu ga masifa idan aka yi mata abu ta kama mita wuni za tayi tana abu daya. Inda kuluwa take maryama ta karaso tana cewa kuluwa kinga har mun taso daga makarantar a hanya na hadu da shamsu yace nazo na kiraki, wa zaki Kira? Iyatu ta fada cike da fada to wlh daga yau babu ke babu gidan nan munafuka, dama ashe kece kike hure mata kunne ko? To maza zo ki fice kije ki ce masa ba zata zo ba kuma maza yaje ya nemi matar auran sa amma ba wannan marar asalin ba ehe, kallonta maryama tayi iyatu ni kuma me nayi miki? Daga shigowa ta zaki fada ni da fada kuma naga ai ni ba wani abu na cewa kuluwan ba da zaki ce ina zuga ta, ke maryama ni kike fadawa haka? Saboda tsabar baki da kunya ko, to tun kafin ranki ya baci ki bar min gida idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya ke kika jawa kanki, juyawa maryama tayi zan bar miki gida amma ina so ki sani duk abinda mutum ya shuka shi zai girba tana gama fadin haka ta juya tabar gidan, take iyatu ta hayayyako ta fara bala'i tare da jan zaninta tana fadin bari naje na jawa uwar taki kunne kar na kara ganin kafarki a gidan nan tunda abin babu mutunci, nagaji da wannan cin kashin da ake min idan da saninta gwara naji, dagowa da kanta kuluwa tayi tabi bayan iyatu da kallo daidai lokacin da take fita daga soron gidan tasan halin iyatu sarai dama dan ta raba su da maryama da shamsu ne yasa ta takalar fadan, saboda ita dai duk wanda zai kaunaci kuluwa to ita kuma shine abokin gabarta,figar mayafin tayi ta fita tana ta ruwan bala'i ita kam kuluwa ko ba a fada mata ba tasan gidan su maryama ta tafi kai togaciya, haka taci gaba da hada wutar har ta kama ta dora tuwon sayarwar, mahaifinta ne ya fito daga cikin daki ya karaso in da take sannu kuluwa kiyi ta hakuri kinji, komai na duniya yana da iyakar sa shiyasa zaki ji kullum bani da magana sai kiyi hakuri domin shi hakuri baya baci kuma komai yayi farko zai yi karshe ni kaina kin ga hakuri nake da ita amma duk da haka bata barni ba, share kwallar idon ta tayi tace babu komai baba insha Allahu zan ci gaba da hakuri kamar yadda ka bukata, yawwa hawwa'u Allah yayi miki albarka ya baki kyakkyawan rabo duniya da lahira, amin baba tafada tana hawaye, to me ya naji kana sa mata albarka ni kuma sai ka tsine min ai, muryar iyatu suka jiyo daga soro tana magana cikin fushi, in banda munafurci meye zaka wani zo ka saka yarinya a gaba kana zagina a wurinta ko dan ka iya ha'inci sai nayi magana kuma ace ni masifaffiya ce to wlh na fara gajiya ehe, shi dai baban kuluwa sa kai yayi ya fice daga cikin gidan ya bar iyatu tana ta masifa wanda hakan ya zame mata jiki domin kullum wuni za tayi tana babatu a unguwar duk makota suna jinta sai kace ita kadai ce mata, juyowa ga kuluwa tayi tafara yi mata fada duk abinki dai ba zaki auri shamsu ba ke da aure sai dai kiga a nayi amma ba dai ke kiyi ba ita dai kuluwa bata ce komai ba taci gaba da girkin da take yi.

Mangarubar fari ta gama tuwon ta zuba a fanteka ta dauka ta nufi dandali inda a ka'ida can take kaiwa kullum da daddare, tana zuwa tuwon ya kare, kudin da shamsu ya bawa mairo ta bata ta dauka ta siyi abinci taci tayi kat, tana shirin harhada kwanukan ta ne mairo tazo inda take cike da damuwa akan fuskarta, kuluwa kinji abinda iyatu taje ta fada a gidanmu dazu? Girgiza kai kuluwa tayi me tace? Wlh kuluwa iyatu tayi duk wani rashin mutunci da kika sani tare da gargadin shamsu wai babu shi babu ke kuma baki ji zagin da tayiwa iyayen mu ba to shine mahaifin mu yace da shamsu kar ya kara kulaki, wasu hawaye ne suka gangaro akan kumatun kuluwa lallai iyatu ta gama nuna mata kiyayya saboda tunda ta rabata da shamsu ta gama da rayuwar ta,share mata hawayen mairo tayi tace kiyi hakuri kuluwa Allah yasa haka shine mafi alkairi, amin mairo nagode kuluwa ta fada tare da kinkimar kayanta ta nufi gida tana hawaye.

      A haka rayuwar kuluwa taci gaba da guduna cikin ukuba da matsati gashi kaf garin babu saurayin da yake zuwa wurinta saboda kowa tsoron masifar iyatu yake domin dama iya shamsu ne ya jajurce to shima iyatu ta raba su kullum kuluwa cikin kuka take mahaifin ta kuwa hakuri kawai yake bata acikin wannan halin ne aka sanya ranar bikin mairo wadda sai alokacin kuluwa taji hankalinta ya tashi saboda ita da mairo ne kawai suka rage gashi mairon ma zata tafi ta barta nan tabi ta rarrame har mahaifinta ya fahimta ya kirata yayi mata nasiha da cewa tayi hakuri in Allah ya yarda za tayi aure wanda za tayi alfahari da mijin, nasihar mahaifin ta tadauka ta dangana yayinda iyatu ita kuma ta samu nayi kullum habaici wai kuluwa tayi bakin jini bata da saurayi gashi shekarunta 19,kuluwa tun abin yana damunta har ta hakura. Yau da gobe babu wahala har lokacin bikin mairo yazo haka aka sha hidimar biki aka kaita dakin mijinta, bayan bikin da kwana 2 ne kuluwa ta dawo daga talla ta ratsa ta gidan mairo, tsayawa tayi tana kallon dakin mairo wanda yasha kwanukan silba da su dan cana ga gadonta mai runfa na karfe, Allah ya sanya alheri mairo kuluwa tafada kamar za tayi kuka dan tausayin kanta saboda ita tasan babu wanda zai yi mata wannan kayan domin babanta ba shi da hali, zaunar ta mairo tayi ta fara bata labarin irin bakar wuyar da tasha a daren farkonta nan da nan kuluwa tsoro ya shigeta take taji ta fara tsoron maza saboda wannan labarin da mairo ta bata saboda tace mata akwai wuya, yan kayayyakin ta ta dauka ta nufi gida tana tafe tana cewa lallai maza ashe abin tsoro ne, tana zuwa kofar gida ta ga wata dalleliyar mota mai kyau sabuwa dal, gidan ta shiga tana shiga taga iyatu a tsakar gida hankalin ta ashe kamar wadda yan sanda suka kama, jin sallamar ta ya sanya mahaifin ta fitowa daga cikin turakar sa ga wata mata kyakkyawa yar gayu a biye dashi, kallon kulawa matar tayi tace wannan ce hawwan? Lallai hawwa ta girma, amma nayi mamaki ace yarinya kamar wannan bata zuwa makaranta, babu komai Salma ai mun gama magana dake kuje kawai nagode Allah ya bar zumunci, kallon kuluwa yayi yace hawwa ga yar uwata Salma nan da nake baki labari yau tazo zata tafi dake birni zakije kiyi karatu Salma kanwata ce uwa daya uba daya dan Allah ki riketa a matsayin uwa, to abba kuluwa ta fada cikin farin ciki saboda zata bar masifar iyatu, cizon yatsa iyatu ta fara yanzu ina ji ina gani zata tafi da yarinyar nan ta zama irin ta? Inama na barta ta auri shamsun ta kare rayuwar ta a wahala ta fada acikin zuciyar ta, maza shiga ki dauko kayanki inji mahaifin ta, no basai ta dauki komai ba yar gayun ta fada tana murmushi, kama hannun kuluwa tayi tace to zo mu tafi hawwa nan fa iyatu ta biyo su kamar zata kurma ihu tana ji tana gani kuluwa ta shige mota ta dare luntsumemiyar kujera. 
2⃣1⃣
~~~Wani bakin ciki ne ya turnuke iyatu take ta fara masifa tamkar wata zautacciya munafuki dama nasan wata kulalliyar ka kulla saboda yarinyar tana yi min talla tana dan samo min kwabo shine kake bakin ciki, to ai gani nayi dai hawwa yata ce ba taki ba ko? Kuma bake ce kika haifa min ita ba dan haka baki isa kiyi min iko da ita ba yana gama fadin haka ya shige cikin gida nan fa ta bishi tana cewa eh dama ai ka saba yi min gorin haihuwa dan yanzu kayi ba zan ji ciwo ba, shi dai baban kuluwa bai sake tanka mata ba saboda yau burinsa ya cika ya raba kuluwa da wahalar iyatu.

       *************
Gudu anty salma take shararawa a motar ta kamar ba mace ba saboda yadda take tuki babu tsoro a take da ita, sai da suka dan yi nisa sannan ta jiyo ta dubi kuluwa tace hawwa yanzu za kije Inda zaki samu sauyin rayuwa kuma insha Allah zan cikawa yaya burinsa na son yaga kin samu kyakkyawar rayuwa.
2⃣2⃣
Dadi ne ya ratsa zuciyar kuluwa saboda idan da abinda take so to karatu ne ita dai a rayuwar ta tana so ta ganta a makaranta tana daukar darasi, maganar anty salma ce ta katse mata tunanin ta, yaya ya fada min komai game da irin rayuwar da kike yi a hannun iyatu da duk irin tsangwamar da tayi miki, na rasa me yasa iyatu bata da halin kwarai ta dauki duniya ta riketa kamar ba zata barta ba, amma yanzu gashi ai kin tafi kin barta sai muga wanda zata takurawa, shiru kuluwa tayi aranta tace Allah sarki babana yanzu kuma shine zai jure jarabar iyatu tunda ni bana nan.

    Misalin karfe 3 na yamma su kuluwa suka isa garin kanon dabo tumbin giwa wanda masu iya salon magana su kance ko da me kazo an fika, kai tsaye unguwar sharada phase 2 suka wuce, kuluwa zare ido tayi ta fara kalle kallen abubuwan ban mamakin da suke cikin birnin saboda ko motocin dake wucewa abin kallo ne gashi dan adam kamar ba a mutuwa,

suna shiga unguwar kuluwa ta cika da mamaki saboda ganin irin gine ginen dake girke a unguwar kowanne gida ya hadu iya haduwa ga shuke shuke ta ko ina.
2⃣3⃣
Manyan gidaje ne iya ganinka saboda unguwa ce ta masu hannu da shuni, kuma unguwar shiru take babu hayaniya gata tsit kamar babu mutane,

wani babban gida mai bene suka isa anan anty salma tayi hon cikin dan kankanin lokaci wani mai gadi yazo ya bude musu kofar gate din, kutsa kan motar tayi ciki taje tayi packing dinta a inda aka tanada, cikin gidan suka hara wanda yake katoton gaske gashi yasha ginin zamani sai kyalli yake, tana gama kuluwa na biye da ita a baya har cikin wawakeken wani falo wanda ya tsaru iya tsaruwa, kujera anty salma ta nuna mata tace zauna ina zuwa, nan kuluwa ta zauna in banda kalle kalle babu abinda take yi komai na falon bakone a wurin ta shiyasa ta tsaya take ta kallon fallon har anty salma ta fito ta kawo mata abinci ta bata.

Abincin ta fara afkawa har ta koshi sannan ta samu nutsuwa, kallonta anty salma tayi hawwa kin san Ummi? Girgiza kai tayi, Ummi yata ce ita ma ba zaki fita a haife ba, tare zaku zauna a gidan nan saboda dama ni ba anan nake da zama ba, zuwa nake yi lokaci lokaci, yanzu ki taso muje ku gaisa da kishiya ta kafin ummin tazo.
2⃣4⃣
Bin bayan anty salma tayi har zuwa wani hadadden sashe mai mutukar kyau da tsaruwa komai na ciki mai tsada ne,

wata farar mata kyakkyawa ta gani zaune a falo tana ganinsu ta fara fara'a da alama suna zaman lafiya da anty salman, zama kuluwa tayi ta gaida ta ta amsa fuska a sake kamar dama ta santa, maman ummi ga yar tawa wadda zasu zauna da ummi dan Allah idan anga tayi ba daidai ba a tsawatar mata, babu komai anty ai shi da na kowa ne, tashi anty salma tayi tace to zo mu tafi hawwa, binta kuluwa tayi suka fita daga bangaren Maman Ummi suka koma nata suna zuwa suka tarar da har Ummi ta dawo nan kuluwa ta saki baki tana kallon ummi wadda take yar gayu kamar yar India gata dai bata fita a haife ba amma ta iya tsara gayu, zaunar su anty salma tayi ta gabatar wa da kowacce  yar uwarta tare da dorawa ta hanyar cewa hawwa zan samo miki teacher wanda zai rinka yi miki lesson kafin ki fara zuwa makaranta murmushi kuluwa tayi nagode anty salma Allah ya saka da alkairi dama wlh ina son makaranta sosai, kiyi hakuri hawwa zaki yi kinji, to anty na gode. Kwana 2 da zuwan kuluwa ta dan goge tayi fes saboda yanzu bata aikin wahala komai yi musu ake yi sai dai kawai suci su sha su kwanta nan fa kuluwa ta fara hada kiba saboda samun jin dadin da take,

tuni anty salma ta nemo mata lesson teacher wanda zai rinka koyar da ita turanci da sauran subjects din da za tayi a makaranta, ita kuma ummi kullum tana zuwa school safe da yamma a halin yanzu tana ss2 zata shiga ss 3.
2⃣5⃣
  Lokaci ne yaci gaba da tafiya da dafarko kuluwa ta dan fuskanci matsala wajen koyon harshen turanci amma koda ta dage ta maida hankali dandanan ta fara fuskanta kan Ummi A'isha ta ankare tuni kuluwa ta zama baturiya domin ita da ummi yanzu basa hausa komai nasu da turanci suke yi, ganin haka yasa anty salma zuwa tayi mata registration a wata private school mai suna sharada standard boys and girls school, ss 2 suka bata saboda tayi girma ta wuce asata a junior section, sai dai ba makarantar su daya da Ummi ba kowa tasa daban ita ummi inda take zuwa da nisa ita kuma kuluwa babu nisa domin acikin unguwar ne.

Tuni kuluwa ta fara zuwa makaranta uniform dinta riga da skirt ne maroon da hijab fari head tied dinma fari ne tun farkon zuwan ta tasaba da mutane tayi kawaye saboda yadda take da farin jini sai dai kuma wani lokacin ta kan shiga damuwa na rashin babanta a kusa da ita. Yau ma kamar kullum bayan sun gama breakfast dinsu da ummi kuluwa ta tashi zata shiga wanka, kallon ta ummi tayi hawwa yau ba zaki school bane? Zanje mana wanka kawai zanyi saboda bana son naje ina tsami a rainani, um to sai kin fito ni kam na tafi, uniform ummi tasa ta dauki school bag dinta ta tafi ita kuma kuluwa wanka ta shiga ta silla ta fito ta shirya tasha turare tasa wankakken uniform dinta kuma gogagge ta sabi school bag tayi hanyar makaranta tasha safa fara da farin combos  ga school bag dinta baka,

daidai kwanar da zata sada ta da makarantar su ta hango wata bakar mota hadaddiya mai black din glasses kirar KIA Rio, in banda tashin sautin music babu abinda kake ji yana fita daga cikin motar kai kace speakers aka doddora ma motar, motar tana zuwa saitin kuluwa ta shiga cikin wani ruwa wanda ke kwance a tsakiyar hanyar ya hadu da jar kasa yayi jawur, fatsalllll ruwan ya fantsama ajikin kuluwa gaba daya farin hijabinta ya wanke da ruwan kwatar ita kanta fuskar ta sai da ruwan ya jikata, tsayawa kuluwa tayi tana son ganin wanda yayi mata wannan aikin, kamar motar ba zata tsaya ba sai kuma taja ta tsaya a sannu aka bude bangaren mai zaman banza wani dan kyakkyawan sauri ya fito, baiwar Allah kiyi hakuri wlh muna sauri ne ya fada yana kallonta, haba malam wannan wanne irin abune kawai kuna driving without...  Rufe kofar motar yayi ya tako inda take kiyi hakuri dan Allah tsaki kuluwa taja amma gaskiya ba kusan mutuncin dan adam ba domin kun cuceni sai da na gama shirina tsaf har na kusa zuwa school zaku batani da kwata? Hon mai karfi aka matsa daga cikin motar da alama wanda ke cikine ya gaji da jiran na wajen, hakuri yaketa bata amma kuluwa ta rufe idonta taci gaba da yaba masa magana, shi kuma na cikin motar sai hon yake,yayi hon sunfi talatin ganin na wajen yaki zuwa su tafi yasa shi bude kofar motar a fusace ya fito, hmmm ni dai ummi A'isha guy din yayi mugun tafiya da hankali na, dogo ne dan madaidaici fatarsa chocolate colour ce tamkar dan kasar Ethiopia yanada dogon hanci gashi da manyan idanuwa kamar kwai idonsa yake saboda round eyes gare shi, gashin girarsa kamar na mace dan sunada yawa, lebensa jajaye ne sosai ga dan madaidaicin bakinsa, yana da dan saje a fuskarsa,kumatunsa na dama kuma dauke yake da beautiful point, ya tara suma him akansa kamar wanda za a kitsa, kunnensa guda daya yasaka earring fari, haka wuyansa ma yasa sarka fara yar sirirya, yana sanye da bakar riga mai gajeren hannu da shorts trouser iya gwiwar sa,

kamar wani wanda yaga kashi ya fara magana kamar me yin rada, bobo meye haka? Kazo mu tafi kawai kana bata min lokaci, wanda aka kira da suna bobo ne ya kalle shi sorry baka ga abinda muka yi bane? And so what? Me zaka yi mata? Zaka wanke mata ne ko kuwa? Ya fada yana yiwa kuluwa kallon banza,ganin haka yasa kuluwa fashewa da kuka, wlh ban yafe muku ba mamugunta kawai yanzu idan naje makaranta a haka dukana za ayi a wurin assembly sai dai na koma gida, kiyi hakuri yanmata bobo ya fada ba wani hakuri da zanyi wlh ban yafe muku ba,

shi dai classic guy dinnan na jikin motar tsayawa yayi kawai yana kallon ta wannan wacce irin shagwababbiyar yarinya ce? Dan kuka bashi da wuya kawai daga haka sai kuka? Maganar bobo ce ta katse shi JUNIOR ka bata hakuri tunda kaine ka bata ta, wannan ne kuma bata isa ba junior ya fada yana komawa cikin motarsa.
2⃣6⃣
  Kara rushewa da kuka kuluwa tayi tace wlhi sai Allah ya saka min mugaye kawai, sake fitowa daga cikin motar junior yayi yace kai bobo wlhi idan ba ka bar wannan village girl din ba zan iya tafiya na barka ka tsaya sai wasting din time dina kake a banza, tahowa bobo yayi yana cewa double sorry my friend, juyawa kuluwa tayi ta kama hanyar komawa tana tafe tana kuka sai kace wata karamar yarinya, bobo yana shiga motar Junior ya fusge ta aguje kamar zai tashi sama yana driving yana bin wakar omalele, dan kallonsa bobo yayi yarinyar nan ta bani tausayi fa, sai kayi kuma junior yafada lokacin da yake kara gudun motar,kai tsaye unguwar jan bulo kubuga suka shiga dai dai first gate suka karasa wani hamshakin gida ginin dutse da dutse gida ne tangameme kuma katoton gaske very massive, tun daga kofar gidan ga wasu mopol nan da sojoji zaune suna ganin mai shiga da mai fita, kan motar junior ya kutsa cikin gidan,yana shiga yaje yayi packing dinta acikin jerin gwanon yan uwanta, ya fito shima bobo fitowa yayi yana cewa ya bahbah na jira ka ne ko naje kawai? Jeka kawai bobo i will call you letter, ok sai na jika, cikin mai falon gidan junior ya wuce yana tafe yana fito gamida wakar oh my Darling i love you! Da wannan wakar ya karasa cikin falon wanda yake unguwa guda mai karatu duk abinda ka sani na jin dadin rayuwa to an tanade shi acikin wannan falon,

mom dinshi ya hango zaune tana waya da wata fankaceciyar wayar ta tasha ado kamar bata manyanta ba, wani dandatsetsen leshi ruwan kwai tasa a jikin ta takafa dauri kunnenta da wuyanta yasha gold mai girman gaske ga zobuna data zubawa yan yatsunta da takalmi hill a kafarta golden colour, inda take ya karasa yana zuwa ya zauna kusa da ita gamida dora kansa akan cinyar ta, kansa ta fara shafawa kamar wani karamin yaro,muryar ta naji tana cewa hajiya yabi ki siyo min setin gold dan saudia guda daya amma ki hado da komai nasa ajiki ina nufin tun daga kan dan kunnensa, zobensa, awarwaron sa da sarkarsa amma bana son mai araha kuma dan Allah ki zabo na yanmata saboda wata girlfriend din junior ce za tayi birthday shine zai bata a matsayin gift, ok sai kin dawo, daidai lokacin ta kashe wayar ta ajiye ta akusa da ita ta fara lailaya sumar kan junior, junior whats happen? Nothing mom, ok har ka dawo daga wurin exercise din?

Mom na dawo amma zan kara yin wani now now yana gama fadin haka ya tashi ya nufi wani injin motsa jiki wanda ke girke acikin falon, hawa yayi ya fara motsa jikinsa har na tsawon mintuna 20 mom dinshi tana zaune tana kallonsa har ya gama.
2⃣7⃣
   Sai da ya gama ya sauko daga kan gym din kai tsaye dakinsa ya wuce, junior ba kayi breakfast ba fa, zanyi mom kin san ban iya yin break da sassafe sai nan da 11 yanzu bacci nake ji saboda am too tired,to je ka huta maza aje ayi bacci, murmushi yayi ya shige dakinsa wanda yake kayace da kayan alatun more rayuwa, toilet ya fara shiga yayi wanka ya fito yazo ya kunna ac din dakin ya fada kan tafkeken gadonsa wanda ya isa mutum 15 su kwanta ba tare da takura ba domin gadon royal bed ne dan gaske, remote ya dauka ya kamo tashar wakokin turanci a tauraron dan adam ta cikin jibgegiyar plasma tv din dake kafe a bangon dakin nasa, kallo ya fara yi sama sama na wakokin da ake sakawa marassa kyan gani domin wata wakar ma mata ne tsirara suke rawa, yana cikin kallonne bacci ya dauke shi nan ya bararraje ya fara sharar baccinsa.

Ya dan jima yana bacci kafin ya tashi ya shiga toilet yayi brush ya fito, falo ya nufa yana zuwa yaga mom dinsa zaune ita da jawaheer  da gudu jawaheer ta taso tayi hugging dinsa tana sanye da riga da skirt matsattsu, rungume ta yayi tareda bata kiss a kumatu hy jawa yakike? Yaushe kika zo? Naje ai na ganka kana bacci, oh yeah ya fada tareda sakalo hannunta cikin nasa ya nufi wurin mom wadda ke zaune tana kallon su sai faman murmushi take, hannun jawa cikin na junior suka zauna kan kujera,bani labarin boyfriend dinki, ya sunanshi, kafadar sa ta dan doka, kasan ni ai ban fara soyayya ba amma kai bani labarin girlfriend dinka, ni? Ni ban da budurwa amma ina da girlfriends da yawa more than 100, dariya jawa tayi tace ai nasanka da farin jinin yanmata sai alokacin mom tayi magana ai junior kam girlfriends domin akwai ma wadda zata yi birthday next week kinga har gida tazo tayi inviting dinsa, dariya jawa ta fara wa yaga na mamajo, duka junior ya kai mata ta rike hannunsa ni dai ummi A'isha yau mamaki ya gama cika ni, kallon junior mom tayi junior baka yi breakfast bafa, mom ki barshi kawai na yi lunch anjima, what? Baka isa ba junior yanzu zan yi maka dura kamar yadda muka saba, wai mom har yanzu junior bai cin abinci sai kin dura masa? Ai haka yake jawa har yanzu, maza dauko min flask din farfesun nan na dura masa da sauri jawa ta mike zata tashi Junior ya jawota ta fado jikinsa, riketa yayi wlh babu inda zaki je yarinya. 
2⃣8⃣ 
~~~ Mom da kanta taje ta dauko abincin tazo inda yake ta tashi jawa ita kuma ta zauna ai tuni Junior ya bata fuska sai kace wani karamin yaro dan yaye mom ki barni Allah anjima zan ci da yawa, a'a my boy ka daure ka danci ko babu yawa kaji, pls junior yawwa maza bude bakin, naman ta yanko wanda yaji tumatur da albasa da tafarnuwa dakyar junior ya bude dan karamin bakinsa mom ta saka masa naman amma yana hadiyewa yaji zuciyarsa na tashi saboda shi baya son garlic kwata kwata, jin cikinsa yayi ya fara murdawa abunku da shagwababbe tuni ya fara langwabewa mom barshi haka my stomach... Mom karki kara min pls, cikin rudu mom ta kalleshi junior menene? Mom cikina ciwo yake duk yadda aka yi ansa garlic ni kuma bana sonta, a fusace mom ta danna inter come kamar zata tsaga gidan dan kara, aguje ma'aikatan gidan suka shigo cikin tsawa tace ina kukun da yayi girkin nan? Da sauri wani mai green din Kaya yace hajiya bata nan taje gida ta dawo, to yana dawowa ku turo min shi, juyowa tayi ga junior ta rikeshi ta kwantar dashi a jikinta tafara shafa bayansa tana jijjiga shi kamar wani yaron goye, sannu Junior jawa ta fada tare da matsowa kusa dashi, kamo hannun jawa yayi yace zaki iya yin driving ki kai mu country mall? Zan iya mana me zaka yi acan? Zanje ne naci abinci na siyo wasu abubuwan da nake bukata, ok tashi muje, to kije dakina ki dauko key din motar mana suna nan akan bedside drawer dina duk wadda yayi miki ki dauko, tashi jawa tayi ta nufi bedroom dinsa ita kuma mom taci gaba da yi masa sannu tana cewa junior zaka iya zuwa kuwa? Ko dai na aika a siyo maka, mom zan iya zuwa ai cikin nawa ya daina ciwon zanje ne kawai na siyo shawarma da dan fish gasasshe, to junior sai kun dawo, tashi yayi lokacin da jawa ta fito suka fita tare yana rike da hannunta domin shi junior ba wani abu bane ya rike hannun mace ko ya rungume ta harma yayi mata kiss duk wannan is nothing a wurinshi dan har ya saba duk lokacin da ya hadu da friends dinshi mata to hugging da kissing din gaisuwar su, suna fita wayar mom ta fara kara, a hankali ta daga tana cewa hello dadyn junior, yes maman junior ya kuke? Lfy lau, ina junior?
Junior yanzu ya fita zaije country mall shida jawa,
Yaci abinci kuwa?
Wlh dad junior yau baici komai ba,
Haba maman junior why ke ba zaki bashi ba tunda kin san shi ba ci zai yi ba,
Am sorry dad junior wlh na fara bashi sai cikinsa ya kama ciwo ashe abincin akwai garlic aciki shi kuma kasan ba ya sonta,
What? Yanzu yana ina?
Yaji relief har ya fita cin shawarma
Ok wanne kukun ne ya dafa abincin? Ki tabbatar kin sallame shi yabar gidan kafin na dawo,
To shikenan sai ka dawo, katse wayar yayi ya ajiyeta cikin fushi domin a duniya ya tsani abinda zai taba lafiyar junior, zai iya yi masa komai a SANADIN GATAN da yake nuna masa. 
2⃣9⃣
Su junior suna fita county mall suka nufa shi da jawa, ga wani kida da yake tashi tamkar a cinema ko kuma wurin wani kwarya kwaryar party suna tafe suna bin wakar har suka karasa, parking din motar jawa tayi tareda fitowa, hannun junior ta kama suka shiga ciki mutane sai binsu da ido suke duk inda suka wulga idone kawai yake binsu sai dai da yawa daga cikin mutanen wurin kama tun daga ma'aikatan su har masu siyayyar ba suyi mamaki ba kasancewar sun San ko waye junior, kallonsa jawa tayi junior what's all this eyes for? What's the meaning of this all looking?? Gaskiya yan garin nan naku akwai gyara har yanzu baku waye ba you are still villagers wlh, dan murmushi junior yayi, that's why I hate 9ja komai nasu abun kallo ne, yanzu dan na rikeki meye abin kallo?? Tsaki jawa tayi forget about them kawai, zagayawa suka ci gaba dayi har suka tsini abinda suke so suka koma wurin shan ice cream.
     *************
A bangaren kuluwa kuwa tana komawa gida ta kwanta taci gaba da kuka, kullum dama tana kewar mahaifin ta, amma yau sai taji tafi tunashi musamman wannan wulakancin da gayen dazun yayi mata, kuka tayi sosai sannan taji zuciyar ta ta dan nutsu yanzu ta danjita ta dama dama, to amma shi wannan guy din waye shi?? Dan gidan waye?? Hakan halinshi ne ko ita kadai yayiwa?? Dan rainin wayo,tsaki tayi tareda yin juyi, Allah sarki babana yanzu ko wanne hali yake ciki gameda masifar iyatu? Allah sarki kauyen mu, ko ina mairo da shamsu? Kila yanzu shamsu yayi sabuwar budurwa but still i love him,

da wadannan maganganun bacci ya saceta ba ita ta tashi ba har sai da Ummi ta dawo daga makaranta ta sameta tana bacci gashi wurin 2 ko salla bata yi ba, tashinta ummi ta fara, wake up jidda, zumbur ta tashi tana kallon ummi, har kin dawo ummi? Ni yau wani banzan gaye ne yayi min sanadin zuwa sch wlhi, shiyasa duk naji na tsaneshi tun lokacin dana fara ganinshi, zaro ido Ummi tayi hmm jidda ba ason a zurfafa a kiyayya kuma ba ason a zurfafa a soyayya domin duk wanda kaji ka tsana to at the end shi zakaji kana tsananin so, God forbid kuluwa ta fada lokacin da take sauka daga kan gadonsu, to shikenan tunda ba zaki yarda da abinda na fada miki ba, toilet kuluwa ta shige ba tareda tace komai ba

3⃣0⃣
    Zama su junior suka yi shida jawa suna shan ice cream har suka koshi sannan suka tashi suka dauko hanyar dawowa gida amma duk da haka kamar tv haka mutane ke rakasu da ido saboda abun nasu sam babu tsari, shi junior daga shi sai wando iya gwiwa da wata body hug dinshi ga sarka a wuyansa,kunnensa na hagu kuma da dan kunne sannan ga wata suma kaya guda ita kuma jawa tasha wata atamfa super mai tsadar amma kuma dinkin fited gown ne wanda ya matsata tsam sannan ga wani dan ziririn mayafinta data dan yafa a iya kanta amma dashi da babu duk daya, hannun junior ta rike suna tafe suna hira tana dan kai masa duka ko kuma shi ya daki kafadar ta da haka suka karasa inda suka ajiye motarsu suka shiga suka fita suka nufi Gida, lokacin da suka isa gida mom bata cikin falon tana dakinta ta sake wanka da shiri cikin wani kyakkyawan leshi, kai tsaye dakinta junior ya shiga yana zuwa ya zauna ajikinta mom wai sai yaushe dad zai dawo?? Sorry junior ya kusa dawowa nan da gobe zai dawo kaji, gashin kansa ta shafa junior kaci shawarman? Mom naci amma yanzu zanje na dan buga kwallo afilin wasa na, tashi yayi kamar an tsikareshi ya nufi dakinsa jawa tana biye dashi kamar jela, yana shiga ya fara cire kayansa jawa tana tsaye tana jiransa babu ruwanshi da wai jawa tana tsaye tana kallonsa kawai wurin saka wandon ball dinshi ne yaji dan kunya yace jawa close you eyes pls, kaima ka cika problem tafada tareda fita daga dakin, wasu fararen kaya yasa wadanda suke gasu nan lodi lodi sababbi fil, riga da wando da abun hannu da wani dan faffadan hankicif wanda yake daurawa akansa, farin combos yasa da safa fara ya fito a bayan rigar tasa an rubuta junior da manyan baki, number rigar number 1 tun daga nan ummi A'isha ta gane junior dan kwallo ne naji da gani, kansa tsaye ya nufi tsakar gidansu acan ya nufi wani babban fili wanda aka tanadi wurin buga kwallo kala kala kama tun daga, handball, volleyball, football, table tennis, racket ball, basketball da sauransu, wasa ya fara bugawa shi kadai, handball ya fara daga bisani ya fara buga football har bobo abokinsa yazo ya sameshi suka ci gaba da bugawa tare. Washe gari da safe junior yana kwance yana bacci da misalin karfe 11 yaji alamun yar hayaniya agidan, ba dan yaso ba yatashi ya shiga toilet ya fito, kai bari anjima nayi sallar kawai ya fada acikin zuciyarsa tareda fita, dad dinsa ne ya dawo dan haka part din dad din ya nufa yana zuwa ya shiga dakinsa, suna tsaye shida mom tana cire masa babbar rigar sa, welcome dad, yawwa junior, zuwa yayi ya rungume dad din nasa, dad i miss you yafada cikeda shagwaba, kayi hakuri junior, dan murmushi junior yayi dad tunda kadawo ina son zanje abuja yau saboda tun jimawa akwai wata girlfriend dina da na jima ina yimata alqawari cewar zanje nayi mata weekend amma ban samu naje ba, no problem my boy ai sai kaje babu damuwa, dad ya fada cikeda rashin damuwa, dariya mom tayi kuma how many days zakayi junior?? Mom ranar Sunday zan dawo saboda ranar Tuesday zanje kd birthday din teemah, ok to amma junior banda sakaci da cin abinci pls, mom ta fada tana murmushi, dan murmushi junior yayi zan kula mom, juyawa yayi yafita ya koma part din mom yaje ya hau kan gym ya fara motsa jikinsa saboda shi dan ball ne koda yaushe cikin motsa jikinsa yake, sai da ya dan jima sannan yashiga dakinsa yayi wanka yafito ya dauki wata jar t shirt mai gajeren hannu yasa, ya dauki black din trouser ya sa, ya taje sumar kansa ya dauki chain yasa ya makalawa kunnensa earring,wani hadadden agogo samfarin bc yadauka ya daura a hannunsa sannan yaja wani takalmi mai mutukar kyau ja yasa a kafarsa.

3⃣1⃣
Turaren imfact ya fesa ya fito hannunsa rikeda wayoyi manya guda hudu, daya wayar ya kara a kunnensa ya fara magana, hello bobo zo mutafi mana nifa na shirya, ok kana gidan? Ok, fita yayi ya nufi wurin bobo wanda ke zaman jiransa acikin gidan. Karfe 2 suka isa abuja kai tsaye unguwar mai tama suka nufa gidansu Lana girlfriend dinsa wadda ita ba musulma bace kuma iyayenta ma Christian ne sannan itama babanta mai kudine gata da kyau kamar ita tayi kanta, lokacin da su junior suka shiga gidan da gudu Lana tazo ta rungume junior ta fara kissing dinsa, riketa sosai junior yayi yana mai wani dan malalacin murmushi, Lana yakike ya fada yana kanne mata ido daya, hannunsa taja zo muje ciki junior, har cikin falon gidansu ta kaisu anan aka cikasu da cima iri iri harda su burkutu sai dai shi junior baya sha, abincin ma sama sama yaci, hannunsa Lana ta kama zuwa wani shiryayyen daki wanda ya tsaru iya tsaruwa, zauna ka huta junior nasan ka gaji, lumshe idonsa yayi ya zube akan gadon yes of course am tired Lana, zama tayi akusa dashi nasani ai saboda nasan halinka junior, sai dai har yanzu baka sauya ba daga tsautsauran ra'ayinka?? Haba junior kaifa big guy ne you are rich,young, handsome, famous,popularly and adorable guy, ka tsaya ka mori kuruciyar ka, agaskiya am very astonished da naji wai baka making love da kowacce mace, kallonta junior yayi tana sanye da wata yar karamar bakar rigarta iya cinya ko hannu rigar bata dashi, hannunsa yasa ya jawota jikinsa, Lana you are very beautiful and attractive, kamar jira Lana take ta fara shafashi, rigar jikinta ta zame da sauri junior ya rufe idonsa, pls Lana stop it, stop it Lana, don't remove it, Lana ba tareda ta saurareshi ba ta cire rigar ta cillarta can gefe ta makalkale junior,nan ta fara sarrafa shi kasancewar ta ba sabin shiga bace, amma shi junior sabin shigane don duk rashin jinsa da iskancinsa baya neman mata barshi dai da rungumarsu da kiss da rike hannunsu amma baya nemansu sai dai su ne suke nemansa, sai ko yan syrup da yake dan kurbawa saboda tsaro shi dinma ba koda yaushe ba sai dai in yaji ransa ya baci, kafin ya ankara har Lana ta gama tubeshi, tuni tafara nuna masa zulamarta a fili, abunku da sharrin shaidan nan junior yaji ya nemi tunaninsa ya rasa haka ya biyewa Lana suka aikata tabargazar su iya son ransu har na tsawon lukuta masu yawa,

    Kumatunsa Lana ta shafa, junior kace baka iya ba, gashi kuma you make me soo happy, murmushi junior yayi batare da yace mata komai ba, Lana gobe zan koma gida saboda akwai wani wasa da zan buga, cikeda damuwa Lana tace shikenan babu damuwa ni duk lokacin dana bukaceka zan zo, ko parents dinka zasu yi fada?? No, Lana mufa wayayyu ne hakama parent dina basuda matsala, wai dan kin kawo min ziyara ai is nothing, dadi Lana taji saboda dama ta dade tana muradin kasancewar ta da junior.

  Wayewar garin junior yabar abuja shida bobo suka dawo kano, aranar da suka dawo ya taradda dad dinsa ya siyo masa babban doki, nan fa junior ya hau dokin ya fara zaga unguwa, kowanne lungu na unguwar sai da yabi, bobo na biye dashi acikin mota ya kure sauti, haka suka wuni suna abu daya duk sun addabi mutane da tseren doki da mota, ga kidan da yaki karewa.

3⃣2⃣
   Sai da yamma lis tayi sannan junior ya iya hakura ya koma gida yaje ya daure dokinsa daga nan direct dakinsa ya wuce yaje ya fada akan makeken gadonsa, ko takalmin kafarsa bai cire ba haka ya kwanta ya fara bacci. Mom ce ta nufo dakin domin dubashi tana shiga ta ganshi kwance yana bacci inda yake kwance ta karasa ta cire masa takalman dake kafarsa taja blanket ta rufe shi ta juya ta fita tana murmushi domin babu abinda take so irin taga junior cikin farin ciki da nishadi, tana zuwa falo taci karo da kawarta hajiya yabi, barka da zuwa mutanen jidda, mom ta fada tana murmushi, yawwa barkanki dai hajiya Fati, wuri suka samu suka zazzauna, momyn junior ga sakon naki ya iso sarkar da na siyo miki agaskiya mai tsada ce kuma ba ta kananan mutane bace, karbar sarkar mom tayi ta fara duddubata yar siririya amma da gani mai tsada ce, yawwa hajiya yabi dadina dake kin iya zabe, dama junior ne zai bawa wata girlfriend dinshi a matsayin gift saboda zata yi birthday ne next week, mom ta fada cikeda farin ciki, kallonta hajiya yabi ta danyi, ni kuwa hajiya fati sai nake ganin kamar abinda kike yi kuskure ne saboda su yara tasu kyau take bata karko domin duk yadda ka dorasu haka suke tashi, shi junior yanzu bai san rayuwa ba saboda baku koyar dashi ba, abin takaici ne ace wai kina goya masa baya akan yayi abota da wata ya mace wadda baki san ko wacece ba alhalin shi kuma yana baligi, hajiya Fati bafa ya mace bace kadai ke dauko abin magana ba wlh da namiji ma yana daukowa kuma ya kamata ki rinka bincikar abokansa saboda bada kowa zaki barshi yayi abota tunda har yanzu junior yarone karami bana tunanin ya wuce 27, take fuskar mom ta sauya bacin rai karara ya bayyana akan fuskar ta, hajiya yabi dama abinda ya kawoki kenan? Kinzo ne kici min fuska ki zage dana tatas? Daidai lokacin junior ya fito daga daki daga shi sai dan karamin blue din wando da rigarsa yar karama irin na yan ball, tsayawa yayi ba tareda ya kalli ko inda hajiya yabi take ba yace mom wai dan Allah wacce talkative din kika samune haka? Haba wannan matar ta cika surutu tun ina bacci take damuna har sai da ta tasheni, gaskiya ni ban son irin wannan mom, adaina tashina da surutu, cikin kwantar da hankali mom tace yi hakuri yarona, koma ka sake kwanciya kaji, mom ai kun riga da kun tasheni kawai, ni yanzu filin ball zanje.

   Yana gama fadin haka ya juya ya fita yana hararar hajiya yabi saboda duk maganganun data fada acikin kunnensa ne, duk ya jisu, yana fita mom tace hajiya yabi naji maganarki kuma nagode amma dan Allah idan babu damuwa daga yau kar ki kara zuwa gidana, yanzu bari na kawo miki kudin sarkarki, rike baki hajiya yabi tayi hajiya fati daga fadar gaskiya? Allah ya huci zuciyarki,ba tareda mom tace komai ba ta mike ta nufi dakinta mintuna kadan sai gata rikeda kudi rafa rafa sababbi fil, mikawa hajiya yabi tayi, gashi hajiya nagode, tashi hajiya yabi tayi shikenan hajiya fati ubangiji Allah ya sada mu da alkairi, amin mom ta fada lokacin da take barin falon

3⃣3⃣
    Junior yana fita ya dauki bicycle dinsa ja domin dama wani lokacin akan keke yake yawo, filin kwallon unguwarsu bobo ya nufa wato sharada, yana tafe yana jin kidan da ya kure acikin wayarsa ya cuccusa earphone acikin kunnensa, daf da wata kwana ya hango kuluwa, kunu yasha itama tana hangoshi tasha kunu ta bata rai, wucewa yayi ba tareda ya kalletaba, itama bata kalleshi ba ta wuce dama lokacin islamiyya zataje Kuma ita kadai take zuwa domin ummi ita tayi sauka tuntuni, filin kwallon kusa da gidansu bobo junior ya karasa yana zuwa aka fara ihu, saboda ganinsa, sauka yayi daga keken ya shiga filin wasan, take aka fara wasa mai zafi sai daf da magrib sannan suka bar ball din shi kuwa dama junior salla ba wani damunsa tayi ba saboda bai ma cika yinta ba, mota bobo ya dauka yake biye dashi shikuma yana kan keke yana kuma buga kwallo da kafarsa, dai dai kwanar dazu da yaga kuluwa yanzu ma nan ya ganota, da saninsa ya daki ball din da karfi taje ta doki keyar kuluwa da sauri ta juyo, ganin junior ya sata daure fuska, bobo ne ya bude motarsa ya fito, yauma an samu akasi matar junior, da sauri junior ya kalleshi what? God forbid me zanyi da bakar fata, wata harara kuluwa ta aika masa sannan tace ai ko Senior ne bashida wannan matsayin balle wani Junior, God forbid me zanyi da jan lebe? Tsaki junior yaja dalla bobo muje kar kasa wannan village girl din ta bata min rai a banza, gaka nan dan kauye tafada tana murguda baki.

    Kallo junior ya bita dashi, kiyi hakuri matar junior bobo ya fada yana dariya, kallonsa bobo yayi Allah kiyaye na auri yar kauye, ni ma babu abinda zanyi dakai, kudai yi hakuri domin ba asan inda rana zata fadi ba, a yamma saboda acan ta saba faduwa kuluwa ta fada tareda daukar hanyar gida, tana zuwa gida ta fara bawa ummi labari, ummi ina dan rainin hankalin nan na rannan dana fada miki? To yauma mun sake haduwa munyi fada, dariya ummi tayi your fighting partner?? Mijinki zaki cemin ai sai nafi ganewa, sai kiyi kuma, nama fasa baki labarin, kuluwa ta fada tana hararar ummi.

   Shi kam junior kekensa ya murza ya tafi ba tareda ya cewa bobo komai ba yana tafe yana jin wakar p square if do me i do you man......! Bobo kuma yana binsa har suka karasa gidansu junior anan suka rabuda bobo shi ya shiga gida bobo kuma ya juya.

3⃣4⃣
Junior yana shiga cikin gidan ya wuce falon mom Wanda yake tafkeken gaske, kan dining ya hau ya fara kokarin duba abinda zai ci, shinkafa ya diba yar kadan wanda ba zata fi cokali biyar ba ya fara ci ahankali, fuskar kuluwa ya hango lokacin da take musu masifa shida bobo "yi hakuri matar junior" maganar da bobo ya fada ta dawo masa cikin kunnensa," ni me zanyi da jan lebe" amsar da ta bawa bobo itace ta sake dawo masa, murmushi yayi shi kadai lallai wannan yarinyar itama tana ji da kanta, fitowar mom ce ta katse masa tunaninsa, junior whats it? Naga kanata murmushi kai Kadai, babu komai mom amma dai kawai yau babu abinda ke damuna shiyasa naji inata annashuwa, murmushi mom tayi to ga sarkar nan can an kawo maka wadda zaka bawa teemah gift din birthday dinta, tnx mom amma matar nan ta dazu ta bata min rai, meyasa mutane suke da munafurci ne mom? Nifa abinda ake min a garin nan ya fara damuna, wlhi matar nan ta dazu taci darajarki mom da sai na zageta, kayi hakuri junior, mutane sun sako min kai a gaba, na rasa me ka tare musu, tsaki junior ya danyi tareda tashi ya nufi dakinsa yana zuwa ya haye gadonsa ya dauki remote ya kamo tashar music ya fara kalla.

   Koda dare yayi kuluwa bata iya runtsawa ba, tunanin junior kawai take yi, kuma shi take ta hangowa a idonta, zaune ta tashi tabi ummi da kallo wadda ke ta sharar baccinta, junior dinnan fa daga gani ba shiryayye bane kuma ba nagari bane saboda yadda yake sa sarka da dan kunne kai idan ba sani ma kayi ba bazaka taba tsammanin musulmi bane saboda yadda  yake dabi'unsa da halayyar sa, kuma da gani bayaji sannan kuma gagararre ne, to ni yanzu meye nawa na tunaninsa? Ta fada acikin ranta, komawa tayi ta kwanta duk kuwa da cewar ba iya baccin zatayi ba, babu shakka junior ya hadu iya haduwa to amma anya zai so mace kamata wadda ta fito daga kauye?? Tambayar da tayi ta yiwa kanta kenan amma kuma bata da amsa.

  Abangaren junior shima hakan take domin koda ya kwanta domin yin bacci kasawa yayi, tunanin kuluwa ne ya addabi ruhinsa, hakika yasan ya kamu da sonta to amma taya zai furta mata? Shifa yanmata hadaddu ma sune ke cewa suna sonsa ba shine yake cewa yana sonsu ba, ruf da ciki ya juya yayi, yafara shafa keyarsa, tab wannan shine gamo ya fada ahankali, daren ranar da kyar ya samu bacci ya dauke shi,washe gari kuwa sai da yakai 11 akwance yana ta bacci, bayan ya tashi ne yayi wanka ya shirya cikin bakin boxer da jar t shirt mai hoton yan yatsu ajiki, tulin sumarsa ya fara tajewa da cumb bayan ya makala dan karamin dan kunnensa ajikin kunnensa na hagu sannan yasa katuwar sarkarsa wadda tsayinta yazo har kan kirjinsa, cumb din ya dauka ya nufi falo yana tafe yana taje sumarsa yana wakar if u see this baby o.oh she was chop my money, because i don't care, don't care, falon dad dinsa ya nufa yana mai ci gaba da tajar sumarsa, afalo ya tarar dasu dad and mom dinsa suna kan dining suna yin breakfast, good morning dad, mom good morning ya fada lokacin da yake Jan kujerar da zai zauna, morning junior, dad ya fada yana dafa kafadar junior tareda dan murmushi, har an tashi?? Dad na tashi dakyar saboda ina son naje na koyawa dokina tsere, bana son na barshi haka, yana da kyau ai hakan, dad ya fada, junior me zaka ci? Mom ta tambaye shi, mom ki barni yanzu babu abinda zan iya ci saboda koko kawai nake son sha, koko junior?? To ni yanzu ina zan samo maka koko junior?? Mom ki barshi bari naje na dawo, tashi yayi yafita zuwa inda dokinsa yake a daure, kunce shi yayi ya hau ya fito daga cikin gidan, yana fitowa yaci karo da bobo, nan bobo yabi shi a baya sukayi bayan layi, tseren mota da doki suka fara take suka hargitsa unguwar da hayaniya dan suna farawa yara suka taru suka cika da samari suna kallo, wasu yaran ma uniform ne ajikinsu suka ki tafiya makarantar suka tsaya kallo,ganin haka yasa malam ladan wato babban ladanin masallacin unguwar yazo wurin, tunda yaga su junior ne ke yin wasan yaji jikinsa yayi sanyi amma duk da haka dai sai da yayi musu magana, kallon hadarin kaji junior yayi masa kafin yace, malam ladan ai lokacin raba zakkar bai yi ba bare kazo min ko? Haba junior yanzu abinda kake yi a unguwar nan ya kamata? Kai Malam ladan wlhi ba don darajar tsufa ba da sai na zageka, junior ya fada yana masa kallon uku saura kwata, juyawa malam ladan yayi ya nufi gidansu junior domin sanar da mahaifansa, yana tafiya junior ya kalli bobo yace, bobo nifa koko nake sha'awa, wanne irin koko? Koko dai da kasani amma ba wanda ake damawa ba, to wanne irin koko? Kai banza ne wlhi baka ganewa, koko damun Allah, oh to ai yanzu na gane, to ba gobe zamu tafi kd wurin teemah ba ai sai ka sha acan, dan murmushi junior yayi hakane fa kuma kasan teemah big girl ce wlh, amma bari gobe tayi.

3⃣5⃣
  Malam ladan na zuwa gidansu junior ya sanarwa da jami'an tsaron ko shi wanene dan haka basu hanashi shiga ba suka bashi hanya ya wuce, har falon saukar baki aka kaishi, nan ya zauna ya jira har dad ya fito, bayan sun gaisa ne malam ladan ya fara magana kamar haka" Alhaji dama ba wani abune yake tafe dani ba illa wani abu da yake faruwa a unguwar nan game da junior, wani abun yayi? Abba ya tambaya, eh to agaskiya dabi'un junior duk ba masu kyau bane, kullum cika unguwar nan yake da kide kide da wake wake, sannan kuma ga tseren mota da na doki da yanzu yake yi mana acikin unguwar nan saboda ya raina kowa babu wanda zai yi masa magana yaji, dan haka Alhaji a kula da yadda junior yake gudanar da rayuwar sa domin acikin hadisi ingantacce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace kowannen mu mai kiwo ne kuma za a tambaye shi akan kiwon da aka bashi, shugaba mai kiwone, magidanci mai kiwo ne zai yi bayanin yadda ya gudanar da dukkanin harkar iyalansa da tarbiyar yayansa, wannan ya hadar da yadda ya ciyar dasu ya tufatar dasu, yadda ya sauke nauyin dake kansa nasu, irin tarbiyar da ya basu da kulawar da ya basu, Alhaji sufa "ya"ya amana ce kuma wlhi kowa sai yayiwa Allah bayanin yadda ya tafiyar da tasa amanar wacce Allah ya bashi, yana da kyau iyaye su kula da tarbiyar "yayansu, su kula da irin abokan da yaransu ke abota dasu domin shi aboki yana taka muhimmiyar rawa awurin gurbata rayuwar yara saboda aboki yana da wani tasiri na musamman" tunda malam ladan ya fara bayanansa dad jinsa kawai yake domin shi a duniya ya tsani azo ace masa ga laifin junior,malam ladan nagode da wannan bayanin naka kuma daga yau kar ka kuskura ka kara shigo min gidana, tunda duk kokarin da nake muku bakwa gani, Allah ya baka hakuri Alhaji amma ni aganina gyara kayanka ba ya taba zama sauke mu raba, kuma malam bahaushe yace ka so naka duniya taki shi ka ki shi duniya ta soshi, will you get out from here ko sai na kirawo securities sun fitar dakai? Dad ya fada cikin tsawa, jiki yana rawa malam ladan ya juya ya tafi.

   Cikin Gida dad ya koma yana faman fada haba jama'a wai junior me ya tarewa mutane ne, kowa a unguwar nan idan ya budi baki junior zai ce kowa junior sai kace shi kadai ne d'a to agaskiya nagaji daga yau duk wanda ya kara kawo min maganar junior sai na daureshi, daidai lokacin mom ta fito dadyn junior what's wrong?? Wannan mutumin ne wai wai malam ladan yazo min da wata magana wai junior bashida da'a bashida halayya mai kyau, ni narasa me yasa junior mutane suka sa masa ido, ka kyalesu dadyn junior babu abinda zai faru da danmu duk bakin cikinsu, kama daina kulawa dasu. Ba ajima ba sai ga junior ya shigo, kallonsa dad yayi junior daga yau duk wanda ya kara tarar ka da wata magana ka zazzage shi komai girmansa ni nasaka, dad ai ni ina dawowa ma daga bufday din teemah zan bar kasar zan koma sch saboda nagaji da yan sa idon nan, gara ma ka tafi yafi sauki, mom ta fada tana kallonsu.

   Washe gari da safe su junior suka tafi Kaduna birthday din teemah, awani shahararren hotel Kings palace aka shirya birthday din wanda manyan yarane kawai suka halatta, yanmata gasu nan burjik cikin shiga ta alfarma riga da wando ko riga da skirt wasu kuma doguwar riga, shi kam junior sanye yake cikin wata t shirt black & yellow mai tsada ga wata top da ya dora asama, black din trouser yasa, ga dan kunne ga sarka, yasha face baki sai shan kamshi yake, bobo yana kusa dashi, bayan an zazzauna ne sai ga teemah wadda ta sha kwalliya cikin wata hadaddiyar gown ja mai hannu daya, daga saitin cibiyarta an dan yanke wurin Wanda kana iya hango cibiyar ta, haka ta gaba an tsaga rigar duk cinyarta awaje take, ga kanta babu ko dankwali sai wani gashinta ta yankoshi ta gaba, tana shigowa aka saka tafi tareda sakin kida, kanta tsaye ta wuce kujerar da junior yake zaune ta kamo hannunsa ya taso suka fito tsakiyar fili, tuni aka sakar musu kidan oya shake body.

3⃣6⃣
     Kowa acikin hall din sai da su junior suka burgeshi especially ma shi junior ya tafi da hankalin yanmata da yawa saboda ya hadu iya haduwa, yayi tako ina kyawunsa ya bayyana afili, sai da suka dan chashe sannan aka je wurin yanka cake, hannun teemah junior ya kama suka yanka cake din ya saka mata a baki, yankowa itama tayi ta mika masa, cikeda yanga ya dan bude bakinsa tasa masa, nan aka fara tafi raf raf raf, wani kidan aka saki wanda yanzu kowa da kowa ne ya shigo filin aka fara dancing, tuni filin ya rincabe gashi dama har duhun magrib ya bayyana sai da aka sha rawa iya rawa sannan wutar wurin tayi dif! Numfashi kawai kake ji yana fita sai ko motsin mutane.

  Acikin duhun junior ya kamo kugun teemah zuwa jikinsa, a hankali ya fara magana, baby ina son koko ne fa, cikin wata irin murya yayi maganar, ita teemah bata iya bashi amsa ba saboda jin da tayi yana shafar kirjinta, mannata ajikinsa yayi, ya fara kokarin fitar dasu daga cikin hall din, mutane suka rinka ketarawa suna wucewa har suka fita suka nufi bedroom din da junior yayi masauki acikin hotel din, suna shiga ya dan kalleta, kamar wacce tasha giya sai layi take yi a tsakar dakin, kan gado taje ta fada, takalmin kafarta junior ya cire sannan ya matsa kusa da ita, baby ya za ayi?? Lumshe idonta tayi, kawai kazo kasha kokon ka, ka manta da batun condom ai nasan kai ba kowacce mace ce zata samu kayi making love da ita ba, rungumeta junior yayi tareda zame rigar jikinta, baby bakida abubuwa fa why ba zaki shiga kanti ba? A ghana ana sayar da breast enlargement cream in dai nakoma i will buy it for you, ita dai teemah bata bashi amsa ba saboda ta gama zurfafa, nan fa junior ya fara sarrafa ta babu ji babu gani.

Tsawon lokacin suna abu daya kafin su dawo hayyacinsu, kallon teemah junior yayi ganin tana bacci ya sashi tashi daga shi sai gajeren wando yasa riga ya fice daga dakin, dakin bobo yaje ya fara bugawa, Jim kadan bobo ya bude ya baabah ya akayi ne?? Bobo zai yiyu mu koma kano a yau?? Meya faru? Bobo ya tambaya cikeda mamaki, bobo nifa na fada maka koko nake so kuma wlhi har yanzu ban ji na koshi ba, to ina teemah take yanzu?? Gata can adaki mana, to ka bari gobe da safe sai mu tafi yanzu kaje ka kula da teemah, ok, junior ya fada tare da juyawa ya koma dakin da teemah take.

    Lokacin da gari ya waye sai lokacin teemah ta tashi ta kalli junior yana ta bacci, kiss ta mannawa lebensa tare da sake rungume shi, murmushi ya saki idonsa arufe ya fara shafar na shanunta, teemah zan koma Kn yau saboda sch zan tafi acikin week dinnan kuma akwai wasan da nake son bugawa da zarar na koma ghana, daga kai teemah tayi babu damuwa zanzo sch din naku ai, dagaske?? Dagaske mana,ok ki bari kawai ni zanzo sch dinku weekend kinji, kai ta daga, dakyar suka iya rabuwa teema ta tafi shima ya shirya ya fito domin tafiya kn, akan hanyarsu ya fara bawa bobo labari, bobo har mom fa sai da na fadawa ina sha'awar koko amma mom ba ta gane abinda nake nufi ba, dariya bobo yayi shege baabah da ta dago fa? Da sai tamin aure kwana kusa, amma har yanzu banji ni daidai ba, saboda teemah tana da yan matsaloli ajikinta, bata hada komai ba dan har Lana tafita cikar halitta.

3⃣7⃣
   Murmushi bobo yayi junior ka zama dan bariki fa, rikakke ma kuwa, junior ya fada yana kallonsa, wlhi bobo a matse nake ne to amma ita teemah ba zata iya dani ba, shiyasa na ke son na koma ghana kwana kusa, haka suka ci gaba da hirarsu har suka isa kanon dabo, suna zuwa gidansu junior suka yiwa tsinke, lokacin da suka shiga mom na zaune tasha ado cikin wani leshi blue mai tsada kai da ganinsa kasan naira tayi kuka, ga wata sarkar gold katuwa da tasaka, kusa da ita junior yaje ya zauna tareda kwantar da kansa akan cinyar mom, sannu da zuwa yarona, mom tafada tana shafa kansa a hankali, yawwa mom ina dad? Dad dinka yaje kasar Singapore amma ba jimawa zai yi ba, mom so nake nakoma sch acikin satin nan, junior zaka tafi ka barni, ta fada cikin alhinin rabuwa da danta, mom 1 month kawai zanyi fa nadawo, to yarona Allah ya kaimu, tashi yayi yakarasa cikin dakinsa sai a lokacin tunanin kuluwa ya dawo cikin kwakwalwar sa, zama yayi a gefen gadonsa ya lumshe kyawawan idanuwansa yana tuno kuluwa da shagwabar ta, shi dai yana son yarinya shagwababbiya kuma macen data iya shagwaba tana burge shi sosai, kayansa ya fara hadawa cikin babbar jaka.

    Tun karfe 7 na safe ya shirya driver ya kaishi airport ya tafi kasar ghana. Awanni kadan suka sauka, tunda ya sauka ya hango dayo abokinsa wanda suke karatu tare, gefensa kuma wata hadaddiyar budurwa ce wadda ta tsuke cikin riga da wando, da sauri dayo yazo ya tareshi suka gaisa suka nufi motar da dayo yazo da ita, gidan da suke haya suka tasamma, tun akan hanya junior yake kallon wannan budurwar yana murmushi saboda ta tafi dashi over. Suna zuwa gidansu yayi mata sign da idonshi daya take ta gane abinda yake nufi, murmushi tayi ta fita daga motar shi kuma junior ya fara diban kayanshi ya shigar cikin dakinsa.

  Karfe 6 na yamma Patricia ta shiryo ta nufi dakin junior dama lokacin ya shirya tsaf ita yake jira, Patricia yar asalin kasar Nigeria ce sai dai yaroba ce amma kuma kyakkyawa ce sosai, tana yin knocking ya dan leko ganin itace ya sashi bude kofar a hankali, shiga Patricia tayi tare da fara dan idanuwanta ta lumshe su, tsayawa tayi ta rike kugunta tana kallon junior wanda ya rikice yana kallonta, a hankali taje ta tsaya agabansa, hy! Tafada tana dan jujjuya jikinta, hy! Junior ya daga mata hannu, jikinsa ta matsa sosai takai hannunta kan fuskarsa tana shafa gashin girarsa wanda yake baki wuluk kuma yalwatacce, kana da kyau! Ta fada a hankali, lumshe idonsa junior yayi domin yasha jin wannan Kalmar abakin yan mata da yawa, zip din gaban rigarta ta ja tafara zugewa, nan ta rikita junior suka fara bawa junansu feeling.

Sai da komai ya kammala sannan junior yaji kuluwa ta fado masa arai duk kuwa da cewa bai san sunanta ba kuma sau 2 kacal ya taba ganinta a rayuwarsa to amma duk da haka yana jinta acikin ransa sai dai bai san me yake ji gameda ita ba.

3⃣8⃣
  Kansa ya fara shafawa saboda tunowa da kuluwa da yayi domin ya rasa me yasa tun ranar da ya fara ganinta yaji ta burgeshi kuma shagwabar da tayi ba karamin tsaya masa arai tayi ba. Zare jikinsa yayi daga jikin Patricia domin acewar sa yau yasha koko ya koshi, wayarsa ya dauka ya fita falo ya fara kiran bobo abokinsa, bobo yana dauka yace kaga masoyin koko, dariya junior yayi kamar kuwa kasan yanzu shi na gama sha, kuma yanzu haka fita zanyi, zanje stadium inda zamu buga wasa, good Allah ya baku nasara, amin bobo sai munyi waya, yana katse wayar kiran mom dinshi ya shigo, hello mom, junior ka sauka lfy, lfy lau mom ya gida, junior gida babu dadi saboda baka nan, mom ai bazan jima ba zan dawo, to junior a tsaya dai ayi karatu kaji, tom mom akula min da horse dina pls, karka damu my boy zan kula maka dashi fiyeda yadda zaka kula dashi, thank you so much mom, bye bye, ok bye, da sauri ya tashi ya nufi akwatinsa da yake ajiyar kudi, kudi mai yawa ya dauko ya ajiyewa Patricia a kusa da ita, toilet ya shiga yayi wanka ya fito dama salla ba dadashi da kasa tayi ba dan haka kayansa kawai yasa ya fito ya nufi stadium acikin taxi, yana sauka yashiga rest room dinsu inda anan kowanne dan wasa yake shiryawa, ana ganinsa aka fara murna welcome junior, cikin sauri ya shirya cikin fararen kayansa na ball, riga da wando da safa da combus duk farare da abin hannu, lambar rigarsa lamba 1 ajiki an rubuta JUNIOR da manyan harrufa, filin wasa suka shiga inda zasu buga da Accra Golden stars, su kuma kungiyar su Super Eagles, bayan an fara wasan da kamar minti goma sha biyar junior ya zira kwallaye har guda biyu acikin raga, tuni wuri ya gauraye da hayaniyar magoya baya,junior kam daman wannan abun shine yafi komai burgeshi a harkar kwallo domin yana son yadda mutane suke sonsa sosai, gashi ko ina yaje an ringa nunashi kenan kuma sai abin yazo daidai saboda he's handsome & good looking guy, shi kansa akaran kansa yasan ya hadu shiyasa baya missing target.

Tuesday, September 4, 2018

DANA SANI (COMPLETE HAUSA NOVEL)

DANA SANI (COMPLETE HAUSA NOVEL)

 AUTHOR AREWAINFINIT
 DATE 4 SEP 2018
        

Written by

Maryam(ummu hanan)

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai tsira da aminci su kara tabbata ga Dan gata annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam,
Yadda na fara wnn novel din lpy ya bani ikon gamawa lpy


     1_5 

Tangamemen gidane kayatacce wanda tsayawa fadar irin kyawun gidan ma 6ata lkc me,.
Kutsa kai nayi har falon gidan wanda yaji kayan alatu da abubuwan more rayuwah sai tashin kamshi yake mai sanyaya xuciya.,

Idanuwa na dinga rabawa ganin ba kowa a falon

"Can idanuna suka kyallo min wani kyakkyawan saurayi da shekarunsa baxa su haura 28yrs ba.
Kura masa ido nayi ina hango tsagwaron kyau da Allah ya hore masa 
Farine tas mai hade da sirkin ja dogon hancinsa da kewayyayen bakinsa mai dauke da pink lips ya kara fito da ainahin kyansa ,kwance yake kan doguwar kujera yana kallon sama idanunshi a lumshe .

Kofa naga an bude wata kyakkyawar yarinya " yar kimanin 16yrs ta fito hannunta dauke da tray kallonta nayi ina hango tsananin kamarsu da wannan saurayin da gani ba tambaya Kasan kanwarsa ce 

Gabanshi ta karaso ta janyo karamin center table din dake gefe ta Dora trayn akai tace yah NAJEEB ga tea din shirun data jine yasa tayi xaton ko barci yake don haka tasa hannu tana dan bubbuga kafarsa a hankali .

Ahankali ya bude idonsa ya watsa mata wani mugun kallo ba shiri ta janye hannunta.sai ynx kika ga damar kawo min? tun yaushe nake xaman jiranki ,
cikin rawar murya tace  dan Allah kayi hakuri wall.......shut up ur mouth kinbar gurinnan gurin nan ko sai na mammake ki da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, wani dogon tsaki yaja tare da daukan cup din tea din yasa karamin cokali yana juyawa.

Saida ta tabbatar ta rufe kofa ta xauna bakin gadonta turo baki tayi tana kunkuni 
Mutum sai sa aikin tsiya in kayi ma ba godiya sai dai ya bika da jaraba ...masifaffe kawai.system dinta ta janyo ta bude ta fara game har barci yayi nasarar dauketa
Emana
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: 💦💧💦💧💦💧
 DANA SANI
💦💧💦💧💦💧

Written by
Maryam(ummu hanan)


       5_10

Karfe 10:13am na hango alh aliyu shida iyalansa kan dining table suna breakfast, hajiya asiya ta dubi alh tace jibine fa tafiyarmu katsina tissue ya yaga ya goge bakinsa sannan yace Allah ya kaimu xuwa anjima sai direba ya kaiki asayo masu tsaraba ko?murmushi tayi tace shikenan anjiman sai muje.

Kallon najeeb yayi yace da kai fa xa,ayi tafiyarnan
Dagowa yayi ya dubeshi yace  
Pls daddy xanje daga baya.
6ata rai daddy yayi yace a,a ban yarda ba yaushe rabonku da xuwa garin Dan haka tare xaku tafi ka fahimta ai?


"Eh daddy"
Ya fada ba don ranshi yaso ba.
Ita kam anisa murna take tayi xasuje kauye.

      ASALINSU:

Alh aliyu haifaffen katsina a wani kauye da ake kira sabon layi.su uku mahaifiyarsu gwaggo hanne ta Haifa hindatu ce babba sai amadu saishi aliyu auta sai kuma daya matar mahaifinnasu gwaggo karime dake da "ya" ya biyu
Sani da lawal sun taso Kansu a hade shi Kadaine ya samu yin karatun boko Dan ya nuna yana sha'awar shi suko sauran basu da ra'ayinshi mahaifinsu mallam tijjani ya bashi dama har yakai ga yin bautar kasa a can ya hadu da mummy sukayi alqawarin ita kuma "yar bauchi ce sai dai yaso samun matsala da mahaifiyarsu da kyar dai ta yadda da auren .amadu ya auri wata yarinya Laure sai dai Allah bai basu haihuwa ba, lawal " ya"yanshi biyu sani kuma uku abin yana matukar damunsu .acikin kano aliyu ya kama haya kasancewar anan yake aiki don haka da yayi auren nan aka....

Shekararsu daya da aure ta haifi danta namiji kyakkyawa sukaci gaba da rain on dansu cikin kulawa .
Watanshi biyar da haihuwa Allah ya kar6i ran mahaifinsu mal tijjani sunyi kukan rashin mahaifi  wata biyu da rasuwarshi itama mahaifiyarsu tace ga garinku sakamakon ciwon ciki daya turniketa lkc daya sun shiga matsananciyar damuwa amma ba yadda suka iya domin wanda yafisu sonsu shi ya kar6i abinsa........,

Ahaka rayuwah taci gaba da tafiya aliyu yana ta samun cigaba ta fannoni da dama kuma tun kan najeeb basu kara samun haihuwa ba.sai bayan shekaru sha biyu Allah ya kawo wani cikin .alokacinne kuma Laure matar amadu itama ta samu ciki, sun tsinci Kansu cikin farin ciki mara misaltuwa don tuni suka fitar da ran samun haihuwa sai gashi ubangiji ya basu......,

Bayan wata tara 

Mummy ce ta fara haihuwar  "ya mace sunan mahaifiyarsu taci wato hannatu sai suke ce mata aneesa.
Satin mummy biyu da haihuwa itama Laure ta sullu6o tata " yar budurwar kyakkyawa shima din dai sunan nata ya maida sai kawai suke ce mata Hannah.,

Hannah yarinyace data taso cike da shagwa6a da sangarta ganin ita kadaice agurin iyayen nata musamman gwaggo laure datafi shagwaba ta ga shegen jan fada duk kauyen an santa kullum cikin kawo kararta ake.....


***************

Haka rayuwah taci gaba da tafiya she karar Hannah goma aduniya babanta amadu ya rasu😭
Sosai mutuwar ta dakesu sai dai fatan Allah ubangiji yayi masa rahma ya kyauta namu xuwan(ameen)
Tun lkcn daddy yaso dauko Hannah ta dawo gidansa da xama
Amma fafur gwaggo Laure tace bata yarda ba "ya dayan da take gani taji dadi ita kadai gareta,
Dole ya hakura.
Bayan wani lkc daddy yayi ritaya ya fada harkar kasuwanci ya kuwa shiga da kafar dama don nan da nan yayi suna arxiki yana ta bunkasa.fili ya siya a nassarawa g.r.a ya tamfatsa gidanshi ginin xamani mai kyau da tsari,..
Najeeb kuwa dama bayan ya gama secondary daddyn ya kaishi kasar waje inda ya karanci xane wato architect bayan ya kammala ya dawo kasarsa don cigaba da aikinsa yayin da aneesa take daf da kammala secondary skull dinta,....


" Hannah kuwa an samu ta gama primary da kyar😓
don ba karatun take so ba dan ma baba sani da baba lawal suna tsaye akanta da bata yishi ba don gwaggo Laure ba takura ta take ba.duk da haka ba wani kokarin kirki gareta ba don in taje banda tsokana da Neman masifa. ba abinda take samarin kauyen da yawa nason xuwa wajenta saboda irin dirin da Allah yai mata da kyan sura ,sai dai suna tsoron halinta don sai ta fadawa mutum bakar maganar daxai Dade bai  manta ba.,.......


Ku biyoni🙋🏻
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: 💦💧💦💧💦💧
DANA SANI
💦💧💦💧💦💧

Written by
Maryam(ummu hanan)

    10_15

Cigaban labari

Saturday 11:34.  Su mummy suka dau hanyar katsina cike da tsarabar da xa,a rabawa "yan uwa da abokan arxiqi.
Aneesa ce ke taba mummy lbrn makarantarsu a fusace najeeb dake gaba ya juyo 
Dalla malama ki mana shiru kin cikamu da surutu


Dagowa mummy tayi daga danna wayar da take,. Harararshi tayi tace ina ruwanka? ko Kai take bawa? Sarkin xafin rai juyawa yayi yana fadin Allah kuwa mummy yarinyarce ta cika surutun tsiya,  toh ai ba bakinka bane sai ka kyaleta.,
Ido suka hada da aneesa ta mirror din motar ya xabga mata harara da sauri ta dauke idonta dan sosai take tsoron shi sam baya yi mata wasa kullum fadan mummy ya dinga sakar mata fuska dan itace sakuwarshi🤣 abinda baya son mummy na fada wai aneesa ce mai binshi.

Gidan su daddy suka sauka gwaggo karime tai murna da xuwansu tabarma ta shimfida masu awajen katuwar bishiyar cediyar dake tsakar gidan nan suka xauna aka gaggaisa ta kawo masu ruwan randa mai sanyi sannan ta xuba a kwanon sha taba sakina  " yar baba sani dake xaune awajenta ta kaiwa direba saida suka huta sukaci abinci dambu tayi musu da yaji attarugu da gyada mummy da aneesa sunji dadinshi sosai shikam najeeb kinci yayi yace ya koshi duk abinda gwaggo karime tace a kawo masa sai yace bayaci ...

Daga nan gidan su Hannah suka tafi a tsakar gidan suka samu Hannah tana ta faman xum6ure_xum6uren baki da alamu an 6ata mata rai ganinsu da tayine yasa ta tashi da murna ta rungume aneesa cikin karadi tace gwaggo ki fito ga "yan kano sunxo."
Fitowa tayi tana gyara daurin xaninta    
Cike da fara,a take fadin ah ah yau su hajiya ne agarin? sannunku da xuwa lale marhabin dasu najibu Ku shigo mana mummy ce tace ai dakinne da zafi yi mana shimfida anan kawai.
Dariya tayi tace toh ai shikenan dakin ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida masu a inuwa suka xauna suka gaggaisa ta kawo musu ruwa da abinci mummy ce tace aiko yaya Laure mun ciko cikinmu gidan gwaggo karime matsar dashi tayi gefe ta ce  bari a ajiye ko xuwa anjima ne sai kuci ....,"

Hannah ta duba tace tun daxu nake fama dake ki debo ruwa kika ki gashi ko ruwan sallah babu a gidan .turo baki tayi tana shura kafafu ni wllh na gaji yau sahuna nawa agidannan murmushi mummy tayi tace oh Hannah har ynx baki daina halayenki ba ko? ta6e baki gwaggo tayi tace kema dai kya fada hajiya.

duban Hannah mummy tayi tace tashi ki debo kinji "yar albarka aneesa ta rakaki kinji .mikewa tayita suri bokitin robar dake gefe dai_dai nan suka hada ido da najeeb da haushinta ya gama kasheshi ace yarinya 16yrs amma Sam bata da nutsuwa ga rashin kunya wata uwar harara ya watsa mata batai kasa a gwiwa ba ta maida masa martani😂 harda Karin murguda baki ta fice aneesa tabi bayanta.,'"

ji yayi kamar ya bita ya damkota ya zazzabga mata mari .
girgixa kai yayi tare da jan kwafa ahankali tashi yayi shima ya fice wajen direba .....",

Duban gwaggo mummy tayi tace yaya Laure akwai wata alfarmar da nake nema awajenki  
sai dai ban sani ba ko xakiyi min ita ,.ina jinki hajiya asiya fadi bukatarki ni kuma indai ina dashi xanyi maki
 
gyara xama mummy tayi tace alfarma nake nema ki bani Hannah in tafi da ita taci gaba da karatunta acan kinga ta gama primary tuni amma bata cigaba ba ga aneesa nan ta kusa gamawa.numfashi gwaggo ta sauke sannan tace agsky ba don tun farko nayi maki alqawarin biya maki bukatarki ba da ban amince ba saboda ita kadai na mallaka arayuwa nake gani inji dadi amma ba komi na amince ko baki tafi da ita ba aure xai rabamu sai ki sanar da su lawal., godiya mummy ta dinga xubawa don ita dai jininta ya hadu dana yarinyar tun tana karamarta ,.

"toh"
sai dai hajiya ki aiko a dauketa daga baya don kayanta ma duk babu wanki saita dan shishshirya tukuna.murmushi mummy tayi tace karki damu yaya Laure bana bukatar komi nata ga na aneesa nan sai ta fara amfani dasu kafin a diddinka mata nata ........,


Toh aranar dai duk "yan uwansu suka ji tafiyar Hannah kano , 

da kyar ta amince xata bisu ...

Sai bayan la'asar sukai shirin tafiya da kuka suka rabu da gwaggo har bakin mota ta rakosu,
" ganin Hannah na shirin shiga motor tana kuka yasa ya matsa kusa da mummy yace wai mummy me wannan yarinyar xata shiga tayi mana a mota??tare xamu tafi yatsina fuska yayi yace xuwa ina ?kano mana ta koma can da xama😳ido ya xaro yana kallon mummy ita kam bata kulashi ba ta shige mota ., lallai kam xa,ayita wannan fitsararriyar yarinyar ce xata xauna tare dasu?
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: 💦💧💦💧💦💧
DANA SANI
💦💧💦💧💦💧

Written by 
Maryam (ummu hanan)

      20_25

"Cikin lkc kankani Hannah ta fara xuwa skull dinsu aneesa hakama ta fara xuwa islamiyya toh ba laifi dai tana dan fahimta ba kamar da ba.haka shashancin data ke duk ta rage yinsa ta fara nutsuwa,"wajen kwalliya ne dai har ynx aneesa ke fama da ita Dan taki daina dige_dige a fuskarta."watanta uku kenan da dawowa kano"......




*******************

Gama dinner dinsu kenan najeeb ya tashi xai bar wajen daddy ya dakatar dashi yace akwai maganar daxa suyi komawa yayi ya xauna. ."

"Zamanshi ya gyara ya fara da " Alhmdllh godiya ga Allah daya kawo mu wannan lkc, "numfashi ya sauke yace hajiya akwai wani alqawarin da na daukarwa yaya amadu wani xuwa danayi daf daxai rasu ."

Shiru yayi yana binsu da kallo cigaba yai da fadin alqawarin kuwa shine na hada "ya" yanmu aure wato NAJEEB da HANNAH😳nima dake gefe ido na zaro ina kallon su.,

Najeeb ji yayi kamar an buga mai guduma akansa wai ko daddy yasan abinda yake fada kuwa🙊
Murmushi mummy tayi tace masha Allah hakan yayi kyau Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lkcn
 
"Kallon Hannah daddy yayi datayi kasake tana tunanin wai ita Hannah ko kuma wata daban ake nufi"'

Toh uwata  kinji irin alqawarin da mukayi da mahaifinki kafin rasuwarshi ina fatan xaki mana biyayya.

Mummy ta kalla sannan ta kalli aneesa dake ta faman murmushi ta juya gun uban gayyar fuskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa "

"Nifa daddy ban isa aure ba ta fada kamar xatai kuka .dariya sukayi gaba dayansu banda najeeb da kansa ke kasa  

Toh banda abinki uwata shekarunki nawa kina fa cikin 17yrs daddy ya fada yana dariya. Toh daddy makarantar dana fara fa?
Karki damu indai makarantace xaki cigaba agidanki kuma ba dogon lkc xa,a dauka ba dan su yaya lawal tuni suka fara min maganar aurar dake  tashi kuje Allah yai maku albarka,
Mikewa sukayi ita da aneesa suka amsa da ameen sannan suka bar wajen".

" wajen najeeb ya juyo daya koma tamkar an dasashi yace"

"Ya bakace komi ba?

Sai a sannan ya dago ya kalle shi da idanuwansa da suka canja color*

Ahankali yace pls "daddy Dan Allah karka hada wannan auren.da mamaki suke dubanshi mummy tace ko xamu iya sanin dalili?

Jijjiga kai ya fara 
haba daddy ya xa,ayi kamar ni in auri wannan yaabinda?
Murmushi daddy yayi yace meye aibunta? " yar uwarkace fah 

Nidai gsky bana sonta afusace daddy yace ko kana so ko baka so sai ka aure ta kaji na gaya maka aure ba fashi tun wuri ka fara shiri    
Afusace yabar wajen."

Mummy ya kalla yace mummy kina jin fa abinda daddy yake fada fa Dan Allah kiyi wani Abu akai .

Hmmm kasan halin daddyn Ku sarai idan ya fadi magana ta Riga ta xauna don haka karma ka fara yin gardama kuma ni banga illar yarinyar nan ba nasan dai bai wuce kace bata waye ba wannan kuma ka bata lkc kadan sai kayi mamaki da haka muka daukota? "*

Haba mummy, haba mummy pls help me mana ya fada kamar xai saki kuka
Mikewa tayi ta bar wajen.binta yayi da kallo yana jin kamar ya fasa ihu.........***





Ummu hanan🙋🏻
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: 💦💧💦💧💦💧
DANA SANI
💦💧💦💧💦💧

Written by 
Maryam(ummu hanan)


     15_20

Gaba ya bude ya shiga yana ta faman yatsina fuska,. direba yaja suka tafi da sun had a ido da Hannah sai ya harareta sai dai ta murguda masa baki ta kauda kanta da haka har Bacci ya dauketa.


Sai bayan Maghreb suka iso gida aneesa ce ta tashi Hannah daga baccin da take Hannah ki tashi mun iso shi kam najeeb dama suna parking ya fice ya nufi side dinshi.

"Tashi tayi tana mutstsuke ido tace kai amma fah munyi sauri 
" dariya sukayi mummy tace dama kina barci ai dole kiga anyi sauri"

Suna shiga falon mummy tace aneesa kuje da ita kuyi wanka ki bata kaya tasa.,

"Toh mummy"

Kamo hannun Hannah tayi data saki baki tana ta faman kalle_kalle suka nufi dakinta.,

Mummy ma wajenta ta nufa wanka tayi sannan tayi sallah fitowa tayi ta shiga kitchen dan samar musu abinda xasu ci.

Suna shiga Hannah ta xaro ido😳 ynx aneesa wannan dakinki ne?dariya aneesa tayi taxe eh mana dakina ne amma daga yau ya xama dakinmu,."*

Bed din ta nufa ta xauna tana shafawa ta6 gsky "yan birni kuna jin dadinku aneesa tace ynx ki tashi ga bathroom nan ki shiga ki wanka ki alwala sai kixo ki sallah tare suka shiga ta nuna mata yadda xatai amfani da komi sannan ta fito "*

Hannah kam ta6e_ta6e kawai take a toilet din taki yin ma abinda ya shigar da ita sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi wankan sai faman wasa da ruwa take.
bayan ta gama tayi alwala ta fito.,

Dariya tayi tace kaiii wllh bandakinnan akwai dadin wanka kuna shan dadinku.murmushi aneesa tayi tare da girgixa kai tace ga kaya nan ki shirya nima bari inje inyi wankan ". Kayan ta dauka ta duba gown ce ta atamfa purple sai dan karamin veil shima purple sawa tayi ta ta daure kanta tamau da veil din😁 hijab ta saka ta dauki prayer mat ta shimfida ta tada sallah.

Aneesa itama tana fitowa ta saka kayanta tasa ka ta saka hijab ta tada sallah 
Bayan sun idar suka cire hijaban sai asannan aneesa ta ga daurin da Hannah tayi wa kanta dariya tayi tace

" oh Hannah wannan fa yafashi xaki yi kin tashi kin kulle kai kamar kullin magani? yatsina fuska tayi ta ce ke ni baxan iya yafe _yafen nan ba gajiya xanyi .
Toh ai shikenan tashi muje falo mikewa sukayi suka fito 

Xo muje kitchen mummy na can shiga sukayi suka sameta har ta gama girkin da yake ba mai whl bane jollof ne na taliya da kayan lambu sannu da aiki mummy 

"Yawwa"

Aneesa dauki abincin kikai kan dining toh Hannah kam nanma banda kalle,kalle ba abinda take,....

Aneesa tana shigowa mummy tace je ki kirawo yayanki,.amsawa tai ta juya xata fita suka ci karo abakin kofa juyowa tayi tace gashi nan ma shigowa yayi cikin takunsa na Kasai ta kusa da mummy ya tsaya yace "wllh mummy yunwa nakeji ya fada cike da shagwa6a
Ta gefen ido Hannah ta kalleshi yatsina fuska tayi tare da ta6e baki cikin ranta tace"

*"Dan Allah dubeshi babba dashi yana wani yin shagwa6a tsaki taja ahankali taci gaba da ta6e ta6en da takeyi.

"Uhumm ba dole kaji yunwa ba mummy ta fada tana wanke hannunta a sink.

Kaje dining ga abinci can an gama.
Fita yayi su dinma fitar sukayi suka nufi dining.
Xama sukayi aneesa ce tayi serving dinsu suka fara chi.

Cike da yanga yake cin abincin kamar bayaso kadan yaci ya Mike yana goge bakinsa da tissue"

"*ba dai har ka koshi ba? Mummy ta tambayeshi
Na koshi mummy

  1. Duk fadar yunwar da kake? Murmushi yadan yi yace "

Monday, July 23, 2018

ZAWARCI Complete Book

*K*wance take a tsakar ɗaki sai muɗiɗɗiƙa take a ƙasa, yunwa kawai take damunta, ga kudaje sun cika ɗaki kamar toilet in daya shekara bai samu wanki ba,,,,, wasu zafafan hawaye suka zubo mata masu zafin bala"i, a bayyane tayi magana , wayyo Allahna, da ina can naci mai kyau , babu ruwana da wata yunwa ko ganin ƙazanta,,,, goge hawaye tayi da bayan hannu lokacin da taji mahaifiyarta tana kiran sunan ta,,,,,

*R*aihana baki ji na ne?""" umma ina zuwa, tsaki tayi , sannan tace idan ma baza ki zo, kin huta, dama wankau ne, aka kawo sunce yau suke so, idan zakiyi to kizo ki karɓa, idan kuma bakya yi ki faɗa masu, a daidai lokacin da ta fito a tsakar gida,,,,,,,

*T*ashin kayan wankin ta gani, ta gyara ɗaurin zaninta, sannan tace umma zanyi, umma ta kace da dariya, sannan ta taɓa hannu, tace yo kice ma baza kiyi ba, zama raihana tayi a ƙasa ta jayo wanki ta fara irgawa, sannan ta kalli yaron tace to wankin na ɗari da hamsin ne, yaron yace Eh, tace ga kuɗin, ya miƙa ma raihana ta ƙarba, tace bayan la"asar ka dawo ka ɗauka yace to yace sannan ya fita daga gidan,,,,,,,,,,,,,,

Umma tace to yanxun dai kafin ki fara wannan wanki, ki fara wanke kayan babanki sannan, raihana tace tou umma,

��������
������
*ZAWARCI*
��������
������
Saida ta wanke kayan babanta kala biyu, sannan ta fara wankin kayan wankau, yinin ranar nan haka ta yini ta wanke kaya,,,,,,

Lokacin da ta gama wankin hijabinta data gama koɗewa ta jawo daga saman iyiga, ta rataya a wuyanta ta fita tabar gidan............

Tana fita umma tayi dariya tace munafikar Allah, ai tunda dai *zawarci* kika zaɓa sai kixo mu zauna kice uwar da nake a gidan,,,,,,,,,

Raihana tana fitowa wani shago taje, suka gaisa da mai shagon, bayan sun gama gaisawa tace don Allah fulawa za"a bata kwata ɗaya, yace to, ya ana mata, tace don Allah ka bani bashin manja na hamsin insha Allah zan kawo maka , yace gaskiya raihana bakya san biyan bashi wallahi, tace kayi haƙuri wallahi zan kawo maka dana samu, shamsu yace, baia san ranar samu ba kenan,

Idan zaka bani kawai ka bani idan baza ka bani ka faɗa man, gaskia bazan bayar ba, tace to yanxn naji magana, ta ɗauki fulawarta da canjin ishirin ɗinta ta fito daga shagon,,,,,,,,

Sallama tayi ta shigo cikin gidan, matar babanta da ta dawo daga unguwa tace ina kika je ne?""""raihana tace fulawa na siyo gwaggo, cikin tashin hankali gwaggo tace waye ya baki kuɗi?""" tace nayi wankyau ne, tsaki tayi sannan taje inda fulawar take ta ɗauketa, tace wallahi saidai a ajiyeta da safe ayi fanke kowa ya samu, raihana tace gwaggo nifa nayi wankin nan na samu kuɗina gwaggo tace koma uwarki tayi haka za"ayi, ta ɗauke fulawar ta shige , cikin ɗakinta,,,,,,,

����
*zawarci*
����

Bayan ta ɗauki fulawar ta shige cikin ɗaki raihana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, kwanciya tayi saboda tun safiya bata ci komai ba, ga azabar yunwa dama tana ji kuma tayi wanki har ta gaji, kuma hdama kowa dai yasan wankindasa jin yunwa,,,,,,

Raihana wasu hawaye suka zubo nata , abinda ta fara tunawa, hango tsareren gidanta, tayi da tsaruwarsa da kuma yanda yake a tsabtace, cikinta ta laluba, lokacin data tuna irin abincin da take ci, uhum Allah sarki rayuwa tace,

Tashi tayi ta fito tsakar gida dan ganin waye yake sallama, wai ance a bada wanki, raihana tace to ɗauki gashi can , ya nufi wurin data nuna mashi ya nufi wurin yana cewa wai mama tace a kawo maki kaɗin taliya?"

Zainaba tace a,a, banda hali, gwaggo data ke alwalla tace kaje kace a kawo, kumin dare tayi ta, yace to, ɗakar wankin yayi ya tafi,,,,,,,,

Gwago tace dan rashin imani ubanki yana can yana fama liƙewa mutane takalmi baza ki tausaya mashi ba?" wai mutum ya haifeka amma kana masa hassada, raihana tayi tsaki ta shige ɗakin su.........



����������
*ZAWARCI*
��������

Gwaggo tace uwarki da ita kike tsaki, shegiyar nan, idan kinki haushi ki fitar da miji kiyi aure,,,,,,,,,
[07:24, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 2⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*A* ɗaki rahaina tayi magana ƙasa ƙasa, tace wallahi ba uwata nayi ma tsaki ba, kuma maganar aure, idan Allah ya kawo man lokaci sai inyi,,,,,,

*U*mma kiyi mata magana ta bani fulawata yunwa nake ji taliya zan kaɗa inci da manja, raihana ce take ma mahaifiyarta magana,,, umma tace bazan mata magana ba, dana ce kada ki kashe aurenki ai cewa kikai ke ba"a sanki, to yanxun ana sanki sai ki zauna kiyi ta haƙuri tunda haka kika zaɓarma rayuwarki,,,, raihana tace umma haka zaki ce?"" Eh haka nace kuma haka ne,,,, uhum raihana tace sannan ta ɗauki buta ta fita daga ɗakin,,,,

��������
*zawarci*
����������
*R*aihana ta kalli wani jikan gwaggo da yake zaune yana cin abinci, da sauri taje inda yake, robar ta ɗauka ta zubar da abincin a ƙasa, tana faɗin tunda banci babu uban da ya isa yaci ko yasha a gidan nan harsai naci, idan kuwa ba haka wallahi ba"a nemi zaman lafiya ba,,,,,,,,

Yaron da raihana ta ɓare na abinci ya faɗi ƙasa ya fara burgima yana ihu yana ƙarawa, da sauri gwaggo tayo waje tana faɗin lafiya?""" raihana tace ina ma lafiya tunda baki nemi zaman ta ba a gidan nan, gwaggo ta tafa hannuwa tana sallalami , sannan ta riƙe haɓarta tace raihana, yanxun da ni zaki yi faɗa a gidan nan?""" raihana tace Eh, tana magana tana zaro idanuwa, tace udan har baki bani fulawata ba yau saidai gidan nan ya tashi saboda bala"i, gwaggo tayi dariya tayi guda, ayyuri yuriiiiii yuriiiiii, to uwarki ma ta buga dani tabarni danni nan da kika bakan gixo ce, dan idan har hadari ya taru saina tsotseshi,,,,,

Rainaha tace aikin banza wanda bakuyi imani da Allah ba baku da aiki sai neman asiri, kuma idan har ina a gidan nan wannan yaron babu shi babu ƙara cin bacci saidai yunwa ta kasheshi kowa ma ya huta,,,,,,,

Gwaggo ta sake sheƙwa da dariya sannan tace, ke yunwa zata kashe, kuma ni yanxun dana ga dama sai in mayar dashi gudan ubanshi, kuma ubanshi yana da abincin bashi dan ubanshi namiji ba kamar ubanki ba, wanda sai ƙato ya cire takallmi sannan ya wanke, raihana tace Eh a haka aka gani kuma aka aura,

Gwaggo tace lallai yarinya dani kike magana, tunda *zawarci* kika zaɓa haka zamu zauna dani dake a gidan nan aure ko saidai kiga anayi,, tana faɗin haka ta kama hannun jikanta ta shige ɗakin ta,,,,,,,,

Raihana tace karyar banza baƙin bakinki ya faɗa ma jikokinki,,,,,, itama daga nan bata sake magana ba, ta ɗauki butarta ta kona ɗaki,,,,,,,,
��������
*zawarci*
��������
Raihana baki kyauta ba, ummarta take mata magana, tace umma barta, ninan walkice daidai ƙugun kowa, umma tace rufa man baki, tunda kinsan halinta kika biye mata,,, umma tace to wallahi nidai saidai in bar maki gidan nan,

Raihana tace kiyi haƙuri, kada kibar gidan nan saboda ni, umma tace idan kuwa ina san zaman lafiya da tsira da rayuwata dole in tafi dan bana iya zama ina kallon wannan wulaƙancin wallahi,,,,,,,,,

Sallamar babansu raihana , umma taji ta tashi ta fito tana mashi sannu da zuwa, ya amsa cikin kulawa, itama raihana fitowa tayi ta mashi sannu da zuwa, ya amsa sannan yace Allah yayi maki albarka, daga ɗaki gwaggo tace ba amin ba, sannan ta fito tsakar gida taci gaba da cewa kace Allah ya tsine mata albarka, wannan da kake gani, tana nuna rainaha da yatsan ta, tace to wallahi bakai sa"arta ba, saboda lalatattar yarinya, baba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu, yace bana san irin wannan kalamin daga yau, gwaggo tace dama haka zaka ce tunda an shanye ka sakarai mai matacciyar zuciya, duk gwaggo take wannan maganar , baba bai sake magana ba ya nufi ɗakinshi,,,,, raihana da umma suma ɗaki suka koma,,,,,,,,

������������
*ZAWARCI*
����������

*T*unda asuba, gwaggo ta fito daga ɗaki ta fara jaraba, tana masifa tana zage zage, babu wanda yayi mata magana, taci gaba da cewa idan banda munafircia matsa ma yarinya ta fito da miji tayi aure sai a barta ta zauna, kuma tana da nasu santa, to tunda *zawarcin* kika zaɓa sai kizo ki zauna,

Raihana dai daga ita har umma babu wanda yayi magana , haka ta kari masifarta ta koma ɗaki,,,, ,,,,,

Bayan hantsi ya fito baba ya fito dan tafiya wajen sana'ar sa, kuma gwaggo batayi wannan famke ba, kuma batayi komai da fulawar raihana ba, haka baba ya fita daga gidan baici kuma baisha komai ba,,

Gwaggo bayan fitar baba itama gyalenta ta yafa itama fita tayi tabar gidan,,,,,

Wata maƙociyarsu tayi sallama ta shigo, bayan gaisuwa tace raihana ga dakan tashshi raihana tace to, da ƙarfe nawa kike so?""" tace bayan azahar, to Allah ya kaimu lafiya, nawa za"a bada?"""inji matar, raihana tace tiya nawa ne?"" biyu da rabi ce, raihana tace to ki bada abinda kikai niyya, tace to, ɗari biyar ta ciro ta bawa raihana, tace ta riƙe sauran canji, godiya raihana tayi, matar ta tashi ta fita, itama raihana fita tayi ta nufi shago, gari da suger ta siyo sannan tayo gida............

*zawarci*
[07:25, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ������������
����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
������������
����������
��������
������
����

*page* 3⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��


*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*S*allama raihana tayi ta shigo gida, umma ta amsa mata, kusa da umma raihana taje ta zauna, garin ta ajiye sannan taje ta ɗauko kofi da cokali, wurin ta dawo ta ɗauki garin ta haɗashi, bayan ta gana , ta miƙawa ummarta tace ummana sha ki rage man, umma tace ni bana sha, raihana tayi juyin duniya tace bazata sha ba,,,,,,,,,,

*R*aihana ta ɗauki garin tasha, bayan ta gama sha ta tashi ta fara dakan tashshin da aka kawo mata,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*B*ayan raihana ta gama dakan tashshi ta kwashe, bayan ta gama kwashewa ta zauna a wurin tabaryar da tayi dakan tana hannunta, ta jingina kanta da ita, hawaye masu zafi suka zubo mata, ta runtse idanuwanta, abinda ta fara tunawa shine,,,

�� ��
*gidan mijinta*
�� ��

*R*aihana ta fara tunawa, wata rana, da sallama ya shigo gidan ko inda yake bata kallaba, shi kuma cikin farin ciki ya shigo yana faɗaɗa murmushin shi, yace raihana barka da gida, tsaki tayi, ita babu sannu da zuwa kuma bata ansa sallamar ba,,,,,,uhum ajiyar zuciya zainaba tayi sannan a bayyane tayi magana tace rabon *zawarci*

������
*zawarci*
������
Idanuwanta ta sake runtsewa, abinda ta ƙara tunawa, raihana zanyi tafiya, ta sake hango lokacin da ta taɓe baki, sannan tace sai wani magana kake man saman kai babu girmamawa, idan zakayi tafiya ina abinda ya dameni"""",,,,,,, murmushi yayi sannan ya ciro kuɗi har dubu ishirin ya ajiye mata a gabanta,,,,,,,,, wasu hawaye suka ƙara kwararowa daga gudan raihana, tace *astagafurulah*

*zawarci* baiyi ba, abinda raihana ta faɗa kenan, sannan ta gige hawayenta, tace abinda nafi ƙarfi yanxun shine yafi karfina,,,,,,,,,, ***

��������
*zawarci*
��������

*R*aihana ta janye taɓaryar gabanta ta jingina da bango ta mike,,,, a daidai lokacin da gwaggo tayi sallama ta shigo,, raihana ta amsa, gwaggo ta cire gyalenta ta rataya a igiya, sannan tace raihana wani mutum ne a kofar gida yake maki sallama, raihana tace naji, ɗakin ummanta ta shiga, ta ɗauko kwandon wanka, ta duba taga babu sabulu a ciki, tsaki raihana tayi tace kai Allah kasa mu dace, saman window ta duba ta ɗauko wata ledar omo, ta zuba ruwa ta shiga wanka,,,,,,

��������
*zawarci ne*
��������

*T*ana fitowa wanka alwalla tayi ta shige ɗakinsu, umma ina man yake?"" in shafa umma tace babu mai ya ƙare fa, raihana tace yanxun ya zanyi a daidai lokacin da take zama saman tabarma, umma tace ɗauko waccan ledar ina da sauran man gyara ki murza , ajiyar zuciya raihana tayi sannan ta miƙe taje ta ɗauko ta shafa, fuskar nan ta ɗauki ƙalli, da kafafuwanta, kuma babu powder, ta kalli kanta a madubi, tace rayuwa kenan, girgiza kanta tayi hawaye masu zafi suka zubo mata, umma ta kalleta tausayin raihana ya kamata, saboda raihana bata san wahala, amma a fili tace haba har kin gaji?"" ai baki komai ba, lokacin dana faɗa maki kiyi haƙuri ki zauna ai cewa gani kikai gara ki dawo gida,,, haushi ya ishi raihana bata sake magan ba, ta ɗaga ƙasan katifarta ta ɗauko wata ƙoɗaɗɗiyar atamfa tasa, da habar zaninta ta goge fuskarta ta fice daga ɗakin,,,,,,

������
*zawarci*
������
Tana fita umma tace kinga da yanxun kina gidanki kina yin rayuwarki yanda kike so, kinzo ki liƙe nan sai wahala kike sha,,,,,

Fitar raihana wani mutum ta hango tsaye bakin bishiyar kofar gidansu kamar ya fiddoshi daga cikin ƙasa, raihana tayi tsaki sannan ta nufi wurin shi cike da masifa, tana zuwa babu ko gaisuwa tace malam yadai?"" yace nine dama nazo ina sanki, to naji kana do na, sai mi kuma?"" maganar aure ce, raihana tace to daga yau kada in sake ganin ƙafarka nan kaji na faɗa maka?"" tana faɗin haka bata jira abinda zaice ba tayi cikin gida, a zaure ta tsaya, tace banda iskanci da shara da bola dan taƙamar kana *zawarci* kowa sai yaxo, tsaki tayi sannan tace shege ƙazamin banza, ...............


Hhhhhhhhhh
��������
*zawarci*
��������
[15:01, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 4⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*gargaɗi a bisa wata ƙungiya, da bama buƙatar saka sunan ta, dan haka muna roƙonsu dasu guji juya mana littafi ta ko wace fuska, idan kunnne yaji ���� gangar jiki ya tsira* ����‍♀

��������
*zawarci*
��������

Sallama tayi a daidai ƙofar ɗakin ummanta ta shige, har kin dawo?""" Eh kawai tace, inda ta ajiye tashshin data daka ta wuce ta ɗauka , sannan tace umma zan kai mata saƙon nan, umma tace sai kin dawo , to tace tayi gaba,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*zawarci*
Raihaina tana fita umma tace Allah ya baki miji kiyi aure raihana ki huta da wannan rayuwa, ,,,,,,,,

*R*aihana tana fitowa maƙotansu ta shiga, gidan badiyya, sallama tayi ta amsa mata tace raihana ki shigo mana, raihana tace to, ta shiga, ta samu wuri ta zauna, suka sake gaisawa, sannan raihana ta fidda tashshin ta bata, godiya tayi , sannan tace bara inxo,,, fitowa tayi taje kicin ta zubo ma raihana abinci,,,, sannan ta dawo ta ajiye mata, murmushi raihana tayi danma kada a ɓata lokaci kawai tace tana azumi,,,,,,,,,,,,

������
*zawarci*
������
*B*adiyya tace Allah sarki azumin mi kike?"" murmushi raihana tayi tace ramuwa nake, badiyya tace to Allah ya bada lada, amin raihana tace, sallamar mijinta suka ji, raihana tana zaune taga badiyya ta tashi cikin sauri ta fita,,,,, tana kallon ta tana zuwa ta rungumeshi tana oyoo yoo barka da dawowa baban sadiq,,, lader hannun ta ƙarɓa cikin girmamawa tana buɗewa dariya tayi saboda ganin abinda yake cikin ledar , sannan ta matsa kusa dashi ta ɗora kanta saman kafaɗarshi tace na gode Allah ya saka da alkairi ubangiji ya ƙara rufa asiri Allah , amin yace yana murmushi,,,,,,,

*zawarci*

Hmmm ajiyar zuciya raihana ta sauke, sannan ta tuna cewa ita idan mijin nata ya kawo cewa take yaje ya ajiye,,,,,,, a bayyane tace gashi an barni da *zawarci* jiki a sanyaye ta fito tsakar gida, tace nidai zan wuce,,,, �� raihana taga masoya suna soyewa hankalinta ya tashi,,,,,,,, badiyya tace haba tun yanxun?"" don Allah ki bari yanxun zai fita sai muyi fira, raihana tace a, a, ina aikine a gida,,,,,, badiyya tace to ngde, a gaishe man da umma, raihana tace to sannan ta fita tabar gidan,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*A* gida raihana ta shiga ɗakinsu,,,, umma ta samu tsaye ta riƙe hijabinta a hannu, raihana tana shiga umma tace mata yawwa, zanje duba bayi bata da lafiya, raihana tace sai kin dawo a daidai lokacin da take kwanciya saman tabarmar kaba,,,,,,, umma ta fice tabar ɗakin,,,,,,

������
*zawarci*
������

*Raihana* tana kwanciya ta ɗaga kanta sama tana kallon izarar ɗakinsu, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, ajiyar zuciya tayi sannan ta gyara kwanciyarta saman hannun ta na dama,,,,,,,,,,,,,,, abinda ta fara tunawa,,,,

��������
*rayuwarta*
��������

*Khadija* shine ai nahin sunan *raihana* babanta malam ibrahim, da ɗan kasuwa ne, ya ɗan riƙe kuɗaɗe babu laifi, daga baya Allah ya kawo mashi karayar arxiki, matan malam ibrahim biyu, binta itace babbar matarsa wanda suke kira da gwaggo, tana da "ya"ya, basai na tsaya lissafo su ba, halima itace mahaifiyar raihana, wanda suke kiranta da umma, umma ta haihu sosai amma Allah bai bata wasu rayuwa ba sai kan khadija, wanda aka sakawa sunan maman malam ibrahim, yayarta ɗiyar gwaggo itace take kiranta da raihana, saboda haka shine dalilin da yasa kowama ya kekiranta da haka, dan yanxunma sunan ta ya ɓata saidai *raihana*

Gyara kwanciya raihana tayi sannan ta goge hawayen da suka zubo mata,,,,,

��������
*zawarci*��
��������

Ku biyo ni sannu a hankali don Allah donjin labari *zawarci*

Ina maku fatan alkairi masoyana , ku biyo ni sannu a hankali don jin wannan labari, *ameenxi writr's association* a shirye muke wajen ƙawata maku da daɗaɗa maku din farin cikin ku,

*jameela musa* ke cewa ku kasance dani lafiya,,,,,,

07060797938, a shirye nake da jin ƙorafinku ����
[15:02, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*gargaɗi a bisa wata ƙungiya, da bama buƙatar saka sunan ta, dan haka muna roƙonsu dasu guji juya mana littafi ta ko wace fuska, idan kunne yaji ���� jiki ya tsira* ����‍♀
������
*ZAWARCI*
������

*B*ayan ta gama goge hawayen da suka zubo mata a ido, ta tashi zaune ta zabga tagumi, sannan ta ɗora kanta saman guiwarta,,,,,

*zawarci*��

Malam ibrahim mahaifin *raihana* shine yayi kyautar raihana ga wani yaronshi mai suna aminu, yana da kirki sosai, ya bashi raihana ne, saboda ya matsa mashi yana santa, shi kuma ya bashi raihana saboda ya yaba da hankalin aminu,,,,,,

*to haka baba ya bawa *aminu* auren raihana, ansha shagali sosai kuma aminu yayi hidima saboda yana san raihana kuma komai zai iya yi, saboda ita idan dai abun baifi ƙarfinshi ba,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*Raihana* da sauri ta goge hawayen idon ta dan kiran sunan ta da taji gwaggo tanayi,,,,, ba tare da ta amsa kiran ba, ta tashi ta fito tsakar gida,,, kallo tabi gwaggo dashi har yanxun batayi magana ba,,,,,,,

Gwaggo tace, wallahi tun ɗaxu nake neman wanda zai kai mana niƙa ban samu ba, raihana ta ɗaure fuska sosai sannan tace idan baki samu mai kai niƙa ba sai akayi me?"""" gwaggo tace wannan ɗaure fuskar naki bazai hana ince kije kikai ba, tunda ba"a samu yaron aike ba,,, kam raihana tace, sannan tace lallai gwaggo kinzo da abinda baya yuwuwa, gwaggo tace ai dan zai yuwu nayi magana, saboda haka sai kinje, raihana tace bazanje ba,,,, sallama umma tayi ta shigo gidan, a daidai lokacin da gwaggo take cewa da kina gidan mijinki zanje in kiraki kikai niƙa ne?""""

*t*saki raihana tayi sannan tace aike kina so kiyi man gorin aure, bayan nasan idan lokaci yaxo sai nayi, gwaggo tace wannan kuma matsalarki, dan wallahi idan baza kikai niƙan nan ba, yau bazanyi tuwon nan ba, saidai ubanki ya kwana da yunwa,,,,, umma tace ɗauki kije kikai ɗinƙan kinji,,,,, raihana zatayi magana umma ta dakatar da ita, ta hanyar cewa ba komai wata rana sai labari, gwaggo tace ba labari ba koma b.b.c ne ina ruwana,,,, ta juya ta wuce ɗakinta, inda gwaggo ta ajiye buhun niƙan da kuɗin raihana taje ta ɗauka sannan ta fita daga gidan,,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

Raihana sai Allah ya isa take har takai shagon niƙa,,,,, mai niƙan ya kalleta ya bushe da dariya, sannan yace baiwar Allah ke aka aiko?""" rahaina bata yi magana ba, ta haɗa hannuwanta ta rugummesu a ƙirjinta,,, mai niƙan yace ni wallahi da zaki yadda kawai in fito muyi aurenmu in rufa maki asiri tunda shi aminun ya kasa,,, ko inda yake raihana bata kalla ba, dariya yayi lokacin daya ɗaga buhunta ya juye masarar a cikin inji, yaci gaba da cewa matana ukku yarana ishirin da biyar, kallon ƙasa da sama raihana tayi mashi, wata irin dariya yayi sannan yace Allah sarki irin wannan kallo ai sai kisa mutum yayi fitsarin zaune dan daɗi, tsaki raihana tayi ta duƙar da kanta ƙasa har ya gama niƙan,,,, ta ɗuka zata ɗauka da sauri ya riƙe yace bari insa akai maki, raihana ta saki, kuɗin ta miƙa mashi yace tabarsu, yana yashe baki yace wannan toshine, murmurshin baƙin ciki raihana tayi taji kamar zuciyarta zata fashe wato da niƙa za,ayi mata toshi,,, yaronshi yace ya ɗauki niƙan yakai gidansu, yaron ya ɗauka yayi gaba, raihana tafi bayanshi, mai niƙa sai ɗago hannu yake yana cewa sai yaxo cin tuwo anjima,,,

��������
*zawarci*
��������
*raihaina* haka tabi bayan yaron tana zance zuci, lallai waƙƙahi mutumnn nan ya raita mata, hankali, addu"ar ta ɗaya kada yazo gudansu dan babanta yana iya cewa ya turo, tunda dama kullum sai yayi mata maganar tayi aure,,,,, a daidai lokacin da tayi sallama cikin gida,,,,

*zawarci*
Yaron ya ajiye niƙan ya fita, gwaggo ga niƙan nan, to aisai kiyi tankaɗe, raihana tace hada wani tankaɗe, tace E , taci gaba da cewa ai da uwarki ce idan tana aiki baki da zama sai kinga an gama, dariya ryhaina tayi sannan tace maida wuƙaƙen zan maki, a daidai lokacin data shiga ɗakinsu,,, hijabinta ta cire ta miƙawa ummanta kuɗin niƙan tace ki ajiye wannan , umma tace na miye?"" raihana tace nawa ne na baki, umma tace to, bayan ta nashi kuɗin ta fito tsakar gida ta fara kama ma gwaggo aiki,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������
*W*ani yaro ne ya shigo da tsirin kayan wanki saman kanshi, sallama yayi sannan ya nufi inda raihana take zaune, kama mashi tayi ya sauke, sannan ya miƙa mata kuɗi yace ga kuɗin ruwa da sabulu, ta ƙarba ta ɗaure a haɓar zani tace idan Allah ya kaimu jibi ku dawo ku karɓa, yaron yace to, sannan ya fita daga gidan,,,,,

*zawarci*
Gwaggo tace raihana wannan wanki ma ai babu wani datti sosai, raihana dai bata yi mata magana ba ta ɗauki kayan mutane ta nufi ɗakinsu dashi, bayan ta ajiye ta fito suka ci gaba da aiki,

��������
*zawarci*
��������

Tunda safe gwaggo tazo kofar ɗakin su raihana ta riƙe ƙugu, tana cewa ki fito ubanki babu lafiya ki kawo kuɗin wankin nan inje in siyo mashi magani, daga ɗaki raihana tace wane irin kufi kuma?"" wanda kike tarawa a daidai lokacin da ta yaye labulen ɗakin ta siga ciki, raihana tace to gaskiya banda wasu kuɗin ni da zan bayar, gwaggo tace kina dasu, raihana tace faɗa man abinda nake siyawar, gwaggo tace wanki mana kina nan kin tara kuɗi dake da uwarki kin boye, dariya raihana tayi sannan tace baki son muna tara kuɗi gwaggo?""" tsaki tayi gwaggo sannan ta fita tabar ɗakin,

*zawarci*
Umma tace idan kina da kuɗi ki bata mana, raihana tace barta, zanje wajen baban dakai na, umma tace to, miƙewa raihana tayi ta fita daga ɗakin, ɗakin baba taje ta shiga tare da sallama, ya amsa , kusa dashi taje ta gaishe shi, ya amsa sannan tace baba miye ya sameka??"" baba yace mura nake, amma da sauƙi yanxun zan fita, raihana tace to Allah ya ƙara sawakewa, baba yace amin, raihana ta miƙe zata zata fita shima baba ya miƙe ya biyo bayanta, yana cewa mamana ki fito da miji kiyi aura kinji ko?"" to kawai tace tayi gaba, shima fita yayi daga gidan dan tafi wurin aiki......

������
*zawarci*
������

Raihana tana fitiwa ɗakinsu ta shiga ta fiddo wankin da zata yi, ta fara wankinta, *zawarci*
[21:18, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 7⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

Wannan shafinki naku ne, *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION*

Godiya ta musamman, *ASMEENAT XEEYAN* ��

*Y*ana fita tafi bayanshi da harara tace banza sakarai,,, kwanciya tayi tare da jawo bargo ta lulluɓe, taci gaba da baccin ta,,,,,

*A*minu kuma yana zuwa ɗakinshi gado ya hau ya kwanta, ya fara tunanin wata ƙawar *raihana* da take masifar sanshi, ajiyar zuciya sannan yace Allah sarki itama haka take ji, yanda yake ji idan raihana ta wulaƙanta shi, gyara kwanciyar shi yayi sannan yace ita kuma babu ruwanta bata jin komai, a bayyane yace Allah sarki rayuwa,,,,,,

****** ƙarfe 9:30am ta farka daga bacci, saboda haka a hanzarce ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka, bayan ta gama wanka ta fito, ta zauna a gaban madubi ta fara shirya kanta,,,,,,,,,****×

*A*minu yana ɗakinshi yaji ƙamshin turaren raihana, shima tashi yayi ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya, sannan ya nufo ɗakin raihana, itama ta gama shiryawa, ta matse cikin riga da wando, yana shigowa ɗakin a siƙwane ya isa inda take, ta rungumota , ta baya, ya ɗora fuskarshi saman kafaɗarta, daidai saitin kunnenta yayi magana, kinyi kyau madam, cikin masifa ta ƙwace jikinta,, ta juyo ta nuna shi da yatsan ta,, sannan tace wallahi daga yau sai yau, idan ka kuskura ka sake tiƙeni , ban yafe maka ba, dariya aminu yayi sannan ya sake matsawa kusa da ita, ya ƙara tallafo ƙugunta, ya ɗora hannuwanshi a saman ƙirjinta, raihana tace Allah ya isa ka taɓa, dariya ya sake yi sannan yasa hannunshi cikin rigarta, da sauri ta ciro hannu sannan ta ɗunƙule hannunta da niyyar kai mashi nushi yayi sauri yaja da baya,,,,,,,,,,

*H*aba madam ya kamata ki kawo man ɗan abinda zanyi break mana,,, raihana tace kaji wani sakarci kuma, madam sai kace wata inyamura`?"" Aminu yacd wallahi ba inyamura kike ba,,,, raihana taci gaba da cewa wallahi har inbar gidan nan bana girki kaji na faɗa maka, dan daga yau ka fara lissafi sati ukku zanyi gidanka, aminu yace Allah ya sawake, ni bana sakin mace duk abinda tayi man, raihana tace baka haɗu da irin raihana ba, dan wani abun idan nayi maka kai da kanka zaka rubuta saki ka bani, kuma idan kazo bani saika duƙa,,, aminu yace to Allah kada ya nuna mana ranar,,,, taɓe baki tayi sannan tace ka kawo man abinda zanyi kalaci, yace bara in dafa maki, ko inda yake bata kalla ba, shi kuma bai sake magana ba ya fita yabar ɗakin"""""""

*A* kicin haka ya zuge yaci gaba da aikin haɗa masu abinda zasuyi kalaci,,, ya daɗe sannan ya gama ya fito, da abinda yayi a farlo yaje ya ajiye,, ya koma kicin ya gyara inda ya ɓata,,, bayan ya gama ya dawo farlo ya zace ranki ya daɗe fito an gama, raihana ta taho cikin isa da ƙasaita, tazo ta zauna, yawo flaks tayi ta fara haɗa kalaci, sannan ta jawo flet na dankali da doya, ta ajiye a gabanta ta fara ci, aminu yabi ta da kallo, saida ta gama shi har lokacin babu abinda yaci ko yasha,,,

***miƙewa tayi zata nufi ɗaki da sauri ya miƙe ya riƙota,,,, farlo ya dawo da ita ya zauna saman kujera, ita kuma ya zaunar da ita saman cinyarshi, raihana kiji tsoron Allah, kada ki manta sadaki na bayar na auroki dan ina sanki, kuma na ɗauki hutu a wurin aiki na dan kawai in more da amaryata, a daidai lokacin da yake kai bakinshi cikin nata, raihana ta fara tureshi , amma a banza, haka taci gaba da halbe halbenta, tana tunkuɗeshi amma ko motsi baiyi ba, haka yaci gaba da bi duk inda jijiyar jikinta take yaci gaba da aika mata saƙonni, a kasalance raihana ta samu ta janye bakinta daga nashi, cikin wani yanyi tayi magana tace ban yafe maka ba, a hankali ya sake mata hannu , ya kwantar da bayanshi jikin kujera, ita kuma tana zaune a ƙasa,,, daga baya kuma ta miƙe ta nufi ɗakinta,,,, tana zuwa gado ta hau tayi ruf da ciki, zuciyarta tana mata saƙe saƙe,,,,,,

Shi kuma har lokacin yana zaune kamar yanda raihana tabarshi,,,,,,,,,,

Kiran sallar la"asar ne yasa umma cewa tashi muyi sallah mu dawo, *raihana* tace to, raihana ce ta fara fita daga ɗakin, umma har yanxun tana zaune inda take, raihana tana fita, umma tace to ai ga *zawarci* Allah ya ɗora maki raihana da ƙananan shekaru saidai addu"ar Allah ya kawo miji na gari,,,miƙewa tsaye tayi itama ta fito, a daidai lokacin da raihana zata shiga ɗaki,,, ta shige umma ta fito,,,,,,

������
*zawarci*
������
*R*aihana, ki fito fa babu ruwa a gidan nan, gwaggo ce take magana, raihana da take zaune saman abin sallah , tace *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un* a daidai lokacin da gwagho ta sake cewa in banda iskanci ina magana sai kiyiman shiru , to ai sai ki fito ki faɗa man idan ni kike so inje in samo ruwan nan, miƙewa tsaye raihana tayi ta fito tsakar gida, ta fara tattara kayan mutane data wanke, gwaggo tace a nan zaki samo man ruwan, wani bokiti ta ajiye a gaban raihana, amma har yanxun raihana batayi magana ba, ta gama ƙwashe kayan ta nufi ɗakin su,

*zawarci*
*B*ayanta gwaggo tabi tana cewa uwarki kika kyale, shegiya mai baƙin halin tsiya, saboda wannan baƙin halin yasa namiji ya sakoki gaki nan kin rasa mashin shini, ita dai raihana batayi magana ba, saboda haka tana ajiye kayan ta ɗauki hijabinta tayi waje,,,,,,,

������
*zawarci*
������
*A* kofar gida ta tsaya har ta samu mai ruwa, tace ya kawo mata jarka ɗaya, yace to, ya ɗauko ruwan tayi gaba yabi bayanta,, har cikin gida, inda gwaggo ta ajiye bakitin ta nuna mashi a ciki ya fara zuba ruwan, gwaggo tana ɗaki taji ƙarar zuba ruwa saboda haka tayo waje, salati ta fara tana tafa hannunwanta yanxun saboda tsabar bakin ciki kije ki samo ruwan shine ke mai arziki zakije ki karawo mai ruwa?""" wannan ai baƙin ciki ne, naira ishirin ɗin idan kika bani ai na siyi omo, raihana ba tayi magana ba, mai ruwa yana gama zuba ta bashi kuɗin shi , ya fita daga gidan ita kuma ta nufi ɗakin su, gwaggo tace kai yarinyar nan Allah yayi maki baƙin ciki , raihana Allah ya tsine maki albarka tunda kika hanani kuɗin nan, raihana da sauri ta fito daga ɗaki sannan tace , baƙin bakin ki ya faɗa kanki dake da "ya"yanki da jikokinki , sannan ta koma cikin ɗaki, gwaggo tayi ta zage zage ita ɗaya a saƙar gida,

*zawarci*
Saboda dama tun dawowar raihana gwaggo bata da yaron aike sai ita, tun tana cewa bata zuwa, ta haɗata da baba yace tayi haƙuri taje saboda a zauna lafiya,,,

***gwaggo sai Allah ya isa take tana ƙarawa tana tsine ma raihana saboda bata bata naira ishirin ba, daga umma har raihana babu wanda ya sake ma gwaggo magana har ta gaji da kanta tayi shiru,,,,,,
[21:19, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 8⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*H*aka gwaggo tayi jarabarta harta ƙoshi dan kanta,,,,,,

*Y*aro ne, tsaye a tsakar gida , sai ƙara nanatawa yake ance ana sallama da *raihana* gwaggo ce ta fito daga cikin ɗaki tana cewa uwar baƙin hali kinaji ana kiranki baza kixo ki fita ba,, to kada Allah yasa ki fito ni bara inje, idan ya shirya zance kawai ya turo, tana faɗin haka tayi waje,,,,
������
*zawarci*
������
*A* zaure gwaggo ta sameshi ya jingina da bango, ƙafarshi ta dama ya ɗorata a bango ta baya,, ya rungume hannunshi a ƙirjinshi, kanshi yana kallon ƙasa, kana ganinsa, sallama gwaggo tayi , ya masa ba tare daya kalli inda take ba, gaban gwaggo ya faɗi, da sauri ta leƙa kofar gida, dan taga ko mai sallamar yana waje, babu kowa dowowa tayi, kallon da tayi mashi yafi ƙarfin ace yaxo neman *raihana* saboda haka ta dawo, tace kaine ka aika yaro cikin gida?"" sai a lokacin ya ɗago kanshi , da sauri gwaggo ta sauke idon ta ƙasa saboda wani abu taji ya shigar mata cikin ido, zuuuuuuu, yace Eh , *raihana nake nema, gwaggo cikin rawar murya tace , lafiya dai?"" yace lafiya qalau ia san ganin ta ne, har yanxun kan gwaggo ƙasa yake, tace an ɗaura mata aura, ummm yace, ba tare da ya sake magana ba, hannunshi ya saka a aljihu ya ɗauko bandir na 1000, ya miƙa mata, gwaggo da sauri ta ƙarɓa, tana godiya shi kuma ya fita, da sauri gwaggo ta miƙe tayi cikin gida,,,,,,,,,,,

<<>> {{}}~~¤
*A* ɗaki gwaggo ta duba kuɗin sannan ta jinjina kanta, tace lallai ina da sauran aiki a gabana,, wannan mai kuɗin idan ya auri *raihana* ai ina cikin matsala, hijabinta ta jawo daga saman kyaure ta zura tayi gaba{{}}}<<>>

������
*zawarci*
������
*S*allamar baba tasa da umma da raihana suka fito tsakar gida, baba sai ƙara faɗaɗa murmushin shi yake,, tabarma umma ta shimfida tana ƙara mashi sannu da zuwa,, yawwa yake cewa lokacin daya ke zama, suma zama sukai baki ɗayansu, baba yace albshirin ku?"" da umma da raihana suka ce goro, sannan umma tace ai yau yanda naga kana murmushin nan, nasan an samu nasara, baba yace gaskiya alhamdulillah a daidai lokacin da gwaggo tayi sallama ta shigo, inda suke zaune ta nufa tare da ɗauko kujera tayani gulma ta zauna, baba yace to yaudai *raihana* Allah ya temakeki kin samu mijin aure, gaban raihana ya faɗi da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta,,, cikin zaƙuwa gwaggo tace sirikin namu daga ina yazo?""" baba yace ai ba ɓoyayye bane , *yusufa* mai niƙa ne,!'""""""" idanuwa raihana ta zaro sannan tace haba baba, ka daina wannan naganar don Allah mutum da mata ukku yara ashirin da wani abu, gwaggo tayi karaf tace rufa ma mutane baki munafikar Allah, ubanki yana magana kina magana?"" wannan ai rashin tarbiyya ne, sannan ta juya wurin baba tace a gaskiya idan kana biye ma yarinyar nan babu ranar da zata aure, tunda an samu mai santa kafin ya zare kawai kace ya turo, baba yace, ai yace zaizo su fahimci juna dai, saboda haka yaune zai fara zuwa, wata irin guɗa gwaggo tayi , sannan tace lallai yarinya kinyi goshi{{}}

*zawarci*
*U*mma batayi magana ba, ta tashi tayi ɗakinta, raihana ma ta rufa mata baya,,,, gwaggo ta zauna taci gaba zuga baba, lallai yace ma yusufa ya turo, kawai a ɗaura aure in yaso daga baya ta tare, haka dai taci gaba da maganganunta, daga baya ta tashi tayi ɗakinta, shima baba ɗakinshi ya shige,,,,,,,,,{{}}

{{}} gwaggo sai zagaye gida take tana cewa wallahi Allah ya rufa maki asiri, kinga kiyi aurenki, ki huta, kai wannan yarinya da sa"ar rayuwar kike,{{}} tanayi tana "yar dariyarta, kana ji kasan dan wulaƙanci take abun,, {{}}

{{}} *zawarci* {{}}
*R*aihana tace umma wallahi da baba baya nan dana fita nayi ma gwaggo magana, ince ta fita harkata, umma tace ki barta tayi duk abinda taga dama, abinda mutum yayi mai kyau ko kishiyar hakan kanshi yayi ma,,,,,,,


*U*mma tace tashi muyi sallar isha"i ki ida man labarin {{}}

������
*zawarci*
��������
*D*ariya *raihana* tayi sannan ta ɗauki buta, alwalla tayo ta dawo ɗaki hijibinta ta saka sannan ta haye saman abin sallah,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER'S ASSICITION* ��✍�� ke maku fatan alkairi, ni *jameela musa* nake cewa ku kasance tare dani, ��💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*page* 9⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*


*R*aihana tana gama sallar isha"i, tana zaune a inda tayi sallar bata tashi ba, umma tace mata tunda kin gama ci gaba da bani labari, umma bata gama rufe bakinta ba, gwaggo ta yaye labulen ɗakin umma babu ko sallama tace, maza fito ga ango can mijin amarya yaxo, yana ƙofar gida yana jiran *raihana* farin cikin shi, ta ƙareshe maganar tana dariya,

*T*saki raihana tayi sannan tace bazanje ba, gwaggo tace ni kike faɗa ma haka?"" raihana tace an faɗa idan kinji haushi shima ki koreshi tunda dama kin saba ƙorama man samari,

Gwaggo tace wani in ƙori yusufa ace ina baƙin ciki?"" tana maganar tana taɓe baki, raihana tace ai dole yanxun kice haka tunda kinga shi ba aminu bane, gwaggo tace keji ɗiya yau kuma jarabar rashin auren naki a kaina zata ƙare?"""""

Rainaha tace dole ta ƙare a kanki tunda babu munafikar da ta kashe man aure sai ke, idanuwa gwaggo ta zaro sannan ta daki ƙirjinta da ƙarfi tace lallai yau naga sherrin rayuwa, raihana tace wallahi idanma har sharrin rayuwane baki ga komai ba, gwaggo tace to babu damuwa yanxun dai kije ga sabon miji yaxo, idan har kika yi auren banma kara zuwa gidan bare aja mani sharri,

Raihana tace zanje bisa cika umarni mahifina, tana faɗin haka ta miƙe tayi waje fuuuuuuuuu tunda dama hijabin da tayi salla bata cire ba, gwaggo tace shegiya mai baƙin hali ai gara dai a lallaɓa a aurar dake ga yusufa ko aikin gidan "ya"ya yasa ki ladafi, ɗiya tsaitsaye haka kamar an jika shinkafa da ruwan sanyi?"""" umma dai bata ce komai ba, haka gwaggo tayi ta wulaƙanci daga baya kuma ta nufi ɗakin ta,,,,,,,,


A ƙofar gida, raihana ta samu yusufa tsaye, yasha gayu fuskar nan ya nemi mai ya lafta mata sai ƙalli take, haƙoran nan nashi kuma dayaci goro suma sai yauƙi suke, haka raihana tabi yusufa da kallo tun daga tsakiyar kansa har ƙafafuwanshi,

Bayan ta gama kalleshi tsaf, ta dawo da duban ta daidai idon shi, suka kalli juna ido cikin ido, sannan tace sannu, ya yashe baki yace raihana raihana, tsaki raihana tayi sannan tace da Allah malam naji saƙonka, yanxun ka shirya auren *RAIHANA* ne?""""

Yusuf yace Eh darling, tsaki raihana tayi sannan tace to na baka daga yau zuwa jibi jibin nan, kaje ka haɗo man milayan biyar, idan har ka haɗo man su to lallai kaxo a ɗaura mana aure,

Idanuwa yusufa ya zaro sannan yace miliyan biyar fa kike magana?"""

Raihana tace Eh ba raihana kake so ba?""" yace Eh tace to madamar kana san aure na, sai ka kawo kuɗin nan idan kuwa ba haka ba, kada ka kuskura in sake ganin ƙafar ka a ƙofar gidan nan,

Ajiyar zuciya yayi zaiyi magana raihana ta ɗaga mashi hannu sannan tace ba wata magana tsakanin ni da kuma kai idan har ka kawo kuɗin to idan har baka kawo ba, bazan sake saurarenka ba, tana kaiwa nan tayi cikin gida..................

Yusufa yabi raihana da kallo har ta shige cikin gida, tana shiga ya ƙare ma gidan su raihana kallo yace lallai wannan yarinyar tama raina ma mutane hankali in banda iskanci ko ubanta bai taɓa ganin miliyan ɗaya ba amma shine har take cewa wani ya kawo mata miliyan biyar, tsaki yayi sannan yace zanga uban naki in faɗa mashi tunda shi mutumin kirki ne, haka yayi ta surutanshi shi ɗaya daga baya kuma ya tafi yabar ƙofar gidan.................

Raihana tana dawowa gida, ɗakin ummarta tayi sallama ta shiga, umma dake kwance har bacci ya fara fizgarta, tace har in dawo?""" raihana tace Eh, umma tace baima wani daɗe ba, raihana tace Eh, umma tace to ya kukayi dashi, murmushi raihana tayi sannan tace umma gaskiya nace mashi kawai ya turo, ta ƙarasa maganar tana taɓe baki, umma tace to Allah yasa hakan shine alkairi, murmushi raihana tayi sannan tace alkairin ma ne, umma tace to bara inje in sanar da babanku, raihana tace tou, tashi umma tayi ta fita daga ɗakin, tana fita raihana ta kece da dariya, sannan tace duk dani ake magana, idan har bazan koma gidan Aminu ba, haƙiƙa dai in su namiji mai tsafta in aura amma na auri yusufa haka ai ko dariyar ƙawaye ta hanani sakat, gyara ƙafafunta tayi sannan ta kwanta, da hannunta ta lalabu ta jawo wani tsohon zani ta lulluɓe, bata daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita...............


Umma bayan taje ɗakin baba ta faɗa mashi cewa raihana tace ma yusufa ya turo, baba yace to Alhamdulillah lamari yayi daɗi Allah ya tabbatar da alkairi, umma tace ameen, itama umma ɗakinta ta tashi ta nufo ta kwanta,



💦💦💦
*Zawarci*
💦💦💦

*T*unda safe raihana tana gama sallah gwaggo ta fito wai lallai yau gidan nan fa babu ruwa, saboda haka raihana ta fito ta tafi wurin mono ta samo masu ruwa, raihana dake kwance, saboda ta gama sallah ta kwanta ta huta gabanta ya faɗi,

Gwaggo ta iso ƙofar ɗakin tace ki fito ki samo mana ruwa nace gidan babu ruwa, raihana daga kwance tace bazanje ba, *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,* raihana saboda rashin mutunci ni kike zagi?"" kuma uwarki tana ji kina zagi na, har cewa take ki ƙara man, daga raihana har umma idanuwa suka zaro suna kallon gwaggo, taci gaba cewa saboda kawai nace ki ɗibo ruwa sai kawai kiyi ta zunguwara iyaye na zagi,

Wayyo Allah da mutunci na gidan nan tunda ɗiyar nan ta dawo take ɗura ma iyayena zagi, lallai yau basai gobe ba, zamana gidan nan ya ƙare, baba dake ɗaki ya fito yana tambayar ba"asi?"""

Kuka gwaggo take sosai tace raihana ce tun shekaran jira da tayi magana sai ta zageta kuma uwar tana ji saidai tayi dariya,

Baba yace ina raihanar take?"" umma ta fito daga ɗaki tace wallahi ba haka akayi ba, yace rufe man baki, umma tayi shiru baba ya kalli inda raihana take tsaye yace daga yau shine magana na ƙarshe nasha faɗa maki idan baki kiyaye ba, haƙiƙa zaki bar man gida kinji na faɗa maki, raihana tace tou baba insha Allah amma wallahi ban zage ta ba, baba yace koma dai miye keta shafa bani ba, maza kije ki ɗauka ki ibo mata ruwan, da kina gidanki zataje can ta kirawo ki?""" raihana tace tou, ɗaki ta koma ta ɗauko hijabinta, kofar ɗakinsu ta ɗauki bokitin ƙarfe, ta ɗauka tayi waje...............................

Raihana bayan ta fita, baba yace ma gwaggo kema banda masifa tunda safe sai kice yarinya saita ibi maki ruwa?""" gwaggo tace ai tuwo zan ɗora dan anjima gidan biki zani, baba yace to miyasa tun jiya ba"a samo ruwan ba?"" gwaggo tace saboda sirikina zai zo, kuma almajira ma idan ka kira basu zuwa, tsaki baba yayi sannan ya nufi ɗakin shi itama umma ɗakinta ta koma gwaggo kuma tabi baba ɗakin shi ta fara tattaro kayan shi da sukai datti........................




A madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ni *MEELAT MUSA* nake cewa ku biyoni ..........................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣0⃣

*AMEENCHI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*T*saye take a bakin mono ta jera layi da bokatin ta, ga ɗan sanyi sanyin asuba, Raihana ta buɗe idanuwanta duk wurin babu mace sai maza, baƙin ciki ko miye raihana ta tuna oho?"" kawai hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanuwanta, haka taci gaba da kuka tana gogewa da gefen hijabinta,

Kuka take tana matsawa da layinta idan an janye, haka kowa yaci gaba da ibar ruwa har layi yazo kanta, haka ta matsa ta tara nata, ta koma ta fara bugawa, har bokatin ya cika, tazo ta janye ta ɗauka ta nufo gida tana mai nadamar wannan *zawarci*

Sallama raihana tayi ta shiga cikin gida, a ƙofar ɗakin gwaggo taje ta ajiye ruwan, har zata juya gwaggo tace yawwa ga kayan babanki nan sunyi datti sai ki siyo sabulu da ruwa ki wanke, raihana tace sabulu da ruwa kuma?"" to a ina zan samu kuɗin siye?"""

Ggaggo tace cikin kuɗin da kikai wanki jiya?""" murmushi raihana tayi sannna tace to Alhamdulillah Allah ya ƙara rufa mana asiri, gwaggo tace Allah ya tona maki asiri raihana muje abinda kike boyewa, raihana tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un Allah dai ya tona maki asiri gwaggo ni kuma nawa ubangiji ya rufe man shi,

Gwaggo tace lallai raihana iskancinki kullum gaba yake, yanxun nan ubanki yayi man tsakani dake amma shine dai baza ki fita hanyata ba?"""

Raihana tace nima idan har baza ki fita tawa ba banga abinda zai fitar dani taki ba saidai a raba gidan nan, dani da ummana daban ke kuma dake da baƙin halinki,


Wannan magana tayi ma gwaggo ciwo saboda haka ruwan da raihana ta ibo ta ɗauko bokatin ta kwarara mata su duka a jikinsu, sannan ta ɗaga bokitin taci gaba da kwaɗa ma raihana,

Raihana sai kuka take tana faɗin a taimaketa gwaggo zata kasheta, baba da bacci ya fara ɗauka da sauri ya fito tsakar gida, amma umma duk abinda ya faru tana ji , amma bata ce ta tafasa bare a shiɗe, kuma haka bata fito tsakar gidan ba,

Baba yazo ya riƙe bokitin sannan yace ma gwaggo wai wannan wane irin masifa ne?""" gwaggo cikin shashsheka ta alamar gajiya kamar wanda tayi gudu sosai, tace tun da safe ɗiyar nan take zungurawa sale mai kanwa zagi, baban gwaggo kenan, taci gaba da cewa kuma idan mutum yayi magana a bashi rashin gaskiya,,,,,

Inda raihana take tsaye tana kuka baba ya kalla wanda duk gwaggo ta farfashe mata kai, baba yace ke kuma baki zaunuwa wallahi, baba na faɗin haka raihana bata sake bi ta kanshi ba tayi ɗakin umma,

Baba yabi ta da kallo, ita kuma tana shiga ɗakin ta fashe da kuka tace umma saboda Allah ni babu mai goya man baya?"" baba kullum bayan matarshi yake bi, umma tace kema da a gidanki kike ai mijinki zaibi bayanki ne, raihana tace Allah yaman sakayya umma dai batace komai ba, ita kuma raihana zama tayi sai Allah ya isa take yi,

Daga baya umma ta fita daga ɗakin, ita kuma raihana zama tayi taci kukanta ta ƙoshi, saida ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta, ta kwanta wani wahalallan bacci yayyi gaba da ita,,,,,,,,,,,


*zawarci*

Ƙarfe 12:30pm raihana ta farka daga bacci, fitowa tayi tsakar gida, a ƙofar ɗakin umma taga wani tashin wanki, an kawo mata, inda gwagg take ta kalla, ita kuma gwaggo surfe take k uwarmi take surfawa oho?""""

Kanta ta dafe da yake mata wata irin sara, dafe kan tayi sannan ta duƙa ta ɗauki buta ta nufi bayi, { *toilet* } tana fitowa ta nufi inda suke sanwa ta fara bubbuɗe kwanuka, gwaggo uwar mi kike nema?"" ko inda take raihana bata kalla ba, taci gaba da buɗe buɗenta, dariya gwaggo tayi ta dakata da dakan da takeyi, ta ɗora guwar hannunta kan taɓaryar dake cikin turmi, sannan ta tallafe fuskarta da tafin hannun ta, tace yarinya babu abinci, sai kinsan matsayi na a gidan nan sannan zaki fara cin abinci, murmushi raihana tayi sannan tace aikin banza kare da gudun layya, tana kaiwa nan tayi ɗakin umma, gwaggo tace saida a mutu da yunwa""" raihana dai bata sake magana ba, ta koma ɗaki madubi ta ɗauko tana kallon yanda gwaggo taci ma fuskarta mutunci,

Allah yayi man sakayya haka rainaha kawai ta faɗa , ta koma ta kwanta, wani bacci wahalar ya ƙarayin gaba da ita,,,,,,,,,,


💦💦💦
*zawarci*
💦💦💦

*R*aihana tashi kiyi sallah mana, umma ce take tashin raihana , a gajiye raihana ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauhi, hawayen wahala suka fara safa da marwa a idonta, umma tace ki tashi kiyi sallah nace, a daidai lokacin da umma take cire hijabin jikinta,

A gajiye raihana ta miƙe ta fito, buta ta duƙa ƙofae ɗakinsu ta ɗauka, gwaggo sai habaici take, tsaki raihana tayi sannan tace idan dai kare yana haushi idan bai samu aboki ba ya zama mahaukaci, gwaggo tace uwarki waccan tana nuna ɗakin su to itace mahaukaci, kuma itace karya, dariya raihana tayi sannan tace ga irin halin nan kinayi , gwaggo tace shegiya mai baƙin hali, raihana tace ai a turbar kika ɗrani tun ina yarinya,

Gwaggo tace zawarar banza, raihna tace , Allah ya kaddara man kuma kema dake da ahalinki Allah ya ɗora maku jawarci kuji abin idan daɗi ne,

Gwaggo tace ni kike cewa "ya"yan na zasui *zawarci*? Tsaki raihana tayi , bata sake magana ba ta fara alwalla,

Gwaggo sai masifa take, ala dole wai raihana tace za"a sako mata "ya"ya daga gidan aure, taci gaba d cewa ke kaɗai kika zamo haka kuma kece kaɗai zaki lalace haka , a daidai lokacin da raihana ta gama alwalla tace tare dai zamu lalace mai faɗa da ɗiyar cikin ta, ki kashe mata aure dan ki aura ma ɗiyar aminiyarki, sai Allah ya maki abinda baki zato, tana faɗin haka ta shige ɗakin su,


Gwaggo kuma taci gaba da cewa anje an kashe aure uban waye yasa tun farko baki san mijin,?"" kuma har ki mutu baza ki samu wanda yakai darajar aminu ba, yar banza lalata,

Raihana dai bata sake magana ba, gwaggo ko banda tsinuwa da la"ana babu abinda take yi,,,,,,,,


Bayan raihana ta gama sallah , uma tace mata ga abinci can badiyya ta aiko maki dashi, kuma tace zata kawo maki wanki idan Allah ya kaimu, raihana tace tou, ɗauko abinci tayi ta matsa kusa da uma tace suci, ua tace ta ƙoshi, haka raihana ta caka hannu ta fara cin abincin,

Tana cin abinci umma tace raihana, kada ki kuskura ki sake cewa gwaggo ta kashe maki aure, abincin data ibo zata kai bakinta ta fasa kaiwa, tace umma wallahi itace ta kashe man aure, umma tace haka Allah ya ƙaddara kada ki kuskura ki sake faɗin haka kinji na faɗa maki ko?"" raihana tace Eh, umma tace gama cin abinci yau ki ƙarasa man labarin nan, murmushi raihana tayi tace to,


Haka tayi ta cin abincin bayan ta gama, ta fita ta wanko hannunta ta dawo, maganin da umma ta siyo mata ta miƙa mata, bayan tasha maganin ne, tace umma zan fara murmushi raihana tayi sannan taci gaba da cewa...........................




*MEELAT MUSA* ke cewa ku kasance tare dani!!!
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣1⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*H*ar yanxun yana zaune inda raihana ta barshi a farlo , ya ɗan zame saman kujera ya kwanta, lallai wannan wane irin fitina ne?"" yana da mata amma shida babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tsaki yayi ya miƙe ya nufi ɗakin shi,

Yana zuwa babu ɓata lokaci wanka yayi ya shirya ya fito fess abunshi , ɗakin raihana ya dawo, bayan ya shiga ya sameta kwance saman gado, shima saman gadon ya hau, da sauri ta matsa da baya, hannunshi yasa ya jawo ƙafarta zuuuu ya matso da ita kusa dashi,

Saman ruwan cikinta ya hau, ya matsar da fuskarshi kusa da tata, daidai bakinta ya ɗora nashi, idanuwanshi suna kallon nata, sannan yace wallahi kiji tsoron Allah idan har kika kuskura a wannan halin kika mutu zaki haɗu da fushin Allah nine mijinki so da kauna yasa na aureki ki baki sona raihana ya kamata wani abun ki riƙa ragewa saboda rayuwa,

Wai miyasa ma baki sona?""" shiru raihana tayi saboda bata da dalili, riƙo haɓarta yayi da hannu, ya haɗa bakinshi da nata, da sauri ta fizge bakinta ta jawo wani kallabi ta goge bakinta , dariya yayi yace kyamata kike?""" raihana tace bana kyamarka nidai kawai bakai man ba,

Yace miyasa ban maki ba?""" a daidai lokacin da ya sauka daga saman jikin ta, raihana tace nifa ban taɓa ganinka ba, duka sau nawa na ganka aka ɗaura mana aure dakai?""" Aminu yace to miye aibuna?"" raihana?"" ya ƙarashe maganar yana kwantar da kanshi yayi yanayin tausayi,

Yace kiji tsoron Allah , ubangiji yana fushi da matar da take ma mijinta irin abinda kike man, ki daina abinda kike tun kafin ki haɗu da fushin Allah,

So nawa aka aurar da mace ga namijin da bata taɓa gani ba?"" kuma suna zamansu hankalinsu kwance, kiyi haƙuri ki soni kinji raihan?""" wallahi zan jiyar dake farin ciki?"" ya ƙareshe maganar hawaye yana bin fuskarshi,

Ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace to kayi haƙuri duk abinda nayi maka insha Allah bazan sake ba, yace yawwa ko kefa?""" haka yayi ta mata nasiha, raihana tanajin nasiha tana bin jikin ta, amma fa har yanxun baiwai dan tana san Aminu ba, kawai saboda yana faɗi nata nau"in azabobin da Allah zaiyi ma wanda bata biyayyar aure yasa jikin ta yayi sanyi,,,,,,,

*** *** *** ***

*B*ayan haka da sati biyu, wata rana gwaggo ta kawo ma raihana ziyara da ita da aminiyarta *Ladi* raihana tayi farin ciki da zuwansu sosai sabida haka taje ta kawo madu ɗan abun ci da sha, bayan sunci sunsha, gawaggo tace raihana niko na ganki duk kinyi baƙiƙirin kin rame,

Murmushi raihana tayi sannan tace babu wani abu da nayi gwaggo, kawai dai dan kin daina gani na kike ganin haka, ta ƙarasa maganar tana taɓe baki, gwaggo tace to ya zaman naku yake?""" raihana tace *alhamdulillah* gwaggo tace amma gaskiya yaron nan yana cutar dake, raihana tace babu wani cutuwa muna zaune lafiya,

Gwaggo tace ai kece kike zaune lafiya dashi shi kwata kwata baya kaunarki, cewa yake daya samu yayi maki ciki zai sakeki ya auro wata, tunda dama baki sanshi, raihana ta ɗago ta kalli gwaggo cikin zaro idanuwa, raihana tace a,a, gwaggo Aminu bazai man haka ba, gwaggo tace baza ki gane ba, aike yarinya ce, tashi muje ladi, har yanxun akwai kuruciya a kanta,

Raihana tana ganin gwaggo ta mike tace gwaggo tsaya, gwaggo tace ai ina faɗa maki gaskiya bakya gani ne, raihana tace ni wallahi yana so na, kuma har kuka yake saboda yanda yake kauna na, gwaggo tace yaudara ce, ba sanki yake ba, raihana tace tou Allah dai ya sawaƙe, gwaggo tace amin, haka suka rantafa ita da ladi suka bar gidan...............

Fitar gwaggo da larai basu zame ko ina ba, sai gidan uwar mijin raihana, bayan sun gaisa gwaggo tace kin gane ni?""" maman Aminu tace na ganeki mana, gwaggo tace dama maganar yarinyar nan ne, dama maman Aminu bata san raihana, tunda taji labarin bata kaunar Aminu taji kuma tace itace ajalinsa, wannan dalilin yasa ta tsani raihana,,

Gwaggo tace dama cewa nayi tunda dai har yanxun naga ta kasa haƙura su zauna lafiya ɗiyar ƙawata na kawo dama ki haɗasu suyi aure, ita dama tana kaunar Aminu , tana sanshi tun tuni, maman Aminu tace to ai dama ya kwana da sannin bana kaunar yarinyar nan dole ya rabu da ita tunda ba tare aka haifesu ba,

Haka gwaggo taci gaba da zuga maman Aminu, daga baya suka tashi suka tafi daga gidan,

Suna fitowa gwaggo tace k sai in bari ta zauna a gidan can?"" duk tafi su bushira gidan miji, wato ɗiyarta kenan, da sauran "yan uwanta, tace shegiya sai ta fito wallahi, kuma babu ita babu ƙara auren mai kufi saidai ta samu talaka ta aura, haka sukaci gaba da magana suna kulla makircin su, daga baya suka rantafa suka nufi gida.................................,


Raihana zaune a gaban Aminu,