AKIDUN ZAMANI: Shin ya dace mace tai aikin ofis.
Author/arewainfinit
Date/7 sep 2018
Akidun Zamani, tare da Fatima Zahra Umar, wani sabon fili ne inda za ku riƙa karanta ƙasida guda duk a mako kan batutuwan da suka shafi mata, masu daɗi da marasa daɗi. Manufar wannan filiita ce samar da wata dama don duba matsalolin da ke damun mata da kuma zaƙulo hanyoyin warware su. Sannan kuma za mu riƙa gabatar da tattaunawa a kan batutuwan da wannan fili ya taɓo a rediyo. Batun da ƙasidarmu ta yau ta yi nazari a kai shi ne "Matsayin mata masu fita aiki".
Mata masu aiki sun fi samun 'ya'ya masu ilimi, masu nutsuwa, kuma masu kokarin neman ci gaba. Na san haka batun yake, domin ni ma haka nake.
Akwai alfanun samun uwa ko mata mai yin aiki. Abin dubawa a nan shi ne idan wani abu ya samu maigidan (kamar mutuwa, rashin lafiya ko ya rasa aikin yi), ita matar ko uwar tana iya daukar nauyin gidanta, ba tare da ta zame wa kowa alaƙaƙai ba
Mutane da yawa suna ganin cewa mace bai kamata ta yi aiki ba, musammam ma idan tana da 'ya'ya. Masu wannan ra'ayin na ganin cewar matar da ke yin aiki na iya watsar da babban nauyin da ke kanta - na zama matar gida ko uwa, wanda abu ne da zai iya janyo mummunan tasiri ga gidanta.
Yawancin mutane na ganin cewa idan mace na yin aiki a wani wuri, yaranta ba za su samu kulawar ƙwarai ba. Mutane kuma na ganin cewa fitar da matar aure ke yi ka iya sanya wa idonta ya buɗe, wanda a ganinsu zai iya ɓata martabarta da ta 'ya'yanta.
Abin da ya kamata mu tambayi kanmu shi ne, shin aiki a wajen mace na iya ɓata tarbiyyar 'ya'ya, ko ya ɓata dangantakarta da mijinta?
Duk da yake, wasu daga cikin wadannan batutuwan haka suke, amma yawancin lamarin al'ada ce kawai. Wasu al'adun kan sa mu rasa ɗumbin alfanun samun mata a ma'aikatu.
A misali, ka ga ba mu da likitoci mata masu yawa a asibitocinmu. A matsayina na mace, ba ko yaushe nake son likita namiji ya duba ni ba, amma na san matan da suka kammala karatun likita, kuma suna gida zaune, ba sa yin aiki. Kawai don maigidan ba ya son ta rika cudanya da maza, amma kuma ya fi son likita mace ta duba matarsa idan ta je asibiti.
Dukkanmu mun san ƙissar Sayyida Khadija (RA) uwargidan Annabi Muhammad SAW. Sayyida Khadija babbar 'yar kasuwa ce, lokacin da ta auri Annabi SAW. Amma duk da yake ita ce uwargidansa ta fuskar kasuwanci (a matsayinsa na hadiminta a wajen kasuwancinta), ta kasance uwa kuma matar gida abar alfahari ga kowa.
Abin har ya kai ga shekaru bayan rasuwarta, Annabi Muhammad SAW yakan yi maganarta cike da martabawa, da soyayya. An ruwaito cewa sauran matansa sun rika kishinta saboda irin yabonta da yake yi.
Abin da nake son nunawa a nan shi ne babu wani dalilin da zai hana mace yin sana'a ko aiki, musammam mace mai nutsuwa da kamun kai.
Zuwa wajen aiki bai zama sanadin rasa mutuncinta ba, domin wannan ya shafi irin halin matar ne tun ainihi. Mata masu yawa sun samu nasarar hada aiki da rike gidansu ba tare da sun zubar da mutuncinsu ba... wannan manuniya ce cewa batun na alaƙa da karfin hali da jajircewa da kuma tarbiyya.
Babban ƙalubalen mata masu aiki ke fuskanta shi ne na tabbatar da ganin sun ba kowanne ɓangare haƙƙinsa.
Yaya za mu iya tabbatar da mun tafiyar da ayyukanmu, kuma mun ba 'ya'yanmu tarbiyya ta gari? Yaya za mu yi adalci tsakanin yin aiki ko sana'a da kula da gida?
Amsar mai sauki ce, muna bukatar mazajenmu su ƙara tallafa mana. Domin babu inda aka ce aikin kula da 'ya'ya da kuma ba su tarbiyya na mace ne ita kaɗai.
Ina kira ga maza magidanta da iyaye maza su ƙara taimaka wa mata wajen kula da gida da kuma 'ya'ya, su taimaka mana wajen sana'o'inmu kuma su yi alfahari da abubuwan ci gaba idan sun same mu.
Manzon Allah SAW ya yi, me zai hana kai ma ka yi?
Ga Fatima Zahra Umar da baƙin da ta gayyata don tattanawa a kan wannan batu