Majalisun Nijeriya Sun Gindaya Wa Shugaba Buhari Wasu Dokoki Guda 12
...idan bai bi ba za mu dauki mataki, cewar majalisun
Majalisun dokokin Nijeriya sun amince da wasu kudurori 12 da suka ce wajibi ne gwamnatin Muhamadu Buhari ta aiwatar da su ko kuma su dauki mataki.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya karanta matsayar da suka cima bayan wani zama na musamman da suka yi domin duba halin da kasar take ciki, wanda wasunsu suka ce yana ci gaba da tabarbarewa.
Ya ce majalisun biyu sun amince cewa wajibi ne Shugaba Buhari ya dauki alhakin abubuwan da mutanen da ya nada suke yi, sannan ya dauki mataki kan duk wanda ya saba wa doka da yin barazana ga demokuradiyya.
Suka kara da cewa wajibi ne jami'an tsaro su tunkari kashe-kashen da ake yi a kasar, sannan a daina takura wadanda ake wa kallon 'yan adawa ne ko kuma masu bambancin ra'ayi da bangaren zartarwa.
"Majalisa ba za ta yi wata-wata ba wurin daukar mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu domin aiwatar da wadannan kudurori da aka a mince da su yau (Talata)".
Wannan zama na zuwa ne a lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shugabannin majalisar.
Kudurori 12
*Kawo karshen kashe-kashe a NajeriyaA daina tsangwama da kuma muzguna wa wadansu 'yan majalisa
*Gwamnati ta rika bin doka da oda
*Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai
*Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah
*Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka shafi majalisar
*Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya don ceto demokradiyyar Nijeriya
*Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya don ceto demokradiyyar kasar
*Shugaban kasa ya magance matsalar rashin aikin yi da kuma talauci a kasar
*Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara
*Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na 'yan sandan Nnjeriya Ibrahim Idris
*Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu.
Wadansu na ganin barazanar daukar matakin da tsarin mulki ya ba su kamar yadda suka yi ikirari zai iya hada wa da yunkurin tsige Shugaba Buhari
A ranar Litinin 'yan sandan kasar suka gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki domin amsa tambayoyi kan zargin daukar nauyin 'yan fashi da makami a mahaifarsa ta jihar Kwara.
Sai dai daga bisani Sanata Saraki ya ce sun shaida masa cewa sun janye gayyatar, kawai suna bukatar "ya amsa ne a rubuce".
Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun fasa ganawa da OsinbajoAPC ta sha kaye a hannun PDP a zaben jihar Oyo
Rahotanni sun kuma ce an rage yawan jami'an tsaron farin kaya da ke bin tawagar Saraki da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da kuma mataimakansu.
Wannan batu ne kuma ya sa kungiyar tsoffin 'yan sabuwar PDP, wacce Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ke kan gaba a ciki, suka ce sun dakatar da tattaunawar da suke yi da gwamnatin kasar da kuma jam'iyyar APC.
Suna dai zargin cewa an mayar da su saniyar-ware ne tare da yi musu bi-ta-da-kulli, a gwamnatin da suka taimaka aka kafa.
A baya dai gwamnatin ta sha musanta wannan zargi.