Zan So Ace Matan Kannywood Su Fara Fallasa Mazan Da Su Ka Yi Lalata Da Su – Rahama
A kwanakinnan jaruman fina-finan Kasar Amurka mata sun fito da wani mataki da suka wa lakabi da Metoo wanda suke fallasa masu shirya fina-finai da kuma wasu manyan jarumai maza da suka yi lalata da su ba da son ransu ba dan su saka su a fim. .
Abin bawai kan jaruman fim kadai ya tsaya ba hadda mawaka da wasu kadan daga cikin al’ummar gari.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi fatan cewa zata so ace suma a masana’antar fina-finan Hausa su kwaikwayi irin wancan tsari.
Rahama ta jinjina maganar, watau inda da za’a yi hakan ‘ Tabdijam!!!’
Sani Musa Danja Zai Auri Priyanka
Chopra Ta Kasar India A Karshen
wannan Shekarar. Ali Nuhu Ya Fito
Acikin Wani Sabon Film Din INDIA
Shida Aamir khan, Rani Mukharjee, da
Saf Ali khan.
* Alakar India da Nigeria zata kara kulluwa
Bayan hadin kai da Nigeria da India suke dashi tawajen yin film,jarumin kannywood zai Auri daya daga cikin jarumai na India,Inda ake ganinhakan zai kara kulla Alaka babba tsakanin India da Nigeria
Shahararren Jarumin nan na Kannywood, Nuhu Adullahi ya kasance daya daga cikin yan wasan da suka shiga farfajiyar shirya fina-finan da kafar dama.
Cikin dan kankanin lokaci da shigarsa harkar jarumin ya samu tarin daukaka da nasarori inda har yayiwa wasu da riga shi shiga harkar zarra. A wata hira da jarumin yayi da jaridar Premium time ya bayyanawa duniya irin son da yake yiwa jaruma Fati Washa kuma har ya jaddada cewan shi zai iya auren ta. Da aka tambaye shi jarumar da ta fib urge shi a masana’antar yace: “ Fati Washa a koda yaushe itace zabina bazanyi nadama ba inma furta cewa ina sonta.” Ina son Fati Washa kuma zan iya aurenta – Nuhu Abdullahi Jarumin ya kara da cewa ita din ta musamman ce,ta kasance tana kyautata min tabbas zan iya yin komai dan ganin nima na kyautata mata dan tana da saukin kai ga girmama manya.
LATEST EPL 2018-19 HAUSA NEWS POLITICS GOSSIP CELEBS ASK NAIJ SPORTS Kiri da muzu: Bidiyon Gwamnan Kano yana cusa kudin rashawa a babbar riga Ina son Fati Washa kuma zan iya aurenta – Nuhu Abdullahi Author: Aisha Musa UPDATED: 4 MONTHS AGO VIEWS: 25973 Category: Labarai, Labaran Kannywood Shahararren Jarumin nan na Kannywood, Nuhu Adullahi ya kasance daya daga cikin yan wasan da suka shiga farfajiyar shirya fina-finan da kafar dama. Cikin dan kankanin lokaci da shigarsa harkar jarumin ya samu tarin daukaka da nasarori inda har yayiwa wasu da riga shi shiga harkar zarra. A wata hira da jarumin yayi da jaridar Premium time ya bayyanawa duniya irin son da yake yiwa jaruma Fati Washa kuma har ya jaddada cewan shi zai iya auren ta. Da aka tambaye shi jarumar da ta fib urge shi a masana’antar yace: “ Fati Washa a koda yaushe itace zabina bazanyi nadama ba inma furta cewa ina sonta.” Ina son Fati Washa kuma zan iya aurenta – Nuhu Abdullahi Jarumin ya kara da cewa ita din ta musamman ce,ta kasance tana kyautata min tabbas zan iya yin komai dan ganin nima na kyautata mata dan tana da saukin kai ga girmama manya. KU KARANTA KUMA: Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki Jaridar ta kara yi masa tambaya da cewa meyasa ka zabi Fati Washa ita kadai acikin duk ‘Yan matan Industry,Sai yace “kamar yadda na gaya maka bazan iya bayyana maka yadda make jiba. “Amma ina matukar mutunta ta duk da ina da kawaye irin su Rahama Sadau da sauran su." Da aka tambaye shi ko zai iya auranta yace: “Tabbas in haka ta faru zanji dadi,in mutum ya kyautata maka zaifi kyau shima ka kyautata masa.” Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai
Kalli jerin yan wasa 7 da muke sa ran cewa zasu maye gurbin fitattun jarumai a 2018
Manyan gobe da zasu zama idon jama'a a masana'antar nishadantarwa ta kannywood cikin 2018
Jaruman "Mansoor" Maryam Yahaya da Umar M.Sheriff
Hakika masana'antar Kannywood ta samu farin jini da daukaka sanadiyar ire-iren damar da take baiwa masu basirar yin waka ko fitowa a wasan kwaikwayo.
Wannan dandalin ta cigaba da bunkasa martaban arewan ta hanyar wasanni don nishadantarwa da fadakar da jama'a da labarurruka masu kayatarwa.
A cikin shekara ta 2017 Kannywood ta samu canji ko kuma ince ta fara sauya yadda aka saba ganin fina-finan ta sanadiyar kaddamar da tsarin Box office wanda zai taimakawa wajen haska fina-finai a sinimomi da gidajen kallo.
Shahararren jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera, ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe kwanaki suna "gaba".
Sakon Adam Zangon ya ce "tuba nake sarki gwiwowina a kasa".
Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya wallafa a shafinsa na Instagram.
SABON FILM DIN HAUSA MAI SUNA TRAILER(WASIYA) ON 2018
SHIRIN YAYI MATUKAR KYAU
YADDA JARUMAI SUKA TAKA RAWA ACIKIN SA
KAMAR
-ALI NUHU
-MARYAM YAHAYA ETC
AUTHOR AREWA INFINIT
DATE 5 SEP 2018
FIM DIN ‘IN SEARCH OF THE KING’ YA SAMU GOYON BAYAN MASARAUTAR RINGIM.
AUTHOR/AREWAINFINIT
A farkon watan nan na Yuli aka shiga aikin wani fim na turanci mai suna In Serach of the King, wanda yake ba da tarihi da yanayin masarautar Kasar Hausa tun tsawon shekaru masu yawa da suka gabata. Duk da cewar fim ne da aka yi shi da harshen turanci amma idan ka dauke yaren na turanci da aka yi amfani da shi, to duk wani abu da aka nuna a fim din yana nuna ydda tsarin rayuwar masarautar kasar Hausa take ta fannin al’adu, ilimi, mulki da mu’amalarsu ta yau da gobe. Wani abin birgewa game da wannan fim din kusan za a iya cewa shi ne fim na farko da aka nuna yadda Sarautar kasar Hausa take a zahiri, ba wai kwaikwayo ba. Domin kuwa an yi amfani da gadon sarautar Ringim ne inda Sarkin na Ringim dake jihar JIgawa ya amince a yi aikin fim din a masarautarsa kuma ya bayar da aron duk wata fada da ake bukata domin gudanar da ikin fim din. Kuma ya ba da mutanesa da suka rinka kula da aikin don su tabbatar an bi tsarin sarautar ba tare da an yi mata kutse ba, kamar yadda aka saba yi a sauran finafinan da ake yi a Kannywood. Fim din dai labarin masarautu ne masu karfi har guda uku a kasar Hausa kuma Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Abba Almustapha suka fito a matsayin sarakuna. Sai Nafisa Abdullahi da ta fito a matsayin Gombiya kuma jarumi mai tasowa Abdullah Amdaz ya fito a matsayin Yarima. Kabiru Musa Jammaje shi ne ya dauki nauyin shiryawa. Ganin yadda fim din ya samu amincewa ga masauratar Ringim har aka yi aikin a cikin fadar, mun tambayi jagoran shirin Malam Kabiru Jammaje a game da matakan da suka bi har suka samu amincewar masarautar da kuma yadda aikin ya gudana. Inda ya shaida mana cewar, “Tun da farko ma dai da muke yin aiki a kan rubuta labarin, gaskiya ba mu dauka za mu je har Ringim domin yin aikin ba, saboda a tunaninmu za mu samu wajen da za mu yi aikin a kusa, sai ya zama mun je gurare da dama amma sai muka ga bai yi mana yadda muke so ba, don haka sai aka kawo shawarar a tafi wajen Sarki Ringim za a iya samu. Don haka da muka je muka yi gaisuwa kuma sai muka ba da takardar neman izini ta a ba mu dama mu yi amfani fa masarautar don gudanar da aikin, kuma abin farin ciki suka nuna goyon baya suka aiko mana da takardar amincewa ta hannun Danmajen Ringim. Kuma wani abu a ya zo mana bazata wanda ya kara inganta mana aikin shi ne yadda masarautar ta ba mu mai kula da mu ya kasance tare da mu wato Yariman Ringim. Don sun ce suna kallon finafinai da ake yi na sarauta, amma ba a nuna masarautu yadda ya kamata, don haka tun da a masarautarsu za a yi ba za su zuba ido su ga an murguda yadda tsarin masarauta yake ba, don haka ba biyan su muka yi ba sune suka ga dacewar yin hakan, don suna daukar cewar wani nauyi ne a kansu musamman da muka nuna musu cewa fim din za a yi shi da turanci ne kuma zai shiga kasashen Turai da ma wasu nahiyoyi na duniya, don haka suka ga hakkinsu ne su tsaya su tabbatar an yi tsarin sarautar da ta shafi Arewacin Najeriya yadda ya kamata. Kuma na gamsu sosai da tsayawar tasu domin kuwa da an bar mu da kanmu da mun yi kurakurai. Saboda hatta yadda Sarki yake zama da kafar da zai kada da yanayin yadda yake magana da saka kaya duk sai da suka nuna mana don ko rawani ma sune suka daura wa Sarki da Galadima da Waziri da Shamaki, don kowa da yanayin yadda yake rawaninsa. Don shi da kansa Yariman wato dan Sarkin ya ce fim din duk wanda ya kalle shi in dai ya san tsarin sarautar to ya san an bi tsarin yadda ake gudanar da ita. Don sarauta aka nuna ta sosai ba ta wasan kwaikwayo ba, kuma gaskiya an samu canji sosai. Ya ci gaba da cewa, “Duk fim din ya kunshi masarautu ne guda uku masarautar Tumashe wadda Sarkinta shi ne Abba Almustapha, sai masarautar Gwani da wadda Yakubu Muhammad ne Sarki sai masarautar Salbana da Alinu Nuhu ya zamo Sarki. Kuma a yanzu mun fara ne da masarautar Salbana a garin Ringim, yanzu abin da ya rage mana sune sauran masaautu guda biyu ta Gwarida da kuma ta Kumashe. Saidai su ba a garin Ringum din za a yu su ba, za a yi su ne a garin Kano da kuma Danbatta.” Sai dai ganin yadda Masarautar Salbana ta samu kulawa daga masarautar Ringim, kasancewar sauran masarautun ba a can za a yi su ba, ko su ma za su samu kulawa daga masarautar? Sai Jammaje ya ce, “Lallai mun yi magana da Yariman kuma ya tabbatar mana cewar duk da ba a garinsu ba ne zai zo da kansa a yi komai a gabansa. Don haka muna godiya a gare shi da kuma masarautar Ringim bisa gudunmawar da suka ba mu.”
Shi ma Daraktan fim din Balarabe Murtala Baharu ya shaida mana cewar, “Ni abin da zance na amfana da shi a fim din In Search of the King duk fim na duniya idan za a yi ana karuwa da Darakta ne daga irin yadda yake gudanar da aikinsa, amma a wannan fim din ni na kara ilimi saboda irin abin da aka zo da shi na nuna ka’idar yadda sarauta take zaman fada, mu’amala, maganganu, sanya tufafi da yadda ake zama. Ni a rayuwata ban taba tunanin haka fada ake ba, don haka a matsayina na mai ba da umarni na karu sosai kuma kalubalen da na fuskanta ban taba yin aiki ina tare da masu ba da umarni har guda hudu ba sai a In Search of the King. Wanda yake kula kalmomin da ake firtawa daban, wanda yake kula da kayan da ake sakawa daban, wanda yake lura da zaman da ake yi daban. Sannan wadanda suke kula da aikin da ni kaina nake yi daban. Don haka wannan fim din ya zama zakaran gwajin dafi. Kuma abin da ya fi saka ni farin ciki da shi mai fim din ya ce shi a shirye yake da ya sake linka wani kudin da ya yi wa fim din kasafi domin a samu aiki mai inganci don bin diddigin da ake yi wa fim cin bai sa shi ya karaya ba, kuma ya yarda fim din da aka ce za a yi sati biyu, ya amince ya kai sati 4 ma ana yin aikinsa. Don haka wannan ba karamar nasara ba ce. Kuma daman abin da muka rasa a cikin finafinanmu kenan shi ya sa za ka ga ana samun kurakurai, domin ka ga a cikin wannan aikin namu akwai rana guda da ta zamo sin daya kawai muka dauka saboda bin tsari na ya kamata a dauke shi daidai yadda mai kallo zai dauke shi ya kalle shi a matsayin gaske ne ake yi shi ba wasa ba.” Nafisa Abdullahi ita ce jarumar da ta fito a matsayin Gimbiya a fim din, ta bayyana cewa, “Duk da cewar wannan fim din ba shi ne na farko da nake fitowa a cikin sarauta ba, to shi wannan ya zo mini da siffa ta daban, kasancewar sa na Turanci. Don haka a nan zan iya cewa In Search of the King ya bambanta da sauran finafinan da na saba fitowa, kuma aikin ya burge ni sosai don na ji dadinsa.” Shi ma jarumin fim din Abdullahi Amdaz wanda ya kasance fim din ne na farko a gare shi da ya zamo babban jarumi, ya shaida mana cewar, “Na yi farin cikin kasancewa a matsayin jarumin wannan fim din, “Duk da cewa shi ne fim na farko da na zamo babban jarumi a cikinsa. Don haka sai na ji a zuciyata zan yi kokari na yi duk wani abu da zai ba da fa’ida kuma ya fito da kima da darajar aikin. Na fito a matsayin Bello da ya ke yawo a tsakanin masarautu guda uku domin neman cimma wani burina kuma a hakan na samu kaina a yanayi kala-kala don na samu na yi.” Zuwa yanzu dai an kammala kashin farko cikin kashi uku na fim din har an tafi hutu, sai a watan Oktoba za a ci gaba da kashi na biyar da na uku a garin Kano da kuma Danbatta. Fim din dai ya kunshi jarumai masu yawan gaske da suke aiki a cikin fitattun ‘yan Kannywood akwai Ali Nuhu, Abba Almustapha, Yakubu Muhammad, Nafisa Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Rukayya Dawayya, Shehu Hassan Kano, Shu’aibu Yawale, Tijjani Faraga da sauransu.
ASABE Madaki, jarumar fim din ‘There is a Way’ da kuma sabon fim din ‘Sarauniya’, ta bada shawarar cewa ya kamata mu yi finafinai da Turanci don mu bada labarin al’adar mu da kan mu. Haka kuma ta fadi yadda a matsayin ta na lauya ta maida hankalin ta ga fitowa a finafinai.
Asabe kwararriyar lauya ce wadda ta ke da matsayin digiri na biyu kuma a yanzu ta na koyarwa ne a bangaren karatun aikin lauya din. Sai dai duk da matakin da ta kai na karatu da aiki a halin yanzu ta samu kan ta a cikin harkar fim, har ma ta fita a finafinai masu dama a Kannywood. Kwanan baya, wakilin mu ya hadu da Asabe a wajen daukar wani fim na Turanci mai suna ‘This is the Way’. Fim din ya na cikin jerin finafinai na Turanci da Kabiru Musa Jammaje ya ke shiryawa.
ASABE Madaki, jarumar fim din ‘There is a Way’ da kuma sabon fim din ‘Sarauniya’, ta bada shawarar cewa ya kamata mu yi finafinai da Turanci don mu bada labarin al’adar mu da kan mu. Haka kuma ta fadi yadda a matsayin ta na lauya ta maida hankalin ta ga fitowa a finafinai.
Asabe kwararriyar lauya ce wadda ta ke da matsayin digiri na biyu kuma a yanzu ta na koyarwa ne a bangaren karatun aikin lauya din. Sai dai duk da matakin da ta kai na karatu da aiki a halin yanzu ta samu kan ta a cikin harkar fim, har ma ta fita a finafinai masu dama a Kannywood. Kwanan baya, wakilin mu ya hadu da Asabe a wajen daukar wani fim na Turanci mai suna ‘This is the Way’. Fim din ya na cikin jerin finafinai na Turanci da Kabiru Musa Jammaje ya ke shiryawa.
Tun ba yau ba ake rade-radi kan mutuwar auren ta wanda ya sanya har ta kwaso kayanta daga Kano zuwa Kaduna, garin iyayenta.Auren ta na biyu da tsohon mijinta wanda yayi sanadiyar komawar ta Kano, Allah ya albarkace su da yara biyu,Ahmed da Yasmin.
A hirar ta da wakilin jaridar Leadership Ayau, Fati KK ta fayyace masa labarin dalla-dalla kan yadda al’amura suka kasance har suka rabu da mijinta.
“To ni dai abin da zan iya cewa, ni dai har ga Allah ya sani, wadanda muke tare da su su ma sun sani, na so zaman aure.In da ba na son zama da shi, wallahi ba zan mike kafafu na yi ta zuba ‘ya’ya ba. Na fuskanci gori daban-daban duk na shanye, kuma hakan bai sa ni bijirewa ba har na ce a sake ni ba, na kan zauna in yi kuka, watarana sai na fada masa, sai na gane in har wani ya ki ka, ai Allah na son ka. Na fuskanci kalubale kala-kala, sai dai in ce mun gode Allah.”
Jarumar wacce aka daina jin duriyarta a fagen shirya fim bayan auren ta ta bayyana cewa dangin mijinta sun zargi ta da bijire ma mijinta bayan ta samu labarin cewa zai kara aure. Tace basu fahimce ta ba domin bata da kishin samun kishiya. Haka zalika bazata zabi rabuwa da mijinta kan matsalar rashin kudi/talauci.
“Mun haihu da shi yara biyu, Abu ya ki ci, ya ki cinyewa, a gaskiya talauci bai taba sa na ce zan rabu da wanda nake tare da shi ba. Na dai samu surutai a cikin danginsa, wai don zai kara aure ne na bijire masa na ce ya sake ni, alhalin wallahi tallahi, wallahi tallahi, wallahi tallahi ban san wannan zancen ba, ban ma taba jin sa ba. ”
A duk lokacin da aka dauko batun aure, wasu da yawa kan yi wa ‘yan fim gani-gani. To amma a wannan karon magana ta kare, domin jarumar da muka tattauna da ita a wannan makon ta ce rashin sani ne ke sa mutane kyamatar auren ‘yan fimIdan mutum ya fahimci lamarin kuwa, zai fi wadanda ke auren wadanda ba ‘yan fim ba jin dadin zaman aure, ko me ya sa?
Sammam Masu karatu ko kun san shahararriyar jaurmar wasan kwaikwayon ta taba yunkurin shiga aikin soja kafin ta fara wasa?
A karanta firar duka a Taurarin Nishadi Muna so mu ji cikakken tarihin rayuwarki Ni dai sunana Ladidi Abdullahi An fi sani na da suna Tubeeless. An haife ni a Kaduna a wata unguwa da ake kira Sabon Gari Nassarawa, wato dirkania ke nan. Na yi Furamare wato a Nassarawa na kuma je makaratar gaba da Furamare.duk a Kaduna wato, ina gama sakandare aka yi min auren fari sai Allah bai yi zamana da mijin ba, sai muka rabu.
Daga nan sai na ji ina son yin aikin kaki, na je na sayi ‘form’ din aikin soja na ruwa na cika na ba da aka kira mu, na je duk abubuwan da ake yi na yi daga, baya ban sake bin ta kan shi kuma ba saboda oda wasu dalillai.
Yaushe kika fara fim din Hausa, da wane fim kika fara, kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga?
Wata rana sai Rabi’u Rikadawa ya zo gida ya same ni ya ce min, ki zo mu je ki yi aikin fim, shi da Obina. Na ce musu ku je zan zo, Amma sai na ki zuwa na neme su. Sai muka hadu da Zainab Abubakar muna hira ta ce min, ki zo mu yi aikin fim mana. Na ce mata zan bi ki. Ta ce, min, duk ran da za ta yi aikin za ta kira ni mu je mu yi tare. Na ce mata ba damuwa. kuma kafin nan, muna Hausa ‘drama’ a makaranta dama. Ran da Alfa ‘care’ zai yi wani fim sai ta ce na zo mu je.
Na ce mata to, muka je muka gana, sai shi ya tambaya da ma ina fim ne?
Saboda ya ga ba na kuskure. Daga nan sai na muka cigaba da zuwa N TA. Oganmu George ya ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani. Daga nan kuma ’yan Kano suka zo Kaduna za su yi wani flm sai aka kira ni. Kafin nan mun yi wani flm wanda Rabi’u Koli ya sa Wada Rikadawa ya kira na yi, sai na ciga da aiki sai aka cigaba da kira na ina yi, shi ne. Sai dai na manta shekarar gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi wani fim Balarabe da Balarabe dila ya kira ina Abuja ya ce na je Kaduna za mu yi wani fim. Shi ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni, na ce musu ina zuwa nako zo muka yiFim din da na fara na Turanci ne, shi ne na Alfa ‘care’.
Daya daga cikin Fina-Finan Kannywood da ya samu ingantaccen aiki wanda aka jima a na jiran fitowarsa wato ‘Yar Mai Ganye ya fito kasuwa a ranar yau Lahadi.
‘Yar Mai Ganye fim ne da mata suka baje kolinsu tare da cin duniyar su da tsinke tamkar an halacce su domin su bautar da maza.
Sabon Fim din ‘Yar Mai Ganye shine ne irinsa na farko da mata ke sarrafa mazajen su son ransu. “Gashin aya a tafin hannu abubuwa ne da magidanci ya fuskanta a fim din.”
Shin ku na son ganin yadda uwar gida ke juyawa tare da sarrafa mijinta son ranta yadda take so? Kuna son ganin yadda maigida ke dafa abinci, ya share gida ya wanke motar uwar gida, idan kuma ya ki aradu ta far masa? To ku nemi ‘Yar Mai Ganye.
“Ko ba komai mata iyayen giji, in ba ku ba gida, idan kuma kun yi yawa gida ya gyaru. Duk da irin baiwar da Allah ya yi masu ta sarrafa mazaje a tafin hannun su amma sun zabi bin bahaguwar hanya domin cimma biyan bukata ta barauniyar hanya.”
‘Yar Mai Ganye fim ne kan yadda Hadiza Muhammad (‘Yar Mai Ganye) ke amfani da karfin bokanci wajen taimakawa mata domin su mallake mazajen su cikin ruwan sanyi tare da mayar da maigida kwatankwacin mijin ta-ce ko mijin kafin- ta – ce.
Ali Gumzak SAK fitaccen Daraktan da tauraruwarsa ke haskawa daidai da farin wata ne ya bayar da umurnin fim din a yayin da fitacce kuma kwararren hazikin Furudosa mai tashe wato Abdul’aziz Dan- Small ya shirya fim din ‘Yar Mai Ganye. Tsinin Alkalamin Masanin Sirrinsu kuma shahararrren marubuci nan na jiya wanda ake jin amonsa a duniyar yau Maje El-Hajeej Hotoro ne ya rubuta tare da tsara labarin. Shi kuwa Dan Kasuwar Kasa da Kasa Alhaji Yusuf Yunusa ya dauki nauyin shirya fim din a karkashin kamfaninsa BGM FILM PRODUCTIONS.
Jaruman da suka jagoranci shirin ‘Yar Mai Ganye sune da Hadiza Muhammad, Rabi’u Rikadawa, Aina’u Ade, Halima Atete, Sulaiman Bosho, Hajara Usman, Saratu Gidado, Nuhu Abdullahi, Jamila Nagudu, Sadiya Adam, Maryam Yahaya, Amar Umar tare da gabatar da sababbin fuskoki biyu wato Momi Chiroma da Lubabatu Muhammad.
‘Yar Mai Ganye Fim ne da aka yi wa ingantaccen aiki a kololuwar mataki na kwararru wanda kuma aka sanya natsuwa tare da zabar ‘yan wasa a bisa ga kwarewa da cancanta. Tabbas hakika ‘Yar Mai Ganye fim ne da da zai kayatar ya kuma burge mai kallo.
Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana'antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cikin shekarar 2017, da suka kunshi masu kayatarwa da marar kyau da matsakaita.
Kuma kafin shekarar ta kawo karshe ana sa ran fitowar wasu sabbin fina-finai, kamar Juyin Sarauta, Sabon Dan Tijara, Dan Sarkin Agadaz, Mu Zuba Mu Gani, Dan Kuka a Birni da dai sauransu.
Don haka daya ko biyu daga cikinsu na iya shiga sahun Fina-finan 2017.
1. There's a Way
Ana ganin wannan ne Fim na Inglishi na farko a masana'antar Kannywood, wanda furodusansa shi ne babban malamin Ingilishi Kabiru Jammaje, sannan Falalu Dorayi a matsayin darakta.
An fito da halayyar wasu 'ya'yan attajirai a Jami'a da kuma rayuwar mata, wanda a haka aka tsara labarin.
Soyayya ce tsakanin Isham (Nuhu Abdullahi) Dan talaka amma hazikin dalibi da kuma Fadila (Hajara Jalingo) 'yar wani babban hamshakin attajiri Alhaji Mahdi (Sani Mu'azu) wanda ba ya kaunar hada zuri'a da talaka inda ya bi duk hanyoyin da zai bi domin ganin ya raba su.
Ana sa ran This is the Way, zai fito kafin karshen shekara. Raunin Fim din shi ne karshensa da kuma amfani da salon harshe mai sarkakiya.
Amma tsarin fim din baki dayansa ya kayatar wanda hakan martani ne ga sukar da ake wa masu shirya finafinan Hausa cewa jahilai ne, da ba su iya da turanci ba.
2. Umar Sanda
Kamal S. Alkali ne Daraktan Fim din, labarin ya mayar da hankali ne a kan mai ra'ayin rikau Umar Sanda (Ali Nuhu) da iyalinsa.
Ko da yake ma'aikaci ne, kuma yana kokarin ganin iyalinsa na cikin wadata. Ana zaman lafiya har zuwa lokacin da 'yarsa ta hadu da wani abokin karatunta Dan shugaban 'Yan sanda da aka shagwaba, wanda kuma ta kashe shi a kokarin kare kanta.
Umar Sanda ne ya binne gawar a yayin da 'yan sanda ke bincike mai tsauri.
Duk da cewa an kwaikwayi fim din ne daga wani fim na Indiya, amma yadda aka tsara shi zai iya kasancewa daya daga cikin mafi shahara a bana. Ya nuna girman gaskiya da hadin kai da dabi'u masu kyau.
3. Ankon Biki
Ali Gumzak ne daraktan Fim din, kuma Ankon Biki ya mayar da hankali ne a kan muhimmin batu da ake fuskanta a yanzu.
Mubarak (Adam Zango) da Fa'iza (Sadiya Bulala) suna shirin aure, sai Fa'iza ta kawo batun "Anko" da bukatar a hada wani babban bikin kasaita a wani wuri mai tsada.
Mubarak da abokansa sun yi iya kokarin ganin sun biya bukatar Amarya da kawayenta amma sun gagara, amma Amaryar ta dage a kan bukatar har ta bayar da kanta a madadin kudin kama wajen da za a yi bikin.
Ya fasa aurenta a ranar bikin bayan asirinta ya tonu, kuma a madadinta ya auri kawarta ta kud da kud. Fim din ya nuna girman nisan da wasu mata ke dauka don cimma bukatunsu.
Duk da yake wasu wuraren a fitowar fim din na da tsayi amma an yi amfani da Hausa mai kyau da salon magana.
Sauran taurarin fim din sun hada da Hafsar Idris da Umma Shehu da Al Amin Buhari da dai sauransu.
4.Rariya
Yaseen Auwal ne Daraktan Rariya, kuma fim na farko da Rahama Sadau ta dauki nauyin fitowarsa, wato matsayin furodusa.
Labarin Fim din ya danganta tasirin wayar salula ta zamani da ake kira "komi da ruwanka". Fim din ya shafi yadda wasu 'yan matan Jami'a ke amfani da wayar salula domin janyo hankalin maza.
Yadda aka hada fim din ya kayatar. Babban muhimmin abu shi ne yadda daya daga cikin 'yan matan ta banbanta da saura inda har ta yi kokarin kammala karatunta.
Mutane da dama ba za su so haka ba, musamman iyaye da ke da'awar karatun 'ya'ya mata. Amma duk da haka linzamin labarin ya shafi abin da ke faruwa kuma ke shafar jama'a.
Taurarin Fim din sun kunshi Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa da Rahma Sadau da Fati Washa da Hafsar Idris da sauransu.
5.Mijin Yarinya
Ali Gumzak ne Darakta, kuma Mijin Yarinya ya shafi labarin wani Dattijo Attajiri Bashir Nayaya (Alhaji).
Wata rana ya ji matansa guda biyu da Allah bai ba su haihuwa ba suna ma shi addu'ar mutuwa domin gadon dukiyarsa kuma don su aure yara samari, su yi sabuwar rayuwa.
Saboda haka ne ya je ya auri budurwa Maryam Yahaya bayan ya saye imanin iyayenta da saurayinta da kudi.
Wannan ne ya fusata manyan 'ya'yansa Aminu Sharif da Sadiya Bulala, inda suka taya iyayensu mata kishi.
Bayan shafe lokaci ana makirci da takaddama, Alhaji ya yanke shawarar sakin dukkanin matansa, hadi da amaryarsa. Fim din na kunshe da darussa masu yawa a yadda aka tsara fim din.
Sabuwar 'yar fim Maryam Yahya ta yi kokari a fim din mai kunshe da gwanaye. Ba tare da zuzutawa ba fim din na cike da ban dariya da ilmantarwa.
6.Kalan Dangi
Wannan ma wani fim ne na barkwanci da Ali Gumzak ya bada umurni wato a matsayin Darakta, Fim din ya nuna yadda talakawa ke neman arziki da kuma attajirai.
Yayin da kuma masu arzikin ke kaskanta Talakawa. Ali Nuhu da Aminu Sharif da Sadiq Sani Sadiq da Jamila Nagudu da Fati Washa da Aisha Tsamiya na rayuwa ne ta nuna arziki da karya da makirci da nuna karfin iko. Idan kana neman nishadantarwa, to ka nemi Kalan Dangi.
Sai dai an raba fim din biyu, na daya da na biyu. Amma an takaita labarin da kuma karshensa, wanda ake sa ran fitarwa a shekara mai zuwa.
Kamar taken fim din Karshen Kalan Dangi zai iya kawo karshen duk wani rikici.
7.Makaryaci
Kamar sauran shahararrun fina-finan barkwanci da aka fitar a 2017, Ali Gumzak ne daraktan Makaryaci.
Sadiq Sani Sadiq ne da Allah ya ba basirar wasan kwaikwayo, ya daukaka fim din a matsayin daya daga cikin fitattu a bana. Labarin Fim din ya shafi yadda kwadayinsa na dukiya ya kai shi ga samun kudi ba tare da ya sha wata wahala ba.
Yakan je ya yi hayar tufafi ya harde cikin babbar motar mai gidan Rabiu Daushe ana tuka shi zuwa wurare har zuwa cikin Jami'a. Yakan yi wa dalibai karyar cewa shi dan gidan minista ne ko ambasada.
A hakan ne ya fara soyayya da daya daga cikin daliban Hafsat Idris. Ba tare da bin umurnin kakanninsa ba, ya je ya kadar da dabbobinsa na gado, domin ya kashe wa budurwarsa kudi wacce daga baya ta gano asalinsa.
Taurarin Fim din sun kunshi Sulaiman Bosho da Mama Tambaya da Mustapha Nabaruska da Musa Maisana'a da sauransu.
8.Husna ko Huzna
Husna (Jamila Naguda da Abdul (Adam Zango) sun shirya yin aure, yayin da kuma Huzna (Fati Washa) ta yi kokarin hana auren saboda matukar son da ta ke wa Abdul.
A yayin da suke hamayya, wata rana Husna ta watsa wa Huzna guba a fuska, ba tare da sanin cewa ashe fatalwa ce. Washegari Huzna ta tafi gidansu ta mallaki Husna.
Wannan ya bude wani sabon babin hamayya tsakaninsu inda Huzna ta shiga jikin Husna kuma ta ci gaba da zama a gidanta. Yadda aka tsara fim din ya ja hankali.
Amma duk da akwai matsaloli da aka samu, Fim din na iya zama daya daga cikin manyan fitattu finafinai a Kannywood.
Fim din dai bai kasance wani abin muni ga mata ba, kamar yadda aka tsara labarin fim din irin na ban tsoro, a rikicin rayuwar aure tsakanin mata don mallakar namiji.
Rawar da Washa ta taka ya kayatar. Falalu Dorayi ne Daraktan Fim din.
9.Burin Fatima
Wasu za su yi mamakin yadda wannan fim ya shigo sahun fitattu. Ya cancanta. Labari ne akan wata matar aure da ta fada tarkon shawarar kawarta.
Aisha Tsamiya tauraruwar fim din ita ce kuma ta dauki nauyin fitowarsa a matsayin furodusa.
Fim din ya ba da labarin wata mata (Tsamiya) da mijinta, Adam Zango a yayin da ta ke makaranta, wata kawarta ta ba ta shawarar ta zubar da juna biyu da take dauke shi don ta samu sukunin karatu.
Ta karbi shawarar kuma ta yi wa mijinta karya cewa cikin ya bare, ba tare da sanin cewa ba ta kara haihuwa ba. Ta fuskanci kalubale daga sarakuwarta kan rashin haihuwa inda ta tursasawa Zango ya kara aure.
Ali Gumzak ne ya bayar umurni a fim din da ba a kashewa kudi ba. Sannan bai samu karbuwa ba.
Amma ba don haka ba da zai kasance daya daga cikin finafinan da suka samu karbuwa ga jama'a. Wannan dai ci gaba ne ga Tsamiya, kasancewar fim dinta na farko a matsayin furodusa.
10.Mansoor
Fim din Mansoor na FKD yana cikin wadanda ake kururutawa a matsayin gwarzon shekara. Ali Nuhu ne Darakta.
An fara fim din ne da soyayyar wasu matasa daliban makaranta, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif.
Amma mahaifin Sharif ne ya kawo karshen abotar, saboda yana zargin Sharif ba ya da uba, wanda wannan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da bincike domin gano asalin mahaifinsa, ba tare da sanin cewa ashe gwamnan jiha ba ne mahaifinsa.
Labari ne ya mamaye fim din. Kuma ko shakka babu, fim din ya kasance kamar a zahiri. Baki dayan fim din ya shafi labarin matasan masoya tsakaninsu da iyayensu.
An aiwatar da fim din da kyau. Taurarin fim din sun hada da Ali Nuhu da Abba El Mustapha da Baballe Hayatu da Teema Yola da dai sauransu.
11. Dawo Dawo
Fim din Kabuwagawa ne wanda Ali Gumzak ya bayar da umurni.
Dawo-Dawo labari ne game da wasu da suka reni yaro (Adam Zango) tun kuriciya har girmansa inda suka kuma aurar ma shi da 'yarsu (Maryam Gidado).
Amma daren farkon aurensu, amaryar ta yi karyar cewa tana da aljannu, ta tursasa ma shi ya sake ta. Nan take iyayen suka daura ma shi aure da kanwarta (Aisha Tsamiya).
Ita kuma (Gidado) ta koma ga tsohon saurayinta (Zahraddeen Sani) wanda saboda shi ta kulla makircin. Daga baya ya yi watsi da ita, inda ta shiga wani hali ta koma kamar mahaukaciya lokacin da ta fahimci cewa ta dauke da cikin Zaharaddeen.
Fim din na cike da makirci da rikici, kuma taurarin fim din Zango da Tsamiya da Gidado suna yi kokari sosai. Wannan ya sa fim din ya sha gaban takwarorinsa a bana.
12. Ta Faru ta Kare
Aminu Saira ne daraktan Ta Faru ta Kare, labarin fim din ya shafi rayuwar Hafsat Idris, gurguwa, makauniya amma 'yar attajiri, da kuma Aminu Sharif (Momo) wanda ya aure ta kuma yake cin amanarta yana kawo 'yan matansa a gidanta har zuwa lokacin da dubunsa ta cika.
Inda Adam Zango, abokin wasanta wanda Momo ya yi wa kanwarsa ciki ya yake shi har ya fitar da shi daga gidan.
Fim din na tattare da nishadi. Hafsat Idris da ta fito mai nakasar jiki da kuma Momo sun yi kokari a rawar da suka taka a fim din.
Sauran taurarin fim din sun hada Hadiza Gabon da Hauwa Waraka da sauransu.