spon

Showing posts with label RARA YASAKI SABUWAR WAKAR SA YANXU. Show all posts
Showing posts with label RARA YASAKI SABUWAR WAKAR SA YANXU. Show all posts

Thursday, August 30, 2018

RARA YASAKI SABUWAR WAKAR SA MEZAFI

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


Rarara da Atiku Abubakar


Fitaccen Mawaƙin Siyasar ƙasar Nigeria Musamman akan abin da ya shafi Jam'iyyar APC , haƙiƙa babu kamar Dauda Adamu Kahutu Rarara a Nigeria.

A kwanakin baya ne dai ma'abota bibiyar wannan shafi na Muryar Hausa24 mai Albarka suke aiko mana da saƙonni daban-daban akan Cewa"Shin da gaske ne rarara yayiwa Abubakar Turakin Adamawa waƙa?, tare da wasu tambayoyi makamantan hakan".

Muryar Hausa24: Magana ta gaskiya Rarara yayi ma Abubakar Turaki waƙa, amma yayi masa lokacin da yake jigo a jam'iyyar APC.

Ga taken waƙar kamar haka:

Kuban kiɗan ƙashin gwiwar duniya...

Amshi: Turaki

Hasken Arewa kai kahaɗe nahiya...

Amshi: Turaki

Ƙashi bugun ƙashi taku ka iya...

Amshi: Turaki

Bango majinginar 'yan Nigeria ...

Amshi: Turaki

Namijin maza kadan garkin duniya ...

Amshi: Turaki

Farin ciki uban ɗakin fariya...

Amshi: Turaki

Ga ɗan kahutu rarara mai kabiya...

Amshi: Turaki

Atiku Abubakar taku lafiya...

Amshi: Turaki

Nigeria ka kafaf kai ne maliya...

Amshi: Turaki

Don kazamo madubin  Nigeria...

Amshi: Turaki

Domin ko kai kasan sirrin tin jiya...

Amshi: Turaki

Kune ku ke tuwo kune am miya...

Amshi: Turaki

A cikin africa kaf kai ne jan wuya...

Amshi: Turaki

Atiku Abubakar Namijin Duniya...

Amshi: Turaki

In kataho ina wani mai tambaya...

Amshi: Turaki

Burin ka taimako baka fariya...

Amshi: Turaki

Wallahi sai da ku za'ai gwamnati..