Tarkon Kauna
Wannan fitaccen wasan Kwaikwayo na tsaywon sa’a guda, shiri ne da ya
maida da hankali a kan labarin Omer da Zehra, Mutane biyu ne da
dabi’unsu su ka sha banban da juna tamkar dare da rana, wadanda
banbancin rayuwarsu ya kasance tamkar na launin Fari da baki, yayin da
suke rayuwa tare da juna sabanin banbancin dake tsakaninsu. Inda Omer ya
dukufa wajen farantawa ‘yar-uwarsa wacce watanni Shida kacal ya rage
mata a rayuwa, amma auren Zehra ya zame masa dole, wacce rayurwata ta
sha banban da tashi.