spon

Showing posts with label kannywood. Show all posts

Tuesday, December 26, 2017

'Yan Kannywood sun zama dankali sha kushe'

Hadiza ta fito a fim sama da dari uku
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.
"Allah yana kallon abin da muke yi; idan muna yi don mu bata ko mu gyara mu fadakar, Allah ya sani.
"A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatun Al-Qur'ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa 'Allah ya ce, Annabi ya ce'. Shi ma duk wannan koya rashin tarbiyya ne?", in ji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da ake yi wa 'yan fim.
Ta kara da cewa: "Ka san mu dankali ne sha kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da haka Allah ya yo mu.
"Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za su fahimce mu. Na san wasu ma sun fahimta yanzu."
Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma sha'awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.

A cewarta, "Karance-karancen littafai da kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma sha'awar shiga fim.
"Na kalli fim din 'Ki Yarda Da Ni' a lokacin ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo karshe sai na ji sha'awar shiga fim. Na soma fim ne sama da shekara 16 da suka wuce kuma na fito a fim fiye da 300.''
"Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a matsayin uwa.
"Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin na taka irin wannan rawar."
Hadiza (ta farko daga dama) ta shaku sosai da Saima (ta tsakiya)Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HADIZAN SAIMA
Image captionHadiza (ta farko daga dama) ta shaku sosai da Saima (ta tsakiya)

Wednesday, December 20, 2017

Hotuna: Zafafan Hotuna Maryam Yahaya Na Yau

Wacece Jaruma maryam yahaya nasan da yawa wasunku sun san wace maryam yaha a wannan lokacin.
Jarumar tafara harkar film da kamar dama Inda yanzu tauraruwarta take haskawa yadda ba’a tunani nasan kunsan haka.
Fim din da jarumar tayi suna shine Mansoor wanda shine fim dinta na farko kuma akansa tayi suna sosai sai kuma mijin yarinya inda a yanzu kuma ake shirya fim din mariya da ita.

Monday, December 18, 2017

Kannywood: Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua

Fittaciyar jarumar wasan  fina-finan Hausa wanda kuma ke fama da rikice-rikece a masana’antar a kwanakin nan, Rahama Sadau, ta sha da kyar a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua, dake Katsina bayan da wasu gungun daliban jami’ar suka yi kokarin murkushe ta a harabar makarantar da aka fi sani da ‘Students’ Centre’.

Rahotanni  sun shaida mana cewa shugabannin daliban jami’ar ne suka gayyaci jarumar domin su karramata a lokacin wani biki da suka shirya don tuna wa da ranar mata ta duniya.

Majiyarmu sun  bayyana mana cewa fitacciyar jarumar wadda tazo a makare a wurin taron bayan anyi nisa a ciki ta nemi wuri ta zauna ne a inda aka tanada domin ta kafin daga bisani a kira ta domin a bata shaidar karramawar da aka tanadar mata.

Tun farko dai rahotannin sun bayyana  cewa zuwan jaruma Rahama Sadau din ke da wuya sai kawai kallo ya koma mata yayin da wurin ya fara harmutsewa da lokacin da dliban jami’ar masoyan ta suka fara kokarin yin tozali da ita wasu kuma suna kokarin yin hotunan nan na dauka-da-kai watau (Selfie) a turance da jarumar.

Monday, December 11, 2017

Abin da ya sa ake kira na Shu'uma — Fati

Matashiyar nan ta fina-finan Kannywood, Fati Abubakar ta ce ana kiranta da suna Shu'uma ce saboda rashin jin da ta nuna a fim din Shu'uma.
Fim din na Shu'uma na koya darasi ne kan mummunar makomar miyagun mutane.
A hirarta da Nasidi Adamu Yahaya, Fati ta ce tana matukar son taka rawa a matsayin "muguwa" a fina-finai.
"Na fi so na fito a matsayin muguwa saboda na fadakar da mutane irin illar mugunta da son rai.
"Ka san yawancin jarumai sun fi son fitowa a matsayin masu kirki, amma ina ganin hakan ba ya aikewa da sako kai tsaye kamar jarumi mugu, wanda ake nuna karshensa bai yi kyau ba", in ji jarumar.
Fati, wacce ta soma fitowa a fina-finan Kannywood a shekarar 2010, ta kara da cewa "Na fito a fina-finan mugunta irinsu Shu'uma da Sai Na Auri Zango da Baya Da Kura da Basma da sauransu".
A cewarta, fim din Basma ne ya fi ba ta wahala "saboda yarinyar da aka hada ni fim da ita, wacce ba ta wuce shekara bakwai ba, shi ne fim dinta na farko, don haka idan na kai mata mangari ko naushi takan ji kamar da gaske ne sai ta tsorata.
"Don haka sai da aka rika sake daukar fim din sau da dama kafin a gama shi".
Jarumar, haifafiyar jihar Bauchi, ta bukaci masu kira a gare ta ta yi aure da su yi mata addu'a, tana mai cewa "idan Allah ya nufa sai ka ga an yi, don haka lokaci muke jira. Amma ina da wanda zan aura".
Fati Abubakar ta ce tana so a hada ta fim da ubangidanta Adam A. Zango da kuma Jamila Umar (Nagudu) saboda suna burge ta "kuma hankalina a kwance yake idan ina tare da su".
Fati Abubakar da Adam A. ZangoHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/FATI ABUBAKAR
Image captionFati Abubakar da Adam A. Zango

Kannywood: Buri Na In Zama Director Kafun Nayi Aure – Jamila Nagudu

Jarumar wadda ta share kimanin shekaru goma a harkan fim ta ce ta samu nasarori a wannan sana’ar da ita kanta ba zata irga ba kuma ba tada wani shiri na gaggawa na barin harkan domin a ganin ta har yanzu tana da sauran rawar da zata taka.
Jarumar yar asalin garin Bauchi ta mika sakon godiya ga dukkan masoyan ta kuma ta bayyana cewa har yanzu ba su gama ganin rawar ta ba.

Chelsea za ta kara da Barcelona a sabon jadawalin da aka fitar na kungiyoyi 16 da za su fafata a Gasar Zakarun Turai. Juventus da Tottenham FC Basel da Manchester City Porto da Liverpool Sevilla da Manchester United Real Madrid da PSG Shakhtar Donetsk da Roma Bayern Munich da Beskitas