Friday, September 7, 2018
AKIDUN ZAMANI: Shin ya dace mace ta yi aikin ofis?
AKIDUN ZAMANI: Shin ya dace mace tai aikin ofis.
Author/arewainfinit
Date/7 sep 2018
Author/arewainfinit
Date/7 sep 2018
Akidun Zamani, tare da Fatima Zahra Umar, wani sabon fili ne inda za ku riƙa karanta ƙasida guda duk a mako kan batutuwan da suka shafi mata, masu daɗi da marasa daɗi. Manufar wannan filiita ce samar da wata dama don duba matsalolin da ke damun mata da kuma zaƙulo hanyoyin warware su. Sannan kuma za mu riƙa gabatar da tattaunawa a kan batutuwan da wannan fili ya taɓo a rediyo. Batun da ƙasidarmu ta yau ta yi nazari a kai shi ne "Matsayin mata masu fita aiki".
Mata masu aiki sun fi samun 'ya'ya masu ilimi, masu nutsuwa, kuma masu kokarin neman ci gaba. Na san haka batun yake, domin ni ma haka nake.
Akwai alfanun samun uwa ko mata mai yin aiki. Abin dubawa a nan shi ne idan wani abu ya samu maigidan (kamar mutuwa, rashin lafiya ko ya rasa aikin yi), ita matar ko uwar tana iya daukar nauyin gidanta, ba tare da ta zame wa kowa alaƙaƙai ba
Mutane da yawa suna ganin cewa mace bai kamata ta yi aiki ba, musammam ma idan tana da 'ya'ya. Masu wannan ra'ayin na ganin cewar matar da ke yin aiki na iya watsar da babban nauyin da ke kanta - na zama matar gida ko uwa, wanda abu ne da zai iya janyo mummunan tasiri ga gidanta.
Yawancin mutane na ganin cewa idan mace na yin aiki a wani wuri, yaranta ba za su samu kulawar ƙwarai ba. Mutane kuma na ganin cewa fitar da matar aure ke yi ka iya sanya wa idonta ya buɗe, wanda a ganinsu zai iya ɓata martabarta da ta 'ya'yanta.
Abin da ya kamata mu tambayi kanmu shi ne, shin aiki a wajen mace na iya ɓata tarbiyyar 'ya'ya, ko ya ɓata dangantakarta da mijinta?
Duk da yake, wasu daga cikin wadannan batutuwan haka suke, amma yawancin lamarin al'ada ce kawai. Wasu al'adun kan sa mu rasa ɗumbin alfanun samun mata a ma'aikatu.
A misali, ka ga ba mu da likitoci mata masu yawa a asibitocinmu. A matsayina na mace, ba ko yaushe nake son likita namiji ya duba ni ba, amma na san matan da suka kammala karatun likita, kuma suna gida zaune, ba sa yin aiki. Kawai don maigidan ba ya son ta rika cudanya da maza, amma kuma ya fi son likita mace ta duba matarsa idan ta je asibiti.
Dukkanmu mun san ƙissar Sayyida Khadija (RA) uwargidan Annabi Muhammad SAW. Sayyida Khadija babbar 'yar kasuwa ce, lokacin da ta auri Annabi SAW. Amma duk da yake ita ce uwargidansa ta fuskar kasuwanci (a matsayinsa na hadiminta a wajen kasuwancinta), ta kasance uwa kuma matar gida abar alfahari ga kowa.
Abin har ya kai ga shekaru bayan rasuwarta, Annabi Muhammad SAW yakan yi maganarta cike da martabawa, da soyayya. An ruwaito cewa sauran matansa sun rika kishinta saboda irin yabonta da yake yi.
Abin da nake son nunawa a nan shi ne babu wani dalilin da zai hana mace yin sana'a ko aiki, musammam mace mai nutsuwa da kamun kai.
Zuwa wajen aiki bai zama sanadin rasa mutuncinta ba, domin wannan ya shafi irin halin matar ne tun ainihi. Mata masu yawa sun samu nasarar hada aiki da rike gidansu ba tare da sun zubar da mutuncinsu ba... wannan manuniya ce cewa batun na alaƙa da karfin hali da jajircewa da kuma tarbiyya.
Babban ƙalubalen mata masu aiki ke fuskanta shi ne na tabbatar da ganin sun ba kowanne ɓangare haƙƙinsa.
Yaya za mu iya tabbatar da mun tafiyar da ayyukanmu, kuma mun ba 'ya'yanmu tarbiyya ta gari? Yaya za mu yi adalci tsakanin yin aiki ko sana'a da kula da gida?
Amsar mai sauki ce, muna bukatar mazajenmu su ƙara tallafa mana. Domin babu inda aka ce aikin kula da 'ya'ya da kuma ba su tarbiyya na mace ne ita kaɗai.
Ina kira ga maza magidanta da iyaye maza su ƙara taimaka wa mata wajen kula da gida da kuma 'ya'ya, su taimaka mana wajen sana'o'inmu kuma su yi alfahari da abubuwan ci gaba idan sun same mu.
Manzon Allah SAW ya yi, me zai hana kai ma ka yi?
Ga Fatima Zahra Umar da baƙin da ta gayyata don tattanawa a kan wannan batu
OH !DUNIYA ABIN TSORO WATA TSINTSUWA TAFA FADO TAZA TSOHUWA
Mara hannu mai digirgir na son ya zama dan majalisa Mintuna 59 da suka wuc
Mara hannu mai digirgir na son ya zama dan majalisa
- Mintuna 59 da suka wuce
Vitalis Lanshima ya rasa hannayensa ne a lokacin da yake yaro, amma wannan larurar ba ta hana shi neman ilimi ba.
Kuma ya samu tallafin zuwa karatu zuwa kasar Amurka a Jami'ar Ballarmine da ke kasar.
Bayan ya gama digiri na daya da na biyu, Vitalis wanda dan asalin jihar Filato ne yana kan hanyarsa na kammala nazarin samun digiri na uku.
Duk da cewa yana aiki a Amurka, Lanshima yana da burin zama dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilan Najeriya.
Labarai masu alaka
Babban labari
Adam Zango ya nemi gafarar Ali Nuhu 06 Satumba 2018
Adam Zango ya nemi gafarar Ali Nuhu
- AUTHOR AREWAINFINIT
- Shahararren jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera, ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe kwanaki suna "gaba".Sakon Adam Zangon ya ce "tuba nake sarki gwiwowina a kasa".Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya wallafa a shafinsa na Instagram.
- Yaushe Ali Nuhu da Adam Zango za su daina rikici?
- Fadan Ali Nuhu da Adam Zango ya 'raba kan Kannywood'
Rayuwar Adam A Zano a takaice- An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
- Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
- Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
- Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
- Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
- Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
- Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
- Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16
Rayuwar Ali Nuhu a takaice- An haife shi a watan Maris na 1974
- Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
- Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
- Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
- Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
- Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
- Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki
Jaruman biyu suna gaba-gaba a masana'antar Kannywood din inda suke da mabiya da dama a shafukan sada zumunta.
NEWS:TROOPS KILL MANY INSURGENTS IN BARNO
NEWS:TROOPS KILL MANY INSURGENTS IN BARNO
Troops of the Operation Lafiya Dole in northern Borno State have ambushed Boko Haram militants, killing many of them and recovering some weapons and 147 assorted livestock earlier rustled from comArmy spokesman, Brigadier-General Texas
Troops of the Operation Lafiya Dole in northern Borno State have ambushed Boko Haram militants, killing many of them and recovering some weapons and 147 assorted livestock earlier rustled from comArmy spokesman, Brigadier-General Texas
Clement westerhof:Supper eagles just too strong eagles for seychelles
Dutch coach Clemens Westerhof has said he does not expect anything but a comfortable win by the Super Eagles in Seychelles in Saturday’s 2019 AFCON qualification clash.
Clement westerhof:Supper eagles just too strong eagles for seychelles.
Clement westerhof:Supper eagles just too strong eagles for seychelles.
Subscribe to:
Posts (Atom)