Mataimakin gwamnan Kano da ke arewacin Najeriya, Farfesa Hafiz Abubakar, ya ce ba zai sake tsayawa takara tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2019 ba.
Farfesa Hafiz ya bayyana haka ne a gidan Mambayya da ke birnin na Kano cikin fushi.
Ya kara da cewa idan sun kammala wa'adin shugabancinsu a shekarar 2019 zai koma Jami'ar Bayero domin ya ci gaba da koyarwa kamar yadda yake yi kafin ya zama mataimakin gwamna.
Ya bayyana cewa wasu shugabannin jam'iyyarsu ta APC sun je mazabarsa ta Mandawari sun cire kanensa wanda shi ne shugaban mazabar na jam'iyyar APC, sannan suka cire hotunansa sannan suka maye gurbinsu da na wasu mutane daban.
"Lokacin da aka sa ni takarar mataimakin gwamna suka ga dama suka sa hotona da na gwamna da na shugaban kasa da kuma na jagora [Rabi'u Musa Kwankwaso, tsohon gwamna], amma yanzu suna bukatar a share hotunana. Kuma don karin cin mutunci sun maye gurbin hotona da na wasu a mahaifata", in ji mataimakin gwamnan.
Mataimakin gwamnan bai fito fili ya soki Gwamna Ganduje ba, sai dai wasu na ganin wasu 'yan siyasa da ke kusa da gwamnan ba sa son a ci gaba da gudanar da al'amura da shi.
Sai dai daraktan harkokin watsa labarai na gwamnan Salihu Tanko Yakasai ya shaida wa BBC cewa Gwamna Ganduje bai san da abubuwan da suka faru ba, yana mai cewa zai dauki matakin gyara su.
A cewarsa, gwamnan da mataimakinsa na zaune lafiya kuma babu abin da zai hada su rigima.
Kazalika wata sanarwa da kwamishinan watsa labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar ta ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi matukar kaduwa da jin bayanan mataimakinsa.
"Gwamna ya bayar da umarni a gaggauta mayar da shugaban jam'iyyar da aka cire, kana ya yi kira ga 'yan siyasa da a kodayaushe su rika tuntubar shugabannin jam'iyya da kuma 'yan siyasar da ke rike da manyan ofisoshi kafin su aiwatar da wata manufa wacce ka iya jawo ce-ce-ku-ce", in ji sanarwar.
Ko da yake har yanzu Gwamna Ganduje bai fito fili ya ce zai sake tsayawa takara a shekarar 2019 ba amma masana harkokin siyasa na ganin da wuya ya ce ba zai yi takarar ba kasancewa wannan shi ne wa'adinsa na farko cikin wa'adi biyu da kundin tsarin mulki ya ba shi ikon nema.
Farfesa Hafiz Abubakar dai makusanci ne ga tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda ke takun saka da Gwamna Ganduje tun bayan zaben 2015..
No comments:
Write blogger