spon

Sunday, December 10, 2017


Subscribe Our Channel


Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce
shi ne "fitaccen dan kwallo a tarihi", bayan da ya
lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya,
wato Ballon d'Or karo na biyar.
Ronaldo ya lashe kyautar karo na biyar jere, inda
ya yi kankankan da dan kwallon Barcelona Lionel
Messi, ya kuma ce bai yi amannar cewa akwai
wani dan wasa da ya fi shi ba.
"Babu dan wasa sama da ni. Ina buga tamaula
sosai, ina da sauri, ina da karfi, ina buga kwallo
da kai, na ci kwallaye, na taimaka an ci, akwai
mutanen da suka fi son Neymar ko Messi, amma
na fada babu wanda yake da irin wadannan
abubuwan fiye da ni," in ji dan kwallon.
Ya kara da cewa," Babu wanda ya lashe
kyautuka iri daban-daban kamar ni. Ba ina
magana a kan kyautar Ballon d'Or kawai ba ne."
Karanta wadansu karin labarai:
Ronaldo ya sake kafa sabon tarihi
Ronaldo ya buga wa Madrid wasa sau 400
Tottenham ta yi wa Stoke ruwan kwallaye

No comments:
Write blogger