Wata matashiya 'yar Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya Mildred Ehiguese, ta lashe gasar sarauniyar kyau ta kasar da aka kammala a Lagos a ranar Juma'a.
Ehiguese ce yanzu sarauniyar kyau a Najeriya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya ya ruwaito inda yanzu ta gaji Chioma Obiadi daga Jihar Anambra.
Jaridar Daily Times da ake bugawa a kasar ce ta dauki nauyin shirya gasar da aka gudanar a Eko Otel a Lagos.
An soma gasar sarauniyar kyau a Najeriya tun a 1957 da nufin karfafawa mata. Kuma duk shekara ne ake gudanar da gasar tsakanin jihohin kasar.
A bana an samu wakilci daga daukacin jihohin kasar 36 hadi da Abuja.
Zamfara da Kano sun shiga gasar duk da an dade jihohin biyu daga arewacin Najeriya na kauracewa saboda tsaraicin da ake nunawa a bikin na sarauniyar kyau.
Alkalai ke tantance 'yan takarar daga jihohin kasar kafin zaben sarauniyar kyau.
A shekarun baya dai duk wadda ta lashe sarauniyar kyau a Najeriya ita ce ke wakiltar kasar a sarauniyar kyau ta duniya.
No comments:
Write blogger