An gudanar da bikin Durbar cika shekara 100 da kafa garin Kaduna wanda ke arewacin Najeriya a ranar Asabar.
- An gudanar da bikin Durba ne a dandalin Murtala Square a tsakiyar birnin, inda dubban jama'a suka halarta
- A shekarar 1917 ne aka kafa garin Kaduna wanda yake yankin arewa maso yammacin Najeriya
- Manyan baki daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin
- Cikin wadanda suka halarci bikin har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo
- Kek din bikin yayin wata liyafa da gwamnatin jihar ta shirya bayan kammala bikin Durban
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daga cikin manyan sarakunan kasar da suka samu halartar bikin
- Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris shi ya kasance mai masaukin baki yayin bikin
- An rika nishadantar da mahalarta bikin da kade-kade da bushe-bushe
- Garin ya taba zama babban birnin jihar Arewa
- An yi kade-kade da raye-raye don nuna al'adun jama'a mabambanta na jihar Kaduna
No comments:
Write blogger