spon

Saturday, December 9, 2017

Home › › Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari

Subscribe Our Channel


Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari




Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce jama'ar jihar Kano sun nuna wa jama'ar kudancin kasar cewa har yanzu yana da gata.
Shugaban ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake jawabi yayin da yake ziyarar kwana biyu.
Ya ce sun yi yakin neman zabe a shekarar 2015 a kan abubuwa uku wato: matsalar tsaro da batun tattalin arziki da kuma matsalar cin hanci da karbar rashawa.
Shugaba Buhari ya ce abin da ya fi ba shi wahala a tsawon mulkinsa na fiye da shekara biyu "shi ne hana yaki da cin hanci da rashawa."
Daga nan ya ba da labarin yadda ya yi yaki da cin hanci da rashawa yayin da yake jaorantar kasar a karkarshin mulkin soja wato a tsakanin shekarun 1983 zuwa 1985.
Ya ce yanzu ba zai iya yakar cin hanci da irin wancan tsohon salon da ya yi amfani da shi ba a wancan lokacin.

No comments:
Write blogger