
Shugaban Facebook, Marck Zukerberg ya ziyarci fadar shugaban da ya ziyarci Najeriya kwanakin baya
Wani bincike ya  nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet  sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma'abota  shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook. 
Kungiyoyin da ke  fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na  tauye 'yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da  shi. Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al'umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.
Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na tauye 'yancin mata                                                   
Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Muhammad Awwal  Garba daga hukumar Hisbah ta jihar Kano da Maryam Ado Haruna, jami'a a  wannan cibiya ta fasahar sadarwa da aka fi sani da CITAD, inda suka yi  masa bayanin yadda girman matsalar take.Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar tasu:

 
No comments:
Write blogger