Dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya ce ya tattauna da wakilan Real Madrid kan batun zuwa can da murza-leda kafin ya koma Paris Saint-Germain a bana.
An bayar da rahoton cewar Real Madrid ta yi zawarcin Mbappe, bayan da ya jagoranci Monaco ta ci French Lik, bayan shekara 17 rabonta da kofin, amma ya amince da zuwa PSG aro a watan Agusta.
Mbappe ya ce ''Anyi ta rade-radin zuwa na Real Madrid, kuma gaskiya ne na tattauna da wakilan kungiyar, amma yanzu batun ya wuce babu maganar komawa Spaniya''.
A hirar da Marca ta yi da dan kwallon a ranar Laraba ya ce ''Ni dan wasan PSG ne yanzu haka, zan kuma ci gaba da kare martabar kungiyar dari bisa dari''.
Mbappe wanda ya cika shekara 19 da haihuwa a makon jiya ya kara da cewar ya amince ya buga wa PSG tamaula ne saboda Paris garin shi ne.
No comments:
Write blogger