spon

Monday, December 18, 2017

Home Nigeria: 'Yan Boko Haram sun sace kayan agaji a Borno

Subscribe Our Channel


Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram
Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari kan yarin motocin shirin samar da abinci na duniya inda suka kashe mutum hudu.
Mayakan sun yi wa ayarin motocin da sojoji ke yi wa rakiya kwanton bauna ne a jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Nigeria ranar Asabar.
Shaidu sun ce maharan sun zo ne cikin wa su motoci biyu inda suka budewa ayarin motocin wuta kuma suka sace abinci a daya daga cikin motocin jami'an agajin.
Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram, tana mai cewa ba su da katabus din kai manyan hare-hare.
Sai dai 'yan kungiyar na ci gaba da kai hare-hare na kunar bakin wake a arewa maso gabashin kasar.
Ya zuwa yanzu mayakan Boko Haram sun kashe fiye da mutum 20,000 a shekaru takwas da suka shafe suna kai hare hare a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.

No comments:
Write blogger