spon

Sunday, December 17, 2017

Home Nigeria: PENGASSAN za ta fara yajin aiki

Subscribe Our Channel


Yanzu haka ana fuskantar karancin man fetur a kasar
Kungiyar manyan ma'aikatan mai a Najeriya wato PENGASSAN ta ce za ta fara yajin aiki a ranar Litinin, bayan sun kasa cinma sulhu a tattaunawar da kamfanonin man kasar.
Galibin mambobin kungiyar suna aikin ne da kamfanonin hako danyen man fetur a tudu.
Kuma wadansu mambobin kunyiyar ne suka samu matsala da kamfanoninsu kan batun sallamarsu aiki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Takaddamar ta fara ne bayan da aka kori ma'aikatan daga kamfanonin hako man kasar.
Daga nan ne sai kungiyar PENGASSAN ta bukaci gwamnatin kasar da ta tilasta wa kamfanin don su mayar da ma'aikatan da aka kora.
Amma sai kamfanonin suka yi kememe.
Mai magana da yawun kungiyar ya Kwamred Obi Fortune ya tabbarwar BBC shirinsu na fara yajin aikin ranar Litinin.
Har ila yau ya ce yajin aikin ne na "sai abin da hali ya yi."
A halin yanzu da ma ana ci gaba da fuskantar karancin man fetur fadin kasar.
Sai dai ma an saba fuskantar irin wannan matsalar yayin karshen kowace shekara.
Karanta wadansu karin labarai

No comments:
Write blogger