Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce goyon bayan da 'yan Nigeria ke nuna masa shi ne babban garkuwan sa.
Ya bayyana haka ne a wani shirin talbijin da fadar shugaban kasar ta dauki nauyi da aka watsa rana Lahadi.
Shugaba Buhari ya ce a duk lokacin da ya yi Sallah ya kan godewa Allah daya sa talakawa ke matukar kaunar sa kuma suka yarda da shi.
Shirin dai ya tattauna ne da shugaban kasar tare da jin ra'ayoyin wasu fitattun 'yan Nigeria.
Daga cikin su har da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da wasu ministocin gwamnatin wadanda suka yi tsokaci kan halayyar shugaban kasar da kuma salon mulkin sa.
Martani
Wasu masu sharhi a shafukan sada zumunta da muhawara sun yi ta sukar shirin da aka watsa ta gidan talbijin.
Wani dan Jarida mai suna Ja'afar Ja'afar ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa;
".....na kwashe sa'a guda ina bata lokaci wajen kallon shirin da babu komai a ciki illa shirme ..Ban yahewa wallah!
Shi kuwa Idris Mohammed ya rubuta a shafin sa na Facebook cewa;
''Kasancewar mutane miliyan 12 ne suka zabi shugaba Buhari har yanzu suna goyon bayan sa fiye da shekaru goma, babu wani dan siyasa da ya kama kafar sa.. Ko yau aka yi zabe shine zabi na."
Sai dai wani mai suna Yakubu Lere cewa ya yi;
''Na fara kallon shirin a matsayina na kwararren ma'aikacin watsa labarai fiye da shekaru 30, amma na ji takaici har sai da na kashe akwatin talbijin di na".....
Wasu dai sun zargi fadar shugaban kasar da neman karkata hankalin 'yan Nigeria game da matsalar karancin mai da ake fuskanta a halin yanzu.
Sai dai a martanin daya mayar, mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa duk da wahalar karancin mai da ake fuskanta na kankanen lokaci, ya zama wajibi a waiwayi wani batu mai farantawa al'umma rai.
Wasu masu lura da al'amura a Najeriyar dai na ganin wannan shiri tamkar sharar fage ne kan shirye shiryen shugaba Buhari na sake tsaya wa takarar 2019.
Sai dai kawo yanzu shugaba Buhari bai fito fili ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takarar ba.
No comments:
Write blogger