Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen yakin guda 12 samfurin A29 Super Tucano a cikin wata wasika sa ta aikewa rundunar sojan samar kasar.
Da yake gabatar da wasikar, jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington ya bayyana kudurin gwamnatin kasarsa na taimakawa Najeriyar cin galaba kan mayakan kungiyar Boko Haram.
Ya kuma ce wannan ya hada da taimakawa Najeriya kawar da duk wani nau'in ta'addanci daga cikin iyakokinta.
Jakadan na Amurka ya ce ko baya ga sayar da jiragen, gwamnatin kasarsa a shirye ta ke ta taimakawa rundunar sojin saman ta Najeriya a kokarin da take yi na kara karfafa mayakanta ciki har da rika samar mata da kayayyakin gyara da kuma tattalin jiragen.
Gwamnatin ta Donald Trump kuma ta ce a shirye take ta mika wa Najeriya wadannan jiragen tun da wuri amma sai ta biya kudinsu lakadan.
Babban hafsan sojan saman Najeriya Air Marshall Sadique Baba Abubakar, wanda ya karbi wannan wasikar a madadin rundunar ya yaba da wannan mataki na Amurka.
Ya kuma ce ba da bata lokaci ba zai bayar da sunayen matuka da kanikawan jiragen yakin rundunar domin a ba su horo a kasar ta Amurka kan yadda za su sarrafa wadannan jiragen.
A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labarai na rundunar sojan saman ta Najeriya Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya ta ce ana sa ran kammala sa hannu a kan yarjeniyoyin cinikin da kuma biyan kudin jiragen kafin ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2018.
Gwamnatin Donald Trump ta amince da bukatar sayar wa Najeriya wadannan jiragen yakin domin yakar kungiyar Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Tun a shekara ta 2014 ne Najeriya ta bukaci sayen jiragen daga kasar ta Amurka.
Amma a wancan lokacin gwamnatin tsohon shugaba Barrack Obama ta ki amincewa da hakan saboda damuwar da take da ita cewa mai yiwuwa a yi amfani da makaman wajen keta hakkin bil adama.
No comments:
Write blogger