Tottenham na fatan kare kambunta, kuma koma dai me zai faru a karawarsu da Manchester City ranar Asabar, su dai suna fafatukar yadda za su kare a cikin manyan kungiyoyi hudu na teburin firimiya.
Sai dai kungiyar har yanzu za ta iya jajircewa a wasan nasu don samun nasara a gaba, inda suka fara yadda zasu tunkari wasan.
A kungiyar da take magana game da kansu a matsayin zakarun gasar Firimiya na nan gaba, tarihin da suka kafa a karkashin jagorancin Pochettino a wasansu a waje da sauran karawarsu a kakar bara sun kare ne a cikin manyan kungiyoyi shida a teburin firimiya.
Ba wai kawai rashin nasarar da suke samu a sakamakon wasansu ba. Ba zan iya tuna wani kokari da kungiyar ta yi a kowanne wasa da ta buga a waje ba, daga White Hart Lane ko Wembley.me.
Saboda haka ya kamata a wannan karon su sauya salo, su kuma jajirce a manyan wasan da zasu tunkara.
Hakan zai iya faruwa idan suka nuna kwazo, musamman a lokacin da zasu fara, fiye da idan suka dogara da tunanin da suke na cewa, "Mun iya buga tamaula, mun zo ne don mu taka leda mai kyau", sai ta zo musu da sanmatsi, kamar yadda suka yi da Arsenal a watan November.
A wurina, Kungiyar tana gani zata iya samun dukkan nasara a wasan da zai zo a nasu tunanin. Ko suna da yakinin cewa kungiyar zata iya samun gurbin zama ta hudu a teburin Firimiya?
Suna son su nuna hakan yauzu, saboda duk abin da na gani a wurinsu a Anfield ko Old Trafford sama da shekaru da dama da suka shude, musamman kuma a filin wasa na Emirates a kakar bana, abu ne da basu da yakini.
Victor Wanyama bai taka leda ba tun watan Agusta sakamakon raunin da ya ji, kuma Pochettino bai samu mai tsaron tsakiya da zai maye gurbinsa ba.
Harry Wink yana kokari wajen taka leda, kuma akwai lokutan da ya taka rawa sosai amma salon wasan da ya buga ya ba wa wasu 'yan wasan dama.
Ba zan ce Spurs sun samu matsala a kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ba, saboda sun sayo Davinson Sanchez wanda kuma yana cikin manyan 'yan wasa.
Sai dai sun rasa fitaccen mai tsaron baya a Firimiya lokacin da Kyle Walker joined ya koma City.
Idan ka kalli City da kuma yadda take taka leda a bana, ta sha gaan kungiyoyi.
Babban fatan da Spurs take yi shi ne ta mamayesu, ba wai su koma tsren baya ba. Idan kuka yi haka kuwa daga karshe City zata kai ku kasa.
Na ga yadda kungiyar Shakhtar Donetsk da Napoli suka yi da City a wasansu na zakarun Turai, dukkansu sun taka rawar gani kodayake ba suyi nasara.
Idan suka jajirce, ina ganin Spurs zata iya cin kwallo ranar Asabar.
No comments:
Write blogger