Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce an samu nasarar kubutar da turawan nan hudu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a makon jiya.
An sace mutanen hudu ne da suka hada da Amurkawa biyu da 'yan kasar Canada biyu a lokacin da suke aikin samar da hasken lantarki ta hanyar amfani da hasken rana a Najeriya. A ranar Talatar da ta gabata ne aka sace turawan a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa Abuja daga Kaduna.
An shiga neman turawan ne gadan-dagan jim kadan bayan sace su, inda aka tura jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma wani jirgi mai saukar ungulu cikin daji domin neman turawan.
Kwamishinan 'yan sanda ta jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, an kubutar da turawan ne a wani daji bayan da wadanda suka sace su suka gudu suka bar su a wajen, amma kuma an yi nasarar kama daya daga wadanda ake zargi da sace turawan
Yanzu haka dai an duba lafiyar turawan.
Wasu 'yan bindiga ne dai suka yi wa jerin gwanon motocin turawan kwantan bauna a wani daji dake da nisan kilomita 200 daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an kashe 'yan sandan Najeriya biyu da ke bawa turawan kariya a lokacin satar turawan .
Satar mutane don neman kudin fansa na dada kamari a Najeriya, a dai-dai lokacin da kasar ke fama da rikicin Boko Haram da matsin tattalin arziki mafi tsanani a shekaru da dama.
Kuma Jihar Kaduna na daga cikin sassan kasar da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa.
Ko a watan Fabrairun bara an taba sace wasu Jamusawa guda biyu, kafin daga bisani aka sake su. Haka ma a watan Oktoban da ya gabata an sace wasu Turawan Birtaniya a yankin Neja Delta inda aka saki uku, bayan an kashe daya daga cikinsu.
No comments:
Write blogger