spon

Monday, April 2, 2018

Home Kannywood: Ni Da Sake Yin Aure Ba Yanzu Ba – Inji Fati Kk

Subscribe Our Channel


Tun ba yau ba ake rade-radi kan mutuwar auren ta wanda ya sanya har ta kwaso kayanta daga Kano zuwa Kaduna, garin iyayenta.Auren ta na biyu da tsohon mijinta wanda yayi sanadiyar komawar ta Kano, Allah ya albarkace su da yara biyu,Ahmed da Yasmin.

A hirar ta da wakilin jaridar Leadership Ayau, Fati KK ta fayyace masa labarin dalla-dalla kan yadda al’amura suka kasance har suka rabu da mijinta.

“To ni dai abin da zan iya cewa, ni dai har ga Allah ya sani, wadanda muke tare da su su ma sun sani, na so zaman aure.In da ba na son zama da shi, wallahi ba zan mike kafafu na yi ta zuba ‘ya’ya ba. Na fuskanci gori daban-daban duk na shanye, kuma hakan bai sa ni bijirewa ba har na ce a sake ni ba, na kan zauna in yi kuka, watarana sai na fada masa, sai na gane in har wani ya ki ka, ai Allah na son ka. Na fuskanci kalubale kala-kala, sai dai in ce mun gode Allah.”

Jarumar wacce aka daina jin duriyarta a fagen shirya fim bayan auren ta ta bayyana cewa dangin mijinta sun zargi ta da bijire ma mijinta bayan ta samu labarin cewa zai kara aure. Tace basu fahimce ta ba domin bata da kishin samun kishiya. Haka zalika bazata zabi rabuwa da mijinta kan matsalar rashin kudi/talauci.

“Mun haihu da shi yara biyu, Abu ya ki ci, ya ki cinyewa, a gaskiya talauci bai taba sa na ce zan rabu da wanda nake tare da shi ba. Na dai samu surutai a cikin danginsa, wai don zai kara aure ne na bijire masa na ce ya sake ni, alhalin wallahi tallahi, wallahi tallahi, wallahi tallahi ban san wannan zancen ba, ban ma taba jin sa ba. ”

No comments:
Write blogger