Ma'aikatar kula da harakokin sufurin jiragen sama a Najeriya ta ce zuwa karshen shekara jirgin saman kasar zai fara aiki.
Ministan ma'aikatar Hadi Sirika ya ce zuwa watan Disamban bana yake fatan kamfanin jiragen saman na Najeriya zai fara aiki.
Sai dai batun farfado da kamfani jirgin saman na Najeriya na hadin guiwa ne da 'yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar kawai da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa.
Ya jaddada hakan ne a yayin da yake karbar takardar shedar amincewa da yarjejeniyar kasuwanci daga babban jami'in hukumar kula da mika ragamar tafiyar da kadarorin gwamnati ga kamfanoni masu zaman kansu (ICRC), injiniya Chidi Izuwah.
Ya kuma ce gabatar da takardar shedar shi ne amincewa da matsayin da ake ciki ga aikin.
Ministan ya kuma musanta ikirarin da wasu ke yi cewa farfado da kamfanin jiragen saman na kasa zai durkusar da kamfanonin jiragen sama na 'yan kasuwa ke aiki a kasar.
"Najeriya mai yawan jama'a sama da miliyan 180 tana da isassun hanyoyin da dukkanin jiragen da suka shirya wa kasuwanci za su iya aiki" in ji Sirika.
Jama'ar Najeriya mai karfin tattalin arziki a Afirka na dogaro ne da kamfanonin jiragen 'yan kasuwa masu zaman kansu.
Wasu na ganin farfado da kamfanin jirgin sama na Najeriya zai taimaka wajen samun saukin tsadar farashin tikitin shiga jiragen sama na 'yan kasuwa a Najeriya.
Ko da yake kamfanonin jiragen saman na cewa dole kujerar jirginsu ta yi tsada saboda yawan kudaden harajin da suke biyan gwamnati.
Za a iya samu wadatuwar jiragen saman zuwa wasu sassa na kasar da jiragen 'yan kasuwa ba su zuwa idan kamfanin na Najeriya ya fara aiki.
A can baya Najeriya tana da kamfanin Air Nigeria da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma'aikata.
Durkushewar kamfanin ya haifar da rasa ayyukan yi ga ma'aikata da dama.
No comments:
Write blogger