Babban bankin Najeriya (CBN) ya ci manyan bankuna hudu tarar dala miliyan 16 (kimanin naira biliyan biyar da miliyan 800) bayan an zarge su da taimaka wa kamfanin sadarwar na MTN fitar da dala biliyan takwas (kimanin naira triliyan biyu da miliyan 900) daga kasar ba bisa ka'ida ba.
An bai wa bankunan da kamfanin MTN umarnin mayar da kudaden.
Bankunan da aka ci tarar sun hada da Standard Chartered Bank da Stanbic IBTC da Citibank da kuma Diamond Bank.MTN ta musanta zargin fitar da kudade daga kasar ba bisa ka'ida ba, kuma daya daga cikin bankunan ya ce yana tattaunawa da babban bankin kasar kan batun.
- Kalli yadda aka mamaye ofishin MTN kan 'muzgunawa' ma'aikata
- Nigeria: Matasa sun kai harin ramuwar-gayya kan ofishin MTN
- MTN zai biya Najeria tarar Naira 330bn
An fara bincike a kan kamfanin bisa zargin karya dokar musayar kudi a shekarar 2016 ne, amma daga baya majalisar dattawan kasar ta wanke shi daga laifi.
Dokokin Najeriya sun yarda a fitar da kudade daga kasar, amma bisa wasu sharudda.
Bankin Stanbic IBTC ya fitar da wata sanarwa inda ta ce tana tattaunawa da babban bankin kasar kan lamarin.
Kawo yanzu dai sauran bankunan ba su ce komai ba kan batun.
MTN shi ne kamfanin sadarwa da ya fi girma a nahiyar Afirka kuma hukumar kula da fannin sadarwar Najeriya ta kakaba masa tarar dala biliyan biyar a shekarar 2015 domin rashin mutunta umarnin gwamnati na katse layuka mutane miliyan biyar da ba a yi musu rijista ba.
Daga baya an rage tarar zuwa dala biliyan daya da miliyan 700.
MTN yana da masu aiki da layinsa fiye da miliyan 50 kuma kasar ta kunshi kashi 30 cikin 100 na masu aiki da mu'amala da kamfanin.
MTN ya mayar da martani
Da yake mayar da martani, MTN ya zargi babban bankin Najeriya da karya wa masu zuba jari gwiwa bayan bankin ya yi zargin cewa kamfanin ya fitar da dala biliyan takwas (wato naira tiriliyan 2.9) daga kasar ba bisa ka'ida ba.
Sanarwar da MTN din ya fitar, ta ce majalisar dattawan Najeriya ta binciki zargin fitar da kudin da aka yi wa kamfanin kuma ta gane cewa kamfanin "bai hada baki ba wajen karya dokokin musayar kudade ba."
Ta kara da cewa MTN kamfani ne mai biyayya ga doka, kuma zai kare kansa.
"Abin takaici ne cewa wadannan al'amura sun sake kunno kai domin zai karya wa masu zuba hannun jari gwiwa, kuma zai iya dakile habakar tattalin arzikin Najeriya," kamar yadda sanarwar MTN ta bayyana.
No comments:
Write blogger