*A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA'I GUDA UKKU*
         *Na farko 1*
*Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.*
*Idan kudinsa ya ragu xai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.*
        *Na biyu 2*
*kullum yana cin arxikin Allah in halal yaci xa'a tambaye shi in haram ne xa'ayi masa axaba akai bai san karshen hisabin mai xai kasanceba.*
      *Na uku 3*
*kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda yadamu da duniya Bai san makomarsa ba shin aljannace ko wutace.*
  *GASKIYA*
 *Babu abunda xai amfaneka sai sallarka/ki*
*wanda yabar karatun Alqur,ani tsawon kwana uku ba tare da uxuriba sunansa MAQAURACI wanda ya qauracewa Alqur,ani kenan.*
  *Duniya kwana 3 ce*
   
 *Jiya: munganta baxata dawoba*
*Yau: muna cikinta baxata dauwama ba xata wuce*
*Gobe: bamusan ina xamu kasanceba.*
*ka gaisa da mutane, kayimusu afuwa kayi sadaka domin ni da kai dasu duk Matafiyane bissalam.*
BARKA DA WARHAKA.
Wednesday, September 12, 2018
Subscribe Our Channel
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Write blogger