spon

Saturday, October 13, 2018

Home › › Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin mataimakinsa

Subscribe Our Channel


Dan takarar mukamin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra a matsayin mataimakinsa a zaben 2019.
Bayanin na cikin wata sanarwa da Mista Gbenga Daniel, babban daraktan kungiyar yakin neman zabe na Atiku ya sanya wa hannu a ranar Jumma'a.
Sanarwar ta ce Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi ne saboda kwarewarsa a fagen kasuwanci da gogewarsa a fagen hulda da jama'a.

Wane ne Peter Obi?

An haifi Mista Peter Obi a 1961, kuma ya halarci makarantar Christ the King College da ke birnin Onitsha, kana daga baya ya je jami'ar Najeriya da ke Nsukka inda ya sami digirin Falsafiya.
Ya kuma halarci wasu makarantun da suka hada da Lagos Business School, da Harvard Business School, da London School of Economics, da Columbia Business School, da kuma jami'ar Cambridge da ta Oxford.
Ya rike mukamai da dama a lokutan da yayi aiki kamar, mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, da gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Ya rike mukamin gwamnan Ananbra na shekara takwas, inda ya sauka a watan Maris na 2014, kuma gwamna mai ci Willie Obiano ne ya gaje shi.
Dan takarar mukamin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra a matsayin mataimakinsa a zaben 2019. Bayanin na cikin wata sanarwa da Mista Gbenga Daniel, babban daraktan kungiyar yakin neman zabe na Atiku ya sanya wa hannu a ranar Jumma'a. Sanarwar ta ce Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi ne saboda kwarewarsa a fagen kasuwanci da gogewarsa a fagen hulda da jama'a. Wane ne Peter Obi? An haifi Mista Peter Obi a 1961, kuma ya halarci makarantar Christ the King College da ke birnin Onitsha, kana daga baya ya je jami'ar Najeriya da ke Nsukka inda ya sami digirin Falsafiya. Ya kuma halarci wasu makarantun da suka hada da Lagos Business School, da Harvard Business School, da London School of Economics, da Columbia Business School, da kuma jami'ar Cambridge da ta Oxford. Ya rike mukamai da dama a lokutan da yayi aiki kamar, mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, da gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya. Ya rike mukamin gwamnan Ananbra na shekara takwas, inda ya sauka a watan Maris na 2014, kuma gwamna mai ci Willie Obiano ne ya gaje shi.

No comments:
Write blogger