A yau Laraba jami’an sojin Nijeriya suka mikawa rundunar ‘yan sanda wasu mutum 13 da ake zargin suna da hannu a batan janar din, a garin Jos hedikwatar jihar Filato.
Dukkan mutanen an kama su inda aka samu motar janar din, wato kusa da unguwar Dura-Du dake kauyen Du, karamar hukumar Jos ta kudu, bayan wani binciken da jami’an sojin suka gudanar a yankin.
Hukumar sojin ta mika mutanen da ake zargin ne ga rundunar ‘yan sanda, don gudanar da cikakken bincike da kuma hukunta duk wanda aka kama da laifi, cikin wadanda aka mika su ga rundunar ‘yan sandan akwai wadanda aka kamasu da bindigu.
Har wayau, jami’an sojin sun ce akwai mutanen da ake zargin da hannun su a batan janar din, amma sun gudu, sai dai jami’an sojin suna sane da su, kuma zasu cafko su, don fuskantar doka.
#Leadership
No comments:
Write blogger