Fim Din ‘Yar Mai Ganye Ya Fito Kasuwa
Daya daga cikin Fina-Finan Kannywood da ya samu ingantaccen aiki wanda aka jima a na jiran fitowarsa wato ‘Yar Mai Ganye ya fito kasuwa a ranar yau Lahadi.
‘Yar Mai Ganye fim ne da mata suka baje kolinsu tare da cin duniyar su da tsinke tamkar an halacce su domin su bautar da maza.
Sabon Fim din ‘Yar Mai Ganye shine ne irinsa na farko da mata ke sarrafa mazajen su son ransu. “Gashin aya a tafin hannu abubuwa ne da magidanci ya fuskanta a fim din.”
Shin ku na son ganin yadda uwar gida ke juyawa tare da sarrafa mijinta son ranta yadda take so? Kuna son ganin yadda maigida ke dafa abinci, ya share gida ya wanke motar uwar gida, idan kuma ya ki aradu ta far masa? To ku nemi ‘Yar Mai Ganye.
“Ko ba komai mata iyayen giji, in ba ku ba gida, idan kuma kun yi yawa gida ya gyaru. Duk da irin baiwar da Allah ya yi masu ta sarrafa mazaje a tafin hannun su amma sun zabi bin bahaguwar hanya domin cimma biyan bukata ta barauniyar hanya.”
‘Yar Mai Ganye fim ne kan yadda Hadiza Muhammad (‘Yar Mai Ganye) ke amfani da karfin bokanci wajen taimakawa mata domin su mallake mazajen su cikin ruwan sanyi tare da mayar da maigida kwatankwacin mijin ta-ce ko mijin kafin- ta – ce.
Ali Gumzak SAK fitaccen Daraktan da tauraruwarsa ke haskawa daidai da farin wata ne ya bayar da umurnin fim din a yayin da fitacce kuma kwararren hazikin Furudosa mai tashe wato Abdul’aziz Dan- Small ya shirya fim din ‘Yar Mai Ganye. Tsinin Alkalamin Masanin Sirrinsu kuma shahararrren marubuci nan na jiya wanda ake jin amonsa a duniyar yau Maje El-Hajeej Hotoro ne ya rubuta tare da tsara labarin. Shi kuwa Dan Kasuwar Kasa da Kasa Alhaji Yusuf Yunusa ya dauki nauyin shirya fim din a karkashin kamfaninsa BGM FILM PRODUCTIONS.
Jaruman da suka jagoranci shirin ‘Yar Mai Ganye sune da Hadiza Muhammad, Rabi’u Rikadawa, Aina’u Ade, Halima Atete, Sulaiman Bosho, Hajara Usman, Saratu Gidado, Nuhu Abdullahi, Jamila Nagudu, Sadiya Adam, Maryam Yahaya, Amar Umar tare da gabatar da sababbin fuskoki biyu wato Momi Chiroma da Lubabatu Muhammad.
‘Yar Mai Ganye Fim ne da aka yi wa ingantaccen aiki a kololuwar mataki na kwararru wanda kuma aka sanya natsuwa tare da zabar ‘yan wasa a bisa ga kwarewa da cancanta. Tabbas hakika ‘Yar Mai Ganye fim ne da da zai kayatar ya kuma burge mai kallo.
No comments:
Write blogger