spon

Monday, July 9, 2018

Zaben Gwamnan Ekiti: Yadda Aka Bada Tsaro

ZABEN GWAMNAN EKITI: A yayin da ake shirye shiryen zaben kujerar Gwamnan Ekiti a ranar Asabar mai zuwa, Shugaban ‘Yan sanda na Kasa, Ibrahim Idiris ya tura ‘yan sanda 30,000, karnuka na musamman, jiragen masu saukar Angulu guda biyu, kananan motocin yaki 10, motocin sintiri 250, sai mataimakinsa, da kwamishinonin ‘yan sanda hudu don tabbatar da tsaro.

A yayin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ( FRSC) ta tura jami’anta har 500, motocin sintiri 24, motocin daukar marasa lafiya guda uku.

RANAR WANKA...

RANAR WANKA...

Hakikanin Abin Da Ya Jawo Rikici Na Da Kwankwaso, Cewar Gwamna Ganduje

 “Kun taba jin muna fada a lokacin da yake (Kwankwaso) Gwamna? San-sam. Ina yi masa biyayya a matsayinsa na Gwamna kuma Ubangidana. Lokacin da Buhari ya fada mani cewa zai yi takarar Shugabancin Kasa, na fada masa cewa ni Kwankwaso zan zaba. Shugaban Kasa (Buhari) ya ji dadin yadda na bayyana masa gaskiyata ba kwane-kwane. Dukkanmu da muka je Legas sai muka zabi Kwankwaso kuma duk da cewa mun fadi zaben amma dai ba mu munafunce shi (Kwankwaso) ba. Ya kasance shugabanmu a Kano, duk da cewa talakawan Kano Buhari suka zaba, mu Kwankwaso muka zaba…
*
“Sai dai abin takaici, Kwankwaso ba ya kallona ko amincewa da ni a matsayin Gwamna, ya yi zaton ladabin da nake masa a matsayina na Mataimakinsa kamar ni wawa ne.
*
“Ka tambayi duk wanda ya san ni, ba na kaskantar da duk wani tsohon Gwamna. Dangantakata da Shekarau mai girma ce kuma mai kyau, shi ma yana daraja ni a matsayina na Gwamna. Shin mene ne yake haddasa rashin jituwa tsakanina da Kwankwaso? Matsalar ba daga gare ni ba ce ko daya, shi ne dai yake son amfani da al’ummar Kano da dukiyar Kano domin ya kalubalanci Shugaban Kasarmu da muke jam’iyya daya. Haba! Ba zan taba amincewa da haka ba, domin Buhari ya taimaka mana a lokacin da ma ba jam’iyya daya muke da shi ba. Buhari ba mamugunci ba ne, ba zai iya makirci don kaskantar da kowa, ko raba shi da mukaminsa ba. Shi ne Shugaba a yau. Da Kwankwaso ne ya ci zaben, ba zan bari Buhari ya wulakanta shi ba.
*
“Duk wanda ke son barin (APC), ya bari kawai. Mu yi siyasa mai tsafta, mai natsuwa…”

Fassara: Bashir Yahuza Malumfashi

DA DUMIDUMINSA

DA DUMIDUMINSA

Membobin Sabuwar Jam'iyyar APC Da Na PDP Sun Yi Zaman Kulla Yarjejeniya Domin Kada Buhari A Zaben 2019

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - Sirika

Ma'aikatar kula da harakokin sufurin jiragen sama a Najeriya ta ce zuwa karshen shekara jirgin saman kasar zai fara aiki.
Ministan ma'aikatar Hadi Sirika ya ce zuwa watan Disamban bana yake fatan kamfanin jiragen saman na Najeriya zai fara aiki.
Sai dai batun farfado da kamfani jirgin saman na Najeriya na hadin guiwa ne da 'yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar kawai da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa.
Ya jaddada hakan ne a yayin da yake karbar takardar shedar amincewa da yarjejeniyar kasuwanci daga babban jami'in hukumar kula da mika ragamar tafiyar da kadarorin gwamnati ga kamfanoni masu zaman kansu (ICRC), injiniya Chidi Izuwah.
Ya kuma ce gabatar da takardar shedar shi ne amincewa da matsayin da ake ciki ga aikin.
Ministan ya kuma musanta ikirarin da wasu ke yi cewa farfado da kamfanin jiragen saman na kasa zai durkusar da kamfanonin jiragen sama na 'yan kasuwa ke aiki a kasar.
"Najeriya mai yawan jama'a sama da miliyan 180 tana da isassun hanyoyin da dukkanin jiragen da suka shirya wa kasuwanci za su iya aiki" in ji Sirika.
Jama'ar Najeriya mai karfin tattalin arziki a Afirka na dogaro ne da kamfanonin jiragen 'yan kasuwa masu zaman kansu.
Wasu na ganin farfado da kamfanin jirgin sama na Najeriya zai taimaka wajen samun saukin tsadar farashin tikitin shiga jiragen sama na 'yan kasuwa a Najeriya.
Ko da yake kamfanonin jiragen saman na cewa dole kujerar jirginsu ta yi tsada saboda yawan kudaden harajin da suke biyan gwamnati.
Za a iya samu wadatuwar jiragen saman zuwa wasu sassa na kasar da jiragen 'yan kasuwa ba su zuwa idan kamfanin na Najeriya ya fara aiki.
A can baya Najeriya tana da kamfanin Air Nigeria da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma'aikata.
Durkushewar kamfanin ya haifar da rasa ayyukan yi ga ma'aikata da dama.

Jirgin kasa ya kauce hanya, ya kashe mutum 24

Jirgin da ya yi hadari a kusa da kan iyakar kasar da Bulgaria
Akalla mutum 24 ne suka mutu bayan da wani jirgin kasa ya kauce wa hanya a arewa maso yammacin Turkiyya, kamar yadda mataimakin Firaminista Recep Akdag ya ce.
Jirgin yana kan hanyarsa ne zuwa Istanbul daga Kapikule da ke kan iyakar kasar da Bulgaria.
Tarago shida na jirgin ne ya kaucewa hanya wanda ke dauke da fasinjoji kusan 360, a cewar kafar yada labarai ta kasar TRT.

Babu tabbas kan musabbabin hadarin amma mahukunta sun alakanta lamarin da rashin kyawun yanayi.
Sai dai sashin Turkiyya na CNN, ya ce rushewar wata gada ce ta haifar da hadarin.
Wata majiya a Rasha ta ce akwai 'yan yawon bude ido na kasar a cikin wadanda suka samu rauni.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya tura sakon ta'aziyyarsa ga wadanda suka mutu bayan ya samu bayani daga ministocinsa.



PSG na son Coutinho, Madrid ta matsa kan Hazard, ina Ozil zai koma?

Paris St-Germain na neman sayen dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 26, kan fam miliyan 239, domin hakan ya taimaka wurin shawo kan Neymar ya ci gaba da zama a kulob din, kamar yadda jaridar Mundo Deportivo ta rawaito.
Wasu rahotannin kuma na cewa Neymar, mai shekara 26, na son ganin Edinson Cavani ya bar PSG, inda ake ganin akwai yiwuwar dan wasan gaban na Uruguay ya koma Napolia cewar (Sport).
Manyan 'yan wasan biyu sun samu sabani a kakar da ta gabata kan neman iko a kulob din.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez tuni ya warewa Eden Hazard jesi da lambar da zai saka idan har dan kwallon mai shekara 27 na Chelsea da Belgium ya koma Bernabau da murza-leda, kamar yadda Diario Gol ta rawaito.

Dan uwan Antonio Conte ya bayyana alamun da ke nuna cewa kocin dan kasar Italiya zai ci gaba da zama a Chelsea, a daidai lokacin da ake nuna rashin tabbas kan makomarsa, a cewar Daily Mirror
Manchester City ta amince ta biya fan miliyan 60 domin sayen dan wasan gaba na Leicester Riyad Mahrez, mai shekara 27, kuma ana sa ran za a gwada lafiyar dan kwallon na Algeria nan da sa'a 48, kamar yadda jaridar Daily Mail ta rawaito.
Arsenal na tattaunawa da Lorient domin sayen dan kwallon Faransa mai shekara 19 Matteo Guendouzi, a cewar (Sky Sports).


Majalisar Borno Ta Tsayar Da Shettima Takarar Sanata

Majalisar Borno Ta Tsayar Da Shettima Takarar Sanata
__¥___
*
'Yan majalisar dokokin jihar Borno sun nemi Gwamnan jihar, Kashim Shettima kan ya fito takarar kujerar dan majalisar Dattawa na Borno ta Tsakiya.

Kakakin Majalisar, Abdulkarim Lawan ya ce, ya zama dole Gwamnan ya fito takara don al'ummar mazabarsa sun amfana da irin kwarewarsa da iliminsa. Tun da farko dai, Gwamnan Shetiima ya fito fili ya nuna cewa idan har wa'adinsa ya cika, zai koma aikin koyarwa ne.