spon

Monday, July 9, 2018

Jack Wilshere ya koma West Ham United

Jack Wilshere ya buga wa Ingila wasa sau 34
Tsohon dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya koma West Ham kan yarjejeniyar shekara uku, inda ya ce ya koma kulob din da ya dade yana kauna tun yana yaro.
Kwantiragin dan kwallon mai shekara 26 ta kare da Gunners a karshen watan Yuni.
"Har yanzu ina tuna lokacin da nake goyon bayan West Ham a lokacin da ina karami, na sha kallonsu a filin wasa na Upton Park," a cewarsa.
West Ham na kuma dab da kulla yarjejeniya domin sayen dan kwallon Ukraine Andriy Yarmolenko.
An fahimci cewa kudin da aka amince da Borussia Dortmund ya kai fan miliyan £17.66.

PDP ta yi kawance da jam'iyyu 40 'don doke Buhari'

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta kulla wani sabon kawance da wadansu jam'iyyu fiye da 40 da ke kasar, gabanin babban zaben shekarar 2019.
Jam'iyyun sun sanar da hakan ne lokacin wani taro da suka yi a Abuja ranar Litinin, inda suka yi wa kawance lakabi da Coalition of United Political Parties (CUPP).
Sanarwar ta biyo bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka cimma da shugabannin jam'iyyun,"don kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019," a cewarsu
Yarjejeniyar ta kunshi wani shiri ta yadda za su tsayar da dan takara daya tilo a zaben shugaban kasa, da na gwamnoni a jihohi da kuma kujerun majalisa.
Sai dai zuwa yanzu jam'iyya mai mulki ta APC ba ta mayar da martani ba, game da batun.
Cikin wadanda suka halarci taron har da shugaban sabuwar jam'iyyar APC Injiniya Buba Galadima da kuma mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da sauransu.
A shekarar 2015 ne jam'iyyar APC ta doke PDP a babban zaben kasar, bayan ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar.

Cristiano ronaldo yasa hannu daga tashi daga Madrid zuwa juventus

Cristiano ronaldo yasa hannu daga tashi daga Madrid zuwa juventus

Ronaldo Dan wasan kwallon kafa ne Wanda yakafa tariyi tun a Manchester saboda ba ayi Dan wasan kamar Ronaldo tun sanda yana Madrid yayiwa juventus cin wula kanci

Buhari Ya Yabawa Juriyar Saraki A Shari`Arsa

Buhari ya yabawa juriyar Saraki a shari’arsa: Yace ya zama abin koyi ga ‘Yan Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da wanke shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da kotun koli ta yi.
Shugaban ya ce duk da kalubalen da bangaren shari’ar kasar ke fuskanta amma hakan ya nuna bangaren na aiki sosai, kuma babu wanda za a bari ya karya tsarin.
Shugaban ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu.

“Na ga shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya bi tafarki mafi wahala na bin matakan shari’a, ya jure, kuma daga karshe kotun koli ta ce ba ya da laifi” in ji shugaban.
Ya kara da cewa:
“Akwai wasu lokutta da dama da wasu mutane cikin rashin tunani suke neman kawo lalaci ga bangaren shari’a duk don su kare kansu maimakon mayar da hankali ga bin matakan da za su wanke kansu.”
“Abinda na yi ke nan a zabuka uku da aka zalunce ni, kafin Allah ya ba ni damar tsayawa takara a karo na hudu.” Inji Buhari
Buhari ya ce yadda Saraki ya dinga yawo tun daga karamar kotu zuwa kotu mafi girma a Najeriya ya zama babban misali da ya kamata dukkanin ‘yan Najeriya su yi koyi da shi.

An Kai Sabbin Hare Hare Kan Fulani A Filato

An Kai Sabbin Hare hare Kan Fulani A Filato
__¥___
*
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar cewa wasu matasa ‘yan kabilar Birom sun kai wasu hare hare a kan wasu makiyaya Fulani da ke zaune kusa da kwalejin ‘yan sanda da ke garin Buruku a karamar hukumar Jos ta Yamma.




Rahotanni sun nuna cewa, babu wanda ya rasa ransa a yayin harin sai da wasu Fulani su biyu da aka yi wa rauni da kuma wata karamar saniya da aka kashe. Kakakin Rundunar ‘Yan sanda, Tyopev Terna ya tabbatar da cewa an warware rikicin bayan wani zama da aka yi tsakanin masu ruwa da tsaki a rikicin.
#Rariya

Zaben Gwamnan Ekiti: Yadda Aka Bada Tsaro

ZABEN GWAMNAN EKITI: A yayin da ake shirye shiryen zaben kujerar Gwamnan Ekiti a ranar Asabar mai zuwa, Shugaban ‘Yan sanda na Kasa, Ibrahim Idiris ya tura ‘yan sanda 30,000, karnuka na musamman, jiragen masu saukar Angulu guda biyu, kananan motocin yaki 10, motocin sintiri 250, sai mataimakinsa, da kwamishinonin ‘yan sanda hudu don tabbatar da tsaro.

A yayin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ( FRSC) ta tura jami’anta har 500, motocin sintiri 24, motocin daukar marasa lafiya guda uku.

RANAR WANKA...

RANAR WANKA...

Hakikanin Abin Da Ya Jawo Rikici Na Da Kwankwaso, Cewar Gwamna Ganduje

 “Kun taba jin muna fada a lokacin da yake (Kwankwaso) Gwamna? San-sam. Ina yi masa biyayya a matsayinsa na Gwamna kuma Ubangidana. Lokacin da Buhari ya fada mani cewa zai yi takarar Shugabancin Kasa, na fada masa cewa ni Kwankwaso zan zaba. Shugaban Kasa (Buhari) ya ji dadin yadda na bayyana masa gaskiyata ba kwane-kwane. Dukkanmu da muka je Legas sai muka zabi Kwankwaso kuma duk da cewa mun fadi zaben amma dai ba mu munafunce shi (Kwankwaso) ba. Ya kasance shugabanmu a Kano, duk da cewa talakawan Kano Buhari suka zaba, mu Kwankwaso muka zaba…
*
“Sai dai abin takaici, Kwankwaso ba ya kallona ko amincewa da ni a matsayin Gwamna, ya yi zaton ladabin da nake masa a matsayina na Mataimakinsa kamar ni wawa ne.
*
“Ka tambayi duk wanda ya san ni, ba na kaskantar da duk wani tsohon Gwamna. Dangantakata da Shekarau mai girma ce kuma mai kyau, shi ma yana daraja ni a matsayina na Gwamna. Shin mene ne yake haddasa rashin jituwa tsakanina da Kwankwaso? Matsalar ba daga gare ni ba ce ko daya, shi ne dai yake son amfani da al’ummar Kano da dukiyar Kano domin ya kalubalanci Shugaban Kasarmu da muke jam’iyya daya. Haba! Ba zan taba amincewa da haka ba, domin Buhari ya taimaka mana a lokacin da ma ba jam’iyya daya muke da shi ba. Buhari ba mamugunci ba ne, ba zai iya makirci don kaskantar da kowa, ko raba shi da mukaminsa ba. Shi ne Shugaba a yau. Da Kwankwaso ne ya ci zaben, ba zan bari Buhari ya wulakanta shi ba.
*
“Duk wanda ke son barin (APC), ya bari kawai. Mu yi siyasa mai tsafta, mai natsuwa…”

Fassara: Bashir Yahuza Malumfashi