An jefi kociyan Manchester United Jose Mourinho da ruwa da madara shi kuma mai koyar da 'yan wasan Manchester City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka yayin wata sa-in-sa bayan wasan kungiyoyin biyu ranar Lahadi.
'Yan United sun harzuka ne kan abin da suke gani ya wuce-makadi-darawa a lokacin murnar da 'yan wasan City suke yi bayan sun bi abokan hamayyar tasu har gida Old Trafford sun casa su 2-1, suka yi musu fintinkau da maki 11 a teburin Premier.
'Yan wasan City sun rika burede a gaban magoya bayansu bayan an tashi daga wasan, kuma 'yan tawagar horar da 'yan wasan sun nemi kociyansu Pep Guardiola shi ma ya bi sahu a cashe da shi amma ya ki.
Bayan 'yan wasan gaba daya sun kama hanyarsu zuwa dakunanunsu na sauya tufafi, a nan ne ake ganin Mourinho ya nuna bacin ransa a kofar dakin tawagar Man City, a kan hanyarsa ta zuwa wajen hira da 'yan jarida.
'Yan Manchester City sun mayar da martani inda mai tsaron ragarsu dan Brazil Ederson da Mourinho suka yi cacar-baki da harshen Portugal.
Daga nan ne kuma aka jefi Mourinhon da wani kwalin madara da aka bari a dakin na bakin, ko da yake ba ta bata shi ba amma ta bata wani daga cikin ma'aikatansa.
Kuma an ga kociyan ya shiga dakin alkalin wasa a lokacin daga bisani ya fito ya tafi wajen hira da 'yan jarida, amma dai bai yi maganar abin da ya faru ba a yayin ganawar.
An ga mai horar da 'yan wasan City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka amma ba a san yadda ya ji ciwon ba, kuma dukkanin bangarorin kungiyoyin biyu sun ce ba a ba wa hammata iska ba.
No comments:
Write blogger