spon

Monday, December 11, 2017

Home Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Africa ta BBC

Subscribe Our Channel


Dan wasan kasar Masar da kuma Liverpool, Mohamed Salah, ya ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta BBC ta shekarar 2017.
Bayan ya samu kuri'u masu tarin yawa, Muhamed Salah ya doke dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da dan kasar Guinea Naby Keita da dan Senegal Sadio Mane da kuma dan Najeriya, Victor Moses.
Dan wasan mai shekara 25 ya shaida wa BBC cewar: "Na yi murnar cin wannan kyautar."
"Mutum zai ji dadi na musamman idan ya ci wata kyauta. Za ka ji ka taka rawar gani a shekara, na yi murna matuka. Zan so in sake cin kyautar a shekara mai zuwa!"
Salah, wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar Firimiya da kwallayensa 13, ya taka rawar gani a wannan shekarar a kulob dinsa da kuma kasarsa.
A farkon shekarar 2017, shi ne ya jagoranci kasar Masar a lokacin da 'yan wasanta suka zo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Daga baya a cikin wannan shekarar, dan wasan gaban mai yawan gudu, ya taka rawa a wajen cin dukkan kwallaye bakwai din da suka sa tawagar kasarsa, Pharaohs, ta samu zuwa gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a karon farko tun shekarar 1990 - ya tallafa wajen cin kwallo biyu kuma ya ci kwallo biyar, ciki har da fenareti na karshen da ya yi amfani da shi ya ci Kongo, lamarin ya sa kasarsa ta samu zuwa gasar ta Rasha.
"Ina so na kasance dan Masar da ya fi fice saboda haka ina aiki tukuru," in ji mutumin da ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar kuma na farko tun shekarar 2008.
"Ina bin hanyata kuma ina son kowa a Masar ya bi hanyata."
Iya taka ledar Salah a kungiyar kwallon kafarsa ta yi kyawun yadda yake taka leda wa kasarsa.
A Italiya, ya ci kwallaye 15 kuma ya taimaka a ci wasu 11 a lokacin da ya tallafa wa Roma ta zo ta biyu a gasar Serie A, mataki mafi girma da kungiyar ta kai cikin shekara bakwai, kafin ya koma Liverpool ya kuma ci mata kwallaye 13 cikin wasannin gasar Firimiya 16.
"Zan so in gode wa takwarorina na Liverpool kuma na ji dadin kakar da na yi da Roma. Saboda haka ya zama dole in gode wa abokan taka leda na a can da kuma tawagar kwallaon kafar kasata," in ji Salah.
"Tun da na zo nan, na so in yi aiki tukuru domin nuna wa kowa salon kwallo na. Na so in dawo gasar Firimiya tun da na bar ta, saboda haka ina matukar murna."
Salah ya dauki hankalin masu kallon gasar Firimiya cikin gaggawa a wannan kakar, maimakon irin rawar da ya taka a kakar 2014-15 da ba ta kai haka ba.
"Ya cancanci kyautar," in ji kocin Liverpool Jurgen Klopp, wanda ya bai wa dan wasan kyautar a makarantar kulob din ta horaswa da ke unguwar Melwood.
"Ni wani mutum ne mai sa'a. Na samu damar aiki da wasu 'yan wasa kwararru kadan kuma ina murnar cewa a yanzu da "Mo" nake aiki.
"Ta inda maganar ta yi da di ita ce kasancewarsa matashi har yanzu, yana da damar kara kwarewa, yana da baiwa mai yawa da zai iya kara kwarewa a kai, amman haka ya kamata, da gaske, in yi aiki da shi."
A yanzu haka sunan Salah ya shiga cikin jerin sunayen 'yan wasan Afirka da suka fi fice irin su Abedi Pele da George Weah da Jay-Jay Okocha da kuma Didier Drogba, ta hanyar cin kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta shekara.
"Ina matukar murnar kasancewa kaman su wajen cin wannan kyautar," in ji dan Masar din, wanda ya bi sahun 'yan kasarsa Mohamed Barakat (a shekarar 2005) da kuma madugu Aboutreika (a shekarar 2008) wajen cin kyautar .
Mohamed Salah ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar bayan Mohamed Barakat da Mohamed Aboutreika
Image captionMohamed Salah ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar bayan Mohamed Barakat da Mohamed Aboutreika
Wadanada su ka ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na shekara a baya :
2016: Riyad Mahrez (Leicester City da Algeriya)
2015: Yaya Toure (Manchester City da Kot Dibuwa)
2014: Yacine Brahimi (Porto & Algeriya)
2013: Yaya Toure (Manchester City da Kot Dibuwa)
2012: Chris Katongo (Henan Construction da Zambiya)
2011: Andre Ayew (Marseille da Ghana)
2010: Asamoah Gyan (Sunderland da Ghana)
2009: Didier Drogba (Chelsea da Kot Dibuwa)
2008: Mohamed Aboutrika (Al Ahly da Masar)
2007: Emmanuel Adebayor (Arsenal da Togo)
2006: Michael Essien (Chelsea da Ghana)
2005: Mohamed Barakat (Al Ahly da Masar)
2004: Jay-Jay Okocha (Bolton da Najeriya)
2003: Jay-Jay Okocha (Bolton da Najeriya)
2002: El Hadji Diouf (Liverpool da Senegal)
2001: Sammy Kuffour (Bayern Munich da Ghana)
2000: Patrick Mboma (Parma da Cameroon

No comments:
Write blogger