Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ba zai kawar da yiwuwar sayen dan wasan Arsenal Alexis Sanchez idan aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan gobe, in ji Sky Sports.
Manchester United ta neman dan wasan West Brom Jonny Evans kodayake City da Arsenal su ma suna zawarcin dan kwallon, a cewar jaridar Sunday Mirror.
Har ila yau Man City da Man U da PSG da kuma Chelsea suna neman dan wasan Juventus Alex Sandro, in ji jaridar Sunday Express.
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce zai bari Daniel Sturridge ya tafi aro a watan Janairu, dan wasan yana neman sa'ar shiga tawagar Ingila a Gasar Cin Kofin Duniya, kamar yadda jaridar Sun on Sanday ta bayyana.
Haka zalika kocin ya ce ba za su sayi dan wasan RB Leipzig Naby Keita ba a watan gobe, a cewar jaridar Daily Star Sunday.
Manchester United tana shirye-shiryen fara zawarcin dan kwallon kungiyar Bordeaux ta Faransa, Malcom, a kan fam miliyan 30, in ji Sunday Times.
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo da kocin kungiyar Zinedine Zidane suna tattauna batun yadda dan kwallon zai yi ritaya a Madrid, in ji kafar yada labarai ta FourFourTwo.
Haka zalika jaridar Sun on Sunday ta ruwaito cewa akwai yiwuwar kocin Chelsea Antonio Conte ne zai maye gurbin Zinedine Zidane a Madrid, wanda yarjejiniyarsa za ta kare a karshen kakar bana.
No comments:
Write blogger