Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin hukumar FIFA na kungiyoyin kwallon kafa na duniya inda ta doke kungiyar Gremio da ke kasar Brazil.
An dai buga wasan ne a birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Asabar.
Kulob din Spaniyan ya lashe kofin har sau shida kenan, fiye da kowane kulob da ya taba buga gasar.
Yanzu dai Real Madrid ta lashe kofin a biyar a wanann shekarar, wanda suka hada da kofin Zakarun Turai, da na La Liga, da na Uefa Super Cup, da Super Cup na Spaniya da kuma na FIFA wanda ta lashe yanzu.
No comments:
Write blogger