spon

Saturday, December 16, 2017

Home Kanu da Diouf sun jagoranci wasan tallafi ga 'yan gudun hijira a Kano

Subscribe Our Channel


Kanu Nwakwo na Najeriya da Elhaji Diouf na Senegal ne suka jagoranci wasan a Kano
Tsoffin gwarzayen Afirka da suka kunshi Elhaji Diouf da Kanu Nwakwo da Garba Lawal da Tijjani Babangida sun kara da kungiyar Kano Pillars a wasan neman tara tallafin kudi ga 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.
'Yan wasan sun amsa kira ne daga bangarori daban-daban na nahiyar Afirka, inda suka hada tawaga guda don yin wasa mai manufa daya. Duk da cewa shekaru sun fara kama galibinsu.
Tsoffin zaratan 'Yan kwallon da suka yi fice a Afrika sun nuna wa duniya cewa har yanzu tauraruwarsu na haskawa.
Sai dai masu iya magana na cewa "Mai laya ya kiyayi mai zamani", inda 'yan wasan Kano Pillars, suka nuna tsoffin zakarun gasar Firimiyar Najeriya ne, ta hanyar nuna wa mazan-jiyan cewa lokacinsu ne.
Kano Pillars dai ta samu nasara a wasan da ci 2-1.
Amma, rashin samun nasarar tsoffin 'yan wasan na Afrika ba shi ne sakon da wasan ke son isarwa ba, illa manufar shirya wasan. Kuma ko ba komai dama ce ta sada zumunci tsakanin tsoffin 'yan wasan da kuma takwarorinsu na yanzu.

No comments:
Write blogger