spon

Saturday, December 16, 2017

Home Madrid na zawarcin Mohamed Salah'

Subscribe Our Channel


Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Gasar Firimiya na watan Nuwamba
Kocin tawagar Masar Hector Cuper ya ce kungiyar Real Madrid tana zawarcin dan wasan Liverpool Mohamed Salah, yayin da Kocin Madrid Zinedine Zidane ya ce yana jinjina wa kwarewar dan kwallon, kamar yadda jaridar Daily Sun ta bayyana.
Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar BBC na Afirka na bana a farkon makon nan.
Tsohon Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti zai koma Chelsea a matsayin sabon kocinta a kakar wasa ta badi, a cewar jaridar Daily Record.
Dan wasan Chelsea Batshuayi zai bar kungiyar a watan gobe amma zai tafi aro ne, kamar yadda jaridar London Evening Standard ta bayyana.
Kocin Manchester United Jose Mourinho zai sayi sabbin 'yan wasa a watan gobe duk da cewa shi ba mai kaunar yin hakan ba ne a kasuwar saye da 'yan wasa ta watan Janairu, in ji jaridar Daily Mail.
Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya ce ya ba Madrid shawarar ta sayi Kylian Mbappe gabanin kungiyar PSG ta riga ta, in ji kafar yada labarai ta Goal.com

No comments:
Write blogger