spon

Sunday, June 3, 2018

Home An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

Subscribe Our Channel


An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

A jiya Juma'a ne dai wasu 'yan bindiga suka kashe Mutane har 23 a jihar Zamfara a kauyen Zanoka bayan da suka budewa mazauna kauyen wuta kan mai Uwa da wabi sannan kuma suka cinnawa Gidajen Mutane wuta suka kone kurmus.

Barayin dai sun zo ne kan Babura a matsayin daukar fansar korar da 'yan sintirin yankin su kayi musu inji shugaban karamar hukumar yankin da abin ya faru Mustapha

"Yanzu haka mun binne mutane 23 ciki har da 'yan sintiri da su kayi kokarin dakatar da su."

Mustapha Muhammad ya bayyana cewa 'yan Bindigar sun fara kai farmakin ne ranar Juma'a inda har suka kwacewa Mutane shanunsu sai dai jami'an sintiri na yankin sun fatattake su sannan suka kwato shanun, a dole suka tafi.

Amma sai dai 'yan awanni kadan bayan faruwar hakan sai Barayin suka sake dawowa da babbar runduna kauyen dake nisan Kilomita 160 daga babban birnin Gusau

Kakakin rundunar 'Yan sanda na jihar ta Zamfara Muhammad Shehu ya shaida cewa sun samu gawawwaki 15 bayan da 'yan Bindigar suka kai harin.

"Mafi yawan wadanda suka Mutun 'yan sintiri ne na yankin da su kayi kokarin dakatar da su."

Barayin sun sha kai hare-hare domin sace shanun Mutane tsawon shekaru da dama su kuma kashe duk wani wanda ya nuna tirjiya ga abinda suka aikata.

Wadannan har-hare da ake kai musu ya sanya 'yan Kauyen suka kafa kungiyoyin 'yan sintiri domin tabbatar da tsaro a yankin, amma sai dai su kansu 'yan sintirin ana zarginsu da cin zarafi da kashe wadanda suka kama bisa zargin su.

Yawaitar aiyukan tsagerun ma ya sanya Gwamnati ta kai rundunonin tsaro jihar domin tabbatar da dawo da doka da oda, amma sai dai har yanzu lamarin na dada kamari.

No comments:
Write blogger