spon

Sunday, June 3, 2018

Home Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda ya kama Saraki

Subscribe Our Channel


Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda ya kama Saraki

A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi masa da zarar takardar gayyatar ta same shi.

Kazalika, Saraki ya musanta cewar akwai wata alaka dake tsakanin sa da mutanen da ake zargi da aikata laifin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.

A yau, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu daga cikin wadanda ta kama dangane da batun fashin bankunan garin Offa sun ambaci sunan Saraki da na gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a matsayin mutanen dake daukar nauyin aiyukan su na ta’addanci.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya , Ibrahim K. Idris, ya kama Saraki bayan gabatar masa da shaidar samun hannun Saraki a cikin aiyukan ta’addanci, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Zuwa yanzu Kakakin shugaban kasa da na hukumar ‘yan sanda sun ki cewa komai a kan wannan batu dama kuma batun ganawar shugaba Buhari da shugaban na ‘yan sanda ta ranar juma’a.

Da yake jawabi cikin sanarwar da mai Magana da yawun sa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar, Saraki yace alakanta shi da fashi wani makirci ne kawai na bata masa suna.

No comments:
Write blogger