Annobar Amai Da Gudawa Ta Barke A Nasarawa
___¥__
*
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun nuna cewa annobar Amai da Gudawa ta barke a yankin Angwan Lambu da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.
A halin yanzu dai, annobar ta yi sanadiyyar mutuwar wata mata yayin da wasu mutane 20 suka kamu da annobar wanda ya hada har da wasu daliban jami'ar Nasarawa da ke Keffi. Da yake tabbatar da barkewar annobar, Kakakin Jami'ar, Abraham Ekpo ya ce, ana duba daliban da annobar ta harba a karamin asibitin jami'ar.
No comments:
Write blogger