GIYA DA SIGARI ZASUYI TASHIN GORON ZABO A NAJERIYA.
A yau akesa ran sabon harajin kudin giya dana taba zai fara aiki a Najeriya, wata majiya mai tushe tace ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan sabon tsarin harajin a yau kuma yafara aiki cikin kwanaki 90 masu zuwa.
A karkashin sabon harajin, Tabar sigari, za'a ma ta karin kashi 20 cikin dari na haraji, yayinda duk karan sigari daya zata samu karin naira 1 a shekarar 2018, a shekarar 2019 karin haraji zai koma Naira 2 akan duk kara daya, a shekarar 2020 kuma karin harajin zai tashi zuwa Naira 2.90 a duk kara daya.
Shi kuma sabon tsarin harajin giya zai shafi Beer, stout, wines da spirits na shekara 3, daga 2018 zuwa 2020.
Ministan kudi, Misis Kemi Adeosun, tace sabon tsarin harajin giya dana taba sigarin wani matakine na gwamnati domin rage matsalolin rashin lafiya da ke tattare da taba da giya.
No comments:
Write blogger