spon

Monday, June 4, 2018

Home TUNATARWA

Subscribe Our Channel


TUNATARWA

'Yan Uwa Musulmi Kada A Manta Da Daren Daren 'Lailatu Qadri'

ABUBUWA 15 DA ALLAH YA FIFITA DAREN LAILATUL QADRI AKAN DUKKAN DARARE BAKI DAYA

Daga Aliyu Ahmad

*1-Allah ya zabi wannan dare na lailatul Qadri, ya fifita shi ya daukaka shi cikin falala da daraja da daukaka akan dukkan sauran darare baki daya*

*2-Sanyawa wata sura daga cikin surorin Alqurani mai girma SURATUL QADRI* (Dan girmama sha'anin wannan Dare.

*3-Allah ya girmama sha'anin wannan dare na Lailatul Qadri*

*4-Daren lailatul Qadri dare ne mai albarka mai yawa*

*5-A cikin Daren lailatul Qadri ne Allah ya saukar da Alqurani zuwa saman Duniya a baitul Izza*

*6-Aiyukan ibada a wannan dare ya fi alkairi da matsayi da falala akan dararen watannin dubu wanda babu daren lailatul Qadri*

*7-Wanda ya dace da wannan dare kuma ya yi ibada a cikinsa, ya sami alkairi mai yawa, wanda kuma ya yi asarar wannan dare, to an haramta masa alkairi mai yawa*

*8-Wanda ya raya daren da ibada yana mai imani da kwadayin samun lada,to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa*

*9-Raya darare goma na karshen Ramadan dan dacewa da Daren Lailatul Qadri, yin hakan sunna ce ta Manzon Allah s.a.w*

*10-Manzon Allah S.A.W ya koyar da yin wannan addu'ar a cikin wannan dare don samun afuwa da gafarar Allah"
*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ*

*11-Mala'iku masu yawa har ma da Shugaban Mala'iku wato Mala'ika Jibrilu suna saukowa cikin wannan dare*

Suna saukowa ne domin yin addu'a da nemawa bayin Allah da suke raya wannan dare da ibada gafara a wajen Allah.

*12-Daren mai aminci da walwala tun daga faduwar rana har zuwa fitowar Alfijir*

*13-A cikin wannan dare ne Allah yake tsarawa da rubuta Arziki da Ajali da sauran al'amurar wannan shekara gaba daya*

*14-Shaidan da rundunarsa ba su iya fitowa dan yada alfasha ga dan Adam a cikin wannan dare*

*15-Nemn Daren Lailatun Qadri da kirdadonsa yana cikin shiriyar Annabi s.a.w*

  Allah ne mafi sani.

*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ

No comments:
Write blogger