spon

Monday, July 23, 2018

ZAWARCI Complete Book

*K*wance take a tsakar ɗaki sai muɗiɗɗiƙa take a ƙasa, yunwa kawai take damunta, ga kudaje sun cika ɗaki kamar toilet in daya shekara bai samu wanki ba,,,,, wasu zafafan hawaye suka zubo mata masu zafin bala"i, a bayyane tayi magana , wayyo Allahna, da ina can naci mai kyau , babu ruwana da wata yunwa ko ganin ƙazanta,,,, goge hawaye tayi da bayan hannu lokacin da taji mahaifiyarta tana kiran sunan ta,,,,,

*R*aihana baki ji na ne?""" umma ina zuwa, tsaki tayi , sannan tace idan ma baza ki zo, kin huta, dama wankau ne, aka kawo sunce yau suke so, idan zakiyi to kizo ki karɓa, idan kuma bakya yi ki faɗa masu, a daidai lokacin da ta fito a tsakar gida,,,,,,,

*T*ashin kayan wankin ta gani, ta gyara ɗaurin zaninta, sannan tace umma zanyi, umma ta kace da dariya, sannan ta taɓa hannu, tace yo kice ma baza kiyi ba, zama raihana tayi a ƙasa ta jayo wanki ta fara irgawa, sannan ta kalli yaron tace to wankin na ɗari da hamsin ne, yaron yace Eh, tace ga kuɗin, ya miƙa ma raihana ta ƙarba, tace bayan la"asar ka dawo ka ɗauka yace to yace sannan ya fita daga gidan,,,,,,,,,,,,,,

Umma tace to yanxun dai kafin ki fara wannan wanki, ki fara wanke kayan babanki sannan, raihana tace tou umma,

��������
������
*ZAWARCI*
��������
������
Saida ta wanke kayan babanta kala biyu, sannan ta fara wankin kayan wankau, yinin ranar nan haka ta yini ta wanke kaya,,,,,,

Lokacin da ta gama wankin hijabinta data gama koɗewa ta jawo daga saman iyiga, ta rataya a wuyanta ta fita tabar gidan............

Tana fita umma tayi dariya tace munafikar Allah, ai tunda dai *zawarci* kika zaɓa sai kixo mu zauna kice uwar da nake a gidan,,,,,,,,,

Raihana tana fitowa wani shago taje, suka gaisa da mai shagon, bayan sun gama gaisawa tace don Allah fulawa za"a bata kwata ɗaya, yace to, ya ana mata, tace don Allah ka bani bashin manja na hamsin insha Allah zan kawo maka , yace gaskiya raihana bakya san biyan bashi wallahi, tace kayi haƙuri wallahi zan kawo maka dana samu, shamsu yace, baia san ranar samu ba kenan,

Idan zaka bani kawai ka bani idan baza ka bani ka faɗa man, gaskia bazan bayar ba, tace to yanxn naji magana, ta ɗauki fulawarta da canjin ishirin ɗinta ta fito daga shagon,,,,,,,,

Sallama tayi ta shigo cikin gidan, matar babanta da ta dawo daga unguwa tace ina kika je ne?""""raihana tace fulawa na siyo gwaggo, cikin tashin hankali gwaggo tace waye ya baki kuɗi?""" tace nayi wankyau ne, tsaki tayi sannan taje inda fulawar take ta ɗauketa, tace wallahi saidai a ajiyeta da safe ayi fanke kowa ya samu, raihana tace gwaggo nifa nayi wankin nan na samu kuɗina gwaggo tace koma uwarki tayi haka za"ayi, ta ɗauke fulawar ta shige , cikin ɗakinta,,,,,,,

����
*zawarci*
����

Bayan ta ɗauki fulawar ta shige cikin ɗaki raihana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, kwanciya tayi saboda tun safiya bata ci komai ba, ga azabar yunwa dama tana ji kuma tayi wanki har ta gaji, kuma hdama kowa dai yasan wankindasa jin yunwa,,,,,,

Raihana wasu hawaye suka zubo nata , abinda ta fara tunawa, hango tsareren gidanta, tayi da tsaruwarsa da kuma yanda yake a tsabtace, cikinta ta laluba, lokacin data tuna irin abincin da take ci, uhum Allah sarki rayuwa tace,

Tashi tayi ta fito tsakar gida dan ganin waye yake sallama, wai ance a bada wanki, raihana tace to ɗauki gashi can , ya nufi wurin data nuna mashi ya nufi wurin yana cewa wai mama tace a kawo maki kaɗin taliya?"

Zainaba tace a,a, banda hali, gwaggo data ke alwalla tace kaje kace a kawo, kumin dare tayi ta, yace to, ɗakar wankin yayi ya tafi,,,,,,,,

Gwago tace dan rashin imani ubanki yana can yana fama liƙewa mutane takalmi baza ki tausaya mashi ba?" wai mutum ya haifeka amma kana masa hassada, raihana tayi tsaki ta shige ɗakin su.........



����������
*ZAWARCI*
��������

Gwaggo tace uwarki da ita kike tsaki, shegiyar nan, idan kinki haushi ki fitar da miji kiyi aure,,,,,,,,,
[07:24, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 2⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*A* ɗaki rahaina tayi magana ƙasa ƙasa, tace wallahi ba uwata nayi ma tsaki ba, kuma maganar aure, idan Allah ya kawo man lokaci sai inyi,,,,,,

*U*mma kiyi mata magana ta bani fulawata yunwa nake ji taliya zan kaɗa inci da manja, raihana ce take ma mahaifiyarta magana,,, umma tace bazan mata magana ba, dana ce kada ki kashe aurenki ai cewa kikai ke ba"a sanki, to yanxun ana sanki sai ki zauna kiyi ta haƙuri tunda haka kika zaɓarma rayuwarki,,,, raihana tace umma haka zaki ce?"" Eh haka nace kuma haka ne,,,, uhum raihana tace sannan ta ɗauki buta ta fita daga ɗakin,,,,

��������
*zawarci*
����������
*R*aihana ta kalli wani jikan gwaggo da yake zaune yana cin abinci, da sauri taje inda yake, robar ta ɗauka ta zubar da abincin a ƙasa, tana faɗin tunda banci babu uban da ya isa yaci ko yasha a gidan nan harsai naci, idan kuwa ba haka wallahi ba"a nemi zaman lafiya ba,,,,,,,,

Yaron da raihana ta ɓare na abinci ya faɗi ƙasa ya fara burgima yana ihu yana ƙarawa, da sauri gwaggo tayo waje tana faɗin lafiya?""" raihana tace ina ma lafiya tunda baki nemi zaman ta ba a gidan nan, gwaggo ta tafa hannuwa tana sallalami , sannan ta riƙe haɓarta tace raihana, yanxun da ni zaki yi faɗa a gidan nan?""" raihana tace Eh, tana magana tana zaro idanuwa, tace udan har baki bani fulawata ba yau saidai gidan nan ya tashi saboda bala"i, gwaggo tayi dariya tayi guda, ayyuri yuriiiiii yuriiiiii, to uwarki ma ta buga dani tabarni danni nan da kika bakan gixo ce, dan idan har hadari ya taru saina tsotseshi,,,,,

Rainaha tace aikin banza wanda bakuyi imani da Allah ba baku da aiki sai neman asiri, kuma idan har ina a gidan nan wannan yaron babu shi babu ƙara cin bacci saidai yunwa ta kasheshi kowa ma ya huta,,,,,,,

Gwaggo ta sake sheƙwa da dariya sannan tace, ke yunwa zata kashe, kuma ni yanxun dana ga dama sai in mayar dashi gudan ubanshi, kuma ubanshi yana da abincin bashi dan ubanshi namiji ba kamar ubanki ba, wanda sai ƙato ya cire takallmi sannan ya wanke, raihana tace Eh a haka aka gani kuma aka aura,

Gwaggo tace lallai yarinya dani kike magana, tunda *zawarci* kika zaɓa haka zamu zauna dani dake a gidan nan aure ko saidai kiga anayi,, tana faɗin haka ta kama hannun jikanta ta shige ɗakin ta,,,,,,,,

Raihana tace karyar banza baƙin bakinki ya faɗa ma jikokinki,,,,,, itama daga nan bata sake magana ba, ta ɗauki butarta ta kona ɗaki,,,,,,,,
��������
*zawarci*
��������
Raihana baki kyauta ba, ummarta take mata magana, tace umma barta, ninan walkice daidai ƙugun kowa, umma tace rufa man baki, tunda kinsan halinta kika biye mata,,, umma tace to wallahi nidai saidai in bar maki gidan nan,

Raihana tace kiyi haƙuri, kada kibar gidan nan saboda ni, umma tace idan kuwa ina san zaman lafiya da tsira da rayuwata dole in tafi dan bana iya zama ina kallon wannan wulaƙancin wallahi,,,,,,,,,

Sallamar babansu raihana , umma taji ta tashi ta fito tana mashi sannu da zuwa, ya amsa cikin kulawa, itama raihana fitowa tayi ta mashi sannu da zuwa, ya amsa sannan yace Allah yayi maki albarka, daga ɗaki gwaggo tace ba amin ba, sannan ta fito tsakar gida taci gaba da cewa kace Allah ya tsine mata albarka, wannan da kake gani, tana nuna rainaha da yatsan ta, tace to wallahi bakai sa"arta ba, saboda lalatattar yarinya, baba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu, yace bana san irin wannan kalamin daga yau, gwaggo tace dama haka zaka ce tunda an shanye ka sakarai mai matacciyar zuciya, duk gwaggo take wannan maganar , baba bai sake magana ba ya nufi ɗakinshi,,,,, raihana da umma suma ɗaki suka koma,,,,,,,,

������������
*ZAWARCI*
����������

*T*unda asuba, gwaggo ta fito daga ɗaki ta fara jaraba, tana masifa tana zage zage, babu wanda yayi mata magana, taci gaba da cewa idan banda munafircia matsa ma yarinya ta fito da miji tayi aure sai a barta ta zauna, kuma tana da nasu santa, to tunda *zawarcin* kika zaɓa sai kizo ki zauna,

Raihana dai daga ita har umma babu wanda yayi magana , haka ta kari masifarta ta koma ɗaki,,,, ,,,,,

Bayan hantsi ya fito baba ya fito dan tafiya wajen sana'ar sa, kuma gwaggo batayi wannan famke ba, kuma batayi komai da fulawar raihana ba, haka baba ya fita daga gidan baici kuma baisha komai ba,,

Gwaggo bayan fitar baba itama gyalenta ta yafa itama fita tayi tabar gidan,,,,,

Wata maƙociyarsu tayi sallama ta shigo, bayan gaisuwa tace raihana ga dakan tashshi raihana tace to, da ƙarfe nawa kike so?""" tace bayan azahar, to Allah ya kaimu lafiya, nawa za"a bada?"""inji matar, raihana tace tiya nawa ne?"" biyu da rabi ce, raihana tace to ki bada abinda kikai niyya, tace to, ɗari biyar ta ciro ta bawa raihana, tace ta riƙe sauran canji, godiya raihana tayi, matar ta tashi ta fita, itama raihana fita tayi ta nufi shago, gari da suger ta siyo sannan tayo gida............

*zawarci*
[07:25, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ������������
����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
������������
����������
��������
������
����

*page* 3⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��


*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*S*allama raihana tayi ta shigo gida, umma ta amsa mata, kusa da umma raihana taje ta zauna, garin ta ajiye sannan taje ta ɗauko kofi da cokali, wurin ta dawo ta ɗauki garin ta haɗashi, bayan ta gana , ta miƙawa ummarta tace ummana sha ki rage man, umma tace ni bana sha, raihana tayi juyin duniya tace bazata sha ba,,,,,,,,,,

*R*aihana ta ɗauki garin tasha, bayan ta gama sha ta tashi ta fara dakan tashshin da aka kawo mata,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*B*ayan raihana ta gama dakan tashshi ta kwashe, bayan ta gama kwashewa ta zauna a wurin tabaryar da tayi dakan tana hannunta, ta jingina kanta da ita, hawaye masu zafi suka zubo mata, ta runtse idanuwanta, abinda ta fara tunawa shine,,,

�� ��
*gidan mijinta*
�� ��

*R*aihana ta fara tunawa, wata rana, da sallama ya shigo gidan ko inda yake bata kallaba, shi kuma cikin farin ciki ya shigo yana faɗaɗa murmushin shi, yace raihana barka da gida, tsaki tayi, ita babu sannu da zuwa kuma bata ansa sallamar ba,,,,,,uhum ajiyar zuciya zainaba tayi sannan a bayyane tayi magana tace rabon *zawarci*

������
*zawarci*
������
Idanuwanta ta sake runtsewa, abinda ta ƙara tunawa, raihana zanyi tafiya, ta sake hango lokacin da ta taɓe baki, sannan tace sai wani magana kake man saman kai babu girmamawa, idan zakayi tafiya ina abinda ya dameni"""",,,,,,, murmushi yayi sannan ya ciro kuɗi har dubu ishirin ya ajiye mata a gabanta,,,,,,,,, wasu hawaye suka ƙara kwararowa daga gudan raihana, tace *astagafurulah*

*zawarci* baiyi ba, abinda raihana ta faɗa kenan, sannan ta gige hawayenta, tace abinda nafi ƙarfi yanxun shine yafi karfina,,,,,,,,,, ***

��������
*zawarci*
��������

*R*aihana ta janye taɓaryar gabanta ta jingina da bango ta mike,,,, a daidai lokacin da gwaggo tayi sallama ta shigo,, raihana ta amsa, gwaggo ta cire gyalenta ta rataya a igiya, sannan tace raihana wani mutum ne a kofar gida yake maki sallama, raihana tace naji, ɗakin ummanta ta shiga, ta ɗauko kwandon wanka, ta duba taga babu sabulu a ciki, tsaki raihana tayi tace kai Allah kasa mu dace, saman window ta duba ta ɗauko wata ledar omo, ta zuba ruwa ta shiga wanka,,,,,,

��������
*zawarci ne*
��������

*T*ana fitowa wanka alwalla tayi ta shige ɗakinsu, umma ina man yake?"" in shafa umma tace babu mai ya ƙare fa, raihana tace yanxun ya zanyi a daidai lokacin da take zama saman tabarma, umma tace ɗauko waccan ledar ina da sauran man gyara ki murza , ajiyar zuciya raihana tayi sannan ta miƙe taje ta ɗauko ta shafa, fuskar nan ta ɗauki ƙalli, da kafafuwanta, kuma babu powder, ta kalli kanta a madubi, tace rayuwa kenan, girgiza kanta tayi hawaye masu zafi suka zubo mata, umma ta kalleta tausayin raihana ya kamata, saboda raihana bata san wahala, amma a fili tace haba har kin gaji?"" ai baki komai ba, lokacin dana faɗa maki kiyi haƙuri ki zauna ai cewa gani kikai gara ki dawo gida,,, haushi ya ishi raihana bata sake magan ba, ta ɗaga ƙasan katifarta ta ɗauko wata ƙoɗaɗɗiyar atamfa tasa, da habar zaninta ta goge fuskarta ta fice daga ɗakin,,,,,,

������
*zawarci*
������
Tana fita umma tace kinga da yanxun kina gidanki kina yin rayuwarki yanda kike so, kinzo ki liƙe nan sai wahala kike sha,,,,,

Fitar raihana wani mutum ta hango tsaye bakin bishiyar kofar gidansu kamar ya fiddoshi daga cikin ƙasa, raihana tayi tsaki sannan ta nufi wurin shi cike da masifa, tana zuwa babu ko gaisuwa tace malam yadai?"" yace nine dama nazo ina sanki, to naji kana do na, sai mi kuma?"" maganar aure ce, raihana tace to daga yau kada in sake ganin ƙafarka nan kaji na faɗa maka?"" tana faɗin haka bata jira abinda zaice ba tayi cikin gida, a zaure ta tsaya, tace banda iskanci da shara da bola dan taƙamar kana *zawarci* kowa sai yaxo, tsaki tayi sannan tace shege ƙazamin banza, ...............


Hhhhhhhhhh
��������
*zawarci*
��������
[15:01, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 4⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*gargaɗi a bisa wata ƙungiya, da bama buƙatar saka sunan ta, dan haka muna roƙonsu dasu guji juya mana littafi ta ko wace fuska, idan kunnne yaji ���� gangar jiki ya tsira* ����‍♀

��������
*zawarci*
��������

Sallama tayi a daidai ƙofar ɗakin ummanta ta shige, har kin dawo?""" Eh kawai tace, inda ta ajiye tashshin data daka ta wuce ta ɗauka , sannan tace umma zan kai mata saƙon nan, umma tace sai kin dawo , to tace tayi gaba,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*zawarci*
Raihaina tana fita umma tace Allah ya baki miji kiyi aure raihana ki huta da wannan rayuwa, ,,,,,,,,

*R*aihana tana fitowa maƙotansu ta shiga, gidan badiyya, sallama tayi ta amsa mata tace raihana ki shigo mana, raihana tace to, ta shiga, ta samu wuri ta zauna, suka sake gaisawa, sannan raihana ta fidda tashshin ta bata, godiya tayi , sannan tace bara inxo,,, fitowa tayi taje kicin ta zubo ma raihana abinci,,,, sannan ta dawo ta ajiye mata, murmushi raihana tayi danma kada a ɓata lokaci kawai tace tana azumi,,,,,,,,,,,,

������
*zawarci*
������
*B*adiyya tace Allah sarki azumin mi kike?"" murmushi raihana tayi tace ramuwa nake, badiyya tace to Allah ya bada lada, amin raihana tace, sallamar mijinta suka ji, raihana tana zaune taga badiyya ta tashi cikin sauri ta fita,,,,, tana kallon ta tana zuwa ta rungumeshi tana oyoo yoo barka da dawowa baban sadiq,,, lader hannun ta ƙarɓa cikin girmamawa tana buɗewa dariya tayi saboda ganin abinda yake cikin ledar , sannan ta matsa kusa dashi ta ɗora kanta saman kafaɗarshi tace na gode Allah ya saka da alkairi ubangiji ya ƙara rufa asiri Allah , amin yace yana murmushi,,,,,,,

*zawarci*

Hmmm ajiyar zuciya raihana ta sauke, sannan ta tuna cewa ita idan mijin nata ya kawo cewa take yaje ya ajiye,,,,,,, a bayyane tace gashi an barni da *zawarci* jiki a sanyaye ta fito tsakar gida, tace nidai zan wuce,,,, �� raihana taga masoya suna soyewa hankalinta ya tashi,,,,,,,, badiyya tace haba tun yanxun?"" don Allah ki bari yanxun zai fita sai muyi fira, raihana tace a, a, ina aikine a gida,,,,,, badiyya tace to ngde, a gaishe man da umma, raihana tace to sannan ta fita tabar gidan,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*A* gida raihana ta shiga ɗakinsu,,,, umma ta samu tsaye ta riƙe hijabinta a hannu, raihana tana shiga umma tace mata yawwa, zanje duba bayi bata da lafiya, raihana tace sai kin dawo a daidai lokacin da take kwanciya saman tabarmar kaba,,,,,,, umma ta fice tabar ɗakin,,,,,,

������
*zawarci*
������

*Raihana* tana kwanciya ta ɗaga kanta sama tana kallon izarar ɗakinsu, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, ajiyar zuciya tayi sannan ta gyara kwanciyarta saman hannun ta na dama,,,,,,,,,,,,,,, abinda ta fara tunawa,,,,

��������
*rayuwarta*
��������

*Khadija* shine ai nahin sunan *raihana* babanta malam ibrahim, da ɗan kasuwa ne, ya ɗan riƙe kuɗaɗe babu laifi, daga baya Allah ya kawo mashi karayar arxiki, matan malam ibrahim biyu, binta itace babbar matarsa wanda suke kira da gwaggo, tana da "ya"ya, basai na tsaya lissafo su ba, halima itace mahaifiyar raihana, wanda suke kiranta da umma, umma ta haihu sosai amma Allah bai bata wasu rayuwa ba sai kan khadija, wanda aka sakawa sunan maman malam ibrahim, yayarta ɗiyar gwaggo itace take kiranta da raihana, saboda haka shine dalilin da yasa kowama ya kekiranta da haka, dan yanxunma sunan ta ya ɓata saidai *raihana*

Gyara kwanciya raihana tayi sannan ta goge hawayen da suka zubo mata,,,,,

��������
*zawarci*��
��������

Ku biyo ni sannu a hankali don Allah donjin labari *zawarci*

Ina maku fatan alkairi masoyana , ku biyo ni sannu a hankali don jin wannan labari, *ameenxi writr's association* a shirye muke wajen ƙawata maku da daɗaɗa maku din farin cikin ku,

*jameela musa* ke cewa ku kasance dani lafiya,,,,,,

07060797938, a shirye nake da jin ƙorafinku ����
[15:02, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*gargaɗi a bisa wata ƙungiya, da bama buƙatar saka sunan ta, dan haka muna roƙonsu dasu guji juya mana littafi ta ko wace fuska, idan kunne yaji ���� jiki ya tsira* ����‍♀
������
*ZAWARCI*
������

*B*ayan ta gama goge hawayen da suka zubo mata a ido, ta tashi zaune ta zabga tagumi, sannan ta ɗora kanta saman guiwarta,,,,,

*zawarci*��

Malam ibrahim mahaifin *raihana* shine yayi kyautar raihana ga wani yaronshi mai suna aminu, yana da kirki sosai, ya bashi raihana ne, saboda ya matsa mashi yana santa, shi kuma ya bashi raihana saboda ya yaba da hankalin aminu,,,,,,

*to haka baba ya bawa *aminu* auren raihana, ansha shagali sosai kuma aminu yayi hidima saboda yana san raihana kuma komai zai iya yi, saboda ita idan dai abun baifi ƙarfinshi ba,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

*Raihana* da sauri ta goge hawayen idon ta dan kiran sunan ta da taji gwaggo tanayi,,,,, ba tare da ta amsa kiran ba, ta tashi ta fito tsakar gida,,, kallo tabi gwaggo dashi har yanxun batayi magana ba,,,,,,,

Gwaggo tace, wallahi tun ɗaxu nake neman wanda zai kai mana niƙa ban samu ba, raihana ta ɗaure fuska sosai sannan tace idan baki samu mai kai niƙa ba sai akayi me?"""" gwaggo tace wannan ɗaure fuskar naki bazai hana ince kije kikai ba, tunda ba"a samu yaron aike ba,,, kam raihana tace, sannan tace lallai gwaggo kinzo da abinda baya yuwuwa, gwaggo tace ai dan zai yuwu nayi magana, saboda haka sai kinje, raihana tace bazanje ba,,,, sallama umma tayi ta shigo gidan, a daidai lokacin da gwaggo take cewa da kina gidan mijinki zanje in kiraki kikai niƙa ne?""""

*t*saki raihana tayi sannan tace aike kina so kiyi man gorin aure, bayan nasan idan lokaci yaxo sai nayi, gwaggo tace wannan kuma matsalarki, dan wallahi idan baza kikai niƙan nan ba, yau bazanyi tuwon nan ba, saidai ubanki ya kwana da yunwa,,,,, umma tace ɗauki kije kikai ɗinƙan kinji,,,,, raihana zatayi magana umma ta dakatar da ita, ta hanyar cewa ba komai wata rana sai labari, gwaggo tace ba labari ba koma b.b.c ne ina ruwana,,,, ta juya ta wuce ɗakinta, inda gwaggo ta ajiye buhun niƙan da kuɗin raihana taje ta ɗauka sannan ta fita daga gidan,,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������

Raihana sai Allah ya isa take har takai shagon niƙa,,,,, mai niƙan ya kalleta ya bushe da dariya, sannan yace baiwar Allah ke aka aiko?""" rahaina bata yi magana ba, ta haɗa hannuwanta ta rugummesu a ƙirjinta,,, mai niƙan yace ni wallahi da zaki yadda kawai in fito muyi aurenmu in rufa maki asiri tunda shi aminun ya kasa,,, ko inda yake raihana bata kalla ba, dariya yayi lokacin daya ɗaga buhunta ya juye masarar a cikin inji, yaci gaba da cewa matana ukku yarana ishirin da biyar, kallon ƙasa da sama raihana tayi mashi, wata irin dariya yayi sannan yace Allah sarki irin wannan kallo ai sai kisa mutum yayi fitsarin zaune dan daɗi, tsaki raihana tayi ta duƙar da kanta ƙasa har ya gama niƙan,,,, ta ɗuka zata ɗauka da sauri ya riƙe yace bari insa akai maki, raihana ta saki, kuɗin ta miƙa mashi yace tabarsu, yana yashe baki yace wannan toshine, murmurshin baƙin ciki raihana tayi taji kamar zuciyarta zata fashe wato da niƙa za,ayi mata toshi,,, yaronshi yace ya ɗauki niƙan yakai gidansu, yaron ya ɗauka yayi gaba, raihana tafi bayanshi, mai niƙa sai ɗago hannu yake yana cewa sai yaxo cin tuwo anjima,,,

��������
*zawarci*
��������
*raihaina* haka tabi bayan yaron tana zance zuci, lallai waƙƙahi mutumnn nan ya raita mata, hankali, addu"ar ta ɗaya kada yazo gudansu dan babanta yana iya cewa ya turo, tunda dama kullum sai yayi mata maganar tayi aure,,,,, a daidai lokacin da tayi sallama cikin gida,,,,

*zawarci*
Yaron ya ajiye niƙan ya fita, gwaggo ga niƙan nan, to aisai kiyi tankaɗe, raihana tace hada wani tankaɗe, tace E , taci gaba da cewa ai da uwarki ce idan tana aiki baki da zama sai kinga an gama, dariya ryhaina tayi sannan tace maida wuƙaƙen zan maki, a daidai lokacin data shiga ɗakinsu,,, hijabinta ta cire ta miƙawa ummanta kuɗin niƙan tace ki ajiye wannan , umma tace na miye?"" raihana tace nawa ne na baki, umma tace to, bayan ta nashi kuɗin ta fito tsakar gida ta fara kama ma gwaggo aiki,,,,,,,,,

��������
*zawarci*
��������
*W*ani yaro ne ya shigo da tsirin kayan wanki saman kanshi, sallama yayi sannan ya nufi inda raihana take zaune, kama mashi tayi ya sauke, sannan ya miƙa mata kuɗi yace ga kuɗin ruwa da sabulu, ta ƙarba ta ɗaure a haɓar zani tace idan Allah ya kaimu jibi ku dawo ku karɓa, yaron yace to, sannan ya fita daga gidan,,,,,

*zawarci*
Gwaggo tace raihana wannan wanki ma ai babu wani datti sosai, raihana dai bata yi mata magana ba ta ɗauki kayan mutane ta nufi ɗakinsu dashi, bayan ta ajiye ta fito suka ci gaba da aiki,

��������
*zawarci*
��������

Tunda safe gwaggo tazo kofar ɗakin su raihana ta riƙe ƙugu, tana cewa ki fito ubanki babu lafiya ki kawo kuɗin wankin nan inje in siyo mashi magani, daga ɗaki raihana tace wane irin kufi kuma?"" wanda kike tarawa a daidai lokacin da ta yaye labulen ɗakin ta siga ciki, raihana tace to gaskiya banda wasu kuɗin ni da zan bayar, gwaggo tace kina dasu, raihana tace faɗa man abinda nake siyawar, gwaggo tace wanki mana kina nan kin tara kuɗi dake da uwarki kin boye, dariya raihana tayi sannan tace baki son muna tara kuɗi gwaggo?""" tsaki tayi gwaggo sannan ta fita tabar ɗakin,

*zawarci*
Umma tace idan kina da kuɗi ki bata mana, raihana tace barta, zanje wajen baban dakai na, umma tace to, miƙewa raihana tayi ta fita daga ɗakin, ɗakin baba taje ta shiga tare da sallama, ya amsa , kusa dashi taje ta gaishe shi, ya amsa sannan tace baba miye ya sameka??"" baba yace mura nake, amma da sauƙi yanxun zan fita, raihana tace to Allah ya ƙara sawakewa, baba yace amin, raihana ta miƙe zata zata fita shima baba ya miƙe ya biyo bayanta, yana cewa mamana ki fito da miji kiyi aura kinji ko?"" to kawai tace tayi gaba, shima fita yayi daga gidan dan tafi wurin aiki......

������
*zawarci*
������

Raihana tana fitiwa ɗakinsu ta shiga ta fiddo wankin da zata yi, ta fara wankinta, *zawarci*
[21:18, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 7⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

Wannan shafinki naku ne, *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION*

Godiya ta musamman, *ASMEENAT XEEYAN* ��

*Y*ana fita tafi bayanshi da harara tace banza sakarai,,, kwanciya tayi tare da jawo bargo ta lulluɓe, taci gaba da baccin ta,,,,,

*A*minu kuma yana zuwa ɗakinshi gado ya hau ya kwanta, ya fara tunanin wata ƙawar *raihana* da take masifar sanshi, ajiyar zuciya sannan yace Allah sarki itama haka take ji, yanda yake ji idan raihana ta wulaƙanta shi, gyara kwanciyar shi yayi sannan yace ita kuma babu ruwanta bata jin komai, a bayyane yace Allah sarki rayuwa,,,,,,

****** ƙarfe 9:30am ta farka daga bacci, saboda haka a hanzarce ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka, bayan ta gama wanka ta fito, ta zauna a gaban madubi ta fara shirya kanta,,,,,,,,,****×

*A*minu yana ɗakinshi yaji ƙamshin turaren raihana, shima tashi yayi ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya, sannan ya nufo ɗakin raihana, itama ta gama shiryawa, ta matse cikin riga da wando, yana shigowa ɗakin a siƙwane ya isa inda take, ta rungumota , ta baya, ya ɗora fuskarshi saman kafaɗarta, daidai saitin kunnenta yayi magana, kinyi kyau madam, cikin masifa ta ƙwace jikinta,, ta juyo ta nuna shi da yatsan ta,, sannan tace wallahi daga yau sai yau, idan ka kuskura ka sake tiƙeni , ban yafe maka ba, dariya aminu yayi sannan ya sake matsawa kusa da ita, ya ƙara tallafo ƙugunta, ya ɗora hannuwanshi a saman ƙirjinta, raihana tace Allah ya isa ka taɓa, dariya ya sake yi sannan yasa hannunshi cikin rigarta, da sauri ta ciro hannu sannan ta ɗunƙule hannunta da niyyar kai mashi nushi yayi sauri yaja da baya,,,,,,,,,,

*H*aba madam ya kamata ki kawo man ɗan abinda zanyi break mana,,, raihana tace kaji wani sakarci kuma, madam sai kace wata inyamura`?"" Aminu yacd wallahi ba inyamura kike ba,,,, raihana taci gaba da cewa wallahi har inbar gidan nan bana girki kaji na faɗa maka, dan daga yau ka fara lissafi sati ukku zanyi gidanka, aminu yace Allah ya sawake, ni bana sakin mace duk abinda tayi man, raihana tace baka haɗu da irin raihana ba, dan wani abun idan nayi maka kai da kanka zaka rubuta saki ka bani, kuma idan kazo bani saika duƙa,,, aminu yace to Allah kada ya nuna mana ranar,,,, taɓe baki tayi sannan tace ka kawo man abinda zanyi kalaci, yace bara in dafa maki, ko inda yake bata kalla ba, shi kuma bai sake magana ba ya fita yabar ɗakin"""""""

*A* kicin haka ya zuge yaci gaba da aikin haɗa masu abinda zasuyi kalaci,,, ya daɗe sannan ya gama ya fito, da abinda yayi a farlo yaje ya ajiye,, ya koma kicin ya gyara inda ya ɓata,,, bayan ya gama ya dawo farlo ya zace ranki ya daɗe fito an gama, raihana ta taho cikin isa da ƙasaita, tazo ta zauna, yawo flaks tayi ta fara haɗa kalaci, sannan ta jawo flet na dankali da doya, ta ajiye a gabanta ta fara ci, aminu yabi ta da kallo, saida ta gama shi har lokacin babu abinda yaci ko yasha,,,

***miƙewa tayi zata nufi ɗaki da sauri ya miƙe ya riƙota,,,, farlo ya dawo da ita ya zauna saman kujera, ita kuma ya zaunar da ita saman cinyarshi, raihana kiji tsoron Allah, kada ki manta sadaki na bayar na auroki dan ina sanki, kuma na ɗauki hutu a wurin aiki na dan kawai in more da amaryata, a daidai lokacin da yake kai bakinshi cikin nata, raihana ta fara tureshi , amma a banza, haka taci gaba da halbe halbenta, tana tunkuɗeshi amma ko motsi baiyi ba, haka yaci gaba da bi duk inda jijiyar jikinta take yaci gaba da aika mata saƙonni, a kasalance raihana ta samu ta janye bakinta daga nashi, cikin wani yanyi tayi magana tace ban yafe maka ba, a hankali ya sake mata hannu , ya kwantar da bayanshi jikin kujera, ita kuma tana zaune a ƙasa,,, daga baya kuma ta miƙe ta nufi ɗakinta,,,, tana zuwa gado ta hau tayi ruf da ciki, zuciyarta tana mata saƙe saƙe,,,,,,

Shi kuma har lokacin yana zaune kamar yanda raihana tabarshi,,,,,,,,,,

Kiran sallar la"asar ne yasa umma cewa tashi muyi sallah mu dawo, *raihana* tace to, raihana ce ta fara fita daga ɗakin, umma har yanxun tana zaune inda take, raihana tana fita, umma tace to ai ga *zawarci* Allah ya ɗora maki raihana da ƙananan shekaru saidai addu"ar Allah ya kawo miji na gari,,,miƙewa tsaye tayi itama ta fito, a daidai lokacin da raihana zata shiga ɗaki,,, ta shige umma ta fito,,,,,,

������
*zawarci*
������
*R*aihana, ki fito fa babu ruwa a gidan nan, gwaggo ce take magana, raihana da take zaune saman abin sallah , tace *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un* a daidai lokacin da gwagho ta sake cewa in banda iskanci ina magana sai kiyiman shiru , to ai sai ki fito ki faɗa man idan ni kike so inje in samo ruwan nan, miƙewa tsaye raihana tayi ta fito tsakar gida, ta fara tattara kayan mutane data wanke, gwaggo tace a nan zaki samo man ruwan, wani bokiti ta ajiye a gaban raihana, amma har yanxun raihana batayi magana ba, ta gama ƙwashe kayan ta nufi ɗakin su,

*zawarci*
*B*ayanta gwaggo tabi tana cewa uwarki kika kyale, shegiya mai baƙin halin tsiya, saboda wannan baƙin halin yasa namiji ya sakoki gaki nan kin rasa mashin shini, ita dai raihana batayi magana ba, saboda haka tana ajiye kayan ta ɗauki hijabinta tayi waje,,,,,,,

������
*zawarci*
������
*A* kofar gida ta tsaya har ta samu mai ruwa, tace ya kawo mata jarka ɗaya, yace to, ya ɗauko ruwan tayi gaba yabi bayanta,, har cikin gida, inda gwaggo ta ajiye bakitin ta nuna mashi a ciki ya fara zuba ruwan, gwaggo tana ɗaki taji ƙarar zuba ruwa saboda haka tayo waje, salati ta fara tana tafa hannunwanta yanxun saboda tsabar bakin ciki kije ki samo ruwan shine ke mai arziki zakije ki karawo mai ruwa?""" wannan ai baƙin ciki ne, naira ishirin ɗin idan kika bani ai na siyi omo, raihana ba tayi magana ba, mai ruwa yana gama zuba ta bashi kuɗin shi , ya fita daga gidan ita kuma ta nufi ɗakin su, gwaggo tace kai yarinyar nan Allah yayi maki baƙin ciki , raihana Allah ya tsine maki albarka tunda kika hanani kuɗin nan, raihana da sauri ta fito daga ɗaki sannan tace , baƙin bakin ki ya faɗa kanki dake da "ya"yanki da jikokinki , sannan ta koma cikin ɗaki, gwaggo tayi ta zage zage ita ɗaya a saƙar gida,

*zawarci*
Saboda dama tun dawowar raihana gwaggo bata da yaron aike sai ita, tun tana cewa bata zuwa, ta haɗata da baba yace tayi haƙuri taje saboda a zauna lafiya,,,

***gwaggo sai Allah ya isa take tana ƙarawa tana tsine ma raihana saboda bata bata naira ishirin ba, daga umma har raihana babu wanda ya sake ma gwaggo magana har ta gaji da kanta tayi shiru,,,,,,
[21:19, 08/11/2017] ‪+234 813 308 2423‬: ����������
��������
������
����
*ZAWARCI*
����������
��������
������
����

*page* 8⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ��✍��

*JAMEELA MUSA*

����������
��������
������
����
�� *ZAWARCI*

*H*aka gwaggo tayi jarabarta harta ƙoshi dan kanta,,,,,,

*Y*aro ne, tsaye a tsakar gida , sai ƙara nanatawa yake ance ana sallama da *raihana* gwaggo ce ta fito daga cikin ɗaki tana cewa uwar baƙin hali kinaji ana kiranki baza kixo ki fita ba,, to kada Allah yasa ki fito ni bara inje, idan ya shirya zance kawai ya turo, tana faɗin haka tayi waje,,,,
������
*zawarci*
������
*A* zaure gwaggo ta sameshi ya jingina da bango, ƙafarshi ta dama ya ɗorata a bango ta baya,, ya rungume hannunshi a ƙirjinshi, kanshi yana kallon ƙasa, kana ganinsa, sallama gwaggo tayi , ya masa ba tare daya kalli inda take ba, gaban gwaggo ya faɗi, da sauri ta leƙa kofar gida, dan taga ko mai sallamar yana waje, babu kowa dowowa tayi, kallon da tayi mashi yafi ƙarfin ace yaxo neman *raihana* saboda haka ta dawo, tace kaine ka aika yaro cikin gida?"" sai a lokacin ya ɗago kanshi , da sauri gwaggo ta sauke idon ta ƙasa saboda wani abu taji ya shigar mata cikin ido, zuuuuuuu, yace Eh , *raihana nake nema, gwaggo cikin rawar murya tace , lafiya dai?"" yace lafiya qalau ia san ganin ta ne, har yanxun kan gwaggo ƙasa yake, tace an ɗaura mata aura, ummm yace, ba tare da ya sake magana ba, hannunshi ya saka a aljihu ya ɗauko bandir na 1000, ya miƙa mata, gwaggo da sauri ta ƙarɓa, tana godiya shi kuma ya fita, da sauri gwaggo ta miƙe tayi cikin gida,,,,,,,,,,,

<<>> {{}}~~¤
*A* ɗaki gwaggo ta duba kuɗin sannan ta jinjina kanta, tace lallai ina da sauran aiki a gabana,, wannan mai kuɗin idan ya auri *raihana* ai ina cikin matsala, hijabinta ta jawo daga saman kyaure ta zura tayi gaba{{}}}<<>>

������
*zawarci*
������
*S*allamar baba tasa da umma da raihana suka fito tsakar gida, baba sai ƙara faɗaɗa murmushin shi yake,, tabarma umma ta shimfida tana ƙara mashi sannu da zuwa,, yawwa yake cewa lokacin daya ke zama, suma zama sukai baki ɗayansu, baba yace albshirin ku?"" da umma da raihana suka ce goro, sannan umma tace ai yau yanda naga kana murmushin nan, nasan an samu nasara, baba yace gaskiya alhamdulillah a daidai lokacin da gwaggo tayi sallama ta shigo, inda suke zaune ta nufa tare da ɗauko kujera tayani gulma ta zauna, baba yace to yaudai *raihana* Allah ya temakeki kin samu mijin aure, gaban raihana ya faɗi da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta,,, cikin zaƙuwa gwaggo tace sirikin namu daga ina yazo?""" baba yace ai ba ɓoyayye bane , *yusufa* mai niƙa ne,!'""""""" idanuwa raihana ta zaro sannan tace haba baba, ka daina wannan naganar don Allah mutum da mata ukku yara ashirin da wani abu, gwaggo tayi karaf tace rufa ma mutane baki munafikar Allah, ubanki yana magana kina magana?"" wannan ai rashin tarbiyya ne, sannan ta juya wurin baba tace a gaskiya idan kana biye ma yarinyar nan babu ranar da zata aure, tunda an samu mai santa kafin ya zare kawai kace ya turo, baba yace, ai yace zaizo su fahimci juna dai, saboda haka yaune zai fara zuwa, wata irin guɗa gwaggo tayi , sannan tace lallai yarinya kinyi goshi{{}}

*zawarci*
*U*mma batayi magana ba, ta tashi tayi ɗakinta, raihana ma ta rufa mata baya,,,, gwaggo ta zauna taci gaba zuga baba, lallai yace ma yusufa ya turo, kawai a ɗaura aure in yaso daga baya ta tare, haka dai taci gaba da maganganunta, daga baya ta tashi tayi ɗakinta, shima baba ɗakinshi ya shige,,,,,,,,,{{}}

{{}} gwaggo sai zagaye gida take tana cewa wallahi Allah ya rufa maki asiri, kinga kiyi aurenki, ki huta, kai wannan yarinya da sa"ar rayuwar kike,{{}} tanayi tana "yar dariyarta, kana ji kasan dan wulaƙanci take abun,, {{}}

{{}} *zawarci* {{}}
*R*aihana tace umma wallahi da baba baya nan dana fita nayi ma gwaggo magana, ince ta fita harkata, umma tace ki barta tayi duk abinda taga dama, abinda mutum yayi mai kyau ko kishiyar hakan kanshi yayi ma,,,,,,,


*U*mma tace tashi muyi sallar isha"i ki ida man labarin {{}}

������
*zawarci*
��������
*D*ariya *raihana* tayi sannan ta ɗauki buta, alwalla tayo ta dawo ɗaki hijibinta ta saka sannan ta haye saman abin sallah,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER'S ASSICITION* ��✍�� ke maku fatan alkairi, ni *jameela musa* nake cewa ku kasance tare dani, ��💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*page* 9⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*


*R*aihana tana gama sallar isha"i, tana zaune a inda tayi sallar bata tashi ba, umma tace mata tunda kin gama ci gaba da bani labari, umma bata gama rufe bakinta ba, gwaggo ta yaye labulen ɗakin umma babu ko sallama tace, maza fito ga ango can mijin amarya yaxo, yana ƙofar gida yana jiran *raihana* farin cikin shi, ta ƙareshe maganar tana dariya,

*T*saki raihana tayi sannan tace bazanje ba, gwaggo tace ni kike faɗa ma haka?"" raihana tace an faɗa idan kinji haushi shima ki koreshi tunda dama kin saba ƙorama man samari,

Gwaggo tace wani in ƙori yusufa ace ina baƙin ciki?"" tana maganar tana taɓe baki, raihana tace ai dole yanxun kice haka tunda kinga shi ba aminu bane, gwaggo tace keji ɗiya yau kuma jarabar rashin auren naki a kaina zata ƙare?"""""

Rainaha tace dole ta ƙare a kanki tunda babu munafikar da ta kashe man aure sai ke, idanuwa gwaggo ta zaro sannan ta daki ƙirjinta da ƙarfi tace lallai yau naga sherrin rayuwa, raihana tace wallahi idanma har sharrin rayuwane baki ga komai ba, gwaggo tace to babu damuwa yanxun dai kije ga sabon miji yaxo, idan har kika yi auren banma kara zuwa gidan bare aja mani sharri,

Raihana tace zanje bisa cika umarni mahifina, tana faɗin haka ta miƙe tayi waje fuuuuuuuuu tunda dama hijabin da tayi salla bata cire ba, gwaggo tace shegiya mai baƙin hali ai gara dai a lallaɓa a aurar dake ga yusufa ko aikin gidan "ya"ya yasa ki ladafi, ɗiya tsaitsaye haka kamar an jika shinkafa da ruwan sanyi?"""" umma dai bata ce komai ba, haka gwaggo tayi ta wulaƙanci daga baya kuma ta nufi ɗakin ta,,,,,,,,


A ƙofar gida, raihana ta samu yusufa tsaye, yasha gayu fuskar nan ya nemi mai ya lafta mata sai ƙalli take, haƙoran nan nashi kuma dayaci goro suma sai yauƙi suke, haka raihana tabi yusufa da kallo tun daga tsakiyar kansa har ƙafafuwanshi,

Bayan ta gama kalleshi tsaf, ta dawo da duban ta daidai idon shi, suka kalli juna ido cikin ido, sannan tace sannu, ya yashe baki yace raihana raihana, tsaki raihana tayi sannan tace da Allah malam naji saƙonka, yanxun ka shirya auren *RAIHANA* ne?""""

Yusuf yace Eh darling, tsaki raihana tayi sannan tace to na baka daga yau zuwa jibi jibin nan, kaje ka haɗo man milayan biyar, idan har ka haɗo man su to lallai kaxo a ɗaura mana aure,

Idanuwa yusufa ya zaro sannan yace miliyan biyar fa kike magana?"""

Raihana tace Eh ba raihana kake so ba?""" yace Eh tace to madamar kana san aure na, sai ka kawo kuɗin nan idan kuwa ba haka ba, kada ka kuskura in sake ganin ƙafar ka a ƙofar gidan nan,

Ajiyar zuciya yayi zaiyi magana raihana ta ɗaga mashi hannu sannan tace ba wata magana tsakanin ni da kuma kai idan har ka kawo kuɗin to idan har baka kawo ba, bazan sake saurarenka ba, tana kaiwa nan tayi cikin gida..................

Yusufa yabi raihana da kallo har ta shige cikin gida, tana shiga ya ƙare ma gidan su raihana kallo yace lallai wannan yarinyar tama raina ma mutane hankali in banda iskanci ko ubanta bai taɓa ganin miliyan ɗaya ba amma shine har take cewa wani ya kawo mata miliyan biyar, tsaki yayi sannan yace zanga uban naki in faɗa mashi tunda shi mutumin kirki ne, haka yayi ta surutanshi shi ɗaya daga baya kuma ya tafi yabar ƙofar gidan.................

Raihana tana dawowa gida, ɗakin ummarta tayi sallama ta shiga, umma dake kwance har bacci ya fara fizgarta, tace har in dawo?""" raihana tace Eh, umma tace baima wani daɗe ba, raihana tace Eh, umma tace to ya kukayi dashi, murmushi raihana tayi sannan tace umma gaskiya nace mashi kawai ya turo, ta ƙarasa maganar tana taɓe baki, umma tace to Allah yasa hakan shine alkairi, murmushi raihana tayi sannan tace alkairin ma ne, umma tace to bara inje in sanar da babanku, raihana tace tou, tashi umma tayi ta fita daga ɗakin, tana fita raihana ta kece da dariya, sannan tace duk dani ake magana, idan har bazan koma gidan Aminu ba, haƙiƙa dai in su namiji mai tsafta in aura amma na auri yusufa haka ai ko dariyar ƙawaye ta hanani sakat, gyara ƙafafunta tayi sannan ta kwanta, da hannunta ta lalabu ta jawo wani tsohon zani ta lulluɓe, bata daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita...............


Umma bayan taje ɗakin baba ta faɗa mashi cewa raihana tace ma yusufa ya turo, baba yace to Alhamdulillah lamari yayi daɗi Allah ya tabbatar da alkairi, umma tace ameen, itama umma ɗakinta ta tashi ta nufo ta kwanta,



💦💦💦
*Zawarci*
💦💦💦

*T*unda safe raihana tana gama sallah gwaggo ta fito wai lallai yau gidan nan fa babu ruwa, saboda haka raihana ta fito ta tafi wurin mono ta samo masu ruwa, raihana dake kwance, saboda ta gama sallah ta kwanta ta huta gabanta ya faɗi,

Gwaggo ta iso ƙofar ɗakin tace ki fito ki samo mana ruwa nace gidan babu ruwa, raihana daga kwance tace bazanje ba, *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,* raihana saboda rashin mutunci ni kike zagi?"" kuma uwarki tana ji kina zagi na, har cewa take ki ƙara man, daga raihana har umma idanuwa suka zaro suna kallon gwaggo, taci gaba cewa saboda kawai nace ki ɗibo ruwa sai kawai kiyi ta zunguwara iyaye na zagi,

Wayyo Allah da mutunci na gidan nan tunda ɗiyar nan ta dawo take ɗura ma iyayena zagi, lallai yau basai gobe ba, zamana gidan nan ya ƙare, baba dake ɗaki ya fito yana tambayar ba"asi?"""

Kuka gwaggo take sosai tace raihana ce tun shekaran jira da tayi magana sai ta zageta kuma uwar tana ji saidai tayi dariya,

Baba yace ina raihanar take?"" umma ta fito daga ɗaki tace wallahi ba haka akayi ba, yace rufe man baki, umma tayi shiru baba ya kalli inda raihana take tsaye yace daga yau shine magana na ƙarshe nasha faɗa maki idan baki kiyaye ba, haƙiƙa zaki bar man gida kinji na faɗa maki, raihana tace tou baba insha Allah amma wallahi ban zage ta ba, baba yace koma dai miye keta shafa bani ba, maza kije ki ɗauka ki ibo mata ruwan, da kina gidanki zataje can ta kirawo ki?""" raihana tace tou, ɗaki ta koma ta ɗauko hijabinta, kofar ɗakinsu ta ɗauki bokitin ƙarfe, ta ɗauka tayi waje...............................

Raihana bayan ta fita, baba yace ma gwaggo kema banda masifa tunda safe sai kice yarinya saita ibi maki ruwa?""" gwaggo tace ai tuwo zan ɗora dan anjima gidan biki zani, baba yace to miyasa tun jiya ba"a samo ruwan ba?"" gwaggo tace saboda sirikina zai zo, kuma almajira ma idan ka kira basu zuwa, tsaki baba yayi sannan ya nufi ɗakin shi itama umma ɗakinta ta koma gwaggo kuma tabi baba ɗakin shi ta fara tattaro kayan shi da sukai datti........................




A madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ni *MEELAT MUSA* nake cewa ku biyoni ..........................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣0⃣

*AMEENCHI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*T*saye take a bakin mono ta jera layi da bokatin ta, ga ɗan sanyi sanyin asuba, Raihana ta buɗe idanuwanta duk wurin babu mace sai maza, baƙin ciki ko miye raihana ta tuna oho?"" kawai hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanuwanta, haka taci gaba da kuka tana gogewa da gefen hijabinta,

Kuka take tana matsawa da layinta idan an janye, haka kowa yaci gaba da ibar ruwa har layi yazo kanta, haka ta matsa ta tara nata, ta koma ta fara bugawa, har bokatin ya cika, tazo ta janye ta ɗauka ta nufo gida tana mai nadamar wannan *zawarci*

Sallama raihana tayi ta shiga cikin gida, a ƙofar ɗakin gwaggo taje ta ajiye ruwan, har zata juya gwaggo tace yawwa ga kayan babanki nan sunyi datti sai ki siyo sabulu da ruwa ki wanke, raihana tace sabulu da ruwa kuma?"" to a ina zan samu kuɗin siye?"""

Ggaggo tace cikin kuɗin da kikai wanki jiya?""" murmushi raihana tayi sannna tace to Alhamdulillah Allah ya ƙara rufa mana asiri, gwaggo tace Allah ya tona maki asiri raihana muje abinda kike boyewa, raihana tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un Allah dai ya tona maki asiri gwaggo ni kuma nawa ubangiji ya rufe man shi,

Gwaggo tace lallai raihana iskancinki kullum gaba yake, yanxun nan ubanki yayi man tsakani dake amma shine dai baza ki fita hanyata ba?"""

Raihana tace nima idan har baza ki fita tawa ba banga abinda zai fitar dani taki ba saidai a raba gidan nan, dani da ummana daban ke kuma dake da baƙin halinki,


Wannan magana tayi ma gwaggo ciwo saboda haka ruwan da raihana ta ibo ta ɗauko bokatin ta kwarara mata su duka a jikinsu, sannan ta ɗaga bokitin taci gaba da kwaɗa ma raihana,

Raihana sai kuka take tana faɗin a taimaketa gwaggo zata kasheta, baba da bacci ya fara ɗauka da sauri ya fito tsakar gida, amma umma duk abinda ya faru tana ji , amma bata ce ta tafasa bare a shiɗe, kuma haka bata fito tsakar gidan ba,

Baba yazo ya riƙe bokitin sannan yace ma gwaggo wai wannan wane irin masifa ne?""" gwaggo cikin shashsheka ta alamar gajiya kamar wanda tayi gudu sosai, tace tun da safe ɗiyar nan take zungurawa sale mai kanwa zagi, baban gwaggo kenan, taci gaba da cewa kuma idan mutum yayi magana a bashi rashin gaskiya,,,,,

Inda raihana take tsaye tana kuka baba ya kalla wanda duk gwaggo ta farfashe mata kai, baba yace ke kuma baki zaunuwa wallahi, baba na faɗin haka raihana bata sake bi ta kanshi ba tayi ɗakin umma,

Baba yabi ta da kallo, ita kuma tana shiga ɗakin ta fashe da kuka tace umma saboda Allah ni babu mai goya man baya?"" baba kullum bayan matarshi yake bi, umma tace kema da a gidanki kike ai mijinki zaibi bayanki ne, raihana tace Allah yaman sakayya umma dai batace komai ba, ita kuma raihana zama tayi sai Allah ya isa take yi,

Daga baya umma ta fita daga ɗakin, ita kuma raihana zama tayi taci kukanta ta ƙoshi, saida ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta, ta kwanta wani wahalallan bacci yayyi gaba da ita,,,,,,,,,,,


*zawarci*

Ƙarfe 12:30pm raihana ta farka daga bacci, fitowa tayi tsakar gida, a ƙofar ɗakin umma taga wani tashin wanki, an kawo mata, inda gwagg take ta kalla, ita kuma gwaggo surfe take k uwarmi take surfawa oho?""""

Kanta ta dafe da yake mata wata irin sara, dafe kan tayi sannan ta duƙa ta ɗauki buta ta nufi bayi, { *toilet* } tana fitowa ta nufi inda suke sanwa ta fara bubbuɗe kwanuka, gwaggo uwar mi kike nema?"" ko inda take raihana bata kalla ba, taci gaba da buɗe buɗenta, dariya gwaggo tayi ta dakata da dakan da takeyi, ta ɗora guwar hannunta kan taɓaryar dake cikin turmi, sannan ta tallafe fuskarta da tafin hannun ta, tace yarinya babu abinci, sai kinsan matsayi na a gidan nan sannan zaki fara cin abinci, murmushi raihana tayi sannan tace aikin banza kare da gudun layya, tana kaiwa nan tayi ɗakin umma, gwaggo tace saida a mutu da yunwa""" raihana dai bata sake magana ba, ta koma ɗaki madubi ta ɗauko tana kallon yanda gwaggo taci ma fuskarta mutunci,

Allah yayi man sakayya haka rainaha kawai ta faɗa , ta koma ta kwanta, wani bacci wahalar ya ƙarayin gaba da ita,,,,,,,,,,


💦💦💦
*zawarci*
💦💦💦

*R*aihana tashi kiyi sallah mana, umma ce take tashin raihana , a gajiye raihana ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauhi, hawayen wahala suka fara safa da marwa a idonta, umma tace ki tashi kiyi sallah nace, a daidai lokacin da umma take cire hijabin jikinta,

A gajiye raihana ta miƙe ta fito, buta ta duƙa ƙofae ɗakinsu ta ɗauka, gwaggo sai habaici take, tsaki raihana tayi sannan tace idan dai kare yana haushi idan bai samu aboki ba ya zama mahaukaci, gwaggo tace uwarki waccan tana nuna ɗakin su to itace mahaukaci, kuma itace karya, dariya raihana tayi sannan tace ga irin halin nan kinayi , gwaggo tace shegiya mai baƙin hali, raihana tace ai a turbar kika ɗrani tun ina yarinya,

Gwaggo tace zawarar banza, raihna tace , Allah ya kaddara man kuma kema dake da ahalinki Allah ya ɗora maku jawarci kuji abin idan daɗi ne,

Gwaggo tace ni kike cewa "ya"yan na zasui *zawarci*? Tsaki raihana tayi , bata sake magana ba ta fara alwalla,

Gwaggo sai masifa take, ala dole wai raihana tace za"a sako mata "ya"ya daga gidan aure, taci gaba d cewa ke kaɗai kika zamo haka kuma kece kaɗai zaki lalace haka , a daidai lokacin da raihana ta gama alwalla tace tare dai zamu lalace mai faɗa da ɗiyar cikin ta, ki kashe mata aure dan ki aura ma ɗiyar aminiyarki, sai Allah ya maki abinda baki zato, tana faɗin haka ta shige ɗakin su,


Gwaggo kuma taci gaba da cewa anje an kashe aure uban waye yasa tun farko baki san mijin,?"" kuma har ki mutu baza ki samu wanda yakai darajar aminu ba, yar banza lalata,

Raihana dai bata sake magana ba, gwaggo ko banda tsinuwa da la"ana babu abinda take yi,,,,,,,,


Bayan raihana ta gama sallah , uma tace mata ga abinci can badiyya ta aiko maki dashi, kuma tace zata kawo maki wanki idan Allah ya kaimu, raihana tace tou, ɗauko abinci tayi ta matsa kusa da uma tace suci, ua tace ta ƙoshi, haka raihana ta caka hannu ta fara cin abincin,

Tana cin abinci umma tace raihana, kada ki kuskura ki sake cewa gwaggo ta kashe maki aure, abincin data ibo zata kai bakinta ta fasa kaiwa, tace umma wallahi itace ta kashe man aure, umma tace haka Allah ya ƙaddara kada ki kuskura ki sake faɗin haka kinji na faɗa maki ko?"" raihana tace Eh, umma tace gama cin abinci yau ki ƙarasa man labarin nan, murmushi raihana tayi tace to,


Haka tayi ta cin abincin bayan ta gama, ta fita ta wanko hannunta ta dawo, maganin da umma ta siyo mata ta miƙa mata, bayan tasha maganin ne, tace umma zan fara murmushi raihana tayi sannan taci gaba da cewa...........................




*MEELAT MUSA* ke cewa ku kasance tare dani!!!
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣1⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*H*ar yanxun yana zaune inda raihana ta barshi a farlo , ya ɗan zame saman kujera ya kwanta, lallai wannan wane irin fitina ne?"" yana da mata amma shida babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tsaki yayi ya miƙe ya nufi ɗakin shi,

Yana zuwa babu ɓata lokaci wanka yayi ya shirya ya fito fess abunshi , ɗakin raihana ya dawo, bayan ya shiga ya sameta kwance saman gado, shima saman gadon ya hau, da sauri ta matsa da baya, hannunshi yasa ya jawo ƙafarta zuuuu ya matso da ita kusa dashi,

Saman ruwan cikinta ya hau, ya matsar da fuskarshi kusa da tata, daidai bakinta ya ɗora nashi, idanuwanshi suna kallon nata, sannan yace wallahi kiji tsoron Allah idan har kika kuskura a wannan halin kika mutu zaki haɗu da fushin Allah nine mijinki so da kauna yasa na aureki ki baki sona raihana ya kamata wani abun ki riƙa ragewa saboda rayuwa,

Wai miyasa ma baki sona?""" shiru raihana tayi saboda bata da dalili, riƙo haɓarta yayi da hannu, ya haɗa bakinshi da nata, da sauri ta fizge bakinta ta jawo wani kallabi ta goge bakinta , dariya yayi yace kyamata kike?""" raihana tace bana kyamarka nidai kawai bakai man ba,

Yace miyasa ban maki ba?""" a daidai lokacin da ya sauka daga saman jikin ta, raihana tace nifa ban taɓa ganinka ba, duka sau nawa na ganka aka ɗaura mana aure dakai?""" Aminu yace to miye aibuna?"" raihana?"" ya ƙarashe maganar yana kwantar da kanshi yayi yanayin tausayi,

Yace kiji tsoron Allah , ubangiji yana fushi da matar da take ma mijinta irin abinda kike man, ki daina abinda kike tun kafin ki haɗu da fushin Allah,

So nawa aka aurar da mace ga namijin da bata taɓa gani ba?"" kuma suna zamansu hankalinsu kwance, kiyi haƙuri ki soni kinji raihan?""" wallahi zan jiyar dake farin ciki?"" ya ƙareshe maganar hawaye yana bin fuskarshi,

Ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace to kayi haƙuri duk abinda nayi maka insha Allah bazan sake ba, yace yawwa ko kefa?""" haka yayi ta mata nasiha, raihana tanajin nasiha tana bin jikin ta, amma fa har yanxun baiwai dan tana san Aminu ba, kawai saboda yana faɗi nata nau"in azabobin da Allah zaiyi ma wanda bata biyayyar aure yasa jikin ta yayi sanyi,,,,,,,

*** *** *** ***

*B*ayan haka da sati biyu, wata rana gwaggo ta kawo ma raihana ziyara da ita da aminiyarta *Ladi* raihana tayi farin ciki da zuwansu sosai sabida haka taje ta kawo madu ɗan abun ci da sha, bayan sunci sunsha, gawaggo tace raihana niko na ganki duk kinyi baƙiƙirin kin rame,

Murmushi raihana tayi sannan tace babu wani abu da nayi gwaggo, kawai dai dan kin daina gani na kike ganin haka, ta ƙarasa maganar tana taɓe baki, gwaggo tace to ya zaman naku yake?""" raihana tace *alhamdulillah* gwaggo tace amma gaskiya yaron nan yana cutar dake, raihana tace babu wani cutuwa muna zaune lafiya,

Gwaggo tace ai kece kike zaune lafiya dashi shi kwata kwata baya kaunarki, cewa yake daya samu yayi maki ciki zai sakeki ya auro wata, tunda dama baki sanshi, raihana ta ɗago ta kalli gwaggo cikin zaro idanuwa, raihana tace a,a, gwaggo Aminu bazai man haka ba, gwaggo tace baza ki gane ba, aike yarinya ce, tashi muje ladi, har yanxun akwai kuruciya a kanta,

Raihana tana ganin gwaggo ta mike tace gwaggo tsaya, gwaggo tace ai ina faɗa maki gaskiya bakya gani ne, raihana tace ni wallahi yana so na, kuma har kuka yake saboda yanda yake kauna na, gwaggo tace yaudara ce, ba sanki yake ba, raihana tace tou Allah dai ya sawaƙe, gwaggo tace amin, haka suka rantafa ita da ladi suka bar gidan...............

Fitar gwaggo da larai basu zame ko ina ba, sai gidan uwar mijin raihana, bayan sun gaisa gwaggo tace kin gane ni?""" maman Aminu tace na ganeki mana, gwaggo tace dama maganar yarinyar nan ne, dama maman Aminu bata san raihana, tunda taji labarin bata kaunar Aminu taji kuma tace itace ajalinsa, wannan dalilin yasa ta tsani raihana,,

Gwaggo tace dama cewa nayi tunda dai har yanxun naga ta kasa haƙura su zauna lafiya ɗiyar ƙawata na kawo dama ki haɗasu suyi aure, ita dama tana kaunar Aminu , tana sanshi tun tuni, maman Aminu tace to ai dama ya kwana da sannin bana kaunar yarinyar nan dole ya rabu da ita tunda ba tare aka haifesu ba,

Haka gwaggo taci gaba da zuga maman Aminu, daga baya suka tashi suka tafi daga gidan,

Suna fitowa gwaggo tace k sai in bari ta zauna a gidan can?"" duk tafi su bushira gidan miji, wato ɗiyarta kenan, da sauran "yan uwanta, tace shegiya sai ta fito wallahi, kuma babu ita babu ƙara auren mai kufi saidai ta samu talaka ta aura, haka sukaci gaba da magana suna kulla makircin su, daga baya suka rantafa suka nufi gida.................................,


Raihana zaune a gaban Aminu,

WASIKAR JINI BOOK 8 COMPLETe book

NAN TAKE KUWA HAIMAN YA SHIGE GABA YAYI
MUSU LIMANCI,BAYAN AN IDAR DA SALLAR ANYI
ADDU'A SAI KOWA YA KIMTSA SUKA DEBI
MAKAMANSU DA DUKKAN KAYANSU SUKAYI
GABA.Tafiyar su yarima Zainur keda wuya bayan
cikar rabin sa'a daidai saiga rundunar su sarki
Marwatu sun baiyna,dukkaninsu a cikin shigar
bakaken tufafi kuma a kasa suke babu mai doki
guda daya,babu sarki Marwatu da Waziri Ridwan a
cikin wadannan zuga sakamakon dole ne su
kwanta suyi jinyar raunikan jikinsu.Daga nesa suka
fara sanda harma a cikin rub da ciki suke tafiya
suna jan jikinsu sai kace macizai.Sa'adda suka
hango sansanin sukaga fitilo a kunne kuma ga
dakarun tsaro a tsaitsaye sun yiwa sansanin
kawanya,abinda basu sani ba shine babu kowa a
cikin sansanin kuma dakarun da suke hangowa a
tsaitsaye duk ba masu rai bane mutum mutumi ne
dukkaninsu.Koda ya rage saura baifi taku ashirin
ba tsakakanin dakarun sumamen da sansanin sai
kawai suka fara harbo ruwan kibiyoyin wuta,nan da
nan tantunan da aka kafa suka kama cin
wuta,suma mutum mutumin dake tsaye suka rinka
faduwa kasa suna ci da wuta,cikin kankanin lokaci
komai dake cikin sansanin ya kone kurmus.Duk
wannan abu dake faruwa dakarun sumamen na
kwance a kasa cikin lambo jira suke kawai suji
dakarunsu Zainur sun rugo daga cikin wutar
sannan suma su taso su afka musu,amma sai
sukaji shiru abin daya kara basu mamaki ma shine
tunda suka harbo kibiyoyin wuta a cikin sansanin
kawo izuwa sa'adda komai ya kone basu jiyo ihun
koda mutum daya ba.Koda fuskantar hakan sai
shugaban dakarun ya mike tsaye zumbur ya kura
idanunsa da kyau izuwa cikin sansanin take ya
gane cewa lallai makircin yaki aka nuna musu
saboda ko mutum daya mai rai babu a cikin
sansanin mutum mutumi ne kawai wadanda basu
haura guda ashirin da wani abu ba kwance a kas
suna ci da wuta.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun sumamen ya kwarara uban ihu cikin
tsananin bakin ciki.Al'amarin da yasa gaba dayan
yaran nasa suka mike tsaye kenan suka dubi cikin
sansanin.Koda suka fahimci abinda ke faruwa sai
suma ransu ya baic nan take shugaban dakarun ya
fiddo wani dan karamin madubin tsafi daga cikin
aljihu ya shafe shi sai ga fuskar waziri Ridwan ta
baiyana,kafin shugaban dakarun sumamen ya bude
baki yace wani abu tuni Ridwan ya tari
numfashinsa yana mai cewa kai shashashan
banza,abokan gaba sun yaudare ku ne kamar
yadda suka yaudare mu da farko,kai wane irin
dakiki ne ashe ban gargadeka ba akan kada ku kai
hari sai kun tabbatar da cewa abokan gabar na nan
a cikin sansaninsu.To ka sani cewa tuni sun matsa
gaba sun kafa wani sansanin kuma a yanzu haka
wasu daga cikinsu sun bar sansanin sun tafi
neman wannan bakon da gimbiya Nauwara
wadanda su tuni sunyi nisa a cikin daji babu
mamaki ma sun fada cikin daji da kogon Hajarul
Aswad yake.Maza ku karaso sabon sansanin nasu
ku kashe duk wani abu mai rai dake cikinsa karku
bar ko kaza guda daya da rai.Ni da sarki Marwatu
da sauran dakaru zamu riske ku a sansanin nan da
zuwa gobe da safe.Koda gama fadin haka sai
hoton fuskar waziri Ridwan ya bace daga kan
madubin.cikin gaggawa shugaban dakarun
sumamen da yaransa kimanin su dubu arba'in
suka nausa da gudu izuwa cikin daji.Wani irin
gudu sukeyi na ban al'ajabi saboda karfin sihirin
tsafinsu domin har tashi sama suke suna dira a
kan kololuwar dogayen bishiyoyi suna karawa
gaba.
*A can cikin kogon kankara kuwa lokacin da
yarima Yazid da Gimbiya Nauwara sukayi arba da
wannan katuwar mummunar halitta mai siffar
macijiya dauke da kan mage,ga hannaye guda
goma sha biyu gami da jelar guda arba'in da
gutsiren daya wacce Yazid ya sare rabinta sai suka
firgita ainun.Ba shiri Yazid ya tunkude Nauwara
bayansa ya daka mata tsawa yana mai bata
umarnin ta cigaba da iyo ta fice daga cikin kogin
kankarar ta isa can daya gabar tasa.Koda halittar ta
fahimci hakan sai ta tasam musu su biyun tana
jeho musu hannayenta da jelunanta tana kawo
musu mugun duka gami da sara da suka da kaifin
faratan hannayenta.A karom farkon data kawowa
Nauwara sara da farcen hannunta guda Nauwara ta
yunkura cikin zafin nama ta zare takobinta ta kare
saran ai kuwa sai kafin farcen nata ya raba takobin
Nauwara gida biyu,kafin Nauwara tayi wani yunkuri
tuni halittar ta gabza mata wawan naushi da jelarta
guda a fuska.Saboda Karfin Naushin saida Nauwara
tayi sama kuma tayi katantanwa sau uku a saman
sa'adda jini yayi feshi daga bakinta ta fado kasa
cikin kogin kankara a sume kuma ta fara lumewa
izuwa karkashin kogin.Koda Yazid yaga abinda ya
faru ga Nauwara sai ya fusata ainun bai san
sa'adda ya kwala kabbara ba ya daka tsalle sama
daga cikin kogin tamkar daga cikin naka aka cillo
shi ya dankarawa halittar wawan sara a tsakiyar
kanta.Nan take takobin tasa ta rabe gida biyu
amma saboda karfin saran nasa saida halittar tayi
wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da zugin
da taji ta fadi da baya cikin kogin tsundum tamkar
daga sama aka jefo giwa.kafin halittar ta taso
saman ruwan tuni Yazid yayi nutso kasa ya dauko
Nauwara yayi ninkaya izuwa bakin gaba ya
shimfideta a kasa amma ko alamar numfashi babu
a tare da ita.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma
hankalinsa kenan ya fara kokarin dawo da
numfashinta yana mai danna kirjinta.Kawai sai yaji
tasowar wannan halittar daga karkashin kogin.A
fusace Yazid ya juyo ya kura mata idanu.Halittar ta
fito daga cikin ruwan tana tafiya sululu a kasa
tamkar macijiya kuma ta tunkaro inda yake.Komai
dakewar mutum gami da karfin zuciyarsa idan yaga
wannan halittar yayin fitowarta daga cikin wannan
kogi tana mai baiyana gaba dayan surarta dole ne
ya
Al amin Ahmed guyson ke magana
firgita.Cikin zafin nama Yazid ya mike tsaye
zumbur ya shafa ko ina a jikinsa yaji babu makami
ko guda daya kawai saiya dunkule hannayensa
yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya shiga
karanta wadansu addu'o'i na musamman a cikin
zuciyarsa a lokacin da halittar ta cigaba da durfafo
shi.Koda ya fuskanci cewa halittar so take ta kawo
musu cafka su biyun har da Nauwara wacce ke
kwance tamkar gawa sai ya rugo da gudu izuwa
kan halittar ya tareta suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa
junansu naushi da bugu,ita halittar tana kai masa
duka da dukkan jelunanta amma sai gashi yana iya
kade hannayen nata da jelunan nata cikin wani irin
bakin zafin nama na gaban kwatance kuma yana
mai da mata martani.Duk sa'adda ya sami nasarar
naushin halittar koina a jikinta sai tayi baya a
sama tamkar da majaujawa aka janyeta saboda
karfin naushin nasa amma saboda naci irin nata
sai kaga ta kuma tasowa sun cigaba da
artabun.Kokarin halittar kawai shine ta samu ta
kanannadeshi da jelarta guda amma ta kasa,shi
kuma kokarin da yake shine ya samu damar
naushinta a fuska ko a kanta saboda ya fuskanci
cewa nan ne lagonta yake,domin sa'adda ya
dankara mata saran nan a tsakiyar kanta saida
idanunta suka wurkile tayi rabin suma ta lume kasa
a cikin kogon kankarar amma saboda bakin naci
tana farfadowa sai ta taso sama suka cigaba da
artabu.Saida Yazid da wannan halitta suka shafe
kusan rabin sa'a suna kwamarzuwa tana bugunsa
yana bugunta ya zamana cewa kowannensu naji a
jikinsa amma an rasa wanda zai sami nasara a
cikinsu.Ita dai halittar tana ta zane masa sassan
jikinsa da jelunanta amma ta kasa sukarsa ko
yankansa da faratan hannayenta,shi kuma ya sami
nasara yana ta gabza mata naushi a fuskarta har
idonta guda ya kumbura subtum yana zubar da
jini,kunnenta guda ya dode ta daina ji dashi,ko ina
a fuskar tata ya kumbura yayi luhu luhu gashi dai
ta jigata ainun amma taki hakura sai cigaba da
fadan takeyi.Ana cikin wannan hali ne halittar ta
shammaci Yazid ta jefa jelarta guda izuwa kan
Nauwara ta kanannade ta ta dagata sama.Koda
ganin haka sai jikin Yazid ya yi sany ya ja da
baya.Koda ganin haka sai halittar ta bushe da
mahaukaciyar dariya mai kama da rurin tsohon
zaki sannan ta dubi Yazid ta bude baki a karo na
farko tayi magana tace,yakai wannan shaidanin
bil'adama kayi sani cewa yau shekarata arba'in da
daya a cikin wannan kogin kankara ina gadin
wannan daji na Hajarul Aswad babu wani mahaluki
daya isa ya ratsa ta cikin kogin nan walau mutum
ko aljan har ya iso nan karshen gabar batare dana
hallaka shi ba.Komai yawan runduna kota mutane
kota aljanu saina karkashe su na karar dasu sun
zama gawawarwaki amma sai gashi ka tsalleke
wannan kogi kuma na kasa kashe ka.Yanzu gashi
na sami nasarar dankar abokiyar tafiyarki wacce
tayi dogon suma sakamkon naushi daya danayi
mata dazu,to ka sani cewa har yanzu tana raye ba
mutuwa tayi ba,amma idan kana son ta cigaba da
rayuwa saidai ka tsaya cak a inda kake na matso
gareka na kashe ka batare da kayi yunkurin kare
kanka ba.Da zarar kayi wani yunkuri na kare kanka
ko cutar dani kuwa zan matse jikin abokiyar tafiyar
taka na kakkarya duk kasusuwan jikinta.Koda jin
wannan batu sai hankalin yarima Yazid ya
dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi take ya
tuna amanar da yarima Zainur ya bashi akan
Nauwara sannan kuma nan take yaji sonta ya sake
kwarara a zuciyarsa fiye da ko yaushe,kawai saiya
tsaya cak yace na yarda kizo ki kashe ni amma na
rokeki bayan kin kashe ni ki kyale Nauwara kada ki
taba lafiyarta Koda jin haka sai Halittar ta bushe da
dariya tace aini burina kawai shine na kashe ka
kuma na hana kowa tsalle wannan kogi saboda
idanban kashe ka ba ka karya lagona kuma ka
rusa tarihin jarumtakata da kwarjini,ina maiyi maka
alkawari cewa lallai bayan na kashe ka zan sauke
abokiyar tafiyarka kasa amma dole sai dai ta koma
da baya ba zata wuce gaba don tunkarar kogon
Hajarul Aswad.Koda jin haka sai yazid yace na
amince da hakan,kawai saiya saki jikinsa ya fara
kiran sunayen ALLAH a cikin zuciyarsa yana mai
neman taimakon Allah.Ita kuwa halittar sai ta
cigaba da durfafoshi tana kyakyala dariyar
mugunta,ashe duk wannan abu dake faruwa
tsakanin Yazid da wannan macijiyar Nauwara ta
dade da farfadowa daga dogon suman da tayi
amma saboda tana kanannade a cikin jelar halittar
a sama babu abinda zata iyayi.Koda Nauwara taga
yadda Yazid ya sallama rayuwarsa domin ceto tata
sai taji ta kara kamuwa da tsananin sonsa fiye da
ko yaushe kuma sai ta kura masa idanu tana mai
zubar da hawaye saboda tasan cewa lallao wannan
shine gani na karshe da takeyi masa.Nan dai
halittar ta cigaba da kyalkyala dariyar farin ciki tana
mai kara tunkarar Yazid.Koda ya rage saura baifi
taku biyar ba a tsakanin Halittar da yarima Yazid
sai halittar ta daka tsalle sama da nufin ta sokawa
Yazid faratan hannayenta biyu a
makoshinsa.kwatsam ba zato ba tsammani sai
Yazid yaga halittar ta sandare a sama tamkar gunki
ta fado kasa tim matacciya ko shurawa batay ba
sakamakon wata takobi data soketa a kunnenta na
dama ta faso cikin kunnenta na hagu.Sa'adda jini
ya kama tsiri daga cikin kunnen hagun.Koda Yazid
yayi arba da wanda ke ruke da takobin sai ya jada
baya cikin kaduwa da mamaki,ba wani bane ba
ruke da takobin data tsire wannan halittar face
Sarauniya Lazwara.Yazid ya dunkule hannyensa
biyu yana mai nuna alamun yin fada a Lazwara
wacce ita kuma fuskarta a cike take da annuri
gami da murmushi a wanann lokaci ne Nauwara ta
zaro jikinta daga cikin jelar matacciyar halittar
tasha gaban Yazid wato ta shiga tsakaninsa da
sarauniya Lazwara ta dubeshi....
TACE WANNAN MAI MULKI KUMA
ABOKIYA CE A GAREMU,ITA CE SARAUNIYA
LAZWARA MAI MULKIN BIRNIN ARNAN DAJI BIRNIN
DAKE MAKWABTAKA DA BIRNINMU.Koda jin
wannan batu sai Yarima Yazid ya dan saki jikinsa
yayiwa Lazwara dan guntun murmushi kawai sai ya
dubi Nauwara yace maza ki zo mu koma can
sansanin abokan tafiyarmu domin zasu kasance a
cikin zulumi da fargabar rashin ganinmu.Koda jin
wannan batu sai sarauniya Lazwara ta dubi Yazid a
fusace tace haba malam kai wane irin mutum ne
yaya na ceci rayuwarka data abokiyar tafiyarka
daga hannun wannan azzalumar halitta amma ko
gode mini nakayi ba zaka dauke gimbiya ku tafi ku
barni.Koda jin wannan batu sai Yazid ya juyo ya
dubi Lazwara cikin nutsuwa yace ai ba kece kika
ceci rayuwata ba ubangijina ne ya cece ni domin
lokacin danaga bani da wata dabara da zan iya
kubutar da rayuwar Nauwara saina kama kiransa a
cikin zuciyata ina mai neman taimakonsa shi kuma
saiya amsa rokona ya turo baiwarsa wato ke kika
ceci rayuwarmu gaba daya.Koda jin haka sai
sarauniya Lazwara tace ta yaya ubangijinka zai turo
ni na cece rayuwarka alhalin ni bashi nake bautawa
ba?Yazid yayi murmushi yace ai dake da abinda
kike bauwata da duk wata halitta dake cikin
sammai da kassai ubangiji nane ya halicce
su.Shine sarki Guda daya wanda bashi da abokin
taraiya bai haifa ba kuma ba a haife shi ba,yana
nan a ko ina kuma yana ji yana ganin komai da
kowa fiye da yadda kusancin ruhi da gangar jiki
yake,idan baki amince da duk abinda na gaya miki
ba ki cigaba da binmu a cikin wannan tafiya da
sannu zaki ga karfin ubangijina da idanunki kiyi
imani dashi.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Yazid yaja gimbiya Nauwara suka nufi hanyar da
zata mayar dasu can sansaninsu da gudu,ita kuwa
sarauniya Lazwara sai ta tsaya tana tunani da
wasu wasi akan abinda ya kamata tayi.Koda taga
Yazid sunyi nisa sai itama ta falfala da gudu ta
riske su suka cigaba da gudun tare.Tun kafin su
karaso sansanin daga can nesa hankalinsu ya
dugunzuma su ukun sakamakon hango wani irin
hayakin wuta a sama yayi tsiri ba kyan gani.Koda
hango wannan hayaki sai zukatun su Nauwara
suka buga da karfi suka kara kaimin gudunsu tun
akan hanya suka fara yin tuntube da gawarwakin
jama'arsu.Aikuwa sai Nauwara da Yazid suka fara
zubar da hawaye bisa ganin yadda aka yiwa
jama'ar tasu KISAN GILLAH duk da sun san cewa
shahada sukayi.Cikin dimauta Yazid da Nauwara
suka kara karfin gudunsu Yazid na kwalawa
Haiman da matarsa kira ita kuma Nauwara tana
kwalawa dan uwanta Zainur kira amma sai sukaji
shiru basu amsa ba.Al'amarin daya kara
dugunzuma hankalinsu kenan,nanfa suka cigaba
da ganin gawarwakin dakarunsu har suka iso
sansanin nasu inda suka iske shi a kone duk
tantunansu da komai nasu kuma ko ina gawarwaki
ne da jini male male a kasa.Bama su Nauwara ba
hatta sarauniya Lazwara bata san sa'adda idanunta
suka ciko da kwalla ba ta fara zubar da hawayen
tausayi sakamakon ganin irin kisan gillar da akayi
yiwa jama'ar su Nauwara.Kusa kowace gawa saida
akayi gunduwa gunduwa da ita.Saida suka dubo
ko ina a sansanin amma basu ga gawar sarkin
yaki ba data matarsa da kuma ta yarima
Zainur.Al'amarin da yayi matukar kara dugunzuma
hankalinsu kenan suka cigaba da kuka ba sassauci
saida suka jima suna kakan sannan suka dawo
cikin hayyacinsu.kawai sai Yazid ya mike tsaye a
fusace ya dubi Nauwara a lokacin daya dauki
takobi da garkuwarsa yace zo mu tafi can
sansanin abokan gaba domin daukar fansa,na
tabbata sun kashe Haiman,Zainur da matar
Haiman.Caraf sai sarauniya Lazwara tace Haiman
da matarsa da kuma Yarima Zainur basu mutu
ba,su kadai ne suka tsira da rayuwarsu a wannan
harin sumame da abokan gaba suka kawo
musu,amma sun kama su sun tafi dasu izuwa can
sansanin nasu wajen sarki Marwatu da Waziri
Ridwan domin a raye suke bukatarsu.Koda jin
haka sai Yazid da Nauwara suka sake fusata
Nauwara ta dubi Yazid tace zo muyi sauri muje can
sansanin abokan gaba ayita ta kare komu ko
su.Dajin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta
bushe da dariya sannan ta murtuke fuskarta tace
ta yaya kike zaton cewa ku biyu rak zaku iya yakar
sama da mutum dubu dari uku da doriya?Ina mai
tabbatar miki da cewa idan kuka kai kanku
sansaninsu waziri Ridwan tamkar sun sayar da
rayukanku ne wai shin ma kun fito ne domin ku
dauki fansa ko kuwa domin kuje kogon Hajarul
Aswad ku dauko wasikar jini ku koneta domin ku
ceto rayuwar al'ummar wannan nahiya?Ku sani
cewa su Waziri Ridwan ba zasu kashe Haiman da
Zainur ba saboda suna son suyi garkuwa ne dasu
domin ku fanshe su da wannan taswira ta zuwa
kogon Hajarul Aswad.Idan kuka kuskura kuka basu
wannan taswirar to ba zasu baku su yarima Zainur
ba zasu kashe su ne kuma su kashe ku,sannan
suje su dauko wasikar jni su cigaba da yin mulkin
zalunci a wannan nahiya.Lokacin da sarauniya
Lazwara tazo nan a zancensa sai jikin Yazid dana
Nauwara yayi sanyi sukayi shiru suna tunani.Daga
can sai Yazid ya dago kai ya dubeta yace to wai ke
menene dalilin da yasa kika biyo mu nan har kika
taimake mu?Shin kema so kike ki yaudare mu ki
sace wannan taswirar daga hannunmu domin ki
mallaki wasikar jini ko kuwa kina da wata manufa
ne daban wacce bamu sani ba?Koda jin wannan
tambaya sai sarauniya Lazwara taja dogon
numfashi sannan ya zauna a kasa dirshan ta dubi
Yazid cikin nutsuwa tace sama da shekaru hamsin
baya tun kafin a haifeni jama'ata basu taba shiga
harkokin wata kasa ba a wannan nahiya.Muna
zaman lafiya da kowane sarki amma bincike ya
tabbatar mana da cewa muddin waziri Ridwan ko
sarki
Al amin Ahmed guyson ke magana
Marwatu dayansu ya mallaki wasikar jini saiya
yake mu ya kawar damu daga doron kasa yadda
har abada za'a sake tunawa damu ba.Kun ashe ya
zama dole na fito na kare birnina da
jama'ata.Tabbas ni daku akan aiki guda muke,kafin
Lazwara ta gama rufe bakinta tuni Yazid ya tari
numfashinta yana mai cewa na yarda muna kan
aiki guda amma ba tafarki iri guda ba,mu muna
kan tafarkinaddinin musulunci ne ke kuwa kina kan
tafarkin tsafi.Yanzu wace shawara zaki iya bamu
dangane da wannan al'amari kuma menene
matsayinki bayan mun sami nasarar dauko wasikar
jini mun koneta,shin zaki karbi addinmu ne ko
kuwa zaki koma kasarko ne ku cigaba da
addininku na tsafi ke da jama'arki?Sa'adda
Lazwara taji wadannan tambayoyi guda boyu sai
tayi gyaran murya tace sai yanzu kayi mini
tambaya mai daraja.Da farko dai inaso ku sani
cewa babu wani mugun nufi a cikin zuciyata ko
son kai a kan wasikar jini,fata na kawai shine
akawar da zalunci a wannan nahiya a sami zaman
lafiya da kwanciyar hankali.Abu na biyu kuma
shine zan zuba ido naga iya karfin abin bautarku
daga nan zuwa isarmu kogon Hajarul Aswad idan
har naga kun iya dauko wasikar jini da taimakonsa
lallai nima zan karfi addinin naku.Ina mai tabbatar
muku da cewa nan da ko yaushe zamu iya gani
manzo daga sansanin abokan gaba zaizo ne da
sakon cewa idan kuna son rayuwar Haiman da
matarsa da Zainur to kuje kukai wasikar jini.Koda
jin wannan batu sai hankalin Yazid dana Nauwara
ya kara dugunzuma ainu,Nauwara ta dubi Lazwara
tace wace amsa ya kamata mu basu ko kuwa
zamu bi manzon nasu ne mukai Taswirar wasikar
jinin.Sarauniya Lazwara ta girgiza kai tace a'a ba
zamubi manzon ba sako zamu bashi kamar yadda
suka aiko.Abinda zaku gayawa manzon shine ya
koma ya gayawa iyayen gidansa cewa ba zaku
bayar da taswirar ba sai acan tsakiyar dajin da
kogon Hajarul Aswad yake.Wannan wata babbar
hikima ce nayi muku sai a nan gaba zaku fahimci
hakan kuma ku gargade su a kan cewa idan suka
kuskura suka taba lafiyarsu Haiman to a bakacin
Taswirar.Har Yarima Yazid ya bude baki zai
tambayi Sarauniya Lazwara ko wace irin hikima
take nufi da cewar sai a tsakiya dajin Hajarul
Aswad zasu bayar da wannan taswirar sai kawai
suka jiyo sukuwar doki an durfafo wannan konan
nan sansanin nasu,suna dago da kawunansu su
ukun sukga ashe kuwa maganar Lazwara ce ta
tabbata wato manzo ne daga sansanin abokan
gaba.Jim kadan sai ga manzon ya iso daf dasu
yana mai jan linzamin dokinsa,take dokin yayi
turjiya ya risina a gaban gimbiya Nauwara ya
kwashi gaisuwa.Tana hada idanu da manzon taga
ashe babban hadimin waziri Ridwan ne wanda ake
kira da suna Ubaiyu bin Marwas.Ubaiyu ya dago
kai ya dubi Nauwara yace ya shugabata mai girma
Waziri Ridwan yace na shaida muku cewa sarkin
yaki Haiman da matarsa da kuma Yarima Zainur
na hannunsu a can sansanin sarki Marwatu idan
har kuna son ku fanshi rayuwarsu to kuje ku kai
musu taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad in ba
haka ba kuwa zasu kure muku gudu su kashe ku
kamar yadda suka kashe sauran jama'arku.Koda
Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Nauwara
ta kyalkyale da dariya.Al'amarin daya baiwa Ubaiyu
mamaki kenan yace haba gimbiya yaya keda kike
cikin wannan hali zakiyi dariya,shin bakya kishin
dan uwanki ne bakya son ya tsira da rayuwarsa?
Nauwara tayi murmushi tace ai idan ma kuka
kashe dan uwana da sarkin yaki farin ciki zanyi
saboda sun sami shahada kuma zasu sami babban
rabo da sakamako na gidan Aljanna.Ka koma ka
sanar da iyayen gidanka cewa ba zamu basu
wannan taswirar ba sai a tsakiyar dajin Hajarul
Aswad.Koda jin wannan batu sai idanun Ubaiyu
suka zazzaro yace haba ranki ya dade kiyi tunani
dai,caraf sai sarauniya Lazwara ta tari nunfashin
Ubaiyu tana mai daka masa tsawa gami da zare
takobinta tace maza kabar wajen nan ko nasa
takobina na sare kanka.Kawai kaje ka isar da
sakon da aka baka.Koda jin haka sai jikin Ubaiyu
ya kama kyarma cikin hanzari ya kama dokinsa ya
haye ya juya da baya ya zabureshi da gudu su
kuwa sai suka bishi da kallo har saida ya bace
musu da gani.Faruwar hakan keda wuya sai
sarauniya Lazwara ta dubi Yazid da Nauwara tace
ku tashi mu ruga da gudu izuwa cikin dajin nan
muyi sauri mu isa can tsakiyar dajin Hajarul Aswad
kafin abokan gabar nan su zo su riske mu domin
Ubaiyu na sanar dasu sakon ki zasu biyo
bayanmu.Ba tare da wata gardama ba kuwa sai
Nauwara da Yazid suka mike tsaye suka falfala da
gudu,itama sarauniya Lazwara saita bisu a
gujen,nan da nan tazo ta tsere musu ta basu
tazara mai yawan gaske domin wani irin gudu
takeyi na ban al'ajabi har tashi takeyi sama kamar
tsuntsuwa kai da gani kasan cewa aikin sihirin tsafi
ne.Koda ganin haka sai shima Yarima Yazid ya
kama yin wata addu'a ta musamman ai kuwa nan
da nan karfin gudunsa ya karu shida na
nauwara.Nan da nan suka zo suka wuce sarauniya
Lazwara kafin ta ankara sun bata rata mai yawan
gaske.Nanfa Lazwara ta kara zage damtse iyakar
iyawarta duk dalasimanta na tsafi babu wanda bata
ambata ba domin ta wuce su amma sai ta
kasa.Al'amarin dayayi matukar girgiza ta kenan
yasa ta firgita da al'amarin ma'abota addinin
musulunci kenan.Saida suka sgafe sa'a uku da rabi
suna wannan gudu suna ta gifta bishiyoyi har ta
cikin koramai suke bi suna taka ruwa tamkar akan
kasa suke tafiya.Wannan shine abinda ya faru ga
su Yarima Yazid bayan su sarki Marwatu sun
kaiwa sansaninsu harin bazato sun kashe gaba
dayan dakarun nasu.
*A can kuma sansanin su sarki Marwatu kuwa tun
daga lokacin da suka ci yaki a sansanin su sa
yarima Zainur sai suka kamo sarkin yaki Haiman
da matarsa da kuma Yarima Zainur suka jefasu
cikin wani keji a ka dora
Al amin Ahmed guyson ke magana
kejin akan keken shanu aka rinka wulakanta su
akan hanya ana wahalar dasu.Har aka iso sansanin
ko ruwa ba'a basu sun sha ba kuma ana isa aka
fito dasu daga cikin kejin aka daure su a cikin rana
ba'a kwance su ba saida rana ta fadi aka kwashe
su kamar tsumma saboda tsananin jigata ta yunwa
da kishirwa bisa wannan dalili suka fita daga
haiyacinsu.Bayan an mayar dasu cikin keji an kulle
ne aka kawo musu ruwa makurwa uku uku kadai
aka basu gami da abinci loma uku uku kadai aka
basu.An basu wannan abinci da ruwa ne don
kawai kada su mutu,lokacin da suka danci wannan
abinci ne suka dawo cikin hayyacinsu sai matar
Haiman ta dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo
mata tace,yakai mijina yanzu shike nan mu tamu
ta kare kenan an kashe gaba dayan dakarunmu
daga mu mu ukun nan sai Yazid da Nauwara ne
kadai muka rage muma din kuma ga dukkan alamu
mutuwar zamuyi.Koda jin wannan batu sai Haiman
ya kamo matarsa ya rungumeta a kirjinsa yace
yake matata ina so ki sani cewa wuya bata kisa
kuma ko mutuwa mukayi akan wannan tafarki
bamu da wata asara dimin shahada ce mukayi.Ni
ina ji a jikina wadannan makiyan Allah ba zasu
taba samun nasarar mallakar wannan wasikar jini
ba.Caraf sai Yarima Zainur ya tari numfashin
Haiman yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne
yakai Abbana kuma zamu cigaba da addu'ar Allah
ya kare mu daga sharrin su waziri Ridwan kuma
ya bamu sa'a akansu mu kawar dasu da zalunci
mu kafa addinin Allah a wannan nahiya.Su Haiman
na cikin wannan zance ne waziri Ridwan da sarki
Marwatu suka taho garesu suna kyalkyala musu
dariyar mugunta,da isowarsu daf da bakin kejin sai
waziri Ridwan ya zura hannunsa cikin kejin ya cafi
makoshin Zainur yace kai yaro kayi asara,a baya
sarkin yaki da sarki Aiyuba sun gagareni kuma sun
jima yana kunsa mini bakin ciki,sun kare dukkan
hanyoyin cigaba rayuwata kuma lokaci yayi da zan
dauki fansa akanka.Tunda shi tasa ta kare gashi
can kwance akan gangar mutuwa,a yau dinnan
abokinka Yazid da gimbiya Nauwara zasu kawo
mana Taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad,mun
yaudare su da cewa zamu basu ku a maimakon
taswirar suna shigowa cikin wannan sansi zamuyi
musu kofar rago mu hallaka su mu dauke taswirar
sannan kuma muyi muku kisan gilla.Tabbas na
tabbata da cewa ba zasu iya tafiya su barku ba
dole ne suzo suyi kokarin ceton rayuwarku.Koda
gama fadin haka sai Ridwan ya saki makoshin
Zainur ya dubi sarki Marwatu suka bushe da
dariyar mugunta tare suna cikin kyalkyala dariyar
ne sarkin yaki Haiman ya tari numfashinsu yana
mai daka musu tsawa yace,ku tsofaffun azzalumai
kuyi sani cewa rana da yawa ta barawo ce rana
daya jal ta mai kaya.Tabbas kun dade kuna sheka
ayarku a doron kasa kuna zalunci kuna tara dukiya
ta gurbatacciyar hanya,babu mai iya taka muku
birki sai Mahaifin Gimbiya Nauwara.Yau sarki ya
fadi amma kuyi tunani da hankalinku da
kwakwalwarku an sami jarumi ma'abocin addinin
musulunci wanda shine zai kawo karshenku.Ina
mai tabbatar muku da cewa sakon da manzonku
zai dawo dashi saiya girgiza ku,kowannenku sai
hantar cikinsa ta kada.Kafin sarkin yaki Haiman ya
gama rufe bakinsa kuwa sai sukaji sukuwar doki
an nufo sansanin,cikin hanzari waziri Ridwan da
sarki Marwatu suka waiga baya sai sukaga ashe
manzo Ubaiyu ne ya dawo.A guje Ubaiyu ya ratso
cikin sansanin da doki,da isowarsa sai yaja tunga
a gaban su sarki Marwatu ya sauko da sauri daga
kan dokin ya zube kasa gabansu sannan ya dago
kai ya zaiyane sakon dasu yarima Yazid suka
bashi cewar ba zasu zo wannan sansani ba kuma
ba zasu bayar da taswirar ba face a tsakiyar dajin
Hajarul Aswad.
KODA
JIN WANNAN BATU SAI RAN SARKI MARWATU
DANA WAZIRI RIDWAN YA BACI,ZUCIYOYINSU
SUKA KAMA TAFARFASA KAMAR ZASU KONE,CIKIN
FISHI SARKI MARWATU YA DUBI RIDWAN YANA
MAI ZARE TAKOBINSA YACE,tunda dai sun hanamu
taswirar zuwa dajin hajarul Aswad banga amfanin
fursunonin da muke tsare dasu ba kawai mu kashe
su.Waziri Ridwan yayi sauri yasha gaban sarki
Marwatu ya dubeshi cikin matukar damuwa yace
a'a idan muka kashe su yarima Zainur yanzu har
abada ba zamu sami wannan raswirar ba bare mu
mallaki wasikar jini zo kaji wata magana.Nan take
Ridwan ya kama hannun sarki Marwatu ya jashi
izuwa can gefe daya suka tattauna sukayi kuskus
na tsawon yan dakiku suna gama tattaunawa ne
suka tara gaba dayan mayakansu suka basu
umarnin a fara shirin cigaba da tafiya kuma a
shirya makaman yaki.Nan take kuwa aka shiga
debo takubba,masu da kibiyoyi aka shiga wasa su
ana rarrabawa mayaka kai kace YAKIN DUNIYA za'a
tafi.Koda Zainur ya ga yadda dubunnan daruruwan
dakaru keta kai kawo a cikin sansanin suna ta
shirye shiryen yaki sai nan take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo
masa.Al'amarin daya baiwa Haiman da matarsa
mamaki kenan Haiman ya dubi Zainur cikin alamun
kaduwa yace yakai dana ina dalilin zubar da
wannan hawaye naka?Zainur yasa hannu ya share
hawayensa sannan ya dubi Haiman cikin nutsuwa
yace yakai abbana kaga wadannan dubunnan
daruruwan dakarun da yawansu magidanta ne,suna
da mata,'ya'ya da yan uwa kuma dukkaninsu
jama'ar birnin mu ne amma dayansu ba zai tsira
da rayuwarsa ba duk mutuwa zasuyi a cikin dajin
hajarul Aswad.Kaga kenan matayensu zasu zama
gwagware,yayansu kuma zasu zama marayu,basu
da ikon gudun shigowa nan dajin saboda tsoron
waziri ridwan,haka suma dakarun yakin da sarki
Marwatu ya taho da su daga kasarsa zasu mutu a
cikin jahilci batare da sun amfani addinin gaskiya
ba sun dandani dadinsa da kuma rahamar dake
cikinsa.Koda Zainur yazo nan a zancensa sai jikin
Haiman dana matarsa yayi sanyi suka kurawa
dakarun yakin idanu suna masu jin
tausayinsu.Kafin cikar sa'a daya an gama shiri tsaf
an kwashe komai a sansanin an zaburi dawakai da
gudu an durfafi hanyar da zata kaisu izuwa dajin
hajarul aswad.Idan mutum yaga wannan falfala
azababben gudu kuma yaga yawansu dole ya
firgita yayi zaton cewa karshen duniya ne yazo.
*A can cikin dajin hajarul aswad kuwa lokacin da
sarauniya Lazwara,Yarima Yazid da gimbiya
Nauwara suka falfala da azababben gudu izuwa
cikin dajin Hajarul Aswad suka shafe sa'o'i suna
gudun batare da sun gaji ba sai suka iso wani
katon fili wanda ke cike da wata irin ciyawa mai
taushi tamkar kilishi aka shimfida gaba daya a
wannan gaili.A zagaye yake da wadansu irin
dogayen bishiyoyi tamkar babu hanyar da mutum
zai iya bi ya wuce.Da isowarsu wannan wuri sai
sarauniya Lazwara ta kwalawa Yazid kira suka
tsaye da Nauwara.Lazwara ta karaso garesu tana
haki data kalli Yazid da Nauwara taga ko haki
basayi kuma babu alamar gajiya a tare dasu duk
da wannan tsananin gudu da suka sha sai ta kamu
da tsananin mamaki amma saita basar ta dubi
Yazid tace,nanne tsakiyar dajin Hajarul Aswad,anan
ya kamata mu tsaya mu tunkari su sarki Marwatu
ayita ta kare,idan mun sami nasarar kashe su mu
karasa kogon hajarul aswad mu dauko wasikar jini
idan kuma sune suka sami nasarar kashe mu sune
zasu je su dauko wasikar jini su mallaketa su
cigaba da yin mulkinsu na zalunci,ina mai tabbatar
muku da cewa gaba dayan masifun dake cikin
wannan dajin anan wurin suke kuma kowacce
masifa daya ta ninka ta waccan halittar dana kashe
a cikin kogin kankara sau uku babu abinda zai
kwace mu anan face tsananin sa'a da kuma iya
yakinmu da juriyarmu amma badai karfin sihiri
ba.Caraf sai yarima Yazid ya tari numfashin
sarauniya Lazwara yace ni dana san cewar
ubangijina zai bamu kariya ke kuma sai mu gani
idan tsafinki zai kareki idan kuma baki da tabbacin
hakan to ki karbi addininmu yanzu take nayi miki
alkawarin babu abinda zai sameki,koda jin wannan
batu sai Sarauniya Lazwara ta kyakyale da dariya
tace ai inda tun farko ban yarda da kaina ba bazan
yarda na biyo bayanku ba har na iso nan.Lallai
inda babu kasa anan ake gardamar kokawa,nidai
burina shine na rayu har izuwa lokacin da za'a zo
dasu yarima Zainur nan kuma naga wadanda zasu
sami nasarar dauko wasikar jini tsakanin su sarki
marwatu da mu.Koda jin wannan batu sai mamaki
ya turnuke Nauwara da Yazid saboda basu san
dalilin da yasa sarauniya Lazwara take son taga
isowar Yarima Zainur wannan wuri ba.Har Nauwara
ta bude baki zata tambayeta dalilin sai kawai sukaji
kasa ta kama girgiza,kafin dayansu yayi wani
yunkuri saiga wadansu irin samudawan dodanni
suna faso kasar suna fitowa su dayawa ba adadi
suka yiwa su yarima Yazid kawanya sai gashi su
Yazid sun zama yan mini mini tamkar tamkar an
ajiye yan tsaki uku a tsakiyar dubunnan kaji.Sudai
wadannan dodanni suna da matukar tsawo gami
da kaurin jiki kuma fuskokinsu nada matukar muni
da ban tsoro idanuwansu jajaye ne tamkar dan
buda aka gasa a cikin wuta.Jikinsu gaba daya a
murde yake cike da kwanji da jijiyoyi tamkar
duwatsu aka cure gaba dayan wadannan dodanni
suna ruke da wani irin gabjejen sungumin itace
mai dauke da wani irin tsini cako cako mai yawa a
samansa.Duk da tsananin jarumtaka irinta yarima
Yazid saida ya firgita bisa ganin wadannan dodanni
da kuma yawansu amma daya tuna cewa yana
tafarkin daukaka kalmar Allah ne sai dukkan tsoro
ya kau daga cikin zuciyarsa.Kawai saiya zare
takobinsa ya gyara tsayuwarsa yana jira yaga
dodon dazai fara kawo masa
Al amin Ahmed guyson ke magana
Hari.Itama Sarauniya Lazwara saita zare takobinta
ta gyara tsayuwarsa.Gimbiya Nauwara kuwa kasa
zare tata takobin tayi saboda tsoro ta koma bayan
yarima Yazid ta tsaya jikinta na karkarwa.Koda
Yazid yaga yadda Nauwara ta tsorata ainun da
ganin wadannan dodanni sai yayi mata rada a
kunne yace ki tsuguna kasa kuma kada ki kuskura
ki motsa daga nan wajen daidai da taku
goma.Gama fadin hakan keda wuya sai dodannin
suka afkawa Yazid da sarauniya Lazwara aka
ruguntsume da azababben yaki,ai kuwa ana fara
wannan yaki ne Yazid da Lazwara suka raina kansu
kuma suka san cewa sun gamu da gamonsu.Sudai
wadannan dodannin basa jin sara da suka a jikinsu
domin duk sa'adda takubbansu Yazid da Lazwara
ya hadu da jikinsu saidai kaji wata irin kara na
tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma
tarwatsin wuta ne ke tashi.Haka kuma basa jin
naushi da bugu domin da zarar su Yazid sun
naushe su hannunsu ne sagewa suji kamar dutse
suka nausa.Bugu da kari dodannin suna da
matukar zafin nama domin kafin su Yazid su kai
musu hari guda su sun kai musu uku nan da nan
suka kuntata Yazid da Lazwara suka fara galabaitar
dasu,wani abin mamaki shine babu wani dodo
daya kaiwa Nauwara hari a inda take tsugune
amma jikinta sai karkarwa yake tana kallon
gumurzun da akeyi cikin tsananin tsoro da tashin
hankali.Ashe Yazid ya karanta wata addu'a ta
musamman ya tofa adaidai wurin da Nauwara ta
tsuguna.Ana cikin wannan mugun artabu ne wani
dodo ya shammaci sarauniya Lazwara ya gabza
mta wani wawan naushi a fuska,saboda karfin
naushin saida tayi katantanwa a tsaye sau uku a
lokacin da gudan jini ya furzo daga bakinta ta
langwabe zata fadi kasa sumammiya.Koda ganin
haka sai yarima Yazid ya dimauce bai san sa'adda
ya kwala kabbara da karfi ba ya cafo Lazwara da
hannu daya ya goyata a bayansa kuma ya afkawa
dodannin da mugun sara da suka cikin bakin zafin
nama na gaban kwatance a lokacin da yaji wani
irin gagarumi karfi ya shige shi,ai kuwa sai gashi
takobinsa na daddatsa dodanni duk tsananin
yawan dodanni sai ya zamana banza domin an
rasa wanda zai iya koda lakutar jikin Yazid kuma
sai kutswa ta cikinsu yake yana bazar dasu,sassan
jikinsu ya rinka shawagi a sama yana zubowa kasa
jini jikinsu ya rinka tsartuwa da fantsama.Wohoho
idan kaji ana ki gudu to sa gudu ne bai zo
ba.Koda sukaga irin mummunar barnar da yazid
keyi musu kuma suka tabbatar da cewa ba zasu
iya kashi ba sai suka ruga izuwa cikin ramukan da
suka fito.Ramukan suka rufe kansu tamkar basu
taba wanzuwa ba a wajen sai gawarwakin yan
uwansu kawai a kwance rututu a filin daji.Adaidai
wannan lokaci ne Yazid ya sauke Lazwara daga
bayansa a kasa.Koda ya ga har yanzu a sume take
bata farfado ba sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun ya dimauce bai san sa'adda ya fisge battar
ruwa ba a jikin Nauwara ya budeta ya zazzage
ruwan akan fuskar Lazwara,faruwar hakan keda
wuya sai Lazwara ta farfado tana mai jan dogon
numfashi.Koda ta bude idanunta taga dubunnan
gawarwakin dodannin zube a kasa kuma ta dubi
yarima Yazid taga takobinsa da duk jikinsa ya rine
da jini sai kawai ta bude baki tace nayi imani da
ubangijin musulunci wanda ya baka karfin da ka
kashe wadannan dodanni,ina ragowar dodannin
suke?Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
Yazid da Nauwara,yazid ya dubi Lazwara yace
bazan baki amsar tambayarki ba sai bayan na
shigar dake cikin addinina,nan take yazid ya
biyawa Lazwara kalmar shahada ta maimaita
sannan ya dubeta yace ragowar daodannin sun
koma cikin ramukan da suka fito.Koda jin haka sai
Lazwara ta mike tsaye tace zasu sake fitowa don
haka mu zauna a cikin shiri.Gama fadin hakan
keda wuya sai suka jiyo sukuwar dubu daruruwan
dawakai an durfafosu suna daga kai sukaga ashe
su sarki marwatu ne suka taho cikin shigar
yaki,akan gaba kejin dake dauke dasu Haiman ne
bisa wani keken doki.Wannan runduna tun daga
nesa ta fara razana,ba komai ne ya razana su ba
face hango gawarwakin wadannan dodanni da
kuma hango Yazid face face a cikin jini takobinsa
ma ta rine da jini.Koda ya rage saura baifi taku
ashirin ba tsakanin rundunar su sarki marwatu da
su Yazid sai rundunar tayi turjiya suka tsaya cak
aka fara kallon kallo har saida kura ta lafa sannan
waziri ridwan ya dubi yazid,lazwara da nauwara
yace yaku abokan gaba gamu mun iso tsakiyar
dajin hajarul aswad dauke da yan uwanku idan
kuma kuka ki bamu wannan taswirar dayanku
bazai tsira da rayuwarsa ba,ku dubi kanku sannan
ku dubemu kun sancewa ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin baki kaza,kai Yazid kabar ganin
cewa ka kashe wadannan dodanni kai kadai to mu
ba dodanni bane mutane ne wadanda sunfi aljani
ma hatsabibanci da jarumtaka.Koda waziri ridwan
yazo nan a jawabinsa sai Sarauniya Lazwara tayi
caraf ta tari numfashinsa tace kai tsohon azzalumi
kayi sani cewa kunyi babban kuskure da ganganci
da kuka kawo kanku nan dajin domin baku isa ku
iya ketare nan wajen ba a raye bare har ku isa
kogon hajarul aswad ku dauko wasikar jini.Gaba
dayanku sai kun zama gawa.Koda jin wannan batu
sai waziri ridwan ya bushe da dariya yace ke
yarinya kiyi sani cewa kowa ya rigaka kwana dole
ne ya riga ka tashi,duk masifun dake cikin dajin
nan munsan dasu kuma mun dauki mataki a
kansu.Caraf sai sarauniya Lazwara ta sake tarar
numfashin ridwan tace na yarda kun san masifun
amma ai sani daban haduwa daban,idan kuna
ganin cewa zaku iya dasu gasu nan ku jaraba mu
gani.Tana gama fadin hakan saita juya ya dubi
yarima Yazid tayi masa wata inkiya shi kuma saiya
kwala kabbara ya naushi kasa da hannunsa guda
take ramukan dodannin nan suka bude dodannin
sukayi fitar burgu daga cikin karkashin Al amin Ahmed guyson ke magana
kasa,maimakon dodannin su afkawa su Yazid sai
suka juya da gudu suka afkawa su sarki Marwatu
aka ruguntsume da masifaffen yaki.Kaico na,nanfa
KASUWAR CINIKIN DAUKAR RAYUKA ta
bude,dodannin suka rinka ragargazar dakarun su
sarki Marwatu suna yi musu mugun kisan
gilla,abinda ya daurewa kowa kai a wajen shine ko
dodo daya bai nufi inda kejin dasu Haiman yake ba
kuma ta cikin dodannin Yazid ya kutsa yaje ya sare
kubar da aka kulle kejin kofar ta bude ya fito dasu
Haiman daga ciki ya tafi dasu can inda Nauwara
da Lazwara ke tsaye.Koda Nauwara ta hango dan
uwanta Yarima Zainur saita ruga gareshi ta
rungumeshi cikin tsananin farin ciki,ita kuwa
Lazwara sai taje gaban Zainur ta dubeshi cikin
murmushi tace masoyina dama na kudurce a raina
anan ne zan baiya maka SIRRIN ZUCIYA ta lallai
tun a farkon haduwa ta dakai na kamu da tsananin
sonka kuma a halin yanzu nima na karbi addinin
Yazid shin kasa so na?Koda jin wannan tambaya
sai Zainur yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin na
Nauwara ya dubi Lazwara cikin tsananin farin ciki
yace nima tun a farkon haduwarmu na nutse a
cikin KOGIN SON...Cikin sauri Nauwara ta rufe
bakin Zainur da tafin Hannuta tace kabar sauran
bayani saimunga yadda karshen wannan yaki zai
kasance,nanfa duk su biyar din suka mayar da
hankalinsu izywa inda ake fafata wannan masifaffen
yaki.Rabin sa'a aka shafe ana wannan yaki ya
zamana cewa wadannan daodanni sun kashe gaba
dayan dakarun sarki Marwatu,Sarki Marwatu da
Waziri Ridwan ne kadai suka rage a raye kuma
kowannensu ya sami mugayen raunika kimanin
guda bakwai a jikinsa.Suma in badon tsananin
karfin damtsensu ba da karfin Sihirinsu da tuni sun
dade da mutuwa.Dodannin na shirin karasa kashe
su sarki Marwatu da waziri Ridwan kenan sai Yazid
ya daka musu tsawa take suka kame kam tamkar
gumaka.Nan take Yazid ya fara kiran sunayen Allah
tsakaka yana yi masa kirari,faruwar hakan keda
wuya sai jikin dodannin gaba dayansu ya kama
tsattsagewa suka rina rugujewa suna zubewa kasa
suna zama gari.Nan da nan dodannin suka hallaka
gaba dayansu guda daya bai tsira da rayuwarsa
ba.Sarki Marwatu da waziri Ridwan na ganin haka
sai suka cika da tsananin al'ajabi gami da takaici,a
wannan lokaci ko motsi ba zasu iyayi ba
sakamakon jinin dake zuba a jikinsu kuma indai
ba'a gaggauta dinke raunikan nasu an tsayar da
jinin dake zuba ba na da wani lokaci zasu iya
mutuwa.Koda Marwatu da Ridwan suka fahimci
cewar lallai zasu hallaka idan ba'a taimake su ba
suka kama rokan su Yarima Yazid dasu
cecesu.Yarima Yazid ya matso daf dasu ya tsaya
ya dubesu yace ina karfin mulkin naku kuma ina
karfin damtsenku dana sihirin tsafinku,ku ceci
rayuwarku mana da abubuwan da kuka dogara
dasu,kun gani da idanunku ayau babu wani karfi
wanda yafi na ubangijin musulunci.Kodon saboda
dubunnan rayukan da kuka sa suka salwantar ba
zamu ceci rayuwarku ba mutuwa ce kadai zata
fanshe zunubanku a wannan doron kasa,ina mai
tabbatar muku da cewa daga yau tsafi ya daina
tasiri a wannan nahiya gaba daya kuma zalunci ya
kau sai adalci a tsakanin masu mulki da
talakawa.Yanzun nan zamu karasa kogon hajarul
aswad mu kone duk abinda ke cikinsa sannan mu
koma izuwa kasashenku mu kafa tutar addinin
musulunci.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Yazid ya juya ya koma inda su Zainur ke tsaye
suka rankaya gaba dayansu suka kara nausawa
cikin dajin na hajarul aswad suka bar sarki
marwatu da waziri ridwan suna murkususu suna
kukan nadama gami da kakarin mutuwa.Kafin cikar
dakika dari duk su biyun sun sandare sun zama
gawarwaki.Kamar Yadda Yarima Yazid ya fada
hakan al'amarin ya kasance wati sun isa har cikin
kogon hajarul aswad suka dauko wasikar jini suka
koneta faruwar hakan keda wuya kogon dutsen
gaba daya ya kama rugurgujewa.A guje suka fito
daga cikin kogon ba tare da dayansu ya hallaka
ba.Lokacin da su Yarima Zainur suka dawo gida
sun riske mahaifin Gimbiya Nauwara ya mutu don
haka sunyi kuka da bakin cikin rashin karbar
addinin gaskiya da baiyi ba.Nan take aka kafa tutar
addinin musulunci a gidan sarautar sannan suka
dunguma izuwa birnin sarauniya Lazwara nan yake
aka kaddamar da musulunci bayan nanne aka
daura aure Yarima Zainur da Lazwara,Yarima Yazid
da Nauwara sannan aka sake dawowa birnin su
Nauwara aka baiwa Yarima Zainur sarautar garin
wato ya gaji sarki Aiyuba.Shi kuma Yazid ya dauki
matarsa Nauwara suka tafi can kasar su,koami ya
dawo daidai yadda ya kamata,aka cigaba da zaman
lafiya a cikin nahiyar da addinin irin na musulunci
aka kautar da tsafi da bautar gumaka.
.
ALHAMDULILLAH
Anan muka zo karshen wannan littafi wato wasikar jini
Dafatan ya kayatar daku
Suleiman zidane whatsapp 09064179602