spon

Monday, July 23, 2018

Home WASIKAR JINI BOOK 8 COMPLETe book

Subscribe Our Channel


NAN TAKE KUWA HAIMAN YA SHIGE GABA YAYI
MUSU LIMANCI,BAYAN AN IDAR DA SALLAR ANYI
ADDU'A SAI KOWA YA KIMTSA SUKA DEBI
MAKAMANSU DA DUKKAN KAYANSU SUKAYI
GABA.Tafiyar su yarima Zainur keda wuya bayan
cikar rabin sa'a daidai saiga rundunar su sarki
Marwatu sun baiyna,dukkaninsu a cikin shigar
bakaken tufafi kuma a kasa suke babu mai doki
guda daya,babu sarki Marwatu da Waziri Ridwan a
cikin wadannan zuga sakamakon dole ne su
kwanta suyi jinyar raunikan jikinsu.Daga nesa suka
fara sanda harma a cikin rub da ciki suke tafiya
suna jan jikinsu sai kace macizai.Sa'adda suka
hango sansanin sukaga fitilo a kunne kuma ga
dakarun tsaro a tsaitsaye sun yiwa sansanin
kawanya,abinda basu sani ba shine babu kowa a
cikin sansanin kuma dakarun da suke hangowa a
tsaitsaye duk ba masu rai bane mutum mutumi ne
dukkaninsu.Koda ya rage saura baifi taku ashirin
ba tsakakanin dakarun sumamen da sansanin sai
kawai suka fara harbo ruwan kibiyoyin wuta,nan da
nan tantunan da aka kafa suka kama cin
wuta,suma mutum mutumin dake tsaye suka rinka
faduwa kasa suna ci da wuta,cikin kankanin lokaci
komai dake cikin sansanin ya kone kurmus.Duk
wannan abu dake faruwa dakarun sumamen na
kwance a kasa cikin lambo jira suke kawai suji
dakarunsu Zainur sun rugo daga cikin wutar
sannan suma su taso su afka musu,amma sai
sukaji shiru abin daya kara basu mamaki ma shine
tunda suka harbo kibiyoyin wuta a cikin sansanin
kawo izuwa sa'adda komai ya kone basu jiyo ihun
koda mutum daya ba.Koda fuskantar hakan sai
shugaban dakarun ya mike tsaye zumbur ya kura
idanunsa da kyau izuwa cikin sansanin take ya
gane cewa lallai makircin yaki aka nuna musu
saboda ko mutum daya mai rai babu a cikin
sansanin mutum mutumi ne kawai wadanda basu
haura guda ashirin da wani abu ba kwance a kas
suna ci da wuta.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun sumamen ya kwarara uban ihu cikin
tsananin bakin ciki.Al'amarin da yasa gaba dayan
yaran nasa suka mike tsaye kenan suka dubi cikin
sansanin.Koda suka fahimci abinda ke faruwa sai
suma ransu ya baic nan take shugaban dakarun ya
fiddo wani dan karamin madubin tsafi daga cikin
aljihu ya shafe shi sai ga fuskar waziri Ridwan ta
baiyana,kafin shugaban dakarun sumamen ya bude
baki yace wani abu tuni Ridwan ya tari
numfashinsa yana mai cewa kai shashashan
banza,abokan gaba sun yaudare ku ne kamar
yadda suka yaudare mu da farko,kai wane irin
dakiki ne ashe ban gargadeka ba akan kada ku kai
hari sai kun tabbatar da cewa abokan gabar na nan
a cikin sansaninsu.To ka sani cewa tuni sun matsa
gaba sun kafa wani sansanin kuma a yanzu haka
wasu daga cikinsu sun bar sansanin sun tafi
neman wannan bakon da gimbiya Nauwara
wadanda su tuni sunyi nisa a cikin daji babu
mamaki ma sun fada cikin daji da kogon Hajarul
Aswad yake.Maza ku karaso sabon sansanin nasu
ku kashe duk wani abu mai rai dake cikinsa karku
bar ko kaza guda daya da rai.Ni da sarki Marwatu
da sauran dakaru zamu riske ku a sansanin nan da
zuwa gobe da safe.Koda gama fadin haka sai
hoton fuskar waziri Ridwan ya bace daga kan
madubin.cikin gaggawa shugaban dakarun
sumamen da yaransa kimanin su dubu arba'in
suka nausa da gudu izuwa cikin daji.Wani irin
gudu sukeyi na ban al'ajabi saboda karfin sihirin
tsafinsu domin har tashi sama suke suna dira a
kan kololuwar dogayen bishiyoyi suna karawa
gaba.
*A can cikin kogon kankara kuwa lokacin da
yarima Yazid da Gimbiya Nauwara sukayi arba da
wannan katuwar mummunar halitta mai siffar
macijiya dauke da kan mage,ga hannaye guda
goma sha biyu gami da jelar guda arba'in da
gutsiren daya wacce Yazid ya sare rabinta sai suka
firgita ainun.Ba shiri Yazid ya tunkude Nauwara
bayansa ya daka mata tsawa yana mai bata
umarnin ta cigaba da iyo ta fice daga cikin kogin
kankarar ta isa can daya gabar tasa.Koda halittar ta
fahimci hakan sai ta tasam musu su biyun tana
jeho musu hannayenta da jelunanta tana kawo
musu mugun duka gami da sara da suka da kaifin
faratan hannayenta.A karom farkon data kawowa
Nauwara sara da farcen hannunta guda Nauwara ta
yunkura cikin zafin nama ta zare takobinta ta kare
saran ai kuwa sai kafin farcen nata ya raba takobin
Nauwara gida biyu,kafin Nauwara tayi wani yunkuri
tuni halittar ta gabza mata wawan naushi da jelarta
guda a fuska.Saboda Karfin Naushin saida Nauwara
tayi sama kuma tayi katantanwa sau uku a saman
sa'adda jini yayi feshi daga bakinta ta fado kasa
cikin kogin kankara a sume kuma ta fara lumewa
izuwa karkashin kogin.Koda Yazid yaga abinda ya
faru ga Nauwara sai ya fusata ainun bai san
sa'adda ya kwala kabbara ba ya daka tsalle sama
daga cikin kogin tamkar daga cikin naka aka cillo
shi ya dankarawa halittar wawan sara a tsakiyar
kanta.Nan take takobin tasa ta rabe gida biyu
amma saboda karfin saran nasa saida halittar tayi
wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da zugin
da taji ta fadi da baya cikin kogin tsundum tamkar
daga sama aka jefo giwa.kafin halittar ta taso
saman ruwan tuni Yazid yayi nutso kasa ya dauko
Nauwara yayi ninkaya izuwa bakin gaba ya
shimfideta a kasa amma ko alamar numfashi babu
a tare da ita.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma
hankalinsa kenan ya fara kokarin dawo da
numfashinta yana mai danna kirjinta.Kawai sai yaji
tasowar wannan halittar daga karkashin kogin.A
fusace Yazid ya juyo ya kura mata idanu.Halittar ta
fito daga cikin ruwan tana tafiya sululu a kasa
tamkar macijiya kuma ta tunkaro inda yake.Komai
dakewar mutum gami da karfin zuciyarsa idan yaga
wannan halittar yayin fitowarta daga cikin wannan
kogi tana mai baiyana gaba dayan surarta dole ne
ya
Al amin Ahmed guyson ke magana
firgita.Cikin zafin nama Yazid ya mike tsaye
zumbur ya shafa ko ina a jikinsa yaji babu makami
ko guda daya kawai saiya dunkule hannayensa
yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya shiga
karanta wadansu addu'o'i na musamman a cikin
zuciyarsa a lokacin da halittar ta cigaba da durfafo
shi.Koda ya fuskanci cewa halittar so take ta kawo
musu cafka su biyun har da Nauwara wacce ke
kwance tamkar gawa sai ya rugo da gudu izuwa
kan halittar ya tareta suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa
junansu naushi da bugu,ita halittar tana kai masa
duka da dukkan jelunanta amma sai gashi yana iya
kade hannayen nata da jelunan nata cikin wani irin
bakin zafin nama na gaban kwatance kuma yana
mai da mata martani.Duk sa'adda ya sami nasarar
naushin halittar koina a jikinta sai tayi baya a
sama tamkar da majaujawa aka janyeta saboda
karfin naushin nasa amma saboda naci irin nata
sai kaga ta kuma tasowa sun cigaba da
artabun.Kokarin halittar kawai shine ta samu ta
kanannadeshi da jelarta guda amma ta kasa,shi
kuma kokarin da yake shine ya samu damar
naushinta a fuska ko a kanta saboda ya fuskanci
cewa nan ne lagonta yake,domin sa'adda ya
dankara mata saran nan a tsakiyar kanta saida
idanunta suka wurkile tayi rabin suma ta lume kasa
a cikin kogon kankarar amma saboda bakin naci
tana farfadowa sai ta taso sama suka cigaba da
artabu.Saida Yazid da wannan halitta suka shafe
kusan rabin sa'a suna kwamarzuwa tana bugunsa
yana bugunta ya zamana cewa kowannensu naji a
jikinsa amma an rasa wanda zai sami nasara a
cikinsu.Ita dai halittar tana ta zane masa sassan
jikinsa da jelunanta amma ta kasa sukarsa ko
yankansa da faratan hannayenta,shi kuma ya sami
nasara yana ta gabza mata naushi a fuskarta har
idonta guda ya kumbura subtum yana zubar da
jini,kunnenta guda ya dode ta daina ji dashi,ko ina
a fuskar tata ya kumbura yayi luhu luhu gashi dai
ta jigata ainun amma taki hakura sai cigaba da
fadan takeyi.Ana cikin wannan hali ne halittar ta
shammaci Yazid ta jefa jelarta guda izuwa kan
Nauwara ta kanannade ta ta dagata sama.Koda
ganin haka sai jikin Yazid ya yi sany ya ja da
baya.Koda ganin haka sai halittar ta bushe da
mahaukaciyar dariya mai kama da rurin tsohon
zaki sannan ta dubi Yazid ta bude baki a karo na
farko tayi magana tace,yakai wannan shaidanin
bil'adama kayi sani cewa yau shekarata arba'in da
daya a cikin wannan kogin kankara ina gadin
wannan daji na Hajarul Aswad babu wani mahaluki
daya isa ya ratsa ta cikin kogin nan walau mutum
ko aljan har ya iso nan karshen gabar batare dana
hallaka shi ba.Komai yawan runduna kota mutane
kota aljanu saina karkashe su na karar dasu sun
zama gawawarwaki amma sai gashi ka tsalleke
wannan kogi kuma na kasa kashe ka.Yanzu gashi
na sami nasarar dankar abokiyar tafiyarki wacce
tayi dogon suma sakamkon naushi daya danayi
mata dazu,to ka sani cewa har yanzu tana raye ba
mutuwa tayi ba,amma idan kana son ta cigaba da
rayuwa saidai ka tsaya cak a inda kake na matso
gareka na kashe ka batare da kayi yunkurin kare
kanka ba.Da zarar kayi wani yunkuri na kare kanka
ko cutar dani kuwa zan matse jikin abokiyar tafiyar
taka na kakkarya duk kasusuwan jikinta.Koda jin
wannan batu sai hankalin yarima Yazid ya
dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi take ya
tuna amanar da yarima Zainur ya bashi akan
Nauwara sannan kuma nan take yaji sonta ya sake
kwarara a zuciyarsa fiye da ko yaushe,kawai saiya
tsaya cak yace na yarda kizo ki kashe ni amma na
rokeki bayan kin kashe ni ki kyale Nauwara kada ki
taba lafiyarta Koda jin haka sai Halittar ta bushe da
dariya tace aini burina kawai shine na kashe ka
kuma na hana kowa tsalle wannan kogi saboda
idanban kashe ka ba ka karya lagona kuma ka
rusa tarihin jarumtakata da kwarjini,ina maiyi maka
alkawari cewa lallai bayan na kashe ka zan sauke
abokiyar tafiyarka kasa amma dole sai dai ta koma
da baya ba zata wuce gaba don tunkarar kogon
Hajarul Aswad.Koda jin haka sai yazid yace na
amince da hakan,kawai saiya saki jikinsa ya fara
kiran sunayen ALLAH a cikin zuciyarsa yana mai
neman taimakon Allah.Ita kuwa halittar sai ta
cigaba da durfafoshi tana kyakyala dariyar
mugunta,ashe duk wannan abu dake faruwa
tsakanin Yazid da wannan macijiyar Nauwara ta
dade da farfadowa daga dogon suman da tayi
amma saboda tana kanannade a cikin jelar halittar
a sama babu abinda zata iyayi.Koda Nauwara taga
yadda Yazid ya sallama rayuwarsa domin ceto tata
sai taji ta kara kamuwa da tsananin sonsa fiye da
ko yaushe kuma sai ta kura masa idanu tana mai
zubar da hawaye saboda tasan cewa lallao wannan
shine gani na karshe da takeyi masa.Nan dai
halittar ta cigaba da kyalkyala dariyar farin ciki tana
mai kara tunkarar Yazid.Koda ya rage saura baifi
taku biyar ba a tsakanin Halittar da yarima Yazid
sai halittar ta daka tsalle sama da nufin ta sokawa
Yazid faratan hannayenta biyu a
makoshinsa.kwatsam ba zato ba tsammani sai
Yazid yaga halittar ta sandare a sama tamkar gunki
ta fado kasa tim matacciya ko shurawa batay ba
sakamakon wata takobi data soketa a kunnenta na
dama ta faso cikin kunnenta na hagu.Sa'adda jini
ya kama tsiri daga cikin kunnen hagun.Koda Yazid
yayi arba da wanda ke ruke da takobin sai ya jada
baya cikin kaduwa da mamaki,ba wani bane ba
ruke da takobin data tsire wannan halittar face
Sarauniya Lazwara.Yazid ya dunkule hannyensa
biyu yana mai nuna alamun yin fada a Lazwara
wacce ita kuma fuskarta a cike take da annuri
gami da murmushi a wanann lokaci ne Nauwara ta
zaro jikinta daga cikin jelar matacciyar halittar
tasha gaban Yazid wato ta shiga tsakaninsa da
sarauniya Lazwara ta dubeshi....
TACE WANNAN MAI MULKI KUMA
ABOKIYA CE A GAREMU,ITA CE SARAUNIYA
LAZWARA MAI MULKIN BIRNIN ARNAN DAJI BIRNIN
DAKE MAKWABTAKA DA BIRNINMU.Koda jin
wannan batu sai Yarima Yazid ya dan saki jikinsa
yayiwa Lazwara dan guntun murmushi kawai sai ya
dubi Nauwara yace maza ki zo mu koma can
sansanin abokan tafiyarmu domin zasu kasance a
cikin zulumi da fargabar rashin ganinmu.Koda jin
wannan batu sai sarauniya Lazwara ta dubi Yazid a
fusace tace haba malam kai wane irin mutum ne
yaya na ceci rayuwarka data abokiyar tafiyarka
daga hannun wannan azzalumar halitta amma ko
gode mini nakayi ba zaka dauke gimbiya ku tafi ku
barni.Koda jin wannan batu sai Yazid ya juyo ya
dubi Lazwara cikin nutsuwa yace ai ba kece kika
ceci rayuwata ba ubangijina ne ya cece ni domin
lokacin danaga bani da wata dabara da zan iya
kubutar da rayuwar Nauwara saina kama kiransa a
cikin zuciyata ina mai neman taimakonsa shi kuma
saiya amsa rokona ya turo baiwarsa wato ke kika
ceci rayuwarmu gaba daya.Koda jin haka sai
sarauniya Lazwara tace ta yaya ubangijinka zai turo
ni na cece rayuwarka alhalin ni bashi nake bautawa
ba?Yazid yayi murmushi yace ai dake da abinda
kike bauwata da duk wata halitta dake cikin
sammai da kassai ubangiji nane ya halicce
su.Shine sarki Guda daya wanda bashi da abokin
taraiya bai haifa ba kuma ba a haife shi ba,yana
nan a ko ina kuma yana ji yana ganin komai da
kowa fiye da yadda kusancin ruhi da gangar jiki
yake,idan baki amince da duk abinda na gaya miki
ba ki cigaba da binmu a cikin wannan tafiya da
sannu zaki ga karfin ubangijina da idanunki kiyi
imani dashi.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Yazid yaja gimbiya Nauwara suka nufi hanyar da
zata mayar dasu can sansaninsu da gudu,ita kuwa
sarauniya Lazwara sai ta tsaya tana tunani da
wasu wasi akan abinda ya kamata tayi.Koda taga
Yazid sunyi nisa sai itama ta falfala da gudu ta
riske su suka cigaba da gudun tare.Tun kafin su
karaso sansanin daga can nesa hankalinsu ya
dugunzuma su ukun sakamakon hango wani irin
hayakin wuta a sama yayi tsiri ba kyan gani.Koda
hango wannan hayaki sai zukatun su Nauwara
suka buga da karfi suka kara kaimin gudunsu tun
akan hanya suka fara yin tuntube da gawarwakin
jama'arsu.Aikuwa sai Nauwara da Yazid suka fara
zubar da hawaye bisa ganin yadda aka yiwa
jama'ar tasu KISAN GILLAH duk da sun san cewa
shahada sukayi.Cikin dimauta Yazid da Nauwara
suka kara karfin gudunsu Yazid na kwalawa
Haiman da matarsa kira ita kuma Nauwara tana
kwalawa dan uwanta Zainur kira amma sai sukaji
shiru basu amsa ba.Al'amarin daya kara
dugunzuma hankalinsu kenan,nanfa suka cigaba
da ganin gawarwakin dakarunsu har suka iso
sansanin nasu inda suka iske shi a kone duk
tantunansu da komai nasu kuma ko ina gawarwaki
ne da jini male male a kasa.Bama su Nauwara ba
hatta sarauniya Lazwara bata san sa'adda idanunta
suka ciko da kwalla ba ta fara zubar da hawayen
tausayi sakamakon ganin irin kisan gillar da akayi
yiwa jama'ar su Nauwara.Kusa kowace gawa saida
akayi gunduwa gunduwa da ita.Saida suka dubo
ko ina a sansanin amma basu ga gawar sarkin
yaki ba data matarsa da kuma ta yarima
Zainur.Al'amarin da yayi matukar kara dugunzuma
hankalinsu kenan suka cigaba da kuka ba sassauci
saida suka jima suna kakan sannan suka dawo
cikin hayyacinsu.kawai sai Yazid ya mike tsaye a
fusace ya dubi Nauwara a lokacin daya dauki
takobi da garkuwarsa yace zo mu tafi can
sansanin abokan gaba domin daukar fansa,na
tabbata sun kashe Haiman,Zainur da matar
Haiman.Caraf sai sarauniya Lazwara tace Haiman
da matarsa da kuma Yarima Zainur basu mutu
ba,su kadai ne suka tsira da rayuwarsu a wannan
harin sumame da abokan gaba suka kawo
musu,amma sun kama su sun tafi dasu izuwa can
sansanin nasu wajen sarki Marwatu da Waziri
Ridwan domin a raye suke bukatarsu.Koda jin
haka sai Yazid da Nauwara suka sake fusata
Nauwara ta dubi Yazid tace zo muyi sauri muje can
sansanin abokan gaba ayita ta kare komu ko
su.Dajin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta
bushe da dariya sannan ta murtuke fuskarta tace
ta yaya kike zaton cewa ku biyu rak zaku iya yakar
sama da mutum dubu dari uku da doriya?Ina mai
tabbatar miki da cewa idan kuka kai kanku
sansaninsu waziri Ridwan tamkar sun sayar da
rayukanku ne wai shin ma kun fito ne domin ku
dauki fansa ko kuwa domin kuje kogon Hajarul
Aswad ku dauko wasikar jini ku koneta domin ku
ceto rayuwar al'ummar wannan nahiya?Ku sani
cewa su Waziri Ridwan ba zasu kashe Haiman da
Zainur ba saboda suna son suyi garkuwa ne dasu
domin ku fanshe su da wannan taswira ta zuwa
kogon Hajarul Aswad.Idan kuka kuskura kuka basu
wannan taswirar to ba zasu baku su yarima Zainur
ba zasu kashe su ne kuma su kashe ku,sannan
suje su dauko wasikar jni su cigaba da yin mulkin
zalunci a wannan nahiya.Lokacin da sarauniya
Lazwara tazo nan a zancensa sai jikin Yazid dana
Nauwara yayi sanyi sukayi shiru suna tunani.Daga
can sai Yazid ya dago kai ya dubeta yace to wai ke
menene dalilin da yasa kika biyo mu nan har kika
taimake mu?Shin kema so kike ki yaudare mu ki
sace wannan taswirar daga hannunmu domin ki
mallaki wasikar jini ko kuwa kina da wata manufa
ne daban wacce bamu sani ba?Koda jin wannan
tambaya sai sarauniya Lazwara taja dogon
numfashi sannan ya zauna a kasa dirshan ta dubi
Yazid cikin nutsuwa tace sama da shekaru hamsin
baya tun kafin a haifeni jama'ata basu taba shiga
harkokin wata kasa ba a wannan nahiya.Muna
zaman lafiya da kowane sarki amma bincike ya
tabbatar mana da cewa muddin waziri Ridwan ko
sarki
Al amin Ahmed guyson ke magana
Marwatu dayansu ya mallaki wasikar jini saiya
yake mu ya kawar damu daga doron kasa yadda
har abada za'a sake tunawa damu ba.Kun ashe ya
zama dole na fito na kare birnina da
jama'ata.Tabbas ni daku akan aiki guda muke,kafin
Lazwara ta gama rufe bakinta tuni Yazid ya tari
numfashinta yana mai cewa na yarda muna kan
aiki guda amma ba tafarki iri guda ba,mu muna
kan tafarkinaddinin musulunci ne ke kuwa kina kan
tafarkin tsafi.Yanzu wace shawara zaki iya bamu
dangane da wannan al'amari kuma menene
matsayinki bayan mun sami nasarar dauko wasikar
jini mun koneta,shin zaki karbi addinmu ne ko
kuwa zaki koma kasarko ne ku cigaba da
addininku na tsafi ke da jama'arki?Sa'adda
Lazwara taji wadannan tambayoyi guda boyu sai
tayi gyaran murya tace sai yanzu kayi mini
tambaya mai daraja.Da farko dai inaso ku sani
cewa babu wani mugun nufi a cikin zuciyata ko
son kai a kan wasikar jini,fata na kawai shine
akawar da zalunci a wannan nahiya a sami zaman
lafiya da kwanciyar hankali.Abu na biyu kuma
shine zan zuba ido naga iya karfin abin bautarku
daga nan zuwa isarmu kogon Hajarul Aswad idan
har naga kun iya dauko wasikar jini da taimakonsa
lallai nima zan karfi addinin naku.Ina mai tabbatar
muku da cewa nan da ko yaushe zamu iya gani
manzo daga sansanin abokan gaba zaizo ne da
sakon cewa idan kuna son rayuwar Haiman da
matarsa da Zainur to kuje kukai wasikar jini.Koda
jin wannan batu sai hankalin Yazid dana Nauwara
ya kara dugunzuma ainu,Nauwara ta dubi Lazwara
tace wace amsa ya kamata mu basu ko kuwa
zamu bi manzon nasu ne mukai Taswirar wasikar
jinin.Sarauniya Lazwara ta girgiza kai tace a'a ba
zamubi manzon ba sako zamu bashi kamar yadda
suka aiko.Abinda zaku gayawa manzon shine ya
koma ya gayawa iyayen gidansa cewa ba zaku
bayar da taswirar ba sai acan tsakiyar dajin da
kogon Hajarul Aswad yake.Wannan wata babbar
hikima ce nayi muku sai a nan gaba zaku fahimci
hakan kuma ku gargade su a kan cewa idan suka
kuskura suka taba lafiyarsu Haiman to a bakacin
Taswirar.Har Yarima Yazid ya bude baki zai
tambayi Sarauniya Lazwara ko wace irin hikima
take nufi da cewar sai a tsakiya dajin Hajarul
Aswad zasu bayar da wannan taswirar sai kawai
suka jiyo sukuwar doki an durfafo wannan konan
nan sansanin nasu,suna dago da kawunansu su
ukun sukga ashe kuwa maganar Lazwara ce ta
tabbata wato manzo ne daga sansanin abokan
gaba.Jim kadan sai ga manzon ya iso daf dasu
yana mai jan linzamin dokinsa,take dokin yayi
turjiya ya risina a gaban gimbiya Nauwara ya
kwashi gaisuwa.Tana hada idanu da manzon taga
ashe babban hadimin waziri Ridwan ne wanda ake
kira da suna Ubaiyu bin Marwas.Ubaiyu ya dago
kai ya dubi Nauwara yace ya shugabata mai girma
Waziri Ridwan yace na shaida muku cewa sarkin
yaki Haiman da matarsa da kuma Yarima Zainur
na hannunsu a can sansanin sarki Marwatu idan
har kuna son ku fanshi rayuwarsu to kuje ku kai
musu taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad in ba
haka ba kuwa zasu kure muku gudu su kashe ku
kamar yadda suka kashe sauran jama'arku.Koda
Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Nauwara
ta kyalkyale da dariya.Al'amarin daya baiwa Ubaiyu
mamaki kenan yace haba gimbiya yaya keda kike
cikin wannan hali zakiyi dariya,shin bakya kishin
dan uwanki ne bakya son ya tsira da rayuwarsa?
Nauwara tayi murmushi tace ai idan ma kuka
kashe dan uwana da sarkin yaki farin ciki zanyi
saboda sun sami shahada kuma zasu sami babban
rabo da sakamako na gidan Aljanna.Ka koma ka
sanar da iyayen gidanka cewa ba zamu basu
wannan taswirar ba sai a tsakiyar dajin Hajarul
Aswad.Koda jin wannan batu sai idanun Ubaiyu
suka zazzaro yace haba ranki ya dade kiyi tunani
dai,caraf sai sarauniya Lazwara ta tari nunfashin
Ubaiyu tana mai daka masa tsawa gami da zare
takobinta tace maza kabar wajen nan ko nasa
takobina na sare kanka.Kawai kaje ka isar da
sakon da aka baka.Koda jin haka sai jikin Ubaiyu
ya kama kyarma cikin hanzari ya kama dokinsa ya
haye ya juya da baya ya zabureshi da gudu su
kuwa sai suka bishi da kallo har saida ya bace
musu da gani.Faruwar hakan keda wuya sai
sarauniya Lazwara ta dubi Yazid da Nauwara tace
ku tashi mu ruga da gudu izuwa cikin dajin nan
muyi sauri mu isa can tsakiyar dajin Hajarul Aswad
kafin abokan gabar nan su zo su riske mu domin
Ubaiyu na sanar dasu sakon ki zasu biyo
bayanmu.Ba tare da wata gardama ba kuwa sai
Nauwara da Yazid suka mike tsaye suka falfala da
gudu,itama sarauniya Lazwara saita bisu a
gujen,nan da nan tazo ta tsere musu ta basu
tazara mai yawan gaske domin wani irin gudu
takeyi na ban al'ajabi har tashi takeyi sama kamar
tsuntsuwa kai da gani kasan cewa aikin sihirin tsafi
ne.Koda ganin haka sai shima Yarima Yazid ya
kama yin wata addu'a ta musamman ai kuwa nan
da nan karfin gudunsa ya karu shida na
nauwara.Nan da nan suka zo suka wuce sarauniya
Lazwara kafin ta ankara sun bata rata mai yawan
gaske.Nanfa Lazwara ta kara zage damtse iyakar
iyawarta duk dalasimanta na tsafi babu wanda bata
ambata ba domin ta wuce su amma sai ta
kasa.Al'amarin dayayi matukar girgiza ta kenan
yasa ta firgita da al'amarin ma'abota addinin
musulunci kenan.Saida suka sgafe sa'a uku da rabi
suna wannan gudu suna ta gifta bishiyoyi har ta
cikin koramai suke bi suna taka ruwa tamkar akan
kasa suke tafiya.Wannan shine abinda ya faru ga
su Yarima Yazid bayan su sarki Marwatu sun
kaiwa sansaninsu harin bazato sun kashe gaba
dayan dakarun nasu.
*A can kuma sansanin su sarki Marwatu kuwa tun
daga lokacin da suka ci yaki a sansanin su sa
yarima Zainur sai suka kamo sarkin yaki Haiman
da matarsa da kuma Yarima Zainur suka jefasu
cikin wani keji a ka dora
Al amin Ahmed guyson ke magana
kejin akan keken shanu aka rinka wulakanta su
akan hanya ana wahalar dasu.Har aka iso sansanin
ko ruwa ba'a basu sun sha ba kuma ana isa aka
fito dasu daga cikin kejin aka daure su a cikin rana
ba'a kwance su ba saida rana ta fadi aka kwashe
su kamar tsumma saboda tsananin jigata ta yunwa
da kishirwa bisa wannan dalili suka fita daga
haiyacinsu.Bayan an mayar dasu cikin keji an kulle
ne aka kawo musu ruwa makurwa uku uku kadai
aka basu gami da abinci loma uku uku kadai aka
basu.An basu wannan abinci da ruwa ne don
kawai kada su mutu,lokacin da suka danci wannan
abinci ne suka dawo cikin hayyacinsu sai matar
Haiman ta dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo
mata tace,yakai mijina yanzu shike nan mu tamu
ta kare kenan an kashe gaba dayan dakarunmu
daga mu mu ukun nan sai Yazid da Nauwara ne
kadai muka rage muma din kuma ga dukkan alamu
mutuwar zamuyi.Koda jin wannan batu sai Haiman
ya kamo matarsa ya rungumeta a kirjinsa yace
yake matata ina so ki sani cewa wuya bata kisa
kuma ko mutuwa mukayi akan wannan tafarki
bamu da wata asara dimin shahada ce mukayi.Ni
ina ji a jikina wadannan makiyan Allah ba zasu
taba samun nasarar mallakar wannan wasikar jini
ba.Caraf sai Yarima Zainur ya tari numfashin
Haiman yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne
yakai Abbana kuma zamu cigaba da addu'ar Allah
ya kare mu daga sharrin su waziri Ridwan kuma
ya bamu sa'a akansu mu kawar dasu da zalunci
mu kafa addinin Allah a wannan nahiya.Su Haiman
na cikin wannan zance ne waziri Ridwan da sarki
Marwatu suka taho garesu suna kyalkyala musu
dariyar mugunta,da isowarsu daf da bakin kejin sai
waziri Ridwan ya zura hannunsa cikin kejin ya cafi
makoshin Zainur yace kai yaro kayi asara,a baya
sarkin yaki da sarki Aiyuba sun gagareni kuma sun
jima yana kunsa mini bakin ciki,sun kare dukkan
hanyoyin cigaba rayuwata kuma lokaci yayi da zan
dauki fansa akanka.Tunda shi tasa ta kare gashi
can kwance akan gangar mutuwa,a yau dinnan
abokinka Yazid da gimbiya Nauwara zasu kawo
mana Taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad,mun
yaudare su da cewa zamu basu ku a maimakon
taswirar suna shigowa cikin wannan sansi zamuyi
musu kofar rago mu hallaka su mu dauke taswirar
sannan kuma muyi muku kisan gilla.Tabbas na
tabbata da cewa ba zasu iya tafiya su barku ba
dole ne suzo suyi kokarin ceton rayuwarku.Koda
gama fadin haka sai Ridwan ya saki makoshin
Zainur ya dubi sarki Marwatu suka bushe da
dariyar mugunta tare suna cikin kyalkyala dariyar
ne sarkin yaki Haiman ya tari numfashinsu yana
mai daka musu tsawa yace,ku tsofaffun azzalumai
kuyi sani cewa rana da yawa ta barawo ce rana
daya jal ta mai kaya.Tabbas kun dade kuna sheka
ayarku a doron kasa kuna zalunci kuna tara dukiya
ta gurbatacciyar hanya,babu mai iya taka muku
birki sai Mahaifin Gimbiya Nauwara.Yau sarki ya
fadi amma kuyi tunani da hankalinku da
kwakwalwarku an sami jarumi ma'abocin addinin
musulunci wanda shine zai kawo karshenku.Ina
mai tabbatar muku da cewa sakon da manzonku
zai dawo dashi saiya girgiza ku,kowannenku sai
hantar cikinsa ta kada.Kafin sarkin yaki Haiman ya
gama rufe bakinsa kuwa sai sukaji sukuwar doki
an nufo sansanin,cikin hanzari waziri Ridwan da
sarki Marwatu suka waiga baya sai sukaga ashe
manzo Ubaiyu ne ya dawo.A guje Ubaiyu ya ratso
cikin sansanin da doki,da isowarsa sai yaja tunga
a gaban su sarki Marwatu ya sauko da sauri daga
kan dokin ya zube kasa gabansu sannan ya dago
kai ya zaiyane sakon dasu yarima Yazid suka
bashi cewar ba zasu zo wannan sansani ba kuma
ba zasu bayar da taswirar ba face a tsakiyar dajin
Hajarul Aswad.
KODA
JIN WANNAN BATU SAI RAN SARKI MARWATU
DANA WAZIRI RIDWAN YA BACI,ZUCIYOYINSU
SUKA KAMA TAFARFASA KAMAR ZASU KONE,CIKIN
FISHI SARKI MARWATU YA DUBI RIDWAN YANA
MAI ZARE TAKOBINSA YACE,tunda dai sun hanamu
taswirar zuwa dajin hajarul Aswad banga amfanin
fursunonin da muke tsare dasu ba kawai mu kashe
su.Waziri Ridwan yayi sauri yasha gaban sarki
Marwatu ya dubeshi cikin matukar damuwa yace
a'a idan muka kashe su yarima Zainur yanzu har
abada ba zamu sami wannan raswirar ba bare mu
mallaki wasikar jini zo kaji wata magana.Nan take
Ridwan ya kama hannun sarki Marwatu ya jashi
izuwa can gefe daya suka tattauna sukayi kuskus
na tsawon yan dakiku suna gama tattaunawa ne
suka tara gaba dayan mayakansu suka basu
umarnin a fara shirin cigaba da tafiya kuma a
shirya makaman yaki.Nan take kuwa aka shiga
debo takubba,masu da kibiyoyi aka shiga wasa su
ana rarrabawa mayaka kai kace YAKIN DUNIYA za'a
tafi.Koda Zainur ya ga yadda dubunnan daruruwan
dakaru keta kai kawo a cikin sansanin suna ta
shirye shiryen yaki sai nan take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo
masa.Al'amarin daya baiwa Haiman da matarsa
mamaki kenan Haiman ya dubi Zainur cikin alamun
kaduwa yace yakai dana ina dalilin zubar da
wannan hawaye naka?Zainur yasa hannu ya share
hawayensa sannan ya dubi Haiman cikin nutsuwa
yace yakai abbana kaga wadannan dubunnan
daruruwan dakarun da yawansu magidanta ne,suna
da mata,'ya'ya da yan uwa kuma dukkaninsu
jama'ar birnin mu ne amma dayansu ba zai tsira
da rayuwarsa ba duk mutuwa zasuyi a cikin dajin
hajarul Aswad.Kaga kenan matayensu zasu zama
gwagware,yayansu kuma zasu zama marayu,basu
da ikon gudun shigowa nan dajin saboda tsoron
waziri ridwan,haka suma dakarun yakin da sarki
Marwatu ya taho da su daga kasarsa zasu mutu a
cikin jahilci batare da sun amfani addinin gaskiya
ba sun dandani dadinsa da kuma rahamar dake
cikinsa.Koda Zainur yazo nan a zancensa sai jikin
Haiman dana matarsa yayi sanyi suka kurawa
dakarun yakin idanu suna masu jin
tausayinsu.Kafin cikar sa'a daya an gama shiri tsaf
an kwashe komai a sansanin an zaburi dawakai da
gudu an durfafi hanyar da zata kaisu izuwa dajin
hajarul aswad.Idan mutum yaga wannan falfala
azababben gudu kuma yaga yawansu dole ya
firgita yayi zaton cewa karshen duniya ne yazo.
*A can cikin dajin hajarul aswad kuwa lokacin da
sarauniya Lazwara,Yarima Yazid da gimbiya
Nauwara suka falfala da azababben gudu izuwa
cikin dajin Hajarul Aswad suka shafe sa'o'i suna
gudun batare da sun gaji ba sai suka iso wani
katon fili wanda ke cike da wata irin ciyawa mai
taushi tamkar kilishi aka shimfida gaba daya a
wannan gaili.A zagaye yake da wadansu irin
dogayen bishiyoyi tamkar babu hanyar da mutum
zai iya bi ya wuce.Da isowarsu wannan wuri sai
sarauniya Lazwara ta kwalawa Yazid kira suka
tsaye da Nauwara.Lazwara ta karaso garesu tana
haki data kalli Yazid da Nauwara taga ko haki
basayi kuma babu alamar gajiya a tare dasu duk
da wannan tsananin gudu da suka sha sai ta kamu
da tsananin mamaki amma saita basar ta dubi
Yazid tace,nanne tsakiyar dajin Hajarul Aswad,anan
ya kamata mu tsaya mu tunkari su sarki Marwatu
ayita ta kare,idan mun sami nasarar kashe su mu
karasa kogon hajarul aswad mu dauko wasikar jini
idan kuma sune suka sami nasarar kashe mu sune
zasu je su dauko wasikar jini su mallaketa su
cigaba da yin mulkinsu na zalunci,ina mai tabbatar
muku da cewa gaba dayan masifun dake cikin
wannan dajin anan wurin suke kuma kowacce
masifa daya ta ninka ta waccan halittar dana kashe
a cikin kogin kankara sau uku babu abinda zai
kwace mu anan face tsananin sa'a da kuma iya
yakinmu da juriyarmu amma badai karfin sihiri
ba.Caraf sai yarima Yazid ya tari numfashin
sarauniya Lazwara yace ni dana san cewar
ubangijina zai bamu kariya ke kuma sai mu gani
idan tsafinki zai kareki idan kuma baki da tabbacin
hakan to ki karbi addininmu yanzu take nayi miki
alkawarin babu abinda zai sameki,koda jin wannan
batu sai Sarauniya Lazwara ta kyakyale da dariya
tace ai inda tun farko ban yarda da kaina ba bazan
yarda na biyo bayanku ba har na iso nan.Lallai
inda babu kasa anan ake gardamar kokawa,nidai
burina shine na rayu har izuwa lokacin da za'a zo
dasu yarima Zainur nan kuma naga wadanda zasu
sami nasarar dauko wasikar jini tsakanin su sarki
marwatu da mu.Koda jin wannan batu sai mamaki
ya turnuke Nauwara da Yazid saboda basu san
dalilin da yasa sarauniya Lazwara take son taga
isowar Yarima Zainur wannan wuri ba.Har Nauwara
ta bude baki zata tambayeta dalilin sai kawai sukaji
kasa ta kama girgiza,kafin dayansu yayi wani
yunkuri saiga wadansu irin samudawan dodanni
suna faso kasar suna fitowa su dayawa ba adadi
suka yiwa su yarima Yazid kawanya sai gashi su
Yazid sun zama yan mini mini tamkar tamkar an
ajiye yan tsaki uku a tsakiyar dubunnan kaji.Sudai
wadannan dodanni suna da matukar tsawo gami
da kaurin jiki kuma fuskokinsu nada matukar muni
da ban tsoro idanuwansu jajaye ne tamkar dan
buda aka gasa a cikin wuta.Jikinsu gaba daya a
murde yake cike da kwanji da jijiyoyi tamkar
duwatsu aka cure gaba dayan wadannan dodanni
suna ruke da wani irin gabjejen sungumin itace
mai dauke da wani irin tsini cako cako mai yawa a
samansa.Duk da tsananin jarumtaka irinta yarima
Yazid saida ya firgita bisa ganin wadannan dodanni
da kuma yawansu amma daya tuna cewa yana
tafarkin daukaka kalmar Allah ne sai dukkan tsoro
ya kau daga cikin zuciyarsa.Kawai saiya zare
takobinsa ya gyara tsayuwarsa yana jira yaga
dodon dazai fara kawo masa
Al amin Ahmed guyson ke magana
Hari.Itama Sarauniya Lazwara saita zare takobinta
ta gyara tsayuwarsa.Gimbiya Nauwara kuwa kasa
zare tata takobin tayi saboda tsoro ta koma bayan
yarima Yazid ta tsaya jikinta na karkarwa.Koda
Yazid yaga yadda Nauwara ta tsorata ainun da
ganin wadannan dodanni sai yayi mata rada a
kunne yace ki tsuguna kasa kuma kada ki kuskura
ki motsa daga nan wajen daidai da taku
goma.Gama fadin hakan keda wuya sai dodannin
suka afkawa Yazid da sarauniya Lazwara aka
ruguntsume da azababben yaki,ai kuwa ana fara
wannan yaki ne Yazid da Lazwara suka raina kansu
kuma suka san cewa sun gamu da gamonsu.Sudai
wadannan dodannin basa jin sara da suka a jikinsu
domin duk sa'adda takubbansu Yazid da Lazwara
ya hadu da jikinsu saidai kaji wata irin kara na
tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma
tarwatsin wuta ne ke tashi.Haka kuma basa jin
naushi da bugu domin da zarar su Yazid sun
naushe su hannunsu ne sagewa suji kamar dutse
suka nausa.Bugu da kari dodannin suna da
matukar zafin nama domin kafin su Yazid su kai
musu hari guda su sun kai musu uku nan da nan
suka kuntata Yazid da Lazwara suka fara galabaitar
dasu,wani abin mamaki shine babu wani dodo
daya kaiwa Nauwara hari a inda take tsugune
amma jikinta sai karkarwa yake tana kallon
gumurzun da akeyi cikin tsananin tsoro da tashin
hankali.Ashe Yazid ya karanta wata addu'a ta
musamman ya tofa adaidai wurin da Nauwara ta
tsuguna.Ana cikin wannan mugun artabu ne wani
dodo ya shammaci sarauniya Lazwara ya gabza
mta wani wawan naushi a fuska,saboda karfin
naushin saida tayi katantanwa a tsaye sau uku a
lokacin da gudan jini ya furzo daga bakinta ta
langwabe zata fadi kasa sumammiya.Koda ganin
haka sai yarima Yazid ya dimauce bai san sa'adda
ya kwala kabbara da karfi ba ya cafo Lazwara da
hannu daya ya goyata a bayansa kuma ya afkawa
dodannin da mugun sara da suka cikin bakin zafin
nama na gaban kwatance a lokacin da yaji wani
irin gagarumi karfi ya shige shi,ai kuwa sai gashi
takobinsa na daddatsa dodanni duk tsananin
yawan dodanni sai ya zamana banza domin an
rasa wanda zai iya koda lakutar jikin Yazid kuma
sai kutswa ta cikinsu yake yana bazar dasu,sassan
jikinsu ya rinka shawagi a sama yana zubowa kasa
jini jikinsu ya rinka tsartuwa da fantsama.Wohoho
idan kaji ana ki gudu to sa gudu ne bai zo
ba.Koda sukaga irin mummunar barnar da yazid
keyi musu kuma suka tabbatar da cewa ba zasu
iya kashi ba sai suka ruga izuwa cikin ramukan da
suka fito.Ramukan suka rufe kansu tamkar basu
taba wanzuwa ba a wajen sai gawarwakin yan
uwansu kawai a kwance rututu a filin daji.Adaidai
wannan lokaci ne Yazid ya sauke Lazwara daga
bayansa a kasa.Koda ya ga har yanzu a sume take
bata farfado ba sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun ya dimauce bai san sa'adda ya fisge battar
ruwa ba a jikin Nauwara ya budeta ya zazzage
ruwan akan fuskar Lazwara,faruwar hakan keda
wuya sai Lazwara ta farfado tana mai jan dogon
numfashi.Koda ta bude idanunta taga dubunnan
gawarwakin dodannin zube a kasa kuma ta dubi
yarima Yazid taga takobinsa da duk jikinsa ya rine
da jini sai kawai ta bude baki tace nayi imani da
ubangijin musulunci wanda ya baka karfin da ka
kashe wadannan dodanni,ina ragowar dodannin
suke?Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
Yazid da Nauwara,yazid ya dubi Lazwara yace
bazan baki amsar tambayarki ba sai bayan na
shigar dake cikin addinina,nan take yazid ya
biyawa Lazwara kalmar shahada ta maimaita
sannan ya dubeta yace ragowar daodannin sun
koma cikin ramukan da suka fito.Koda jin haka sai
Lazwara ta mike tsaye tace zasu sake fitowa don
haka mu zauna a cikin shiri.Gama fadin hakan
keda wuya sai suka jiyo sukuwar dubu daruruwan
dawakai an durfafosu suna daga kai sukaga ashe
su sarki marwatu ne suka taho cikin shigar
yaki,akan gaba kejin dake dauke dasu Haiman ne
bisa wani keken doki.Wannan runduna tun daga
nesa ta fara razana,ba komai ne ya razana su ba
face hango gawarwakin wadannan dodanni da
kuma hango Yazid face face a cikin jini takobinsa
ma ta rine da jini.Koda ya rage saura baifi taku
ashirin ba tsakanin rundunar su sarki marwatu da
su Yazid sai rundunar tayi turjiya suka tsaya cak
aka fara kallon kallo har saida kura ta lafa sannan
waziri ridwan ya dubi yazid,lazwara da nauwara
yace yaku abokan gaba gamu mun iso tsakiyar
dajin hajarul aswad dauke da yan uwanku idan
kuma kuka ki bamu wannan taswirar dayanku
bazai tsira da rayuwarsa ba,ku dubi kanku sannan
ku dubemu kun sancewa ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin baki kaza,kai Yazid kabar ganin
cewa ka kashe wadannan dodanni kai kadai to mu
ba dodanni bane mutane ne wadanda sunfi aljani
ma hatsabibanci da jarumtaka.Koda waziri ridwan
yazo nan a jawabinsa sai Sarauniya Lazwara tayi
caraf ta tari numfashinsa tace kai tsohon azzalumi
kayi sani cewa kunyi babban kuskure da ganganci
da kuka kawo kanku nan dajin domin baku isa ku
iya ketare nan wajen ba a raye bare har ku isa
kogon hajarul aswad ku dauko wasikar jini.Gaba
dayanku sai kun zama gawa.Koda jin wannan batu
sai waziri ridwan ya bushe da dariya yace ke
yarinya kiyi sani cewa kowa ya rigaka kwana dole
ne ya riga ka tashi,duk masifun dake cikin dajin
nan munsan dasu kuma mun dauki mataki a
kansu.Caraf sai sarauniya Lazwara ta sake tarar
numfashin ridwan tace na yarda kun san masifun
amma ai sani daban haduwa daban,idan kuna
ganin cewa zaku iya dasu gasu nan ku jaraba mu
gani.Tana gama fadin hakan saita juya ya dubi
yarima Yazid tayi masa wata inkiya shi kuma saiya
kwala kabbara ya naushi kasa da hannunsa guda
take ramukan dodannin nan suka bude dodannin
sukayi fitar burgu daga cikin karkashin Al amin Ahmed guyson ke magana
kasa,maimakon dodannin su afkawa su Yazid sai
suka juya da gudu suka afkawa su sarki Marwatu
aka ruguntsume da masifaffen yaki.Kaico na,nanfa
KASUWAR CINIKIN DAUKAR RAYUKA ta
bude,dodannin suka rinka ragargazar dakarun su
sarki Marwatu suna yi musu mugun kisan
gilla,abinda ya daurewa kowa kai a wajen shine ko
dodo daya bai nufi inda kejin dasu Haiman yake ba
kuma ta cikin dodannin Yazid ya kutsa yaje ya sare
kubar da aka kulle kejin kofar ta bude ya fito dasu
Haiman daga ciki ya tafi dasu can inda Nauwara
da Lazwara ke tsaye.Koda Nauwara ta hango dan
uwanta Yarima Zainur saita ruga gareshi ta
rungumeshi cikin tsananin farin ciki,ita kuwa
Lazwara sai taje gaban Zainur ta dubeshi cikin
murmushi tace masoyina dama na kudurce a raina
anan ne zan baiya maka SIRRIN ZUCIYA ta lallai
tun a farkon haduwa ta dakai na kamu da tsananin
sonka kuma a halin yanzu nima na karbi addinin
Yazid shin kasa so na?Koda jin wannan tambaya
sai Zainur yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin na
Nauwara ya dubi Lazwara cikin tsananin farin ciki
yace nima tun a farkon haduwarmu na nutse a
cikin KOGIN SON...Cikin sauri Nauwara ta rufe
bakin Zainur da tafin Hannuta tace kabar sauran
bayani saimunga yadda karshen wannan yaki zai
kasance,nanfa duk su biyar din suka mayar da
hankalinsu izywa inda ake fafata wannan masifaffen
yaki.Rabin sa'a aka shafe ana wannan yaki ya
zamana cewa wadannan daodanni sun kashe gaba
dayan dakarun sarki Marwatu,Sarki Marwatu da
Waziri Ridwan ne kadai suka rage a raye kuma
kowannensu ya sami mugayen raunika kimanin
guda bakwai a jikinsa.Suma in badon tsananin
karfin damtsensu ba da karfin Sihirinsu da tuni sun
dade da mutuwa.Dodannin na shirin karasa kashe
su sarki Marwatu da waziri Ridwan kenan sai Yazid
ya daka musu tsawa take suka kame kam tamkar
gumaka.Nan take Yazid ya fara kiran sunayen Allah
tsakaka yana yi masa kirari,faruwar hakan keda
wuya sai jikin dodannin gaba dayansu ya kama
tsattsagewa suka rina rugujewa suna zubewa kasa
suna zama gari.Nan da nan dodannin suka hallaka
gaba dayansu guda daya bai tsira da rayuwarsa
ba.Sarki Marwatu da waziri Ridwan na ganin haka
sai suka cika da tsananin al'ajabi gami da takaici,a
wannan lokaci ko motsi ba zasu iyayi ba
sakamakon jinin dake zuba a jikinsu kuma indai
ba'a gaggauta dinke raunikan nasu an tsayar da
jinin dake zuba ba na da wani lokaci zasu iya
mutuwa.Koda Marwatu da Ridwan suka fahimci
cewar lallai zasu hallaka idan ba'a taimake su ba
suka kama rokan su Yarima Yazid dasu
cecesu.Yarima Yazid ya matso daf dasu ya tsaya
ya dubesu yace ina karfin mulkin naku kuma ina
karfin damtsenku dana sihirin tsafinku,ku ceci
rayuwarku mana da abubuwan da kuka dogara
dasu,kun gani da idanunku ayau babu wani karfi
wanda yafi na ubangijin musulunci.Kodon saboda
dubunnan rayukan da kuka sa suka salwantar ba
zamu ceci rayuwarku ba mutuwa ce kadai zata
fanshe zunubanku a wannan doron kasa,ina mai
tabbatar muku da cewa daga yau tsafi ya daina
tasiri a wannan nahiya gaba daya kuma zalunci ya
kau sai adalci a tsakanin masu mulki da
talakawa.Yanzun nan zamu karasa kogon hajarul
aswad mu kone duk abinda ke cikinsa sannan mu
koma izuwa kasashenku mu kafa tutar addinin
musulunci.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Yazid ya juya ya koma inda su Zainur ke tsaye
suka rankaya gaba dayansu suka kara nausawa
cikin dajin na hajarul aswad suka bar sarki
marwatu da waziri ridwan suna murkususu suna
kukan nadama gami da kakarin mutuwa.Kafin cikar
dakika dari duk su biyun sun sandare sun zama
gawarwaki.Kamar Yadda Yarima Yazid ya fada
hakan al'amarin ya kasance wati sun isa har cikin
kogon hajarul aswad suka dauko wasikar jini suka
koneta faruwar hakan keda wuya kogon dutsen
gaba daya ya kama rugurgujewa.A guje suka fito
daga cikin kogon ba tare da dayansu ya hallaka
ba.Lokacin da su Yarima Zainur suka dawo gida
sun riske mahaifin Gimbiya Nauwara ya mutu don
haka sunyi kuka da bakin cikin rashin karbar
addinin gaskiya da baiyi ba.Nan take aka kafa tutar
addinin musulunci a gidan sarautar sannan suka
dunguma izuwa birnin sarauniya Lazwara nan yake
aka kaddamar da musulunci bayan nanne aka
daura aure Yarima Zainur da Lazwara,Yarima Yazid
da Nauwara sannan aka sake dawowa birnin su
Nauwara aka baiwa Yarima Zainur sarautar garin
wato ya gaji sarki Aiyuba.Shi kuma Yazid ya dauki
matarsa Nauwara suka tafi can kasar su,koami ya
dawo daidai yadda ya kamata,aka cigaba da zaman
lafiya a cikin nahiyar da addinin irin na musulunci
aka kautar da tsafi da bautar gumaka.
.
ALHAMDULILLAH
Anan muka zo karshen wannan littafi wato wasikar jini
Dafatan ya kayatar daku
Suleiman zidane whatsapp 09064179602

No comments:
Write blogger