TRUE LIFE STORY
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±k)
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Dedicated to MEELAT A.H.K
REAL KHADY AND HUMYLUV
SANNU BAYIN ALLAH, ALLAH YA BAKU LAFIYA, ALLAH YASA KAFFARA NE MASOYA ANNABI KUCE AMEEN
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI
_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN KOWA DA KOMAI, DA YA ARAMN NUMFASHI YA SAKE BANI IKON FARA WANAN LABARIN MAI SUNA ~KA CUTAR DANI~, INA ROKON ALLAH YASA NA KAMMALA SHI LAFIYA._
_YA ALLAH KAYI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI._
_WANAN LABARIN BA KIRKIRARRE BANE, YA FARU DA GASKE, KUYI KOKARI KU BIYO SHI TUN DAGA FARKO DOMIN DAUKAN DARUSSAN DAKE CIKIN SHI._
_ALLAH YA BANI IKON RUBUTA ABINDA ZAI AMFANE KU, KU KUMA MAKARANTA ALLAH BAKU IKON DAUKAN DARASIN DA KE CIKINSHI_
```LIKE AND DROP UR COMMENT```
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 1 to 5
Ihu take tana fad'in " wayyo Allah! jama'a ku taimake ni, zai kashe ni. "
abinda suhailat take ta maimaitawa kenan
shi kuwa kamal kukan ta ko a jikin sa, cigaba yayi da dukanta, sai k'wallo yake da ita.
matar dake zaune a kusa da d'akinta ce ta fito ita da mijinta da gudu, suka nufi d'akin, domin kai mata d'auki.
ko da suka shiga sun tarar har yanzu bai dena dukanta ba
makwabcin nasu mai suna ishaq shi ne yai sauri ya rik'e kamal, tare da bashi baki.
kamal ya fisge hannun shi, tare da yi wa ishaq wani wulak'antaccen kallo, sanan ya nuna shi da yatsa yace " ishaq kake ko wa, to daga yau ina maka kashe di na k'arshe, karka kuskura ka sake gigin shiga tsakani na da mata ta, idan ba haka ba hukuma ita zata raba mu dakai, ku fitarmn daga d'aki malamai. "
ya juyo da kallon shi ga matar tashi suhailat wadda take numfashi da k'yar, jikinta duk ya farfashe saboda dukan da ta sha, ya kalle ta yace " ke kuma gobe idan na sake baki guga kya k'ara k'onamn riga. "
yana gama fad'in haka ya fice ya bar gidan.
su kuwa ishaq da matar shi da ke tsaye sun daskare saboda tsabar mamakin tijara da rashin tausayi irin na wanan mutumi, duk a tunaninsu laifi tayi gagarumi ashe ma akan guga ne yake ta faman dukanta kamar jaka.
tausayin ta ne ya kama su, ga cikin da take tare da shi, ga duka, babu k'wak'k'waran dalili, ga kuma horo da yunwa.
hakuri suka bata, sanan ishaq ya fita ya bar matar shi me suna fadeela tana taimaka mata.
haka suhailat ta wuni tana fama da ciwon jiki, ga matsanancin zazzabi me zafi da ya rufe ta.
shi kuwa goga kamal, tnda yasa k'afa ya fita, be k'ara ko lek'o cikin gidan ba.
yana can majalisa zaman kashe wando, cikin banzayen abokai yanata fallasa sirrin gidan shi, tare da fad'a musu abinda yaiwa matar shi yau, nan da nan abokan nashi suka d'auki ihu tare da fad'in dakyau goga mata ba'a musu sakwa sakwa.
suhailat kuwa baiwar Allah jiki yai zafi, mak'wabciyar ta fadeela ce keta kai kawo a kanta, ita ta bata abinci sanan ta aika aka siyo mata magani ta bata ta sha.
da dare ma haka tai mata, ta kawo mata abinci ta ci, sanan ta bata magani ta sha, sai da taga tayi bacci tukunna ta fito ta koma nata d'akin.
kamal kuwa ba shi ya dawo cikin gidan nan ba, sai wajen k'arfe d'aya na dare.
.....................
b'angaren gidan iyayen suhailat kuwa, mahaifiyar suhailat ce cike da damuwa tun safe, saboda mafarkin da tayi da d'iyar ta suhailat jiya da daddare.
har dare wanan damuwar bata bar fuskarta ba, mahaifin su suhailat ne ya shigo d'akin, ya tarar da ita ta zuba tagumi, ta shiga kogin tunani.
zama yai kusa da ita , tare da cire mata tagumin da tayi.
mahaifiyar suhailat me suna Asiya ta kalle shi, ta d'an saki ranta, tare da yi mashi sannu da zuwa.
bayan sun gaisa ta tashi ta je ta kai mishi ruwan wanka, ta dawo ta sanar dashi.
kafin ya fito daga wanka ta shirya mishi abincin shi, yana fitowa bayan ya shirya suka ci abinci.
mahaifin suhailat me suna Adam yana lura da ita, ba wani abincin kirki ta ci ba.
ajiye cokalin shi ya yi shima, ya kalle ta yace " maman suhailat wai meke damunki ne ? "
Asiya ta kalle shi tace " wallahi wani mafarki nayi mummuna da suhailat jiya, nayi addu'a amma abun har yanzu yakasa barin raina."
Adam ya kalli matar shi yai murmushi, sanan yace " banda abinki ai mafarki ba lallai bane ya zama gaskiya."
Ummi Asiya tace " dan Allah ni dai idan ka amince zan tura maryam da zainab gobe in Allah ya kaimu, su dubo mana halin da take ciki. "
Mal Adam yace " Allah ya kaimu, amma ki saki ranki, ki kwantar da hankalinki, autarki tana nan lafiya insha Allah. "
ummi Asiya tai murmushi, sanan tace " Allah yasa abban suhailat, nagode. "
ku biyo ni
urs π ±Kπ
[12/22, 10:23 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
#https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to AYSHAN UMMA
_MASOYANA NA NESA DA NA KUSA,_
_NA FILI DA NA B'OYE_
_NAGODE DA ADDU'O'INKU GARENI,_
_NAGODE DA DUMBIN SOYAYYAR DA KUKE NUNAMN,_
_ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKHAIRI_
_ALLAH SA KU GAMA DA DUNIYA LAFIYA_
NAGODE NAGODE NAGODEππ»π
_MAMANEEY NAGODE K'WARAI DA ADDU'O'IN DA NAKE SHA DAGA GAREKI, ALLAH YA BAR K'AUNA, ALLAH SAKA MIKI DA ALKHAIRI_
page 5 to 10
Washe gari da sassafe maryam ta buga sammako, bayan sun karya zainab ta gama shiryawa, suka d'auki hanyar katsina, domin dubo halin da yar uwarsu take ciki.
sun d'au a k'alla awa d'aya da rabi, sanan suka iso cikin garin katsina.
cikin tasha motarsu ta parker, kowa ya firfito.
maryam da zainab suma suka fito, suka tari napep, sukai mishi kwatancen unguwar da zai kaisu.
yana tafe suna nuna mai inda zai shiga, har suka kawo k'ofar marusa.
goga kamal yana tsaye a k'ofar gida, shi da abokan shi, hira suke suna kwasar dariya, babu abinda ke damunsu.
amma koda kamal ya hango su maryam sai ya had'e rai, tamkar be taba dariya ba.
bayan sun sallami me napep sai suka tunkaro gidan, sunxo daf dasu zasu shiga sai maryam tace "sannunku, " ko kallon inda take basu yi ba, suma suka wuce abinsu suka shige cikin gidan.
da sallamar su suka shiga gidan, mak'wabciyar suhailat me suna fadeela suka tarar a tsakar gida tana shara.
sai da suka gaisa da fadeela, sanan suka shiga d'akin suhailat.
zaune suka sameta ta kifa kai da guiwa, da alamu kuka take.
sanan gabanta ga plate nan, da alama abinci ta gama ci a ciki.
Aunty maryam ce tayo kanta da sauri, ta d'ago kanta, tana tambayarta abinda ke faruwa.
fashewa da kuka ta sake yi, zainab ta kalli aunty maryam tace " naga ma duk ta rame ko dai bata da lafiya ne."
suhailat ce ta kalle su cikin kuka tace " yunwa nakeji, yanzu fadeela ta zubomn abinci, kuma ban k'oshi ba."
Aunty maryam da zainab sukai shiru, tausayin yar uwar tasu ne ya kamasu sosai,
aunty maryam tace " to meyasa baki daure kin dafa ba?"
suhailat tace " ai babu abincin ya k'are, dama gwangwani yake bani na dafa kuma tazarce har dare kuma ya k'are."
Aunty maryam tace " yanzu ina za'a samu abincin siyarwa?."
suhailat tace " nan gidan ne kusa da namu, da an fita daga namu sai gidan a gefen hagu, amma alale ne suke siyarwa."
maryam ta bawa zainab kud'i ta je ta siyo musu alale ta dawo
bayan sun gama cin abinci, fadeela ta shigo cikin d'akin, suka k'ara gaisawa.
sanan fadeelan ta juyo gun suhailat tace " suhailat ya k'arfin jikin?"
suhailat tace " da sauk'i "
aunty maryam tace " wai meke damunta ne?"
fadeela tace " zazzab'i ne, sai kuma tsamin jiki na dukan da ta sha."
maryam tace " duka kuma, wa ya dake ta?"
nan dai fadeela ta kwashe duk abinda ya faru ta fad'a musu
maryam me raunin zuciya har ta fara kuka, ta kalli yar uwar tata tace " meyasa baki kira kin fad'a mana ba."
suhailat tace " aunty maryam ko na gudu gida kuma kona fad'a a gida, da kamal ya je ya shiryo k'arya ake bashi gaskiya, k'arshe ma abba ya d'ora laifin kaina, shiyasa na d'au Alk'awari ko kashe ni zai yi bazan k'ara guduwa gida ba."
maryam tai shiru, fadeela ta kallesu tace " ni dai in zakuji shawarata ku tafi da ita gida."
wayar maryam ce tai k'ara,
k'arar wayar yai dai dai da shigowar kamal, ko sallama be yi ba, sanan ko kallon inda suke be yi ba, balle su sa ran zai musu magana.
maryam ta d'auki wayarta suka tashi suka koma d'akin fadeela, nan ta kwashe komai ta fad'awa ummie duk abinda suka tarar.
daga k'arshe maryam tace " ummie ko dai mu taho da ita ne? "
ummie tace " bari muyi magana da abban ku tukun."
bayan yan mintuna sai ga kiran ummie ya shigo cikin wayar maryam tasu
maryam ta d'aga ummie tace " na fad'awa abban ku abinda ke faruwa, yace karku taho da ita, ku bari gobe mazan suzo su d'auko ta, yace in kuka ce zaku taho da ita zai iya yi maku lahani."
maryam tace " to ummie "
ummie tace " bawa suhailat d'in wayar mui magana "
maryam ta mik'awa suhailat waya, suhailat tana jin muryar ummien su ta fashe da kuka, zuciyar uwar tai rauni, haka dai tai ta bawa suhailat d'in hak'uri, tare da jaddada mata lallai za'a zo a tafi da ita tare da wasu kayanta.
bayan sun gama magana ummie tace ta bawa maryam wayar, bayan maryam ta karba ummie tace " kud'in da ta ware musu su se mata kayan tea tunda bata jin dad'i bazata iya girki ba, ragowar canjin su bata ta rik'e a hannunta ko zata nemi wani abun, daga k'arshe tace suna se mata suyo haramar tahowa gida.
bayan sun gama wayar suka fita su biyun, suka je bakin ti'ti suka siyo mata kayan tean kamar yanda aka umurce su, tare da bata sauran canjin, sanan sukai sallama da ita tana hawaye, ji take a ranta kamar ta bisu.
ku biyo ni
urs π ±Kπ
[12/22, 10:23 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NIπ
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
edited by MEELAT
Dedicated to UMMIEXEEY
_NAGA WASU HAR SUN FARA GUNDURA DA HALIN KAMAL, HMM TO KU GYARA ZAMA DAN BAKUJI KOMAI BA_
MUJE ZUWA DAI
page 10 to 15
Suka fito suka tari a daidaita sahu, ya kaisu tasha, suka hau mota.
B'angaren suhailat kuwa ko da su maryam suka tafi tana d'akin fadeela, sai da taga mijin fadeelar ya dawo sanan ta tashi ta koma nata d'akin.
tana shiga ko zama bata yi ba kamal ya kalleta yace " Annamiman yan uwan naki sun tafi, to me suka zo yi, kuma da suka zo ke me kika ce musu? "
ita dai bata ce mishi komai ba, haka ya tasa ta gaba yana ta zage mata yan uwa, da yaga bata kula ba sai ya tashi ya fice daga gidan.
su maryam sun isa gida lafiya, zainab tace " ummie a zubo mana abinci yunwa muke ji wallahi."
ummie ta zubo musu abinci ta basu suka ci suka gama, zainab ta kwashe kwanukan ta fita dasu takai gun wanke wanke.
bayan ta dawo ummie ta kalle su tace " sannunku da hanya "
suka amsa da " yauwa ummie."
ummie tace " to meyasa da kuka je baku girka abincin ba kuka siya"
zainab tace " ai babu abin girkawan duk ya k'are, kuma ko akwai ma auna mata yake gwangwani d'aya zuwa biyu ta dafa, kinga idan mukace ma zamui girki rashin mutunci zaiyi mana.
maryam ta cigaba da cewa " ummie yanzu fa suhailat matar gidan fadeela ita ke ci da ita, ko yau ma ita ta bata abincin munje ma mun tarar da ita tana ta kuka, abincin be ishe ta ba, sai da muka se alale sanan ta k'ara."
zainab tace " dan Allah ummie wanan karon karku share batun ta, idan da tana fad'in halayen shi ana k'aryatawa yanzu munje mun gani da idonmu."
zainab ta cigaba da cewa " matar gidan faddela ta fad'a mana komai tace duk abinda take zuwa gida tana fad'in yai mata babu k'arya a ciki, baya yi ne a gaban mu yan uwanta saboda kar muzo mu fad'a."
maryam tace " wanan karon ma Allah ne ya tona asirin shi, tunda muka je har muka fito fa kallon arzik'i bamu samu daga gare shi ba, balle har yai mana magana."
ummie tace " Allah ya kyauta, mun fara maganar da abban ku a waya idan ya dawo zamu k'ara sa. "
bayan Abba ya dawo yai wanka ya ci abinci, suna hira ummie ta shigo da hirar suhailat ciki.
Abba yace " d'azu mijin matar gidan su suhailat d'in ya kirani, har nai mamakin inda ya sami number ta, sai yacemn suhailat ce tai saving d'in tawa da taki a wayar matarshi ko da zata kiramu, saboda yanzu ba waya a hannunta kamal ya d'auka ya siyar, yaimn bayanin komai duk abinda ya faru duk ya fad'amn komai. "
Abba ya numfasa, sanan ya cigaba da fad'in " ashe yaron nan d'an iska ne ban sani ba,"
ya sake numfasawa sanan yace " yanzu babu kud'i a hannuna ne, amma zanyi k'ok'ari in samu wanda za ai shatar mota aje a d'aukota a taho da wasu kayan nata."
washe gari Abba ya je wajen aminin shi kuma mak'wabcin shi ya aro mota ya dawo, to dama yayyin suhailat guda biyu sun iya mota, yana dawowa gida ya tara mazan gidan su duka ukun, yace " ku shirya yanzu zaku je katsina ku d'auko ummie, ku taho da wasu daga cikin kayanta, dan naji labarin ance ya fara siyar da kayanta."
ya kalli khalil babban cikinsu yace " khalil kai ne zaka ja motar,"
khalil yace " to Abba "
Abba ya ciro kudi dubu uku a aljihun shi ya ba khalil su sha mai, sauran kuma idan zasu buk'aci wani abu."
ummie ta kalli abba tace " dan Allah Abban suhailat ka bari in bisu muje tare, kar a barsu su tafi su kad'ai ba wani babba aje ai aika aika."
Abba yai shiru can sai yace " ta shirya su tafi."
bayan ta shirya suka fito suka d'au hanya.
k'arfe d'aya suka fito daga gida, suka isa katsina k'arfe biyu da rabi.
suka k'arasa k'ofar gidan khalil yai parking d'in motar suka firfito
suka shiga cikin gidan, suhailat tana ganin su ta taso da murnarta, ta tarbesu.
goga kamal yana ganinsu amma ko kallon inda suke be yi ba.
suka sami waje suka zauna, ummie ta kalli su khalil tace ba zama zakui ba ku tashi ku fita da pridge dinta da kayan kallonta,
ya'ya khalil yace " to "
suka tashi suka fara had'a kayan
ummie ta kalli yarta suhailat tace " tashi ki shirya mu tafi"
sun d'auko pridge zasu fita da shi goga kamal yai wuf ya tare k'ofa, yace " wallahi babu uban da ya isa ya fitarmn da mata ta daga cikin gidan nan. "
tofhaπ€
muje zuwa
urs π ±Kπ
[12/22, 10:24 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT
Dedicated to AYSHA A. MUH'D
_GAISUWAR BAN GIRMA A GAREKU YAN EXCLUSIVE WRITER'S,_ππ»
_BABBAN ABUNE RAYUWA TARE DA KUπ_
_MASOYANA_
_KU SANI CEWA A DUK INDA KUKE BK TANA KAUNARKU,_
_KUMA KU RIKE KARKU MANTA KUNE NAWA A KODA YAUSHE_
#https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
Page 15 to 20
" Wallahi babu wanda ya isa ya fitarmn da mata daga cikin gidan nan. "
abinda kamal ke ta maimaita wa kenan, bayan ya tare k'ofa ya hanasu su wuce.
shi kamal ya tare hanya, su kuma su khalil suna k'ok'arin sai sun fita da kayan.
kamal ya cakume rigar khalil zaiyi dambe dashi, shima khalil ya aje pridge ya cakumi tashi zasui fad'a, ummie tai sauri ta mik'e ta kifawa d'anta khalil mari tace " abinda ya kawo mu kenan "
ummie ta kalli musbahu k'anin khalil tace, " je ka kiramn baban asiya ya zo ya zama shaida. "
yana fita shima khalil ya ciro wayar shi ya kira kawun shi, ya kira abokin shi da kuma wani d'an unguwar, kafin baban asiya yazo ya kira mutam hud'u.
nan da nan suka cika d'akin, baban asiya ne yazo daga k'arshe.
bayan an bud'e taro da addu'a sai baban asiya ya kalli ummie yace " hajiya meke faruwa ne? "
ummie tace " munzo tafiya da suhailat ne, mijinta ya tare k'ofa ya hanamu wuce wa."
caraf sai abokin shi da wanan d'an unguwan suka ce " ai dole ya tare k'ofa tunda matar shi ce. "
sai baban asiya ya kalle su yace " idan har zakui taku maganar ku bari har in gama magana dasu, in har na isa, mun zauna nan ne domin samun maslaha da neman sulhu, ba wai don rikici ba."
ya juyo ya kalli ummie yace " hajiya meyasa zaku tafi da ita, meke faruwa ne? "
nan ummie ta fad'a mishi duk abinda ya faru koma ace yake faruwa, kamal tana magana yana k'aryatawa, fad'i yake " wallahi k'aryane, wallahi sharri sukemn kawai dai tana so ta rabamu ne take fad'in haka."
baban asiya ya daka mai tsawa, yace " kamal baka da hankali ne, surukar taka tana magana kana yi kuma har kake k'aryata ta. "
baban asiya ya kalli suhailat yace " haka ne duk abin da hajiya ta fad'i? "
suhailat tace " eh duk abin da ta fad'a gaskiya ne, idan ya musa ai nayi recording d'in wasu abubuwan da yakemn a waya."
kafin kowa yace komai kamal ya shek'e da wata irin dariya, yace taje ta d'auko, ya fad'i hakan da k'warin guiwan shi saboda yana da tabbas akan suhailat bata da waya, ya d'auke wayarta ya siyar.
baban asiya ya kalli suhailat yace " je ki d'auko wayar a sa muji."
suhailat ta tashi ta fita, shi kuwa kamal murmushi yake ta yi na samun nasara, har ta dawo yana dariya.
tsagaitawa ya yi da dariyar saboda ganin wayar da ta mik'awa baban asiya
baban asiya ya kunna recording d'in, sai ga muryar nura ta fito tangaran, sukai shiru suna sauraron irin rashin mutuncin da yake gurzawa.
nan fa kamal ido ya raina fata
bayan sun gama ji baban asiya ya mik'awa suhailat wayar, suhailat ta karb'a, sanan tace " mijin fadeela shaida ne itama fadeelan shaida ce, dan itace ta koma ciyar da ni a gidan nan."
baban asiya yace " suma a kira su"
akaje aka kirasu, aka fara tambayar matar ta fad'i abnda ta sani tsakaninta da Allah, bata b'oye komai ba ta fad'a musu.
shima mijin aka tambaye shi, ya fad'i iya abinda ya sani, yace " shekaranjiya ma akan tana goge mai kaya rigar shi ta k'one yai mata duka, da nazo ina bashi hak'uri sai yacemn karna k'ara shiga maganar su da matar shi, tun daga ranar ya daina yimn magana, ko nayi mishi be amsawa. "
kowa duk jikin shi yai sanyi da al'amarin kamal, uncle d'in kamal da tunda aka fara magana bece komai ba, ya kalle shi yace " kasan irin aika aikar da kake yi kenan ka sa aka kira ni, to ni nabasu goyon baya d'ari bisa d'ari akan su tafi da yar su har sai ka gyara halin ka. "
uncle d'in ya numfasa sanan ya dubi ummie yace " hajiya dan Allah kuyi hak'uri, wallahi daga ni har mahaifinsa bamu da masaniyar wanan d'anyen aikin da yake aikatawa, kuma nasha kiran shi ina tambayar shi suna dai zaune lafiya koh sai yacemn eh, sai yau yaga damar nemana bayan ya gama bata komai."
ummie tace " ba komai Alhaji "
uncle ya kalli baban asiya yace " malam ka barsu kawai su tafi. "
baban Asiya yace " hajiya kuyi hak'uri dan Allah, sanan abi komai a hankali. "
ummie tace " bakomai,
ta kalli su khalil tace ku tashi ku sa kayan a mota. "
a lokacin kamal ya sami bakin magana, fad'i yake " wallahi duk wanda ya tafimn da mata bada yawuna ba, yaita surutun shi babu wanda ya kula shi. "
an d'auki akwatunan ta, da pridge, sai kayan kallo.
bayan sun gama shirya kayan sukaiwa mutanen d'akin sallama, sanan suka fito itama fadeela sukai mata sallama, tare da godiyar kulawar da sukai da suhailat ita da mijinta.
har mota suka biyo su suna basu hak'uri, sai da suka ga tashin su sanan uncle d'in kamal ya koma ciki gun kamal yace " tunda ka kunyata ni a gaban mutanen nan masu mutunci, kuma ka nuna ban isa da kai ba to karka sake ka k'ara nema na akan wanan maganar na cire hannuna, yana gama fad'in haka ya fito ya tarar da baban asiya a k'ofar gida, sun dad'e suna magana sanan sukai sallama, kowa ya kama gaban shi.
............ ............
da yake motar gida ce ba tsaye tsaye, shiyasa nan da nan suka iso gida.
bayan sun iso, suka firfito da kayan, aka shiga su cikin gida.
bayan sun ci abinci sunyi sallah, suka zauna suna bawa ragowar yan uwan labarin abinda ya faru, tare da nuna mamakin su k'arara kan tijarar kamal duk irin hallacin da sukai masa.
bayan suhailat tayi wanka, tai sallah, ta ci abinci, bacci ne me dad'i yai awon gaba da ita.
ummie ta k'urawa d'iyar tata ido, tare da zuba tagumi, wani irin tausayinta taji ya kamata,
wayar ta ta jawo, ta kira baban su suhailat, ta shaida mishi sun dawo.
da daddare bayan Abba ya dawo ya natsa, ta kwashe duk abinda ya faru da yanda sukai da mutanen da ya tara musu ta fad'a mishi.
da yake abba yana da zafi sosai, ummie ta fishi hak'uri nesa ba kusa ba, yad'au abun da zafi sosai, kuma yace shi yarshi ba zata koma gidan Azzalumin mutum irin shi ba, ta dawo kenan, sedai ya bata takardar ta.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:24 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to REAL KHADY
_GAISUWAR BAN GIRMA AGAREKU DA JINJINAR KASAITAππ»_
ummiexeey
real khady
mareeya
khady fresh
_sannu bayin Allah_
_ALLAH YA BAKU LAFIYA, YASA KAFFARA NE_
_Allah ya dorar da lafiyarsa gareku_
_YA ALLAH KA BAWA DUKKANIN MUSULMIN DUNIYA LAFIYA_ππ»
LIKES AND COMMENTS
FB PAGE #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
20 to 25
Wanan karon ma ba shi kad'ai ya zo ba, har da kawun shi wato waliyin kamal d'in, da kuma abokin kawun.
wanan karon be shiga kai tsaye ba, saboda da manya yazo, sai da suka tsaya akai musu iso sanan suka shiga.
ummie tai musu kyakkyawan tarba kamar yanda ta saba, sanan tace musu bari ta kira malam wanda ya zama waliyinta.
an ci sa'a yana gida, ummie ta sanar da shi zuwan iyayen su kamal d'in.
bayan ta fad'a mishi sai ta kira yayan suhailat musbahu tace shima ya zo, ba'a kira khalil ba saboda yafi musbahu zafi.
bayan kowa ya hallara har suhailat d'in sai malam ya bud'e taro da addu'a.
bayan ya gama addu'ar sai uncle d'in kamal ya gyara zama yace " to Alhamdulillah, nasan kowa yasan abinda ya had'amu anan, wato kan maganar suhailat da kamal,
tabbas kamal ya yi laifi, abubuwan da ya yi be kyauta ba sam, mu kanmu abinda ya yi yai mana ciwo sosai, hakan ne ma yasa muka fita harkar shi, muka barshi yai ta zarya shi kad'ai,
to yanzu abinda yasa muka shigo maganar saboda ya nuna mana nadamar shi, ya kuma tabbatar mana da bazai bamu kunya ba, yanzu abinda muke rok'o daga gareku shine, dan girman Allah hajiya ayi hak'uri, a bashi dama ta k'arshe. "
ummie tace " ga suhailat d'inan ai, sai a ji ta bakinta."
suhailat tace " ummie ni gaskiya ba zan koma gidan sa ba, wallahi ba zai taba canja halin shi ba, nadamar shi ta kwana biyu ce. "
abokin uncle d'in kamal yace " kiyi hak'uri suhailat, kafin mu zo nan sai da muka yi mai kashedi akan idan har yai sakacin k'ara ruguza auren shi da kanshi to ba ruwan mu, kiyi hak'uri ki bamu wanan damar kinji. "
musbahu yace " tunda tace ba zata koma ba a yi hak'uri kawai a k'yaleta, tunda ta dage ita kad'ai tasan wahalar da ta sha a hannunshi, menene amfanin auren mijin da be san darajar matar shi ba, be girmama iyayenta balle kuma yan uwanta. "
sai yanzu malam yai magana yace " a'a baza'ai haka ba, ke suhailat kiyi hak'uri ki koma. "
" ya ta bazata tab'a komawa gidan wanan yaron ba. "
maganar da suka ji kenan daga bakin k'ofa, dukkan su suka juya domin su ga ko wane ne.
Abba ne tsaye a bakin k'ofa, ya nuna kamal da yatsa yace " me ya kawo ka gida na, ban yi maka kashe di kar ka k'ara shigomn gida ba, to bari kaga k'aryar taurin kai da rashin kunya. "
wayar shi ya ciro daga cikin aljihu zai kira yan sanda, ummie ta taso da sauri ta k'wace wayar tare da girgiza mishi kai, alamar kar ya aikata haka.
dagewa ya yi kan sai ya fitar mishi daga gida, da k'yar da sid'in goshi aka bashi hak'uri, ya zauna domin ai sulhu.
abba yace " ya hak'ura ne ba don wanan fitsararren ba sai don darajar iyayen shu da yazo da su. "
godiya sukai mishi, sanan ne ya sami guri ya zauna.
malam yai mishi bayanin irin tattaunawar da akai, tare da fad'a mai abinda ya kawo su, bayan ya gama suma iyayen kamal d'in suka k'ara rok'on shi akan ya basu dama ta k'arshe, dan zasu sa ido sosai kan zamantakewar auren nasu.
shima kamal hak'uri ya basu yace " abba dan girman Allah kayi hak'uri, ummie kiyi hak'uri dan Allah, ya juya gun suhailat itama ya bata hak'uri. "
kamal ya cigaba da cewa " suhailat kiyi hak'uri, na yi nadamar abinda nai miki, ki yafemn, in sha ALLAH hakan ba zata sake faruwa ba. "
malam ya kalli abba yace " tunda manya sun shigo maganar, kuma shima yaron ya yi nadama to ina ganin a yi hak'urin ta koma.
Abba yai shiru yana tunani a ranshi, maganar gaskiya yanzu shi kanshi yaron ya gama ficemai daga rai, amma kuma yana jin nauyin iyayen shi bazai iya tsawaita jayayya da su ba.
d'agowa yai ya kalli suhailat yace " suhailat kina jin abinda suka ce, kin amince zaki koma d'in? "
suhailat tace " Abba dan Allah a yi hak'uri kar a maida ni, wallahi bazai fasa halinsa ba, kuma yanzu beda sana'ar yi, duk hatsinmu ya k'are. "
uncle d'in kamal yace " maganar abinci ba matsala, zan nemo mai aiki, idan ba'a samu ba zan bashi jari. "
kamal yace " wallahi na canja suhailat, kiyi hak'uri dan Allah, a bani damar k'arshe, idan na sake ko wane irin hukunci ne aimn. "
malam yace " suhailat kiyi hak'uri ki koma d'in, idan be canja ba se a d'au mataki.
suhailat tace nidai.........
ummie ta katseta tace " tunda kowa yace kiyi hak'uri to kiyi hak'urin, aje a gwada zaman a gani.
Abba yace " suhailat kiyi hak'uri tunda yace hakan, duk idan kkaga ya cigaba da yin abinda yake yi a baya to kar kiy shiru, ki sanar domin a d'auki mataki. "
abba ya cigaba da cewa " amma maganar komawarta sai ta haihu sanan zata koma. "
cikin sauri kamal yace " eh nayarda, a bari ma sai ta yaye abinda ta haifa dai dai lokacin na samu sana'ar yi. "
Abba ya kalli kamal yace " ai sai ta amince da zata koma tukun yallab'ai. "
Abba ya juyo ya kalli suhailat yace " suhailat kin amince kin yarda zaki koma? "
cikin natsuwa suhailat tace " Abba bani da wani zab'i a duniya da ya wuce zab'inku, duk abin da kuka zartar ku daina neman shawarata akai, se dai ku bani umurni, ni kuma nai biyayya ga umurninku. "
kowa na d'akin seda ya ji dad'in maganganunta, sanan suna yaba ladabi da biyayyarta.
iyayenta da iyayen kamal sai shi mata albarka suke, tare da yi masu addu'ar d'orewar zaman lafiya. "
uncle's d'in kamal sukai godiya, sanan sukai musu sallama, suka fito suka tafi.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:24 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to KHADIJA IBRAHIM (meredil)
_Wanan page d'in d'ungurumgun sadaukarwa ne a gareki KHADIJA IBRAHIM (MEREDIL), ke ta daban ce a nan d'in BK ❤, halinki daban ne, zuciyarki me kyau, tunaninki me kyau, kai madalla dake ππ», Allah ya k'ara tsarkake zuciyarki._
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 25 to 30
tun daga lokacin kamal da suhailat suka daidaita, yana zuwa akai akai har lokacin da cikinta ya cika wata tara, ta haifo d'iyarta ya mace kyakkya
ta haifo ya me kama da babanta kamal sak, se dai farin uwar kawai da ta d'auko.
kowa ya ganta yana sa mata albarka, tare da yi mata Addu'ar Allah sa kar tai halin ubanta.
da ranar suna ta zagayo aka rad'awa yarinya suna Zainab, an sha suna inda angon k'arni ya kawo atamfar shi biyu da rigar jaririya biyu masu kyau.
anyi taro lafiya an watse, sedai fatan Allah ya raya zainab.
bayan anyi arba'in da sati d'aya nura ya zo yana rok'o a kan a bar suhailat ta koma, tunda yanzu haka ya samu aiki a abuja.
lokacin da yazo abba bayanan, haka ma malam, se tace mishi yai hak'uri yaje idan mahaifinta ya dawo zata sanar dashi, duk yanda sukai zata kira ta fad'a mishi a waya.
bayan abba ya dawo ta fad'a mishi sak'on kamal, tare da rok'on shi kan ya barta ta koma tunda ta yi arba'in.
Abba yace " shikenan sai ki sanar da ita, idan ta amince nan da sati d'aya su maryam sai su rakata ta koma. "
bayan sati d'aya su maryam suka raka suhailat d'akin mijinta suka juyo, se dai mui musu fatan d'orewar zaman lafiya.
tun da ta koma kamal ke nan nan da ita, yana lallab'ata kamar k'wai, ya sha mamaki da yaga yan iskan abokan shi sun d'auke k'afa daga gare shi, tun lokacin da suka rabu da suhailat.
sun yi wata biyu uku suna zaune lafiya.
sun fara samun matsala ne daga ranar da mugayen abokan nan nashi suka dawo mai, daga lokacin komai ya fara dawowa kamar da ko ma ace ya zarce na da.
yarinyar su zainab ta k'ara wayau, a lokacin ne kuma uban ke hantarar yar, ko wurin shi ta tunkaro sai ya daka mata tsawa, har takai ga yarinyar ta fara tsoron shi.
kwata kwata kamal baya sallah sam, dama tun suhailat na amarya sallar bata dame shi ba, to yanzu kwata kwata ya daina.
tayi tayi ya sakata a islamiyya ya k'i, kuma shi bata ga ya tab'a zama yai karatun litattafan addini ba balle tace ya rik'a koya mata,
aikin da ya samu a abuja daman adaidaita sahu yake ja, wanda ya bashi, ita ya karbe abin shi yanzu babu inda yake zuwa daga gida sai majalisar zaman fasa wando.
da suhailat taga zaman haka bazai yiwu ba sai ta rok'i abbanta da ya bata jari zata fara sana'ar saida itace.
abban suhailat ya bata jari me d'an dama, ta saro itace, sanan dama tana da pridge, sai ta fara yin zob'o ana fita mata da shi bakin nan wata makarantar boko dake kusa da su.
bayan yan kwanaki jarin ya karye saboda da kud'in take ciyar da su, sanan idan ta ajiye wasu kud'in a d'aki kamal ya kwashe.
akwai wata rana da ya wuni a gida kuma tana lura dashi sam beyi sallah ba, tun ta asuba da ya yi.
ita babban abinda ke damunta nata karatun da ya dak'ile.
suhailat ta kalle shi tace " baban zainab dan girman Allah ka barni na koma makarantar islamiyya. "
kamal yace " wallahi ba wata makaranta da zaki shiga. "
suhailat tace to dan Allah ka koyamn, tunda bazaka barni na cigaba da neman sani akan addini na ba. "
kamal ya kalleta yace " ni na manta gaskiya, bazan iya koyar da ke ba. "
suhailat tace " baban zainab ka ji tsoron Allah, rayuwar nan ba matabbata bace, ka tuna cewa duniya, makaranta ce, kuma jarrabawa ce, kayi tunanin sanadin halittarka da Allah ya yi, kaji tsoron Allah ka gyara tsakaninka da mahaliccinka, ka bauta mishi kamar yanda ya umurce mu muyi, ina lura da kai sam sallah bata dameka ba, kafi jin dad'in zaman majalisa ko zaman kallon k'wallo to k............
d'auketa ya yi da mari sau uku, ya rufeta da duka wai ta ce mishi jahili, dukanta yake yana k'wallo da ita, yana dukanta tana kuka d'iyarta zainab na yi, sai da ya jibgeta son rai sanan ya tsallaketa ya fita ya barta.
tun daga ranar halayen shi na da suka dawo, abinda zai mata kullum na safe daban, na rana daban, haka ma na dare daban.
gashi ya fara dare a waje, idan ya fice tun dare baya dawowa sai cikin dare, haka zai fice ya barsu da yunwa, sai abinda mak'wabta suka bata, kuma sabida zurfin ciki irin nata ko yan uwanta sunzo bata fad'a musu.
babu dama tai kuskure kad'an sai duka, yauma da daddare daga tayi shinkafa da mai da yaji, ya rufe ta da duka, bayan kuma ita ta nemo kud'in da kanta ta girka masu, k'wandalar shi babu a ciki.
da abin ya ishe ta washe gari ranar laraba da safe yana ficewa ta had'a kayanta tasa a jaka ta goya d'iyarta ta fito, ta rok'i mak'wabciyarta rancen kud'i ta bata ta kamo hanyar kano.
tana isowa gida ta fad'a jikin ummien ta tana kuka, duk mutan gidan hankalinsu ya tashi nan da nan suka cika d'akin domin jin abinda ke faruwa.
suhailat ta fad'awa ummie duk abinda ya faru, duk hak'urin ummie yau cewa tai " bari abban ku ya dawo wallahi daga yau kin gama auren kamal. "
bayan abba ya dawo ummie ta sanar da shi komai, yace ai daman nasan baxai fasa halin shi ba tunda ya zamar mishi jiki. "
cikin kuka suhailat tace " abba wallahi na tsane shi, dan Allah abba karku k'ara maida ni gidan shi. "
Abba ya kalle ta yace " yi shiru suhailat, ai muna k'aunarki, ba jaka muka haifa mai ba, saboda haka ko ya baki takardarki ko in maka shi k'ara kotu.
washe gari misalin k'arfe goma kamal ya kwad'a sallama gidan su suhailat ya shigo tsakar gidan, a dai dai lokacin khalil ya gunguro mashin d'in shi zai fita kasuwa.
ummie ta amsa mai sallama ya shiga cikin d'akin ya zauna, khalil ya parker mashin d'in shi, ya shiga kitchen ya d'auko tab'arya ya nufo d'akin ummie inda kamal ke zaune ya nufa, ya d'aga tabaryar kenan zai buga mai ummie ta rik'e.
ummie tace " khalil menene haka, baka da hankali ne. "
khalil ya kalli ummie yace " ummie ya fita daga gidan nan ko kuma in raunata shi "
ummie tace " to saki tab'aryar ka tafj gun aikin ka zai fita yanzu "
khalil ya saki tab'aryar ya je ya d'auki mashin d'insa ya tafi.
maganar gaskiya khalil da zainab da maryam duk sun gado zuciyar mahaifin su, amma kuma duk tsananin fushin su basa k'etare maganar iyayen su.
bayan ummie ta kad'a khalil ya tafi saii ta dawo ta zauna, sanan ta kallli kamal tace " meke tafe da kai? "
kamal yace " nazo ne in ji suhailat nan ta taho?"
ummie tace " eh nan ta zo, sai me kuma?"
kamal yace " jiya da safe na fita yo cefane ko da na dawo na tarar da k'ofa a rufe, ashe gida ta taho."
ummie ta kalle shi tace " shi kuma farfashewan jikinta fa a ina ta samu? "
nan da nan kamal ya daburce, ya fara inda inda.
sai ummie ta kalle shi tace " to yanzu me ya kawo ka? "
kamal yace " nazo ne in gani idan tana nan sai mu tafi gida"
ummie tace " to suhailat tace ta hak'ura da aurenka, abbanta kuma yace ko kazo baka same shi ba in fad'a maka ka bada takardar suhailat ko ya shigar da k'ara kotu."
kamal ya mik'e tsaye, sanan yace " gaskiya bazan saketa ba, dan kuwa ina son mata ta."
yana gama fad'in haka ya fice daga gidan.
anya kuwaπ€
muje zuwa dai
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
writen by BILKISU Z. YA'U(π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to ASIYA (SEE SEE)
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
_sannu bayin Allah MY MEELAT A.H.K And AUNTY AYSHAN UMMA Allah ya baku lafiya d'orarra, Allah yasa kaffara ne_
_MUYI ZAMANTAKEWA DA JUNANMU DA WADATAR ZUCI, IYAYE, MIJI, YAN'UWA, DA ABOKAN ARZIK'I NA NESA DA NA KUSA,_
Page 35 to 40
ASALIN LABARIN
Malam Adam d'an kasuwa ne, ada yana zuwa legos ya saro kaya yazo kano ya siyar, da wanan sana'ar ya siya gida, ya kuma siya karamar mota ta hawa.
daga baya ya bar wanan sana'ar ya dawo siyan gidaje da filaye yana siyarwa, shine sana'ar shi ta yanzu, kuma sanin kowa ne wanan sana'ar sai lokaci zuwa lokaci ake samun cinikinta.
malam Adam yana da mata d'aya sunanta Asiya, sunada yara bakwai.
Aunty aysha itace yarsu ta farko, sai mai bi mata Aunty maryam, sai na ukunsu shine yaya khalil, sai yaya musbahu, sai ustazun gidan yaya habib, sai zainab sai autar su wato suhailat.
malam Adam yanada hak'uri, amma in aka tab'o shi yana da zafi sosai.
matar malam Adam me suna asiya tanada matuk'ar hak'uri sosai da zurfin ciki
malam adam da asiya sun tarbiyantar da yaransu ta yadda addinin islam ya shar'anta.
Aunty aysha da maryam sunyi aure kowaccensu tana d'akin mijinta.
yaya khalil yana jami'a yana karatu, yayin da yaya musbahu, da ustaz yaya habib sun kammala karatun su na secondry, yanzu haka suna jiran result, sedai shi habib be zauna haka ba, cigaba ya yi da neman ilimin addinin shi, a can ne yai wani aboki kuma malamin ajin yara mai suna mahmud
mahmud be wuce sa'an yaya habib ba shima, sun shak'u sosai har takai yan gidan su habib sun san shi saboda lokuta da dama suna yawan zuwa gidan su habib d'in tare da mahmud.
anan ne mahmud ya ga suhailat, kuma yace duk duniya baida mata da ta wuce suhailat.
tun yan gidan suna d'aukan abun da wasa har suka zo suka gasgata saboda irin kulawar da yake bawa suhailat, lokaci guda ya ware na cigaba da karantar da ita litattafan da bata sani ba.
zainab tana s.s 1, yayin da ita kuma suhailat take j.ss 2.
Allah yaiwa yaran malam adam baiwar kyau da farin jini, duk inda suka gifta kowa sha'awarsu yake yi.
suhailat yarinya ce kyakkyawa, tanada natsuwa sosai, ga hak'uri tamkar mahaifiyarta, sedai akwai k'urucciya sosai a tattare da ita, yanzu haka shekarunta basu fi goma sha biyu ba.
kowa na gidan yana maruk'ar k'aunar mahmud, amma banda mahaifin suhailat, a cewar shi idan ya ganshi baya gaishe shi.
mahmud bak'ine kuma gajere ne sosai tamkar wada, yana da kyau amma ba sosai ba.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Suhailat ta kammala karatun ta na secondry, lokacin tana da shekara goma sha shida, kuma har lokacin suna tare da mahmud, duk da tasan cewa bayan mahaifinta acikin yan uwanta ma wasu daga ciki basa k'aunarta dashi, ita kuma ba ruwanta da gajartar shi da kuma rashin kyawun shi, a haka take son kayanta.
yaya khalil yana da wani aboki mai suna kamal, karatun jami'a ya had'asu har suka zama abokai.
shima kamal ba wanda be san shi ba acikin gidan, hakan yasa kai tsaye yake shigowa gidan, ya shiga d'akin khalil dake cikin gidan.
ana haka wata rana ya shigo gidan ya ci karo da suhailat a tsakar gida, tun daga ranar Allah ya jarabce shi da matsananciyar k'aunarta.
kamal d'an garin katsina ne, karatu ya kawo shi kano, ya na zaune a wani gidan student na haya, tsakanin inda yake haya da kuma gidan su suhailat,babu nisa.
kamal yana da yawan gaisuwa, sanan akwai shi da k'arya acikin duk wata magana da zaiyi, ga d'an karen dad'in baki.
shi kuma mahaifin suhailat irin mutanen nan ne masu yawan son gaisuwa, indai kana yawan gaishe da su to kai d'an gaban goshi ne, duk inda kamal ya ga abba to sai yazo ya gaishe shi cikin ladabi da biyayya, hakan yasa kamal ya shiga ran malam adam sosai,
tun ranar da ya ga suhailat ya k'ara nacewa zaman gidan.
da farko kamal ya sha wahala wajen samun soyayyar suhailat, kuka kuwa ya sha yi wa suhailat akan ta so shi, haka kuma duk yan'uwanta daga mazan har matan yabi duk yai musu kuka yana rokonsu akan su taimaka su shawo mai kan suhailat ta so shi.
haka ma mahaifiyarta da mahaifinta ya bisu yaita yi musu magiya su bashi auren suhailat yai musu Alk'awarin zai rik'eta amana.
hakan yasa kowa ya tausaya mishi, musamman abba da yake ta shan sintiri akan a bashi auren suhailat.
abba ne ya tara meeting na gaggawa, bayan an bud'e taro da addu'a sai abba ya dubi kowa yace " dalilin taruwarmu anan saboda suhailat ne, kowa ya san yanda kamal yake son suhailat, kuma kowa yasan yana da ladabi da biyayya, domin duk inda ya ganni sai ya gaishe ne,
abba ya numfasa sanan ya kalli suhailat, ya cigaba da cewa suhailat har ga Allah bana k'aunar yaron nan mahmud, dan haka a matsayi na na mahaifinki na zab'a miki kamal a matsayin mijinki, shi kuma mahmud ki sallame shi, yana gama fad'in haka aka rufe taro da addu'a kowa ya watse.
suhailat taci kuka ta gode Allah, daga baya ta hak'ura.
ummie ta d'auki kamal tamkar d'an da ta haifa a cikinta, har ya zamana abincin gidan da kwanon shi a ciki kullum, ko be zo ba za'a aika mishi da nashi abincin.
amma duk da haka tafi son yarta da mahmud akan kamal.
A hankali sha'k'uwa me k'arfi ta shiga tsakanin kamal da suhailat, basu ankara ba suka fad'a k'aunar junansu, sai hankalinta kuma ya fara karkata kan kamal d'in.
mahmud yana da wani hali guda, idan ya had'u da wanda ya sani a hanya baya tsayawa a gaisa, wucewarshi yake, hakan ya zama tamkar nature d'inshi ne.
wanan halin nashi ya jawo sonshi ya fara fita daga ran suhailat, musamman da taga hatta abbanta baya k'aunar mahmud d'in.
A tsarin mahaifin su suhailat baya bari yaran shi mata su cigaba da karatu, daga secondry skul yake aurar da su.
tun lokacin da suhailat ta fara soyayya da kamal ta rage sauraron mahmud, ko yazo gunta bata fita, haka zai k'araci zaman shi ya tashi ya tafi.
soyayyar suhailat da kamal tai nisa, yayinda shi kuma mahmud son shi ya ja baya.
mahmud ne zaune a k'ofar gidan su suhailat, tun d'azu yake zaune a gun yana jiran suhailat, amma har yanzu bata fito ba.
habib ne ya fito daga cikin gida ya tarar da mahmud zaune a k'ofar gidan ya zuba tagumi.
habib ya kalli mahmud yace " wai daman har yanzu kana nan, tunda mukai sallama dakai na shiga na kwanta, har nayi bacci na tashi nai tunanin tun d'azu ka tafi. "
mahmud yace " ban tafi ba, har yanzu bata fito ba. "
habib yace " ina zuwa, bari na turo maka ita. "
be jira amsar shi ba ya shige cikin gidan.
suhailat! suhailat!! suhailat!!!
suhailat dake zaune kusa da ummie tace " na'am yaya "
shigowa falon ya yi ya tarar da ummie tana ta fama da ita kan taje gun mahmud tak'i, habib yace " suhailat me mahmud yai miki kike mai wulak'anci kwana biyun nan? "
suhailat ta b'ata rai, sanan tace " yaya ni bana sonshi, yaya kamal nake so. "
yaya habib yace " ok har ya siye zuciyarki da yaudararrun kalaman shi koh, to ina jiye miki yin dana sani a gaba," yana gama fad'in haka ya juya yai ficewar sa.
gun mahmud ya koma ya bashi hak'uri, sanan ya lallab'a shi ya tafi gida.
iyayen kamal sunzo ansa rana wata uku kacal.
koda yaushe kamal yana tare da suhailat, yauma kamar kullum suna zaune a k'ofar gida suna zance, sai kamal ya kalli suhailat yace " malama suhailat amma kenan, ke ko yaushe hijab kike zumbulawa, amma dai in mukai aure gyale zaki koma sawa gaskiya dan shine ra'ayi na, sun d'an tab'a hira, har tai mishi magana kan ya kamata ya fara koya mata litattafan addini, sai yace " shi gaskiya be iya litattafan ba, Qur'anin ma ya manta rabon shi da karantawa,"
suhailat tace " to gaskiya ya kamata ya rik'a karantawa, kuma ya koma makarantar islamiyya. "
kamal yace " in sha Allah zai yi k'ok'ari yaga ya koma d'in "
bayan suhailat ta shiga gida ta fad'awa ummie abinda kamal yace mata.
tun daga ranar jikin su ya fara sanyi da kamal, gashi lokacin biki bai fi saura sati d'aya ba.
ana saura kwana uku biki yauma kamar kullum suhailat da kamal suna zaune a k'ofar gida suna hira, sai ga wata k'awar zainab mai suna hadiza ta kawo mata ziyara, tana zuwa k'ofar gidan ta tsaya cak, kallon kallo sukai wa juna sanan ta shiga cikin gidan.
tana shiga cikin gidan suka gaisa da ummie, sanan zainab ta ja ta suka shiga cikin d'aki.
hadiza k'awar suhailat ce, kuma aminan juna, tun suna yara suke tare, tare sukai primary, sukai secondry, yanzu haka hadiza tana jami'a.
shak'uwarsu yasa iyayensu ma suka zama aminai.
bayan sun shiga d'aki hadiza ta kalli zainab tace " k'awata kar dai kamal wanda na wuce su yanzu shi da suhailat shi zata aura ? "
zainab tace " shi zata aura insha Allah. "
hadiza ta zazzaro ido, sanan tace " dank'ari "
_tsoro da fargabar jin me hadiza zata fad'i tasa na yarda abun rubutun, amma idan ta sakeni zan cigaba da sambad'o muku da cigaban labarin kuna k'wamushewa_
INA SONKU MASOYA NA
_ku biyoni_
URS π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U(π ±K)
_(Autan exclusive writer's)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to MEELAT A.H.K
*Zamo na kowa koda kowa bai zamo naka ba. Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yima fatan sharri, saka dukkanin musulmi acikin addu'arka koda babu mai sakaka acikin addu'arsa. Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufarka da sharri. kyautata tsakaninka da Allah kada kadamu da abinda mutane suke cewa akanka. Allah ya kyautata rayuwarmu Amin*ππ»
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 30 to 35
Anyi anyi kamal ya bawa suhailat takardarta, amma ya dage akan shi fa ba zai saki matarshi ba, saboda yana sonta.
Ummie da Abba sun yanke shawara akan a bari sai an kwana biyu, damuwar suhailat d'in sun ragu sai a shigar da k'ara.
kulawa suke bawa suhailat sosai, kowa k'ok'ari yake wajen faranta ranta, hakan yasa ta saki ranta, kuma hankalinta ya kwanta, musamman d taga ba'a mayar da ita gidan kamal ba, nan da nan ta mayar da k'iban ta, walwalarta da ta rasa a baya ta dawo.
Abu d'aya ke damunta shine k'in bata takardar ta da kamal ya yi.
…………
BAYAN SHEKARA D'AYA DA RABI
a wanan lokacin har an yaye zainab, amma har yanzu anyi anyi kamal ya sake ta ya k'i.
Abba ne zaune a falo shi da ummie, suna tattaunawa kan maganar suhailat.
Abba yace " tunda kamal ya k'i bawa suhailat takardarta, kuma shi kamal d'in ya ma daina zuwa kuma ita yarinya tana zqune har yanzu da auren shi a kanta, to yanzu idan na fita zan biya ta kotu in shigar da k'ara. "
ummie ta numfasa, sanan tace " to Allah ya taimake mu, ya sa hakan shine mafi alkhairi agare mu. "
Abba yace " ameen, je ki kiramn suhailat kice ta shirya ta zo mu je kotun, idan mun gama abinda za'ai sai ta dawo gida ni sai in wuce gun aiki. "
ummie tace " to "
ta tashi ta je ta isar da sak'on abba gun suhailat, nan da nan ta shirya ta fito suka tafi.
bayan sun isa kotun suka shigar da k'ara, bayan sunyi duk wani abu da ya kamata aka ce gobe da safe wajen k'arfe goma su zo a had'asu da masinja domin kaiwa kamal sammaci.
bayan sun fito daga kotu abba ya tarar wa suhailat adaidaita sahu ta tafi gida, shi kuma ya wuce gun aiki.
washe gari wajen k'arfe bakwai dai dai suhailat ta shirya, ita da ya'ya khalil suka tafi station, suna zuwa aka had'asu da masinja tare da takardar sammaci, suka fito suka d'auki hanyar katsina.
k'arfe goma dai dai suka iso garin katsina, suhailat na gaba khalil da masinja suna biye da ita a baya.
sedai duk inda suhailat take tsammanin za'a ga kamal babu shi babu alamar shi, har gidan iyayen shi suka je amma basu same shi ba.
gidan me unguwa suka nema suka bashi takardar ya bawa kamal, suka juyo suka dawo gida.
da ranar shiga kotu ta zagayo suhailat da su abba suka shirya harda d'iyar su zainab suka tafi kotu.
lokacin da suka isa kotun Alk'ali be riga da ya zo ba, saboda mutanen da suka gaggani a waje, suna jiran k'arasowar shi.
A harabar asibitin suka tarar da kamal, shi da wani hatsabibin abokin shi kabir.
koda kamal ya hango su suhailat sai su kalli juna shi da abokin shi sai su kwashe da wata irin hatsabibiyar dariya, har suka zo daf da su zasu wuce basu dena kallon su suna masu mahaukaciyar dariyar nan ba.
babu wanda ya tanka su, saboda dama abba ya ja wa yaran shi kunne akan duk abnda kamal zai yi musu kar su sake su tanka, har suka shige cikin harabar kotun kuwa babu wanda ya tanka su.
suna shiga cikin kotun suka sami waje suka zauna, basu dad'e da zama ba sai ga kamal da abokin shi kabir sun tunkaro inda su suhailat suke zaune, zainab da ke jikin yayar suhailat wato aunty aisha, yasa hannu ya d'auke zainab daga jikin Aunty aysha, tana kuka tana kiran umma amma be dawo da ita ba, babu wanda ya bi shi, domin kuwa Abba yace kar wanda ya tanka shi.
bayan wasu lokuta sai ga Alk'ali ya shigo, kowa da kowa ya mik'e, sai da ya zauna sanan aka koma aka zazzauna.
An fara karanto k'ararrakin mutane biyu kafin a zo ta su suhailat.
bayan an gama da su sai aka fara karanto na su suhailat, kamar haka " A yanzu kuma zamu saurari karar da suhailat Adam ta kawo, na mijin ta kamal Aliyu, a kan tana so ya saketa yak'i shine suka zo wanan kotun domin a raba auren. "
yana gama karantowa ya mik'awa alk'ali takardar, ya koma ya zauna.
bayan alk'ali ya yi rubutu na yan mintuna sanan ya umurci kamal da suhailat su bayyana.
bayan sun fito alk'ali ya kalli suhailat yace " malama suhailat ko zaki iya fad'a mana dalilin da yasa kike so mijinki ya sauwak'e miki? "
suhailat tace " dalilan sunada yawa Allah ya taimake ka, kuma zama na da shi akwai cutarwa. "
kamal yai caraf ya cafke yace " k'arya take yi ranka ya dad'e. "
alk'ali ya dakawa kamal tsawa, yace waya baka izinin magana, karka k'ara sa bakin ka har sai na waiwayo kanka tukun."
alk'ali ya kalli suhailat yace " wad'anne irin dalilai ne, kuma wane irin cutarwa ne, kotu tana so ta sani? "
suhailat tace " Allah gafarta malam labarin yana da tsawo sosai "
Alk'ali yace " to malama suhailat kotu tana so tasan wanan labarin tunda munada isashen lokacin sauraro "
suhailat tace " to " sai ta fara basu labari.
TUSHEN LABARIN
ASALIN LABARIN
ABUBUWAN DA SUKA FARU A BAYA
_ku biyo ni domin jin farkon labarin._
urs autar marubuta da makaranta π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
Writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive_)
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to JANNART LAMEEDO
_Wanan page d'in sadaukarwa ne ga gwanata acikin gwanaye, jarumar jarumai, fitacciyar fitattu, wato JANNAT LAMEEDO, Allah ya k'aramaki lafiya da hazak'a da kwanciyar hankali._
~ZUMUNCHI~
_MU SADA ZUMUNCI DA WANDA YA YANKE TA DA MU, ABIN HAUSHI KUMA ABIN MAMAKI YANZU ZUMUNCI YA ZAMA TAMKAR GASA, ME KUDI DA DAN UWANSA ME KUDI KADAI YAKE YI,_
_TALAKA DA DAN'UWANSA TALAKA._
_ME KUDI YANA YIN ZUMUNCI DA DAN'UWANSA ME KUDI NE KAWAI SABODA WADANCAN RAGOWAR YAN'UWAN BASU DA SHI,_
_TALAKA YANA ZUMUNCI DA DAN'UWANSA TALAKA NE KADAI SABODA GUDUN WULAKANCIN YAN'UWANSA MASU KUDI,_
_TO JAMA'A MUJI TSORON ALLAH, MU SANI CEWA DA TALAKA DA MAI KUDI DUK ALLAH NE YA HALICCE SU, KUMA ME KUDI BEDA TABBAS DIN KASANCEWAR SHI ME ARZIKI HAR MUTUWA, HAKAMA TALAKA BEDA TABBAS ZAI DAWWAMA CIKIN TALAUCI HAR MUTUWA, MUJI TSORON ALLAH MU GYARA ZAMANTAKEWARMU DA YAN UWANMU._
~NAGODE~
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 40 to 45
Zainab ta kalli hadiza tace " meyafaru, kin sanshi ne ? "
hadiza tace " ni kuwa na sanshi, makarantar mu d'aya fa, kuma ya dad'e a makarantar be gama ba, saboda dak'ik'i ne yanada carry over's da yawa, dalilin da yasa har na tarar dashi a makarantar kenan, sanan yana neman mata sosai da shi da abokan shi, ni kaina akwai d'aya daga cikin abokan shi da yace yana sona, na amince masa, a ahankali sai ya fara fitomn da siffarsa, ba arzik'i nai mishi kaca kaca muka rabu. "
Zainab tai shiru na wasu lokuta, tunani take anya maganar da ta fad'i gaskiya ne kuwa, tunda kowa yasan halinta na had'a husuma irin haka, amma dai duk da haka zata sanar da ummie domin ayi bincike sosai akai.
zainab ta numfasa, sanan tace " gaskiya kin kyauta da kika fad'a mana halin shi, haka ake son mutum daman idan kaga d'an uwanka zai shiga halaka k'ok'ari kake kaga ka tsamo shi, nagode sosai k'awata. "
sun dad'e suna hira, sanan hadiza tai musu sallama ta tafi gida.
bayan hadiza ta tafi zainab ta je ta sami ummie a d'aki, ta kwashe duk abinda hadiza ta fad'a mata ta sanarwa ummie.
ummie ta kalli zainab tace " kin riga da kinsan halin hadiza sarai, tunda halinta ne ko gaskiya take fad'a ba lallai bane a gasgata ta. "
ashe duk maganar nan da suke a kunnen suhailat sukayi shi, domin kuwa tana lab'e taji komai, kuka ta fara yi tare da fara yin nadamar zab'en shi a matsayin mijin aure.
WANENE KAMAL?
Kamal d'a ne ga Alhj Aliyu, matan shi uku, mahaifiyar kamal mai suna fateema itace uwar gida, tana da yaya hud'u, kamal ne babba, sai mai bi mishi Hauwa'u, sai na ukunsu Abdurrahman, sai na hud'u shine umar.
sai matar shi ta biyu, mai suna Harira, yaranta biyu maza kuma k'anana ne.
sai matarshi ta uku mai suna haule, d'anta d'aya tak.
matar shi ta farko wato mahaifiyar kamal yanzu haka basa tare sun rabu, sakamakon husuma da take ta had'amai cikin gida, ta hana shi zaman lafiya da iyalin shi, ga kuma raba mai kan yaya da takeso ta yi.
Kamal duk shine babba acikin gidan, kuma shine tak'adiri baya jin magana magana ko kad'an.
karatu ne ya kai kamal kano, inda yake karantar hausa islamic, amma sam bashi da k'ok'ari, saboda baya maida hankali kan karatun nashi, kamar wani shed'an haka ya koma, ga k'arya, ga had'a fad'a sanan neman mata kawai yasa a gaba.
mahaifin kamal dattijon k'warai ne, yanada kirki sosai ga hak'uri, amma sam kamal be d'ebo halin shi ba, shi kad'ai ne ya fita zakka a cikin su.
matan gidan kwata kwata basajin dad'in zama dashi domin abune me sauk'i gunshi yai masu rashin mutunci sosai, har takai a yanzu suna mugun jin tsoron shi.
lokacin da kamal yazo wa da baban shi maganar aure yak'i amincewa sam saboda shi uban so yake kamal yai karatu, idan ya gama ya samu aiki se yai auren don yanzu haka beda sana'a kuma baya nema.
da kamal yaga baban shi yak'i amincewa da auren shi sai yaje gun kawun shi ya fad'a mishi, kawun nashi shi ya shige gaba akan maganar auren har ya bashi d'akuna biyu ya zauna acikin d'aya daga cikin gidajen shi da yake yin haya da su. wanan kenan
CIGABAN LABARIN
da daddare bayan Abba ya dawo suhailat taje d'akin shi tai mishi sannu da zuwa, sanan ta duk'ar dakai tai shiru, koda abban yaga haka sai ya kalleta yace " suhailat ya akai ? "
suhailat tace " Abba umm daman akan maganar," sai kuma tai shiru.
abba ya kalle ta yace " inajinki dama me?"
suhailat tace " abba kan maganar kamal ne, dan Allah a fasa auren nan wallahi bashi da ha…………
abba ne ya daka mata tsawa yace " baki da hankali ne, dan gidanku yau saura kwana uku biki zaki zomn da wanan maganar, so kike ki maida ni k'aramn mutum. "
cikin kuka suhailat tace " Abba kayi bincike kan halayen shi wallahi babu na d'auka aciki, kuma ba fasa auren za'ai ba, yaya mahmud nake so ka auramn.
abba ya kalleta cike da takaici yace " bana son mahmud domin bashi da tarbiya, baya girmama mahaifinki, kuma da ba ke kika kawo mahmud d'in ba, daga baya kika ce dashi bakya yi, kafin shi mutum nawa kika turomn kuma daga baya kika ce bakya son su, to kamal nake so ki aura domin bazaki maida ni k'aramn mutum ba, tashi ki fice ki bani wuri sakarya kawai. "
suhailat ta tashi ta bar d'akin, ta koma d'akin su tana ta kuka.
bayan ta fita ummie ta kalli abba dake ta faman huci, tace " abban suhailat ya kamata ka duba maganar yarinyar nan, ayi binciken, itafa ta zab'e shi, to tunda kaga yanzu tace ta fasa dan Allah ka d'aga bikin domin samun damar yin bincike akan shi. "
cikin b'acin rai abba ya kalleta yace " ok yanzu na fahimta, daman ke kike d'aure mata gindi kenan take wanan babbotsarewar, to ku sani cewa ko menene zakuyi baza a fasa wanan auren ba, " yana gama fad'in haka ya juya yai kwanciyar shi ranshi a b'ace. "
HATTARA IYAYE
_hattara iyaye, maganar gaskiya yana da kyau iyayenmu su rik'a zurfafa bincike kan mazan da yaran su suke aura, sanan iyayenmu su sani cewa mazan yanzu suna b'oye mugayen halayen su a lokacin da zasu auri mace, to shawara ta anan shine su rik'a sauraren yayansu a duk lokacin da suka tsinci wata magana daga waje akan mijin da zata aura, su dakatar da auren, sanan su tsananta bincike, ba k'aramin mutum za'a kiraku ba, ko da ce muku ake dattijan banza yafi a kiraku hakan, akan ku rik'a d'aukar yaranku masu daraja, wadanda kukai matukar shan wahala wajen tarbiyarsu ku bawa wad'anda basu san darajar d'an adam ba, basuma san miye auren ba, yaku iyayenmu kuyi tunani dakyau wasu mazan bayan sun auri yarku zasu gurb'ata tarbiyarta mekyau da kuka d'auki tsawon lokaci kuna ginawa, ya b'ata muku tarbiyar yara kuma daga k'arshe ya sako muku ita, ta dawo gabanku kuma kuita ganin canje canje daga tarbiyarta kuyi ta tunanin a ina ta samo miyagun hali haka._
_to ba fata ake ba amma idan hakan tar faru k'arshe wa gari ya waya?_
_dan girman Allah mu gyara, mudaina sa son zuciya, yaya amana ne a garemu, kuma ALLAH zai tambayemu amanar da ya bamu,_
_iyaye suna da iko akan idan sukai bincike akan mijin da yarsu zata aura suka ji mummunan ayyuka daga gare shi, suna da damar da zasu iya hanata auren shi, maganin ayi kar a fara, da muguwar rawa gwamma k'in tashi_
_ALLAH KA K'ARA SHIRYATAR DAMU, KA KARE DUKKANIN MUSULMI DA AUREN MAZA MASU MUGUN HALI KWATANKWACIN IRIN NA KAMAL, ALLAH KA BAWA IYAYENMU IKON YIN BINCIKE AKAN MAZAJEN DA ZAMU AURA ameen ya rabbi_ππ»
_muje zuwa dai_
URS π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusiv)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to ASIYA (SEE SEE)
TAIMAKO BABBAN MAKAMIN MUMINI NE NA HANYAR SHIGA ALJANNAH
_HANYOYIN SAMUN LADA SUNA DA YAWA, MU YAWAITA TAIMAKO, IDAN KAGA DAN UWANKA NA BUKATAR TAIMAKO TO KA TAIMAKA MISHI, DA TAIMAKO KADAI IN ALLAH YA SO YANA IYA ZAMA SILAR SHIGEWARKA ALJANNA, MU DAINA LA'AKARI DA WAI YANDA ZAMANI YA ZAMA NA MIYAGUN MUTANE, KAI DAI KA TSARKAKE ZUCIYARKA, DUK WANDA YAI NIYYAR NUFIN YIN ALKHAIRI ALLAH BAYA TABAR DA SHI._
~Allah kasa mu dace~
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 45 to 50
Babu yanda suhailat bata yi ba wajen ganin rashin faruwar wanan auren, amma sam abba yak'i ya saurareta.
k'arshe ma sai abba ya tara meeting, akan ko ta auri kamal ko kuma ya cire hannun shi daga kan maganar aurenta.
babu yanda ta iya, kuma a yanzu bata da wani zab'i da ya wuce ta hak'ura, domin kuwa gobe ne d'aurin aure.
washe garin ranar wadda ta kama ranar asabar, wajen k'arfe biyu, dubban mutane suka halarci d'aurin auren SUHAILAT ADAM, da KAMAL ALIYU akan sadaki dubu talatin.
bayan an gama d'aura aure angwaye suka ce " a fito da amarya su d'auki hanya.
tun daga wajen d'aukar amarya ango ya fara nunawa mutane halinsa, yace motoci hud'u ko biyar zai kawo sai suka ga mota d'aya, yayyin mahaifin suhailat kuwa suka ce " baza su fito da amarya ba se an k'aro musu mota."
nan da nan ango ya hassala, ya kalli abokan shi yace " dan Allah ku zo mu tafi, ku bar musu ita, su rik'e yar tasu. "
da yawa daga cikin abokan sukaita k'ara zuga shi yana k'ara hawa kamar biredi, biyu daga cikin abokan shi ne suka bashi shawara ta k'warai, suka ce " ya bari zasu kira abokan su da suke nan kano suzo su d'ebi wasu.
to ango dai ya rigada ya hassala, yace " wallahi bazai zauna ba sa same shi a gida, ya kama hanya yai tafiyar shi."
bayan an k'aro motoci wasu daga cikin yan iskan abokan nan nashi suka ce su k'awayen amarya kawai zasu d'iba aciki, yayyin mahaifin suhailat ne suka fito da kansu, suka bud'e motocin suka zuzzuba mutane aciki, sai da suka ga kowa ya samu waje har an fara yin gaba da mutane sanan suka fito da amarya aka sata cikin wata mota me d'an karen kyau, yayyin iyayenta uku suka shiga, sai manyan k'awayenta guda biyu, aka saki wak'ar aure ta nura m. inuwa, haka suka biyo hanya a jere gwanin ban sha'awa, har suka iso gidan.
har aka firfito, aka shiga cikin gidan, aka kaita d'akinta, amarya suhailat bata daina kukan rabuwa da iyaye ba.
gaskiya masha Allah d'akin amarya ya had'u, iyayenta sunyi matuk'ar k'ok'ari wajen had'amata kayan d'aki, da kayan kicin na gani na fada.
abokanan ango kowanne ya ja tashi budurwar, amma k'arshe baram baram aka rabu kowacce ta shige gida suka barsu anan k'ofar gida, saboda gaba d'ayansu yan iska ne, maganar iskanci kawai suke masu.
babban abun takaici ma da wani abokin ango ya tari yayar suhailat wato zainab da maganar iskanci, har yana ce mata tazo suje d'akin shi gayi can ba nisa, bazasu dad'e ba yanzu zasu dawo, kuma tasan shi sarai da shi akaita kai kawo a bikin, saboda yana d'aya daga cikin manyan abokan shi.
a lokacin sai da yasha kunya don saida zainab ta tara mai jama'a a wurin, saura kad'an aljanunta su tashi, aka shiga da ita gida, kuma aka hana kowace mace k'ara fita daga gidan, haka abokan angwaye suka juya ba tare da sun cimma k'azamin nufinsu ba.
tunda abin nan ya faru zainab take ta kuka tana tausaya wa yar uwarta, saboda ganin irin abokan da ango yake tare dasu, ta tabbatar shima yana d'aya daga cikinsu, nan da nan maganar da hadiza ta tab'a fad'a mata ta fad'o mata a rai, sai ta k'ara fashewa da kuka.
suhailat kowa yai bacci amma banda ita, daga ita sai yar mahaifiyarta inna wadda take ta nafilar dare, bayan ta idar ne ta jiyo sheshek'a da ta juyo ne taga suhailat ce dai har yanzu take kuka, bayan tayi addu'a ta shafa sai ta kalli inda suhailat take tace " suhailat "
suhailat tace " naam inna "
inna tace " taso ki zo nan "
suhailat ta tashi taje kusa da inna ta zauna.
inna ta kalle ta tace _" ya ke yata ki sani cewa da ana barin aure don jin dad'in gidan iyaye, da kinfi cancantar kada kiy aure, sedai hakan bazata tab'a yiwuwa ba, saboda mu mata an yi mu ne don maza, maza kuma dan mu mata._
_ya ke yata ki sani cewa yanzu kin bar gidan da aka haifeki kika taso kikai wayau a cikin shi, kika sava dashi, da mutanen gida wadanda kika saba dasu, zuwa wani gida na daban wanda baki sani ba, kuma baki saba da shi ba_
_da abokin zama wanda baki saba zama shimfida daya dashi ba,_
_to ki zamto tamkar baiwa a gare shi, zaki same shi tamkar bawa a gareki._
SABODA HAKA GA WASU NASIHOHI KADAN DAGA GARENI KIY AMFANI DA SU A ZAMAN AURENKI:
1. _kiyi zamantakewa da mijinki da wadatar zuci_
2. _ki girmama shi, kiyi mishi biyayya gwargwadon iko, matuk'ar ba sab'on Allah ya saki aikatawa ba._
3. _ki kula da dukiyar sa_
4. _ki rik'a gama abinci da wuri, domin jin yunwa yana tafasa zuciya_
5. _kada kiy farin ciki lokacin da yake cikin bacin rai, kuma kada ki bata rai a lokacin da yake cikin farin ciki_
6. _karki sake ki lek'a koda k'ofar gida, in har kika fita ba tare da izinin sa ba mala'iku zasuita tsine miki har kije inda zaki ki dawo._
7. _ki kyautatawa iyayensa, da yan uwansa_
8. _karki tashe shi a lokacin da yake bacci, domin yin hakan yana sa b'acin rai._
9. _ki zama me tsabta a koda yaushe, ki kula da tsabtar jikin ki da ta d'akin ki_
10. _a koda yaushe da safe karki bari ya rik'a rigaki tashi, ki rigashi tashi ki shek'a kwalliya ya zamto idan ya tashi ke zai fara gani a idon shi, hakan zaisa ki wuni a kwakwalwarsa, yaita Allah Allah ya dawo gida._
11. _karki bari ya rik'a dawowa yana ganinki a k'azance, kamar yanda zaki shek'a kwalliya in zai fita, haka zaki shek'a idan zai dawo._
daga k'arshe ina maki fatan Alkhairi, Allah ya sawa aurenku albarka, ya bada zuri'a d'ayyiba, tashi kije ki kwanta kuma bnso in sake jin kukanki.
suhailat ta tashi taje ta kwanta, bata dad'e da kwanciya ba bacci ya d'auke ta.
washe gari da safe aka aiko musu da abin kari, bayan sun karya kowacce tai shirin tafiya gida ana jiran ango.
suna ta jira shiru ba ango babu alamar shi, da aka kira wayar shi itama a kashe.
tofhaπ€
muje zuwa dai
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
Writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan Exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to UMMU KHADY
_Wanan page d'in naki ne ke kad'ai UMMU KHADY, ina gwanar wani, nidai ga tawaππ». hadari malafar duniya, an buga dake an barki, wa yace dake ba ke ba, nima ince dashi ba shi ba kuma in tsinka mai mari yasin, inasonki, kuma ina ji dake kamar yanda nake ji da lemun b'awoπππ_
_TUNATARWA_
_Duniya ba matabbata ba, rayuwa babu tabbas, shin me muka tanadarwa kanmu domin guzurin k'iyamar mu?, kada k'yale k'yalen duniya ya shagaltar damu, mutuwa bata k'wank'wasa k'ofa, kuma da tazo ko second baza'a k'ara maka ba, karmu manta mutuwa dole ne, shiga k'abari dole ne, tsallake sirad'i dole ne, hisabi ma dole ne, shin ka/kin shiryawa zuwan wanan ranar? mu gyara tsakaninmu da ALLAH domin samun sakamoko me kyau._
~NAGODE~
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 50 to 55
Duk inda ake tunani da sa ran ganin shi anje bayanan, har gidan iyayen shi anje an duba bayanan, gashi basu rik'o kud'in komawa ba saboda ango da kanshi yace " duk yawansu zaisa a maida su gida."
har k'arfe biyu babu ango ba alamar shi, hakan yasa masu kud'in mota sukai sallama da amarya suka d'auki hanya, wad'anda basu da shi kuma suka tsaya jiran zuwan ango.
shiru shiru har k'arfe shi 6 dai dai ba ango ba alamarsa, can kano da akaji shiru har yanzu basu dawo ba, sai aka kira wayar Aunty Aysha, tai musu bayanin ai har yanzu basu ga ango ba, yar babansu suhailat tace " to ku jira shi, tnda dare yayi be dawo ba ku kwana washe gari sai ku taho. "
bayan sun gama waya sai suka ji sallamar ango da abokan shi sun rako ango, da sallamar su suka shiga d'akin, mutanen da suka gani ne a zazzaune cikin d'akin kowacce ranta a bace yasa ango da abokan shi sukai turus suka ja suka tsatstsaya.
babu wanda ya kula su acikin yan d'akin, saboda ransu a b'ace yake, d'aya daga cikin tawagar ango ne yai k'arfin halin yi musu magana, yace " wai dama baku tafi ba, kuyi hak'uri dan Allah mun barku kuna ta jiranmu, wani uzuri ne ya tsaida mu, amma bari muje mu nemo motar da zata kai ku gida.
babu wanda ya kula su, har Angon da abokan sa suka juya suka fita.
sun dad'e da fita sanan suka dawo da wata bus me d'aukar mutum goma, suka ce " kowa ya firfito.
tashi sukai dukkansu dama sun gama shiryawa, suka fito suka shiga mota aka biya me mota kud'i, suka d'auki hanyar kano cikin daren nan.
bayan ango da amarya sun sallami kowa sai suka dawo cikin gidan, suka shiga d'akin amarya.
bayan sunyi barkwancin da akasan abokan angwaye sukan yi idan sun raka ango, sai suka tashi ba wani nasiha, da d'an tunatarwa sukai musu sallama, ango ya raka su ya dawo.
bayan ya dawo yazo kusa da amaryar tashi ya zauna, sanan ya jawo ledar kaji da suka shigo da ita, kamal ya kalli suhailat yace " Bismillah mu ci. "
suhailat ba musu ta sauko ta zauna, amma ta kasa sakewa ta ci, kad'an taci sanan ta sha lemo.
kamal ya kalle ta yace " har kin k'oshi ? "
cikin sanyin murya suhailat tace " Eh "
kamal be sake cewa komai ba, kuma be tashi daga kan kazar nan ba' sai da ya cinye tas.
suhailat taje tai wanka, sanan ta canja kaya, tasa kayan bacci, sanan ta je kan gado ta kwanta farkon gado ta rakub'e, gaban ta sai fad'uwa yake, tsoro duk ya kama ta.
kamal yana gama cin abinci ya wanke hannu ya sha ruwa, ya fad'a gado ba maganar sallar nafila, balle addu'ar da akeso ango ya yi.
yana hawa kan gadon ya fad'a mata kamar bunsuru babu wani yan wasanni na aure babu komai, da k'arfin shi kawai ya fad'a mata, tana ihu tana rok'on shi ya k'yaleta har da su zagi, amma duk be saurareta ba, k'arshe ma sai ya sa mata k'arfi.
bayan ya gama kuma ya k'ara, tana ihun tana sanar dashi ka jimn ciwo amma ina, bema sauraron ta, har ya gama a sume take shi bema sani ba.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to MAIMUNA ADAM
HADISI
_manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace ( duk wanda yai imani da Allah da ranar k'arshe, ya fad'i alkhairi, ko yai shiru.)_
TUNATARWA
_mu sani akwai mala'iku biyu a hannun damar mu, da na hagu, suna rubuta dukkan abinda muka aikata, khairan au sharran, basa boye komai komi k'ank'antarsa,_
_Ya Allah kasa aikin alkhairinmu ya rinjayi na sharriππ»_
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 55 to 60
Sai da ya dawo hayyacin sa sanan yaga aika aikar da yai mata, amma da yake burin shi ya cika, bai bi ta kanta ba, juyawa yai ya kama baccin shi.
Washe gari koda ta farka bata ga kamal ba, har ya fice daga gidan.
tayi tayi ta yunk'ura ta tashi, domin ta gyara kanta amma ta kasa, ko yaya tai motsi jikinta ciwo yake mata, ga wani irin matsanancin ciwo da rad'ad'i da k'asanta ke mata, kuka take ta yi kamar ranta zai fita.
A haka Auntyn ta zainab tazo ta tarda ita, ta kawo mata ragowar kayanta.
Da sallamarta ta shiga cikin d'akin, ba kowa a falon sai ta zauna a d'aya daga cikin kujerun d'akin.
sheshshek'ar kuka take ji daga cikin d'aki, ta tashi ta lek'a sai taga ashe ma mijin bayanan, gefen gado kuma suhailat ce kwance cikin mawuyacin hali tana ta kuka.
gaban zainab ne ya fad'i, da sauri ta k'arasa gun yar'uwar ta'ta, tambayarta zainab take meya faru take kuka.
suhailat ganin yar'uwar ta'ta yasa ta k'ara fashewa da kuka, dak'yar ta samu tai shiru.
zainab ce ta had'a mata ruwan zafi, sanan ta taimaka mata domin ta tashi taje tai wanka.
tana d'agota ta sake fashewa da kuka, cikin kukan tace " anty zainab gaba na zafi yakemn "
koda zainab ta duba wajen sai ta saki salati da sallallami, tace " ai dole kiji zafi suhailat, domin kuwa ya ji miki ciwo sosai, dole sai an miki d'inki, yanzu ki k'ok'arta in taimaka miki ki tashi muje kiy wanka, in ya shigo sai muje asibiti.
haka ta rik'eta suka je bayi ta taimaka mata ta gasa jikinta, tai wanka, sanan ta rik'ota suka dawo d'aki.
a falo zainab ta kwantar da ita kan doguwar kujera, ta shiga cikin d'aki ta cire zanin gadon kai da ya b'aci ta saka wani, wanda ya b'aci kuma ta fito dashi ta wanke shi tas ta shanya.
shiru kamal be dawo ba har k'arfe biyu,, gashi tana so ta koma gida, ga kuma halin da yar uwarta ke ciki, ba damar ta tafi ta barta cikin wanan halin.
wayarta ta d'auko ta kira kamal, ta fad'a mai gata a gidan shi, kuma tazo ta tarar suhailat ba lafiya, tana so ta kaita asibiti kafin ta koma gida.
kamal yace " Allah ya sauwak'e, yanzu ni bana kusa ne, amma ki kaita kawai in da kud'i a wajenki."
bayan sun gama magana da kamal a waya ta d'auko wa suhailat hijab ta saka, suna fitowa Allah ya taimake su wani me a daidai ta sahu ya shigo unguwar, ya ajiye pasinja, suka fad'a mai inda zasu, suka hau ya ja suka tafi.
bayan sun isa asibiti aka dubata doctor tace " gaskiya sai anyi mata d'inki, saboda ta k'aru da yawa, kuma a d'auki mataki akan wad'anda sukai mata wanan d'anyen aikin, dan bazai wuce yan unguwa ba, ta cigaba da sababi tana fad'in fyad'e a yanzu ya zama ruwan dare basa tsoron had'uwarsu da Allah."
zainab tace " ba fyad'e akai mata ba, mijinta ne yai mata haka."
doctor ta zaro ido tace " mijinta fa kika ce?"
zainab tace " wlh shine, amarya ce, shekaran jiya muka kawo ta."
doctor tace " tab, amma ko wanan mutumin jaki ne, ranar farko yaiwa matar shi hauka haka gata yarinya k'arama, doctor taita sababi, tana kuma jin tausayin yarinyar.
bayan an gama yi mata d'inki aka basu magunguna, sukai sallama da doctor, suka fito, suka tari adaidaita sahu, suka shiga sukai hanyar komawa gida.
bayan sun dawo gida zainab ta had'awa suhailat tea me kauri, ta bata ta sha sanan ta bata magani.
sai da ta jira kamal ya dawo, sanan tai matu sallama ta tafi.
…………
tun daga ranar suhailat ta fara jin tsoron shi, gashi baya fita ko'ina, a koda yaushe sedai yace mata " ta tashi su shiga daga ciki, hirar da ake tsakanin miji da mata shi sam babu a tsakanin su, ko yaushe shi kawai a shiga daga ciki.
sanan ya tsani kowane mahaluk'i yazo inda take, hatta yan uwanta da nashi, shidai ko yaushe kawai su kasance su biyu a d'aki, kuma muddin su biyu ne zai ce mata a tashi a shiga daga ciki.
gashi duk idan zai kusanceta se yai mugun yi mata rauni, abin ya fara damunta, duk ta rame, ko yaushe cikin zullumi take da fargaba, idan ya fita taita farin ciki, da taji muryar shi sai taji gabanta ya fad'i.
_wlh bnda lfy ne kuyi hkr da wanan._
muje zuwa
URS BKππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to JIDDA SAMUSA
MY MEELATπ
_gaisuwar ban girma a gareki da jinjinar k'asaita_
_gaisuwa wadda bata k'arewa har sai rai ya yi halinsa,_
_sannu baiwar Allah, Allah ya kara miki lafiya me dorewa. AMEEN YA ALLAHππ»_
LIKES ANDS COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 60 to 65
Abubuwa da dama sunata faruwa, bayan suhailat ta samu ciki sai halin kamal ya k'ara canjawa, idan yasa k'afa ya fita sai cikin dare zai dawo gida, wata rana ma baya kwana acikin gidan.
kafin ya aureta yai mata k'arya akan yana aiki, amma tunda ta aure shi bata taba ganin ya fita gun aiki ba, daga zaman majalisa sai gida.
maganar cigaba da karatunta ma da yai alk'awari a gaban iyayenta duk tabi iska, tayi mishi maganar islamiyya ma har ta gaji.
Abu kad'an zatai mishi ya rufeta da duka, idan tai girki baya ci, gaba d'aya ma kamar k'yank'yaminta yake, abincin da zata ci ma auna mata yake.
kullum idan tai bak'i sai sunyi k'orafi akan ramar da tayi.
kwatsam wata ranar asabar suhailat tayi bak'i, kuma ba kowa bane bak'in illah yayyinta su aunty maryam da aunty Aysha, kuma gashi kamal tun safe da ya fita har yanzu bai dawo ba.
kawai sai ta auni shinkafa dai dai yanda zai ishe su, ta dafa jelop rice suka ci.
sun fara cin abincin kenan sai gashi ya shigo, yana ganin su ya kama fara'a kamar faske, ya zauna suka gaisa sanan ya wuce cikin d'aki.
bayan sun gama cin abincin ya fito ya zauna aka hau hirar duniya tare da shi, k'arfe hudu dai dai suka shirya suka fito, kamal ne ya tarar musu me adaidaita, kuma shi ya biya kud'in, sukai mishi godiya, sanan suka hau suka tafi.
yana komawa cikin gidan tun daga k'ofar gida ya fara kwad'a mata kira, suhailat! suhailat!!,
suhailat dake cikin d'aki ta fito tsakar gidan jikinta na rawa, tazo kusa da shi ta tsugunna tace " gani ya'ya "
kamal ya d'aga hannu ya watsa mata mari har sau uku, ji kake tass tass tass, ya hau k'wallo da ita, yana dukanta da k'afa da hannu, wani wawan naushi ya kai mata a cikinta, wani razanannen k'ara ta saki, sanan ta fad'i k'asa sumammiya.
magana ya fara yi, yana nunata da yatsa, tana a sumen yace " wato kin fara karyamn dokokin dana shimfida miki ko, to mu zuba, yana gama fad'in haka ya tsallaketa ya wuce.
_kamal haka yake, idan a gaban iyayenta da yan uwanta ne, in dai a gaban wani nata ne, koda kuwa k'awayenta ne to baya tab'a cutar da ita a gaban su, ko fuska baya canja mata, sai bayan sun tafi._
hakan yasa ake yabon shi, kowa gani yake yana kyautata mata sosai, sanan ko yai mata laifi idan ta kai k'ara ba'a goyon bayanta.
wata mak'wabciyar su ce me suna maimuna ta shigo gidan, ta tarar da ita cikin wanan halin, ga jini yana ta gangarowa ta k'afafunta, da gudu ta koma gida ta sanar da mahaifiyarta, salati uwar ta saka, sanan ta zari mayafinta suka yi gidan su suhailat d'in.
mahaifiyar maimuna duk ta rud'e, saboda ganin halin da suhailat ke ciki.
a rud'e ta kalli maimuna tace " maza kiramn me adaidaita sahu "
maimuna tace " to " sanan ta juya da sauri tai hanyar waje.
mahaifiyar maimuna ta kasa komai sedai takai ta kawo, can sai dabarar shafa mata ruwan sanyi ya zo mata a rai, da sauri ta d'ebo ruwa ta shafa mata, ba'a dad'e ba kuwa ta farfad'o.
godita tai ga Allah, ta gyarata tsaf, ta canja mata kaya, a dai dai maimuna ta dawo, tace "umma na samo napep d'in gayi can a waje, "
umman maimuna tace " to zo ki kamata mu fita da ita."
suka fito da ita, suka sata cikin napep d'in, me a dai dai ta yace " hajiya ina muka nufa? "
umman maimuna tace " asibiti zaka kaimu wanda be da nisa, kuma me sauk'in kud'i dan Allah. "
me napep yace " angama hajiya, " sanan yaja suka tafi.
suna zuwa Allah ya taimake su aka karb'eta, bayan doctor ya duddubata ya tabbatar musu da cikinta na wata uku ya b'are, sanan ya kalli umma yace musu, munyi k'ok'arin tsaida zubar jinin, sanan akwai magunguna da allurai da za'ai mata, ki biyoni office yanzu ki karb'a a siyo.
umma ta kalli doctor tace " to doctor ai mana total d'in kud'in dubata da akai, " doctor yai mata total gaba d'aya zasu biya dubu biyu duk da magunguna, tace "to ai mata hak'uri zata je gida ta d'auko kud'in ta dawo."
doctor yace " ba matsala," umma ta bar maimuna a gunta ta tafi gida d'auko kud'i.
bayan ta dawo ta biya su kud'in su, sai wajen k'arfe takwas na dare sanan aka sallame su suka taho gida.
anyi anyi ta shiga gidan nata tak'i shiga, k'arshe ma sai ta durk'ushe a k'asa ta saka musu kuka.
suhailat cikin kuka tace " umma dan Allah ki dubi girman Allah ki barni na kwana a gidanki, washe gari sai in tafi kano, wallahi kamal kashe ni yake son yi, sai ta sake fashewa da kuka.
umma itama k'wallah har ta taru daga idonta, ta kalli suhailat tace " suhailat ki rufamn asiri da tijarar mijinki, kiyi hak'uri ki shiga gidan ki kwanta, washe gari ni zan baki kud'in mota sai ki tafi gida. "
da haka ta samu ta lallab'ata ta shiga gidan, sanan sukaje gidan su suka d'auko mata abinci ta ci, umma ta bata magungunanta ta sha, sanan sukai mata sai da safe, suka tafi nasu gidan.
umman su maimuna mak'wabciyar su suhailat ce, daga gidansu suhailat sai nasu, tunda aka kawota umma ta shigo tai mata nasiha taji tana k'aunar tsohuwar, kuma ta d'auketa tamkar mahaifiyarta, maimuna kusan sa'ar suhailat ce, hakan yasa suka zama k'awaye.
washe gari, da safe bayan kamal ya fita suhailat ta shirya, ta fito ta shiga gidan umma, bayan sun gaisa umma ta bata kud'in mota sanan suka rakota har tasha, basu dawo ba sai da suka ga tashin motar su.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to KHADY FRESH
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 65 to 70
suhailat da sallamarta ta shiga cikin gidan su, mahaifiyarta dake tsakar gida tana yan kaye kaye ne ta tsaida abinda take tare da amsa mata sallamar.
ummie ta kalli suhailat tace " suhailat lafiya kuwa? "
suhailat tace " ba lafiya ba ummie," sai kuma ta fashe da kuka.
ummie tace " kinga shiga d'aki gani nan zuwa "
suhailat ta shiga d'aki, ta zauna kan kujera sanan ta cigaba da rera kukan ta.
ummie ce ta shigo d'akin itama, ta zauna kusa da kujerar da suhailat ta zauna, ummie ta kalli suhailat tace " kiyi shiru mana kiymn bayanin abinda ke faruwa."
suhailat ta tsagaita da kukan, sanan ta fayyacewa ummie dukkan abinda ke faruwa, da irin zaman k'uncin da take a gidan kamal.
ummie tai shiru, can sai tace " to kiyi hak'uri suhailat, bari abbanki ya dawo muji hukuncin da zai yanke. "
bayan abba ya dawo ummie ta kawo mai abinci, yana ci suna hira.
suhailat ce ta shigo falon da sallama, suka amsa mata dukkans, abba cikin fara'a yace " a'ah suhailat yaushe kika zo?"
cikin sanyin murya tace " abba d'azu da safe nazo," bayan sun gama gaisawa sanan ta tashi ta bar d'akin, abba ne ya bita da ido har ta fita daga cikin d'akin.
abba ya kalli ummie yace maman suhailat wai meke damun yar taki ne, naga duk ta rame kamar ba ita ba, kuma tayi sanyi sosai ? "
ummie ta gyara zama, sanan ta kwashe duk abinda suhailat ta fad'a mata, ta sanar da shi.
abba yai shiru yana nazarin abun, can sai ya numfasa, sanan yace " naji abinda ita suhailat d'in tace, amma ban gasgata ba, dan nasan kamal bazai yi mana haka ba, amma ina nan ina jiran zuwan shi, domin inji ta bakin shi.
suna cikin maganar sai wayar abba tai k'ara, ya d'auko wayar ya duba yaga waye ke kiran shi, sai ya d'ago ya kalli ummie yace " kinga d'an halak, kamal ne ya kira, sai ya d'aga wayar sanan ya kara a kunnensa tare da yin sallama.
bayan sun gaisa sanan kamal yace " abba dama tambaya zanyi ko suhailat tazo nan ? "
Abba yace " eh tazo,"
kamal yace " to insha Allah gobe zan zo,"
abba yace "Allah ya kaimu", sukai sallama sanan abba ya kalli ummie, yace " kinga magana ta ta fara fitowa ko, be ma san ta fito ba. "
washe gari kuwa sai ga kamal ya buga uban sammako, domin lokacin da yazo ko abba ma be fita gun aiki ba.
bayan an gaggaisa sai kamal yace " abba naje yo cefane kawai ina dawowa sai na tarar da k'ofar d'akin a rufe, hankalina ya tashi, duk inda nasan zan ganta na duba, naita nemanta amma ban ganta ba, shine na yanke shawarar na kira ka inji ko ta taho nan.
abba yace " tana nan, amma ka fad'amn gaskiya me ya had'a ku da suhailat ? "
kamal yace " wallahi tallahi abba babu abinda ya had'amu, lafiya lau muka rabu na fita yo cefane, duk da naga kamar ranta a b'ace yake. "
abba ya kalli ummie yace " kiramn suhailat "
ummie ta tashi taje ta kira suhailat, suka dawo tare.
abba ya kalli suhailat yace " suhailat meke faruwa ne tsakaninki da mijinki ? "
suhailat ta fad'awa mahaifinta duk abinda kamal ke mata, kamar yanda ta sanarwa ummienta.
abba ya dubi kamal yace " kamal kaji abinda suhailat tace, hakane abinda ta fad'a ? "
kamal yai murmushi sanan yace " a'a abba, wallahi ba haka bane, taya za'ai ku d'au amana ku bani in yi mata irin wanan rik'on, nidai nasan abu d'aya ke had'amu fad'a."
abba yace " ehen inajinka "
kamal ya b'ata fuska kamar me shirin yin kuka, sanan yace " abba k'arfina da na yanzu da da ba d'aya bane, to amma duk da haka ina iya k'ok'arina gun faranta ran suhailat, amma sam bata gani, gashi taita kawomn buk'atun ta, duk ina k'ok'arin naga nayi mata, amma duk ranar da bani da shi banyi ba sai tayi ta yimn gori, har tana cewa tayi nadamar aurena, da ta sani mahmud ta zab'a a matsayin miji, tasan shi ko me tace bazai k'i yi mata ba, to irin hakan ne ke had'amu fad'a banajin dad'in furucinta a kaina sam abba, sai hawaye shaaaaa kamar gaske. "
Abba da umma suka rufe suhailat da fad'a, sam sunk'i barinta ta yi magana, bayan sun gama fad'an kuma abba ya umurceta da ta tashi ta bi mijinta.
suhailat da ke zaune a gefe zuciyarta na matuk'ar zafi saboda jin irin k'azafin da bawan Allahn nan ya shirya mata, tasan babu me fitar da ita sai Allah, take taji tsanar shi ta sake kama zuciyarta.
tashi tayi ta nufi inda abbanta ke zaune, ta durk'usa a gaban shi sanan tace " abba dan girman Allah ku saurare ni, wallahi duk abinda ya fad'a ba gaskiya bane, abinda na fad'a muku shine gaskiyar, wallahi abba na tsane shi bana k'aunar shi, dan Allah ku rabani da shi kar wataran a kawo muku gawata ya kashe ni," tana kaiwa nan a zancenta ta sake fashewa da kuka.
abba ya sassauta fad'an shi, ya koma yi muta nasiha, sanan ya juya kan kamal d'in shima yai mishi nasiha, sanan daga k'arshe yace ta tashi ta ta shirya ta bi mijinta.
CIGABAN LABARIN
cikin kuka Suhailat ta kalli alk'ali tace " haka na cigaba da hak'urin zama da shi, idan abun yai k'amari duk sanda naje gida na fad'awa iyayena basa goyon bayana, saboda irin k'aryar da yake zuwa ya sharata ko waye ya ji dole ya yarda, haka zasu koroni mu dawo tare, shi kuma da na koma sai ya cigaba daga inda ya tsaya, memakon sauk'i sai abu ya cigaba, ya koma kwana a waje, dama kuma na dad'e da sanin yana bin mata, a gabana kuwa sai ya shafe rabin awa yana hira da yan mata a waya, kuma ya kwashe kayana ya siyar har da fanka ta, da tukwane na, da abubuwana masu amfani duk ya siyar, ahaka dai muka ci gaba da zama da shi har Allah ya sake bani ciki.
nan dai ta cigaba da bawa kotu labarin rayuwarta har zuwa lokacin da yan uwanta suka je gidan su kamal d'in ya gwada musu halin shi suka gani, da dalilin zuwansu kotu.
Alk'ali ya duk'a yai rubutu, sanan ya d'ago ya kalli kamal yace " kaji abinda suhailat tace, gaskiya ne duk abinda ta fad'a ? "
kamal ya kalli alk'ali yace " eh naji abinda ta fad'a yallab'ai, wasu gaskiya ta fad'a amma sauran duk k'aryane ni ban cutar da ita, amma tabbas na saida wasu kayan ta shima rashi ne ya jawo hakan, amma ina mai bata hak'uri, kuma dan Allah ina neman sulhu. "
alk'ali ya k'ara duk'awa yai rubutu sanan ya d'ago ya kalli suhailat yace " kinji abinda mijin ki yace, kin yarda da abinda ya fad'a ? "
suhailat tace " a'a ranka ya dad'e, ni bana k'aunar shi, kawai a rabamu. "
Alk'ali yai rubutu sanan ya d'ago yace " na baku dama kuje ku sasanta kanku, ya juya kan kamal yace kaje ka nemi sulhu gun matarka, idan hakan bai yiwu ba nan da sati to ku dawo a yanke hukunci.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Dedicated to JAMEESHA
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 70 to 75
bayan an gama shari'a kowa ya firfito, suhailat sun tsaya suna magana da lauyanta, tana yi mai bayanan da ya kamata, bayan sun gama magana sai suka fito zasu tafi gida, kamal suka gani shi da abokin shi, basu tafi ba ashe.
sun zo daf da su zasu fita daga gate d'in suka sake kwashewa da dariya har da tafawa shi da abokin shi, kamal yace " ka barsu zasu gane kuren su, an fad'a musu shari'a gidan wasa ne. "
su dai su suhailat basu ce komai ba, aunty zainab ta d'auki takwararta zainab suka wuce suka fita daga kotun, suna fitowa suka tari abun hawa, suka hau suka tafi gida, batare da sun sake ko waiwayen kotun ba.
washe gari wajen k'arfe goma na safe, sai ga kamal a kano ya zo neman sulhu, kamar yanda aka umurce shi.
yai sallama ya shiga cikin gidan, ummie ta amsa mishi sallamar shi da fara'arta, kamar babu wani abu na b'acin rai a tsakanin su.
bayan sun gaisa da ummie, sai ta tashi taje d'akin su zainab, ta turo mishi da suhailat.
suhailat ce ta shigo d'akin ummie, inda kamal ke zaune, bayan sun gaisa sai kamal yace " my wife nazo biko ne, kiyi hak'uri, ki koma d'akin ki. "
suhailat ta d'ago da kanta, ta kalli kamal tace " kaima kayi hak'uri bazan iya cigaba da zama da kai ba," tana gama fad'in haka ta mik'e tsaye, sanan tace " ka gaida gida," ta juya zata fita daga d'akin.
taje dai-dai bakin k'ofa kamal ya k'wala mata kira, tsayawa tayi cak ba tare da ta waigo ba, kamal yace " to ki sani ni dai bazan tab'a sakin ki ba, se dai kiyta zama da aure na a kanki. "
suhailat bata tanka mishi ba, ta fice daga d'akin.
shima kamal fitowa yai daga d'akin, sukai sallama da ummie, sanan ya tafi.
da sati ya zagayo sukaje kotu, aka k'ara bashi damar ya sake zuwa ya nemi sulhu, a tak'aice dai sai da alk'ali yace yaje bikon matar shi har sau uku, yaje sau biyu amma na k'arshen da akace ya sake zuwa bai je ba.
kuma tun daga lokacin kamal bai sake halartar kotun ba, har akai zama wajen sau uku duk kamal bai zo ba, be kuma turo dalili ko wakili ba, kuma a zaman da akai sau ukun nan an aika mishi da sammaci again har sau uku amma bai zo ba.
a yau ne zama na hud'u, bayan an saurari wasu k'ararraki na mutum biyu, sai akazo kan su suhailat.
bayan an karanto k'arar sai alk'ali yace " ina suhailat ? "
suhailat tace " gani nan ya me shari'a," sai ta taso tazo gaban kotu ta tsaya. "
alk'ali ya sake cewa " ina kamal ? "
lauyan shi ne ya mik'e yace " ranka ya dad'e yauma be zo ba, ayi mishi afuwa, k'ila akwai uzuri me k'arfi da ya rik'e shi. "
Alk'ali ya duk'a yai rubutu a takarda sanan ya d'ago yace " ina masinja ? "
masinja ya taso tare da fad'in " gani nan ranka ya dad'e "
alk'ali ya mik'awa masinja takarda, sanan yace " gobe in Allah ya kaimu ka d'auki yan sanda guda biyu, kuje katsina ku taho da kamal. "
masinja ya karb'i takardar cike da rissinawa, sanan ya juya ya tafi.
alk'ali ya juyo da kallon shi gun mutanen kotun, yace " wanan kotun ta d'aga sauraren wanan k'arar, zuwa gobe da misalin k'arfe goma, Alk'ali ya buga gudumarsa kowa ya watse.
washe gari ta kama ranar talata kenan, misalin k'arfe goma kowa ya halarci kotun, alk'ali ma yazo, kuma a dai-dai lokacin masinja da yan sanda suka danno kai cikin kotun, rik'e da kamal.
shigo da shi sukai suka sa shi a bayan kanta, sanan alk'ali ya kira suhailat, itama ta fito ta tsaya a gaban kotun.
alk'ali ya kalli kamal yace " kamal menene dalilinka na k'in zuwa kotu a zaman da kotu tayi na baya ? "
kamal ya fara inda-inda, alk'ali yace " kamal kai muke saurare, kotu tana son jin dalilinka na yin hakan. "
muryar shi na rawa yace " ayi hak'uri yallab'ai ban lahiya ne. "
Alk'ali yace " ka kiyaye, idan ka sake yin irin haka to kotu zata hukunta ka. "
alk'ali ya kalli kamal yace " kaje bikon matarka suhailat ? "
kamal yace " eh, naje. "
alk'ali ya juya b'angaren suhailat yace " malama suhailat, hakane mijinki yazo biko wajenki ? "
suhailat tace " eh, yaje ranka ya dad'e. "
alk'ali yace " sau nawa kamal yaje ? "
suhailat tace " sau biyu yaje. "
alk'ali ya duk'a ya d'an yi rubutu a takarda, sanan ya d'ago kai ya kalli suhailat, yace kun samu dai-daito a tsakanin ku ? "
suhailat tace " a'a, bamu samu ba ranka ya dad'e, na fad'a mishi yanzu bana k'aunar shi, ina rok'on kotu da ta raba auren mu. "
alk'ali ya kalli kamal yace " malam kamal da kaje biko me suhailat tace maka ? "
kamal yace " cewa tai bata k'aunata, a yanzu rabuwar mu shi yafi, dana sake komawa ma haka ta sake fad'amn. "
alk'ali yace " to tunda tace bata k'aunarka ka sauwak'e mata. "
kamal yace " to ta biyani dukkanin kud'in da na kashe wurin aurenta. "
alk'ali ya juya gun suhailat yace " suhailat kinji abinda kamal yace, kin amince zaki biya shi sadakin shi ? "
suhailat ta d'ago kai ta kalli mahaifinta, aka taki sa'a shima mahaifin nata ita yake kallo, sai ya d'aga mata kai alamun ta amince da hakan.
suhailat tace " eh na amince zan biya ya me girma me shari'a. "
alk'ali ya kalli kamal yace " nawa ne sadakin naka ? "
kamal yace " dubu talatin ne. "
alk'ali ya duk'a yai rubutu sanan ya d'ago kai yace " suhailat kotu ta baki sati d'aya ki kawo kud'in sadaki dubu talatin, sanan kai kuma kamal ka tabbatar sati me zuwa ka halarci kotu tare da kud'in kayan suhailat daka kwashe ka siyar wanda akai lissafi zasu kai dubu ashirin," alk'ali yana gama fad'in haka ya buga guduma, kowa ya watse.
muje zuwa dai
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to MAMAN KHAIRAT
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 75 to 80
BAYAN SATI DAYA
Yau litinin, kuma a yau ne za'a koma kotu, kuma ga dukkan alamu shine zama na k'arshe.
kamar kullum yau ma kotun ta cika mak'il, domin kowa yana so ya ji k'arshen yanda wanan shari'ar zata kasance.
kowa ka gani a cikin kotun tattaunawa suke akan shari'ar Suhailat da Kamal.
lokaci d'aya kuma kotun tai tsit, kamar babu mutane a cikinta, ko da na juyo domin inga menene ya natsar da kotun haka, sai naga ashe me gayya me aiki ne ya shigo, wato Alk'ali, take anan nima na natsu domin jin yadda za'a k'are wanan shari'a.
bayan Alk'ali ya zauna, sanan kowa ma ya zauna.
Alk'ali ya d'ago ya kalli inda Suhailat ke tsaye, yace " malama Suhailat kin kawo kud'in sadakin da kotu tace ki kawo ? "
Suhailat ta kalli Alk'ali sanan tace " eh' ya mai girma me shari'a, na taho da shi, gasu ma. "
Suhailat taje ta mik'awa Alk'ali kud'in, sanan ta dawo inda take ta tsaya.
Alk'ali ya irga kud'i naira dubu talatin cif, sai Alk'ali ya kalli Kamal, yace " Malam Kamal ka taho da kud'in kayan Suhailat da kotu tace ka kawo ? "
Kamal yace " a'a ranka ya dad'e, wallahi banda kud'i. "
Alk'ali ya k'irga kud'in nan na sadaki, ya cire dubu ashirin ya ajiye gefe guda, sanan ya kalli Kamal yace " tunda baka da kud'i an cire mata kud'in kayanta dubu ashirin a cikin na sadakinka, kaga kanada ragowar dubu goma kenan, duk kuzo ku karb'a. "
Alk'ali ya fara kiran Kamal ya karb'i dubu goma, sanan aka kira Suhailat itama ta karb'i kud'in kayanta dubu ashirin.
Alk'ali ya rubuta takardar shaidar sakin Suhailat, sanan yasa hannu, itama Suhailat aka kirata tasa hannu, sanan Kamal shima yasa hannu.
Alk'ali ya kira Suhailat ya bata takardar sakin, ta karb'a hannu bibbiyu tare da yiwa Alk'ali godiya.
bayan Alk'ali ya d'an yi rubutu, sanan ya d'ago kai yace " Malam Kamal yau kotu ta raba aurenka da Suhailat, sanan daga yau babu wani abu da zai k'ara had'aku face zuwa ganin yarka, kuma idan muka samu labarin ka cigaba da tayar musu da hankali jami'an tsaro zasu hukunta ka. "
Kamal yace " yallabai ina son in karb'i ya' ta. "
Alk'ali yace " yanzu shekararta d'aya, kotu bata amince da buk'atarka ba a yanzu, ko zaka karb'eta sai tayi wayau sosai ta girma, kamar nan da shekara goma sha biyar, amma zaka iya zuwa kana ganinta, nan muka kawo k'arshen wanan shari'ar, " Alk'ali ya bubbuga guduma kowa ya watse.
Kamal kuwa takaici duk ya bi ya ishe shi, bai tab'a tunanin k'arshen shari'ar nan haka zai kasance a gare shi ba, be yi tunanin mahaifin Suhailat zai biya sadakin ba, sanan be tab'a tunanin zabtare kud'in sadakin za'ai haka a bata ba, ya kama yatsan shi guda d'aya ya ciza, yana takaicin ya yi biyu babu, babu matar babu kud'in.
yanzu dai an gama shari'a, hankalin kowa ya kwanta musamman ma suhailat, ta cigaba da harkokinta, da kuma kula da diyarta zainab.
BAYAN YAN WATANNI DA RABUWARSU
Kamal ne zaune shi da abokin shi gaban wani malami me suna malam tanimu, bayan sun gaisa da malam sai kamal ya kalli malam ko kuma kai tsaye ince boka, yace " malam kamat yanda na sanar dakai tun a waya cewa mun rabu da mata ta, to dalilin zuwanmu kenan. "
kamal ya numfasa, sanan ya cigaba da cewa " kamar yanda ka taimakamn a farko ka karkatomn hankalinta ta dawo gareni, haka ma yanzu nakeso ka taimakamn ta dawo. "
boka ya kalli kamal yace " yanzu me kakeso ai mata ? "
kamal yace " so nake a sa mata tunani na da yawa, taji kawai so take ta dawo guna, sanan nasan wanan saurayin nata mahmud nasan yanzu ya samu labari akan mun rabu, zai iya komawa gareta, to dan Allah malam ko yaje a hanata sauraron shi. "
malam au boka yace " to ba matsala in dai wanan ne, zaka kawo bak'ar kaza, zanyi maka aiki insha Allah nan da kwana biyu zaka ga biyan buk'ata. "
kamal ya ciro kud'i kimanin dubu goma ya bawa malam yace " gashi nan a siya abinda ake buk'ata, sauran kuma kud'in aikinka. "
malam ya washe baki, tare da yi musu godiya, kamal da abokinsa sukaiwa malam godiya suka tafi.
HATTARA
_irin wad'anan malaman kai tsaye bokaye za'a kirasu, kuma zuwa gurinsu shirka ce, kiransu malamai kuskure ne, mun sani cewa babu wani wanda yake yi sai Allah, kuma gare shi kad'ai ake neman taimako, muyi k'ok'ari mu rik'a banbance bokaye da malamai domin gujewa fad'awa ga halaka, duk wanda yaje gun boka muddin be tuba ba har ya mutu to wuta ce makomarsa, Allah yana yafe kowane irin laifi banda abu biyu,_
1. _laifin da kaiwa bawansa, dole sai shi bawan ya yafe._
2. _ka mutu kana shirka, kana had'a Allah da wani, wa'iyazubillah_
_ya Allah ka hanemu da sab'a maka, kasa mu mutu muna bauta maka kai d'aya._
a hankali - a hankali sai yanayin suhailat ya fara komawa daga me dad'i zuwa mara dad'i, ko yaushe bata da wani aiki sai tunani, wasu lokutan ma har kuka take, kuma tambayar duniya idan akai mata cewa take babu komai.
akwai wata rana tana zaune tana aikin da ta saba wato tunani had'e da kuka, sai ga bab ar yaya Aunty aysha tazo, tambayar duniya tai mata amma tace bakomai, sai da taga tayi fushi da ita har ta tashi zata bata waje sanan ta jawo hannunta tana bata hak'uri.
Aunty aysha ta koma kusa da suhailat ta zauna, sanan ta kalleta tace " to fad'amn meke damunki ? "
suhailat cikin kuka tace " wallahi nima bansan meke damuna ba, haka kawai naji inata tunanin kamal, shine idan tunanin yaimn yawa nake kuka, amma aunty dan Allah karki fad'awa su ummie. "
Aunty aysha tace " ai wanan maganar ba ta k'yalewa bace, dole sai sun sani, amma inaso in baki shawara, a maimakon kukan nan da kike yawan yi ki yawaita nafila ne kina kai kukanki wajen Allah, kuma kiyi istihara akan wanan lamarin koma menene Allah zai bayyana mana, bari naje naiwa su ummie bayani. "
suhailat dai bata ce komai ba har aunty aysha ta tashi ta fita daga d'akin, ta shige sashen ummien su.
_naso in bita amma bazan iya tashi ba saboda jikina ba dad'i, mu jira har ta fito, idan ta fito sai na sanar muku abinda suka tattauna_π€π
muje zuwa
urs π ±K
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to MAREEYA
_Ina Rokon Allah Ubangiji Ya Amintar Da Ruhinmu, Ya Tsarkake Zuciyarmu, Ya Haskaka Tunaninmu, Ya Kawar Da Damuwarmu, Ya Yafe Zunubanmu, Ya Karbi Ibadarmu, Ya Kyautata Karshenmu,ya haskaka kabarinmu, Allah Yasa Aljannace Makomarmu da iyalanmu, Amin._
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 80 to 85
Aunty Aysha tana shiga d'akin ummie ta zayyana mata duk yanda sukai da suhailat, sanan aysha ta cigaba da cewa " ummie sai an dage da yiwa suhailat addu'a, dan ni ina zargin wani abu game da ita. "
Ummie tace " Allah ya kyauta, bari yayanta ustaz Habib ya shigo. "
Bayan ustaz ya dawo gida ummie ta sanar da shi halin da yar' uwarsa take ciki, habib yace " ta dage da addu'a kuma tai istihara nima a bani kwana biyu zanyi istiharar, abinda yasa nace itama tayi shine, anfi so idan abu ya sami bawa to ya dage da addu'a da kanshi, in yaso kana yin addu'ar ana tayaka hakan ba laifi bane, babu abnda yafi k'arfin Allah. "
BAYAN KWANA BIYU
Falon gidan malam adam cike yake da mutane, sedai kowa ka gani fuskar shi cike take da damuwa, saboda halinda suhailat take ciki.
Bayan kowa ya natsu sai abba ya kalli habib yace " ustaz kai muke sauraro. "
Ustaz habib ya gyara zama sanan ya kalli suhailat yace " kinyi istiharar da nafil'filin da nace kiyi ? "
Suhailat tace " eh nayi. "
Ya'ya habib ya sake cewa " to yanzu ya kike ji ? "
Suhailat tace " tunanin shi ya ragu, sai kuma mafarki da na yi akan shi."
Ustaz habib yace " wane irin mafarki kikai ? "
Suhailat tace " nayi mafarki ina kwance ina bacci, kamal yazo kaina yana barbad'a mun wani abu a jikina, kuma yana kiran sunana a hankali, yana cikin yin hakan na farka daga bacci, da farko tsoro ya hanani komawa baccin ma, amma daga baya se nai addu'a na koma na kwanta. "
Ustaz habib yace " to Alhamdulillah!, kamar yanda tayi istiharar nima nayi, maganar gaskiya kamal be bar suhailat haka ba, amma kuma a duniya kaf babu abinda yafi k'arfin addu'a,
istiharar nan tana da matuk'ar amfani, duk wani abu da ya shige maka duhu a rayuwa, ko kuma kake kokwanto akansa, to kayi istihara Allah zai bayyana maka gaskiyar abinda ke tattare da kowane irin lamari,
Idan abinda mutum yake so ne yai istihara akai domin neman zabin Allah, to idan Alkhairi ne Allah zai nunka maka k'aunar abin acikin ranka, ko kuma Allah ya nuna maka a mafarki,
Hakama duk abinda kake k'i, ko kuma kokwanto akai, muddin kayi istihara idan ba alkhairi bane, Allah zai k'ara maka k'in abin acikin zuciyarka, idan kuma alkhairi ne Allah zai musanya k'iyayyar da kakewa abin da soyayya, Allah kasa mu dace. "
kowa na d'akin ya amsa da " ameen "
Ustaz ya kalli abban su yace " abba zamu dage da addu'a, itama zan rubuta mata wasu ta cigaba da yi, insha Allah' Allah zai ruguza dukkan wani shiri nashi a kanta."
Abba yace " Allah yasa mu dace, ya juyo gun suhailat yace kiyi hak'uri yar Abba duk ni na ja miki da na dage ki aure shi, yawan son gaisuwata ya jawomn yata ta fad'a ga hannun mugun miji."
Abba ya kawar da kanshi gefe, yai saurin share k'wallar da ta fito daga idon shi.
Suhailat ta kalli abbanta tace " haba abba, be kamata ka rik'a fad'in haka ba, halin da na shiga k'addara ta ce, kuma rubutacce ne, ka daina d'ora laifin a kanka,
Idan ma laifin ne to ni na jawa kaina konai, ruwan idona ya jawomn naje nai zab'en tumun dare, nabar kula masu k'aunata da gaskiya "
tana kaiwa nan a zancenta sai ta fashe da kuka, a cikin d'akin kaf babu wanda bata bawa tausayi ba, dak'yar aka samu tai shiru, ummie tace " abar zancen haka," aka rufe taro da addu'a kowa ya kama gaban shi.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Autan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited MEELAT A.H.K
Dedicated to HUMY LUV
_my humyluv ina kike ne yaki yaki in saki idanuwa na, bazan daina zubar hawaye ππ ba in banyo arba dake ba_
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 85 to 90
A hankali - a hankali walwalar suhailat ta dawo, bayan ta gama iddah mahmud ya dawo gareta, kuma ta amshe shi hannu biyu, yakan zo ya b'ata lokuta da dama domin d'ebe mata kewa.
Yauma kamar kullum suna tare, zaune suke a k'ofar gida, suhailat ta kalle shi tace " ya-ya mahmud yanzu yaranka nawa ? "
Mahmud ya kalleta yace " hmm ai tunda na rasa ki ban samu macen da zan mata kallo a matsayin matar aure ba, saboda matan duniya kaf kallon maza nake musu, ke kad'ai ce mace a gabana. "
Suhailat ta kalle shi cike da tausayawa, tace " ashe da gaske kake da kace idan ka rasani bakai ba aure, kayi hak'uri yayana, nima bansan yanda akai na juya maka baya ba, har na auri wani ba kai ba. "
Mahmud ya kalle ta yai murmushi sanan yace " kibar fad'in haka suhailat, nasan ba laifinki bane, kuma rabon zainab yasa kika aure shi, nima kuma zanyi k'ok'arin gyara kuskurena da nai a baya."
Suhailat ta kalle shi tace " wane irin kuskure kuma kai kayi ? "
Mahmud yace " laifina zan goge a wajen Abba, ni nature na ne bana iya tare mutum a hanya in gaishe shi,r sai inga hakan kamar be dace ba, na fiso inje har gida in gaida mutum, shima baba a hanya ne kawai bama gaisawa amma ina zuwa har gun aikin shi in gaishe shi, sedai a daure yake amsawa, kuma duk lokacin ban fahimci laifina ba, amma insha Allah yanzu dana fahimta zan gyara kuskure na. "
Suhailat tace " Allah ya baka iko "
Mahmud yace " Ameen my Blood, dan Allah wanan karon karki bari na rasaki, ki bani izini in turo gidanku a tsaida magana. "
Suhailat tace " bazaka rasa ni ba in sha Allah, amma maganar turowa kar kai gaggawa kad'an bani lokaci tukun."
Mahmud yace " to shikenan ba matsala. "
Sun dad'e suna hirar su irin ta masoya, daga k'arshe sukai sallama ya tafi.
Yau ta kama asabar, ummie ita da zainab suna ta yan aikace - aikacen tsakar gida, ita kuma suhailat ta shek'a wankan ta, ta yi wa zainab itama, tana cikin yi wa zainab d'in kwalliya sai suka ji sallamar kamal shi da abokin sa.
Da saurin su suka shiga cikin d'aki suka saka hija bai saboda sun san goga kamal babu ruwan shi da jiran izinin masu gida, bayan sun saka hijaban ne suka fito suka cigaba da aikinsu.
A lokacin da suka shigo suhailat tana cikin d'aki tana sawa zainab kaya, bayan ta gama shiryata ta bata maganin zazzab'in da take fama da shi, sanan fito zata fita daga d'akin, idon kamal na kanta har ta fice.
Ummie ce ta shiga d'akin da sallamarta, su kamal suka amsa, suka gaisa, sanan kamal ya kalli ummie yace " dama munzo ganin zainab ne. "
Ummie tace " ai ko kun kyauta, bari na kirata, bata jin dad'i ma, yau ta tashi da zazzab'i."
Bayan ummie ta d'auko zainab daga wurin suhailat sai ta zubo musu abinci, sanan ta aika aka siyo musu lemun kwalba, suka ci abinci sukai k'at sanan suka kora da lemu.
Bayan sun gama cin abinci lokacin ummie na tsakar gida, kamal ya fito rik'e da zainab a hannun shi, ya kalli ummie yace " bari muje shago na siya mata biskit da sabulai mu dawo, kuma wanda mukazo tare da shi abokina ne, yace yana son magana dake. "
Ummie tace " to sai kun dawo, bari naje naji. "
Kamal ya ja zainab suka fita, ita kuma ummie ta shiga d'aki gun abokin kamal d'in.
Ba wata magana bace sabuwa face rok'o yake akan ayi hak'uri, a dai-daita suhailat ta koma d'akinta.
Ummie ta bashi labarin duk irin rashin mutuncin da kamal ya shuka musu, sun dad'e suna magana amma shiru har yanzu kamal be dawo ba, tun abokin kamal me suna hafiz yana duba agogo har dai ya k'are ya kalli ummie yace " kodai za'a dubo kamal ne yazo mu tafi, naga shiru har yanzu be dawo ba."
Ummie tace " to bari na sa a dubo shi. "
Ummie ta saka hijab d'inta ta lek'a da kanta, amma bata ga alamar kamal ba.
Yaron mak'wabtansu ummie ta gani zaune a k'ofar gidan, shi ta tambaya ko yaga inda kamal mijin ummie shi da zainab suka yi ?
Yaron yace " eh na ganshi yaje shagon mansur, ya dad'e zaune a shagon, daga baya naga ya tsayar da me mashin ya hau sun tafi. "
Ummie ta saka salati, da kanta taje shagon ta tambaya akace ai ya hau mashin shi da zainab sun tafi, tana ta kuka ma tana umma na suka tafi.
Ummie ta dawo gida, tana shigowa suhailat ta kalle ta tace " ya tafi da ita koh ? "
Ummie tace " wallahi ya gudu da ita, abokin shi ya fito daga cikin d'aki, yace " ba'a ganshi bane?"
Suhailat tai caraf tace " dama haka kuka shiryo kui mana, yanzu zaka nuna kamar baka san komai ba."
Hafiz yace " ban gane ba, " ummie ta sanar da shi ai kamal ya gudu da zainab.
Hafiz yace " anya kuwa tafiya da ita ya yi, bari dai in kira shi inji, ya ciro wayar shi a aljihu ya kira kamal, amma har ta katse ba'a d'aga ba.
Yaita kiran shi be d'aga ba, daga k'arshe ma da ya kira akace wayar a kashe take.
Suna nan jugum-jugum suna jimamin wanan al'amari, anyi-anyi da abokin nashi ya tafi kawai yak'i tafiya, yace " wallahi babu kud'in mota ma a hannun shi," sai wajen k'arfe shida na yamma sai wayar hafiz d'in tai k'ara, yana dubawa ya d'ago kalle su yace " kamal ne ke kirana," sanan ya d'aga wayar.
Hafiz yace " kamal kana ina ne ka barmu muna jiranka anan, kuma ka tahi da yarinya batta da lahiya?"
Maganar da kamal ya fad'a mai ne yasa shi mik'ewa, had'e da sakin salati, hafiz yace " haba kamal me yasa zakai haka," sai d'if ya kashe wayar.
Ummie ce ta kalle shi tace " me yace maka ? "
Hafiz cike da jin nauyi kanshi na k'asa yace " wallahi ya tai da ita, yanzu haka suna funtua."
Yayar suhailat me suna zainab ta kalli hafiz din tana kuka tace " INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN, wanan wane irin rashin imani ne, so yake ya kashe mana yar uwa da b'acin ranshiπ."
Suhailat ta fashe da kuka, sanan tai d'aki da gudu.
_wayyo tausayi ya sani kuka nimaπ, bana ganin rubutun da kyau, idan mun gama kukan zan ci gaba gobe insha Allahππ_
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Yar gatan exclusive)_
Edited by MEELAT A.H.K
Dedicated to Ermeenat
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's_)
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
_gaisuwar ban girma a gareku masoya naππ»_
_BK tana mai bawa masoyanta hak'urin rashin jinta na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon rasuwa da akaimn, hade da kwantar da d'iyar yayata da akai a asibiti, ga kuma babbar aminiyata wato MEELAT A.H.K Itama ba lafiya!!! OH YA ALLAHππ._
_ina k'ara baku hak'uri, kuma ina fatan zaku karb'i uzuri na, ina fatan masoyana zasu taya ni da addu'aππ»π_
_NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!ππ»ππ»_
page 90 to 95
Ummie ta rasa ta ina ma zata fara, kowa mamaki yake da irin wannan shammatar da kamal ya yi na d'auke zainab.
Zainab ce ta kalli abokin kamal d'in cikin zubar da hawaye tace " Tunda kunyi abin da kuke so ai sai ka tafi, amma ku sani duk halin da yar'uwa ta ta shiga a dalilin shi to baza mu tab'a yafe mishi ba, haba dan Allah zainab nawa take da za'a raba ta da mahaifiyar ta, tana kaiwa nan a zancen ta sai ta fashe da kuka. "
Abokin kamal dai ya rasa yadda zai yi, suhaila da mahaifiyarta kai har da yan'uwan ta ma gani suke kamar da had'in bakin shi aka shirya yi musu haka, basu san shima ta kanshi yake ba dan ko kud'in koma wa gida bai da shi.
haka nan ya gama jimami, sanan ya fita daga gidan domin nemar wa kan shi mafita.
Tun daga ranar damuwa tai wa Suhailat yawa, kuma tun da abin ya faru take kuka, bata iya cin abinci sosai, duk ta bi ta rame kullum cikin tunani, tun ummie na rarrashin ta har ta fusata ta, ta fita harkar ta.
Haka nan yana yin gidan su Suhailat ya ci gaba da kasancewa, walwalar gidan tai k'aranci, kowa da tausayin Suhailat yake kwana da shi yake tashi, tun tana damuwa kad'an har ta kaita ga kwanciya.
jinya ta kwanta a gida ba yar kad'an ba, ga wata irin muguwar rama da tayi, hakan yasa aka tattage ta aka tafi asibiti da ita, suna zuwa gwajin farko aka tabbatar musu da ta kamu da ciwon xuciya, kuma muddin bata rage tunanin da tasa wa ranta ba to zata iya rasa rayuwar ta, doctor ya dad'e yana yi mata nasiha tare da bata shawar-wari, daga nan ya basu magun-guna, suka biya kud'in da aka caje su had'e da yi mishi godiya, sanan suka fito, suka koma gida.
Suhailat ta dad'e tana jinya, ba ita kad'ai ba ma harda yan gidan gaba d'aya, domin zainab yarinya ce me shiga rai.
A hankali-a hankali ta rage damuwar ta, amma duk tym d'in da ta tuno takan b'oye ta ci kukan ta sosai.
Abban su Suhailat ya je ya sanar wa da kotun da sukai shari'a ta farko, sun tura jami'an tsaro a kamo shi, sedai ko da suka je aka ce musu ya samu aiki ya koma Abuja da zama, kullum suka je abin da ake sanar da su kenan.
Haka suka hak'ura saboda rashin sanin taka mai-mai inda ya kai zainab d'in, shi kuma ya gudu abuja.
bayan kwana biyu kamar daga sama sai ga kiran wayar k'anwar kamal me suna hauwa'u a cikin wayar suhailat, da dai kamar ba zata d'aga ba, sai ummie tace " ki d'aga mana baki san dalilin kiran nata ba.
Suhailat ta d'auki wayar tare da yin sallama, hauwa'u ta amsa, bayan sun gaisa sai hauwa'u tace " ashe abin da kamal yazo yai muku kenan na d'auko zainab? "
Suhailat tace " uhm "
Hauwa'u tace " kiyi hak'uri suhailat Allah zai miki sakayya, nima baya min magana k'ila da ni zai kawo wa zainab d'in, yaje gida da ita baban mu yace ya wuce ya maida ta gunki, shine ya je ya kaiwa k'anwar maman mu.
Ai kuwa suhailat na ji an yi mata maganar zainab sai ta warware, kuma hauwa tai ta kora mata bayanin abubuwan da ke faruwa, bayan sun dad'e suna magana, daga k'arshe sai suka yi sallama sanan ta ajiye wayar.
suhailat ta kalli ummien su cikin farin ciki tace " ummie anga zainab, ashe gidan k'anwar maman shi ya kai ta," nan dai ta zayyane mata duk abin da hauwa'u ta fad'a mata.
Bayan suhailat ta gama fad'a wa ummie sai tace " ummie dan girman Allah ki barni in je in ganta."
Ummie tace " ba ruwa na ki tambayi Abban ku."
Auntyn ta zainab ita da Aunty maryam ne suka sa baki, suka ce " dan Allah ummie ki bar ta taje mu sai mu raka ta."
Ummie tace " na fad'a muku ba bu ruwa na, dan bakue da hankali mutumin da ya zo har cikin gidan nan yai tijara shine zaku bishi har garin shi koh, to na dani ba."
magiya sukai ta yi mata suna rok'on ta har ta amince, amma tace " duk abin da akai musu babu ruwan ta."
farin ciki suke ta yi da d'oki gobe zasu ga zainab, musamman ma suhailat.
_topha, shin ya zata kasance?_
_ga dai suhailat da yan uwanta nan sun yi haramar tafiya katsina domin suje suga zainab_
_Amma abin tambaya anan shine wane irin tarba kamal zai yi musu?_
_Anya ma zai barsu su ganta kuwa?_
ku biyo BK domin sanin amsar wad'an nan tambayoyin.
taku ce dai π ±Kππ
[12/22, 10:27 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited by MEELAT A.H.K.
Dedicated to MAMAN SAFWAN
_Masoya na❤, da mak'iya na, ina sonku!!! domin kullum nasan ina cikin ranku_ππ
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 95 to 100
Washe gari da safe su suhailat suka hau shiri, dama su uku zasu je, Suhailat da Aunty Maryam, sai Aunty Zainab.
bayan sun shirya sukai wa ummie sallama, suka tafi.
Bakin ti-ti suka je, suka tari ke-ke napep, ya kai su tasha kuma suka taki sa'a saura mutum uku ta cika, suna shiga ba b'ata lokaci driver ya ja mota suka d'auki hanyar katsina.
Suhailat ce ta kalli yan'uwan ta, tace " kodai mu sauka mu koma gida ne? "
Zainab tace " ok mu koma ki ci gaba da yi mana kuka koh,"
" k'yaleta zainab kawai abi shawararta d'in mu koma gida cewar Aunty maryam kenan. "
Cikin sauri Suhailat tace " wasa fa nake yi, wallahi wasa ne,"
yanda suka ga tai magana cikin sauri da zaro ido yasa su darawa, se dai suma a cikin ran su suna yin fargabar irin tar-bar da za'ai musu.
Sha biyu dai dai suka iso, bayan sun iso katsina da yake daga bakin ti-ti zuwa gidan k'anwar maman nashi akwai nisa, sai suka tari Adai-daita sahu ya shiga dasu cikin unguwar.
Suna tafe Suhailat na nuna mishi hanya, har suka iso k'ofar gidan.
Bayan sun sallami me napep sai suka shiga cikin gidan tare da sallama, wata mata ce ta amsa sallamar da fara'ar ta, tare da fad'in " Suhailat yau kune a gidan namu, sannun ku da zuwa, ku shigo mana."
Suka shiga cikin d'aki, ita kuma ta bud'e pridge d'inta ta d'auko musu pure water da zobo, sannan taje ta zubo musu abinci duk ta dire a gaban su.
Zama tayi suka gaisa suka sha ruwa da zob'on da aka aje musu, sannan Aunty Maryam tace " inna ina zainab take, ita muka zo gani, ance mana tana wajen ki, shine muka zo mu duba ta. "
Inna tace " wallahi tana can gidan su kamal, d'azu k'anin shi umar yazo ya d'auke ta. "
Suna jin haka sukai shiru, can sai Zainab tace " to mu k'arasa can d'in mana A gaisa, sai mu wuce gida."
Suka mik'e, inna tace " ba dai har zaku tafi ba,"
Maryam tace " eh inna, muna so mu biya ta gidan ne mu duba zainab, daga can sai mu wuce gida."
Nan dai sukai sallama da inna, sannan suka fito suka nufi gidan su kamal d'in.
ko da suka shigo cikin unguwar sai suka hango hafiz abokin kamal, wanda aka zo tare da shi ranar da aka d'auke zainab d'in, kusa dashi wani ne kwance kamar kamal yana bacci, ko da muka zo daf da su sai hafiz ya d'auke kai tamkar be san mu ba.
Suhailat ta kalli zainab tace " ji mutumin da yace shi da kamal sunyi hannun riga, babu shi ba kamal tunda yai mana haka."
Zainab tace " ah to ba na fad'a muku bakin su d'aya ba, dama sun tsara hakan tun kafin suzo gidan mu kun k'i yarda, ai gashi idon ku ya nuna muku."
Aunty maryam tace malamai muyi abin da ke gaban mu mu tafi, kowa fa ya yi dakyau zai ga da kyau, kuma mu yanzu ina ruwan mu da su ma, sannan ke zainab na san ki da saurin fushi, kin ma fi Abba da kika gada gun shi zuciyar, to ina gargad'in ki da babbar murya ko me zasu yi mana kar kice komai. "
Zainab tace " to Aunty. " haka sukai ta hira a hanya har suka k'araso k'ofar gidan.
Suna shiga cikin gidan sukai sallama, matan shi Laraba da Adama suka Amsa, sukai mana lale marhabin da zuwa, d'akin uwar gidan me suna Laraba muka shiga muka zauna.
Laraba ita da Adaman suka shigo cikin d'akin muka gaisa da su, sannan Adama ta fita saboda Aikin girkin da take ta yi.
Aunty maryam tace " mun biyo mu gaida zainab ne sai mu wuce gida, ina take? "
Laraba tace " wallahi ban san inda take ba, d'azu dai umar ya shigo da ita, kuma ba'a dad'e ba kamal ya shigo ya d'auke ta. "
Suna cikin magana sai ga kamal ya shigo, lek'o wa cikin d'akin ya yi, sanan ya kalle mu a wulak'ance, ya buga tsaki yace " aikin banza, wai nan an zo tafiya da zainab ne, to wallahi baku isa ba,"
Zainab ce ta d'auko wayar ta ta danna recording saboda tsaro, ya kalleta yace " ki danna recording din mana sai me, shegiya munafuka,
shegu yan bura-uba, ku ta shi ku fita wallahi ko kuma……sai ya juya da sauri, yai cikin gidan, Laraba itama ta fito da sauri dai-dai ya d'auko tab'arya ta tare shi, ta rik'e hannun shi, tare da k'ok'arin k'wace tab'aryar, se dai sam yak'i saki.
Fad'i kawai yake " su fito su bar gidan nan bana k'aunar sake ganin su, su bar gidan nan tunda ba gidan uban su Malam Adam da Asiya ba ne. "
Aunty maryam tace " kunga ku tashi mu tafi kar ya nak'asa mu, " suka mik'e suka fito tsakar gidan, Laraba da Adama matan baban shi suka ce " dan Allah kuyi hak'uri. "
Maryam tace " ba komai," suka fito, kamal ya biyo su a baya, nan da nan ya tara musu yan unguwa yan daba yan'uwan shi, sunzo dukan su suhailat.
d'aga murya yake yana antayo musu ashar, nan da nan mak'ota suka cika unguwar, da shi da yan daban unguwar wad'an da suka d'auko gorori sai kace zasu daki gardi fad'i suke su bar musu unguwa ko sui musu duka.
sun juya zasu tafi kamal ya wullo tab'aryar nan sai kan hannun Aunty zainab, sanan ya k'ara d'aga murya yace " ke kuma suhailat kike ko wa, ki fad'awa Adam cewa " yanda yake da iko da ke haka nake da iko da yata, idan ya raba ni da ke to be isa ya raba ni da ya'ta ba."
Zainab fa ta zo iya wuya, taga cin kashin yai yawa, sai ta kalle shi ita ma ta d'aga murya tace " Kamal kake ko wa, tabbas sai yau na k'ara tabbatar wa da kai d'an Akuya ne, baka da tarbiyya, kai jahili ne, to ka sani duk bak'in cikin ka na rabuwar ka da Suhailat se dai ka mutu, kuma duk asirin da kake kan ka zai koma, sanan ka zagi mahaifan mu to ka sani Aliyu da maimuna su ka zaga, bunsuru kawai, kare dangin karnuka. "
haba taho wa yai gadan gadan zai dake ta, aka rik'e shi, zainab tace " ku bar shi ya zo ya dake ni, ku bar shi yai nadamar aikata kuskure mafi muni."
duk maganar nan da zainab take a tsorace take, ko'ina an kewaye su da gora kamar an kama b'arayi, tana tsoron shan duka amma bakin ta yak'i mutuwaπππ
wani mak'wabcin su ne wanda a shekaru ba zai wuce sa'an kamal d'in ba, ya zo gun mu ya kalli zainab yace " ke baki neman sulhu,"
Zainab ta kalle shi tace " oh yanzu ka sami bakin magana ko, ina ce kana tsaye a nan gun yake ta antayo mana ashar, kuma ya buga mun tab'arya a hannu amma bakai magana ba sai yanzu."
_lallai wanan bugun ya tab'a zuciyar oganniya zainabπ_
kallon Aunty maryam ya yi yace " ku zo muje gida na," idan ya bar unguwar sai ku tafi, babu musu suka bishi.
Suna shiga mutumin ya tambaye su meke faruwa ne, Aunty maryam ta fara mishi bayani kenan sai ga kamal ya shigo cikin gidan, yana fad'in nan ma ku zo ku fito, ku bar mana unguwar, gaba d'aya ya haukace musu sai kace tab'ab'b'e.
mai gidan yace " kamal menene haka, nan ai gidana ne ba naka ba,"
Kamal yace " wallahi akan su zan iya b'atawa da kai,"
sai mutumin yace "Yanzu zasu tafi, muna magana ne, kamal yana zage zage ya juya shi da aboka nan da ya kira su dake mu suka fita.
Mutumin ne ya je ya rufe k'ofar gidan shi sannan ya dawo, yace " ina jinki, " Aunty maryam tana kukan bak'in cikin abin da akai musu, ta ci gaba da yi mashi bayanin komai.
k'anin kamal ne ya k'wan-k'wasa k'ofa aka bud'e yace " baban mu yana kiran ku, ashe umar d'in ya kira mahaifin su a waya ya sanar da shi.
mutumin ya kalli zainab yace " ke ki zauna a nan gidan, ga mata ta nan ku zauna tare mu je mu dawo, in kuma kika fito suka dad-datsa ki shike nan."
sannan ya kalli Maryam da Suhailat yace ku mu tafi, suka fita daga gidan, suka shiga gidan su kamal d'in.
Bayan sun fita matar mutumin ta kalle ni tace " Ai kamal bashi da mutunci, wallahi ni da naji yana zage zagen nan nayi tunanin da matan baban shi yake, tunda haka yake musu kusan kullum, shi yasa suke mugun jin tsoron shi.
Nan zainab ta fad'a mata duk irin tijarar da, kamal yai musu, matar tace "zai aika wallahi kome akace zai iya aikatawa.
B'angaren su kamal kuwa, dattijan unguwar sun tabbatar wa da mahaifin shi cewa kamal ne baida gaskiya, yayin da abokan shi ke fad'in shine me gaskiya, aka tambayi Laraba matar baban kamal d'in yanda akai, bakin ta na rawa tace " tabbas kamal ne bai da gaskiya, dan bada neman fitina suka zo ba."
mahaifin kamal ya kalli kamal d'in yace " A karo na farko na umurce ka da ka maida yarinyar nan gaban iyayen ta bakai ba, to a karo na biyu na k'ara umurtar ka da ka d'auko ta duk inda ka kai ta ka b'oye ta ka mayar musu da ita, idan bakai yanda nace ba wallahi ban yafe maka ba."
juyo wa gun su Aunty maryam ya yi, yace " dan Allah ku yi hak'uri, sam banda labarin kamal be maida ta kano ba, amma kuyi hak'uri ku je gida, zai dawo da ita da kan shi."
Su maryam sukai mishi godiya, sannan suka fito suka shiga gidan wannan mutumin suka d'auki zainab, tare da yi wa masu gidan godiya, suka fito suka d'auki hanyar gida.
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:28 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (BK)
_(Yar gatan Exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Edited to MEELAT A.H.K
Dedicated to SARDY BASH
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 100 to 105
Tun da suka dawo suhailat take aikin kuka, ta kasa samun natsuwa sam, ko yaushe tunanin ta ya za'ai Yar ta ta dawo gareta.
Ta rage magana da kowa, ko yaushe daga tunani sai kuka, idan mahmud ya zo ma bata fita, saboda gani take kamar be damu da d'auke zainab da akai ba.
Washe gari suhailat na d'aki tana sana'ar da ta zamto mata jiki, wato tunani, sai wayar ta tayi k'ara, tana duba wa taga kamal ne ke kiranta, k'in d'agawa ta yi har ta katse, haka ya yi ta kira bata d'agawa, daga k'arshe sai ya turo mata da txt kamar haka:
" _suhailat dan girman Allah kiyi hak'uri da abin da ya faru jiya, wallahi sharrin shaid'an ne, kuma na zauna nayi nazari abinda nai muku ban kyauta ba, kuyi hak'uri, ki bawa su Aunty zainab, da Aunty maryam hakuri kafin na kira._"
Tana gama karantawa wani ya shigo,
" _Dan Allah kiyi hak'uri ki dawo ko dan zainab, wallahi tun lokacin da na d'auko ta har zuwa yau kuka take kullum tana kiran umman ta, ki tausaya mata ki dawo gareta_"
Tana gama karantawa a dai-dai Aunty zainab ta shigo d'akin, sai Suhailat ta mik'a mata wayar tace " kalli wasu txt da kamal yake min na rainin hankali."
Bayan Aunty zainab ta gama karantawa sai ta juyo ta kalli yar uwar ta tace " ki fad'a mishi kin yarda zaki koma, saboda mu samu ya dawo da zainab d'in."
Haka kuwa aka yi, da ya sake kira ta shaida mishi ta amince zata dawo, amma ya dawo mata da yarinyar ta tukun, sun dad'e suna magana yana k'ara rokon ta ta dawo, har aunty zainab sai da aka bawa ya bata hak'uri sanan sukai sallama.
tun daga ranar take sa ran ganin zainab shiru, kullum cikin sa mata ranar zuwan su yake.
Daga k'arshe ranar wata Alhamis ya kira ta a waya yace mata shi bazai kawo zainab ba, ta bari idan sun koma da auren su ta ganta.
Koda suhailat taji haka sai ta yi mishi txt itama tace "
" _nima bazan iya ci gaba da auren mutum irin ka ba, 'ya ce dai kaje ka rik'e in da rai wata rana zata neme ni_. "
Ba'a dad'e ba da tura mishi sak'on shima kamal ya turo mata da rply kamar haka:
" _kar Allah yasa ki dawo, dad'in abun ni ne na fara farke budurcin ki, na d'auke 'ya ta ne saboda tunanin ta yasa ki dawo, amma tunda haka kika ce to mu zuba, in dai ni na haifi zainab maga ta yanda za'ai ta zo gareki._"
Tana gama karantawa sai ta goge, ko iyayen ta bata nuna mawa ba, kuma daga lokacin sai Allah ya sa mata k'arfin zuciya, daga ranar ta dangana, koda ta tuna da zainab bata nunawa a fuskar ta balle hakan ya tada hankalin yan'uwan ta.
Sun shirya da mahmud, kuma yana zuwa kullum domin d'ebe mata kewa, kuma ya nemo mata Admision domin ta cigaba da karatun ta, ta mik'a wa Allah dukkan lamuran ta tare da dagewa da rok'on kariya daga gare shi, ta tattara tunani ta aje shi gefe, yanzu karatun ta da ta fara zuwa kawai tasa a gaba.
Bayan shekara d'aya da wata uku, aka bawa mahmud dama ya turo, aiko ranar kamar an sa shi a aljanna, yana koma wa gida ya shaida wa iyayen shi.
washe garin ranar kuwa iyayen shi suka zo, aka biya sadaki sannan aka sa ranar aure nan da wata biyu.
BAYAN WATA BIYU
A yau juma'a kuma a yau ne aka d'aura auren mahmud da suhailat, bayan anyi sallar juma'a.
Daga amaryar har angon farin ciki ne fal acikin zuciyar su, bayan an sha shagalin biki, da yamma aka tattara amarya ita da k'awayen ta aka tafi kai su gidan ango.
Bayan manyan da suka kawo ta sun tafi, sai suka rage daga ita sai k'awayen ta, amarya ta zage sai hira suke da k'awayen ta, suna shewa, su kan su k'awayen nata suna fad'i yanzu ne suhailat tai aure.
bayan d'an wasu lokuta sai ga ango ya shigo shi da abokan shi, aka d'an tab'a hira da barkwanci tsakanin abokan ango da k'awayen amarya, sanan akai musu nasiha da tunatarwa akan abinda suka riga da suka sani.
Ango dai yana ta faman duba agogo, tun yana sa ran tafiyar su yaga shiru dai hira kawai suke kwasa, sai ya dubi abokan nashi yace " malamai dare yayi kar ku rasa motar hawa fa. "
Gaba d'ayan su suka kwashe da dariya, babban abokin shi yace " lallai ango, halan ka manta a motocin mu muka zo, to bari mu tashi kar anjima kad'an ka fara kai mana bugu, aka k'ara kwashewa da dariya.
abokan ango suka taso k'awayen amarya, kowacce suka maida ta gidan iyayen ta, sannan suka wuce gidajen su suma.
B'angaren ango kuwa bayan ya rufe ko ina sai ya dawo ya iske amaryar sa suhailat zaune gefen gado, kusa da ita ya zauna, sannan ya yaye mayafin da ya rufe fuskarta, d'agowa ta yi suka kalli juna, sannan suka sakarwa junan su murmushi.
Mahmud yace " Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka cika min buri na, ya Allah ka bani ikon tattalin wanan baiwa taka ta hanyar faranta mata."
Suhailat tai murmushi sannan tace " ameen "
mahmud yace " tashi muje mu yi Alwala mu yi nafila domin godiya ga Allah da ya bamu ikon mallakar juna," tashi sukai a lokaci d'aya suka nufi ban d'aki domin yin Alwala.
bayan sunyo Alwala sukai sallar nafila raka'a biyu, bayan sun idar ya dafa kanta yai Addu'a yace:
_"ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA KHAIRAHA, WA KHAIRA MA JABALTAHA ALAIH, WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRA MA JABALTAHA ALAIH_"
bayan sun ci kaza da lemo sai kowanen su yaje ya watsa ruwa, suna fitowa suka sa kayan bacci suka kwanta, ni kuwa da nake bakin k'ofa na ja musu k'ofar sanan nace asuba ta gari.
…………
B'angaren kamal kuwa, abokin shi dake zaune a nan kano kusa da su suhailat shine ya tsegunta mishi yau ne bikin suhailat, duk da be yarda ba amma yace bari ya kira aminin babanta domin ya gasgata zancen.
wani shago dake k'ofar gidan su ya fito ya se kati, sanan ya koma majalisa ya zauna.
bayan ya shigar da katin cikin wayar shi sai ya kira lambar aminin abban suhailat, bugu daya a na biyu aka d'aga tare da yin sallama, kamal ya amsa sallamar sanan suka gaisa.
Bayan sun gaisa sai kamal yace " ashe suhailat tai aure, to Allah sanya alkhairi."
Aminin Abba yace " ai kuwa suhailat tai aure yau, yanzu haka tana d'akin mijinta, ameen mun gode da addu'a."
Kamal yace " ashe dai da gaske auren ta yi, to kuwa kasan wanan abun akwai munafunci a ciki."
Aminin Abba yace " uban wa ke maka munafuncin," kamal be sake cewa komai ba sai ya katse wayar.
_topha wai wanan mutumn zai bar suhailat ta rayu kamar kowa a gidan auren ta kuwa_π€π€π€
muje zuwa
urs π ±Kππ
[12/22, 10:28 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
TRUE LIFE STORY
ππππππππππ
Writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
Dedicated to Maman Useey
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 110 to 115
Washe gari wajen k'arfe goma sha d'aya, suhailat da mahmud sun gama shirya wa, suka rufe ko ina na gidan nasu, sannan suka fito, suka shiga mota, suka d'auki hanyar katsina.
Suna fara tafiya suhailat tai bacci a jikin mahmud, sai da yaga sun shigo garin katsinan sannan ya tashe ta, domin ta gwada mishi hanya.
Suhailat tai ta gwada mishi hanya har suka k'araso k'ofar gidan inna asabe.
Mahmud yace " ki shiga ku gaisa, ki fito mu koma. "
Suhailat ta shagwab'e fuska kamar za ta yi kuka, tace " kai "' MY HONEY ... ba zaka shigo ba?"
Mahmud yace " A'a shiga dai ki fito mu koma," suhailat ta juya tana gun guni ta nufi k'ofar gidan, mahmud ya bita da kallo, sannan yai murmushi tare da gyad'a kan shi.
Da sallamar ta ta shiga cikin gidan, Zainab ta hango daga gefe zaune cikin yaran gidan suna wasa, inna ta amsa mata sallamar da fara'ar ta, suka shiga d'aki suka zauna.
Bayan sun gaisa, sai Inna ta k'wala wa zainab kira, zainab ta amsa, sanan ta taso ta shigo d'akin.
Bayan ta shigo taje gaban inna tace " gani," sai inna ta kalle ta tace " ga umman ki can ta zo duba ki."
Zainab ta juyo saitin da suhailat ke zaune ta k'ura mata ido, ta dad'e tana kallon ta, sannan suhailat tace " Zainab zo nan ".
Da saurin ta taje ta fad'a jikin mahaifiyar ta sanan ta fara magana da bagwariyar hausar ta, tana fad'in " Umma kinjo tafiya dani ne?"
K'wallar farin ciki Suhailat ta share, a zuciyarta tana godiya ga Allah da d'iyar ta bata manta da ita ba.
Suhailat ta kalli inna tace " tare da mahmud muke," ina ta saki salati sannan tace " shine kika bar shi a waje," inna ta mik'e ta d'auki hijab tasa ta fita k'ofar gida, sai gasu sun shigo tare da mahmud d'in.
Tun da mahmud ya shigo ya fahimci farin cikin matar shi ya k'aru, ga kuma d'iyar ta zainab kwance kan jikin ta ta mak'alk'ale ta, sai yaji sun bashi tausayi matuk'a.
kallon zainab d'in ya yi, yace " zo nan zainab," sai ta d'aga kafad'a alamar baza ta zo ba, kuma ta k'ara mak'alewa a jikin suhailat.
Ba yanda be yi ba zainab ta zo amma ta k'i zuwa, sai da suhailat ta kalle ta tace " zainab jeki mana Abba ne fa," sanan zainab ta yarda taje gun mahmud, kuma tana zuwa bata dad'e ba ta dawo wajen umman ta.
Suhailat cike da murna ta kalli mahmud tace " honey! ka gani zainab bata manta da ni ba."
Mahmud yana murmushi yace " na gani RAI NAH, Alk'awarin Allah kenan."
Inna ta cika musu gaban su da Abinci da lemu, sannan ta fita ta basu wuri.
Mahmud ya dawo kusa da su suhailat, suka zuba abinci suna ci suna hira, har suka gama.
Bayan sun gama mahmud ya d'auko wayar shi yai ta d'aukan su hotu na.
Bayan sun gama d'aukan hotuna yasa aka kira inna yace mata su zasu tafi, nan suhailat ta fito da kayan da ta d'inka wa zainab, da yan kanti da ta se mata, har da takalmi da jaka na yara.
Zainab tana ta murna, wata yarinyar inna ta kalli zainab tace " iyye zainab, shikenan na sami jakar zuwa anguwa. "
Zainab ta kalle ta mak'e kafad'a tace " A'ah bajan baki ba, " aka kwashe da dariya
Mahmud ya bawa inna dubu goma, sanan yabi duk yaran gidan ya raba musu d'ari d'ari.
Inna sai zuba godiya take, zainab tana jikin suhailat, anyi anyi da ita ta sauka su tafi ta k'i, sai inna ta kalli babbar yarinyar ta tace " ku je tare ku raka su, sai ku dawo tare da zainab d'in".
Suhailat ta karb'i lambar inna, sannan sukai sallama da inna, suka fito daga gidan.
Sai da suka zo daf da motar su sannan Suhailat ta sauke zainab, tana sauke ta ta fara kuka tana fad'in " umma jan bi ku "
Yarinyar inna tana jan zainab ita kuma tana tirjewa, tana ihu, tana zata bi su.
Mahmud ne ya kalli Suhailat da ke kuka ita ma, yace " haba rai nah ki dena kukan nan please, to ko dai zamu sace ta ne muma?"
Suhailat tai sauri ta d'ago kai ta kalle shi tace " A'a honey, kar mu rama sharri da sharri, kuma ko ba komai be kamata mu yiwa matar nan haka ba, kalli fa yanda ta karb'e mu hannu bibbiyu."
Mahmud yace " to ki daina kukan nan haka in ba haka ba wallahi zan je in k'wato ta daga hannun waccan yarinyar mu tafi da ita."
Suhailat ta share hawayen ta, suna nan a wajen har su zainab suka b'ace wa ganin su, sannan suka d'auki hanyar komawa gida.
Tun daga wannan lokacin suhailat suke waya da zainab a cikin wayar inna, a haka suke shan hira da suhailat da bagwariyar hausar ta, wata ta gane, wata kuma ta bata dariya.
Rayuwa haka take dama, bak'in ciki baya dauwama a rayuwa, domin kuwa farin cikin suhailat ya dawo, tana ziyar tar 'yar ta akai akai, sannan suna waya a koda yaushe.
B'ANGAREN KAMAL KUMA FAH
Rayuwa ta juya wa kamal baya, duk yarinyar da yace yana so, da an binciki halayen shi sai ta barshi, kowace yarinya tana tsoron fad'awa irin halin da suhailat ta shiga, iyaye suna nema wa yayan su tsari da irin kamal.
Ana haka kwatsam ya sami matar aure a abuja, se dai shi be sani ba fasik'a ce irin shi, ta amince da auren shi, ba'a wani ja lokaci da tsawo ba sukai aure, kuma sukai zaman su a Abuja.
Bayan shekara d'aya da yin aure matar shi ta fara rashin lafiya sosai, ga kuma wasu irin k'uraje da suka fito mata abun ba kyan gani, bayan sunga likita aka gwagwada ta, likita ya tabbatar wa kamal da tana d'auke da cutar k'anjamau, kuma ta ci k'arfin ta dan ta dad'e a jikin ta.
Iya rud'ewa kamal ya yi, domin yasan tabbas shima ya samu, basu bar asibitin ba sai da yasa shima a gwada shi, ana gwada shi kuwa aka tabbatar mishi yana da cutar a jikin shi.
Bayan sun dawo gida kuka sosai kamal yake, ya kalli matar tashi yace " kin cuce ni, yanzu daman kin san kina da wanan cutar kika aure ni, Allah ya isa tsaka ni na dake, kuma kije na sake ki saki uku.
matar kamal tana kuka tana rok'on shi gafara amma ina, ko bi ta kanta be yi ba, kayan shi ya shiga had'a wa, ya fito yaje banki ya kwashe dukkanin kud'in shi dake cikin account yaje tasha ya shiga mota sai katsina.
Duniya tai mishi zafi, gashi ya b'ata da mahaifin shi, koda ya dira katsina ya ma kasa zuwa gidan su, shi kan shi yasan Abubuwan da ya shuka yake girba, funtua ya wuce, a can ya samu gidan haya ya cigaba da rayuwar shi a ciki, har zuwa lokacin da Allah zai d'auki rayuwar shi, in da yai shirme shine daga mahaifin shi, har tsohuwar matar shi be neme su ba domin neman gafarar su, a tunanin shi ko yaje baza su saurare shi ba.
Se dai ya koma ga Allah tare da neman afuwar sa sanan yasa inna ta mayar wa da suhailat zainab har gida
inna asabe ita ta fad'a wa mahaifin kamal inda kamal yake, mahaifin kamal da kan shi yaje ya taho da kamal, ya shaida mishi ya yafe mishi, sanan ya cigaba da kulawa da shi
Bangaren suhailat kuwa, rayuwar ta ta baya ta zama tarihi, kuma ta riga da ta dad'e da yafe wa kamal abinda ya yi mata, ga 'yar ta zainab a gaban ta, sanan yanzu haka tana da tsohon ciki wanda ze kai wata takwas, mahmud an kusa zama uba, sai ririta matar shi yake fiye da yadda ake ririta goald.
ALHAMDULILLAH
_INA GODIYA GA ALLAH S.W.A DA YA BANI IKON GAMA LITTAFIN NAN MAI SUNA KA CUTAR DA NI LAFIYA._
_KUSKUREN DA NAI A CIKI ALLAH NA ROKE KA KAI YAFIYA A GARE NI, ABIN DA NAI DAI DAI KUMA YA ALLAH KA BANI LADAN SHI_
_ALLAH KA BAMU IKON AIKATA ABIN DA YAKE DAI DAI, KA KARE MU DAGA AIKATA ABIN DA KA HANE MU A KANSHI_
_ALLAH KARE MU DAGA AIKATA DUK WANI AIKI DA ZAI SAMU YIN DANA SANI_
_godiya a gare ku_
MEELAT A.H.K
AYSHAT A. MUH'D
_da irin d'umbin gudummawarku akan wanan labarin, wallahi bazan taba mantawa da ku ba, domin kuwa har in mutu bazan manta halarcin ku gare ni baππ»ππ»ππ»_
JINJINA GA YAN
_EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_
_kune jigo na, ina godiya da kaunarku gareni, Allah ya kara hade kanmu_
INA KUKE MASOYA NA
_Ban manta da ku ba, wallahi ina matuk'ar jin dad'in k'aunar da kuke nuna min, ina fatan zata d'ore har mutuwa, Allah ya saka muku da alkhairi, ya barmu tare, ina sonku har kullumππ_
TAMMAT BI HAMDULLAH
urs π ±K
[12/22, 10:28 PM] +234 810 320 7299: ππππππππππ
KA CUTAR DA NI!π
ππππππππππ
writen by BILKISU Z. YA'U (π ±K)
_(Yar gatan Exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace honour and super writer's)_
Dedicated to ~ππΏRUQEEY CE π
_Ina kike ne marubuciyar NAGA RAYUWA!!!, wanan shafin naki ne ke kad'ai, mun gani kuma mun yaba da k'aunar ki gare mu, Allah ya bar mu tare, ya k'ara had'e kan mu._π€π€π»
FATAN SAMUN SAUKI A GAREKU
_ummukhady_
AND
_jamila k/mashi_
_Allah ya d'orar da lafiyar sa gareku, Allah yasa kaffara ne_
LIKES AND COMMENTS
FB #https://www.facebook.cm/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
ππΌππΌππΌππΌ
*NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITTATTAFANMU*
page 105 to 110
Soyayya suke gwada wa junan su, tare da tattali, gami da kulawa.
Sam mahmud baya k'aunar ganin b'acin ran suhailat, abubuwan more rayuwa, har zuwa kan kayan ciye ciye duk ya san zab'in ta, tun kafin tace yake ajiye mata.
A tak'ai ce dai mahmud ya zama mijin kafin tace,π namiji d'aya tamkar da dubu.
Zaman su gwanin ban sha'awa, kowa yana sha'awar su, kama daga kan iyaye, yan uwa, k'awaye, da abokan arzik'i.
Haka suka ci gaba da rayuwa cike da farin ciki, da k'aunar juna.
BAYAN WATA D'AYA DA AUREN SU
Sai zaman su ya fara canja wa, idan suhailat na cikin gidan mahmud sai ta yi ta ciwo kamar ba zatai rai ba, amma da zarar an fito da ita daga gidan sai komai nata ya dawo normal kamar ba ita ba.
Haka rayuwar suhailat ta ci gaba da kasancewa, yau gidan miji gobe gidan iyayen ta.
Anje asibiti an yi gwaje gwaje had'e da hotuna kala kala amma babu abinda likito ci suka gani.
Haka dai auren ya cigaba da tangal tangal, har zuwa wata rana suna zaune suna cikin hira kawai sai suhailat taga mahmud ya mik'e tare da cewa " suhailat nifa yanzu na tsane ki, kema kuma kin tsane ni, to kawai mu hak'ura da juna."
Suhailat ta mik'e ita ma, tare da fad'in " da gaske kake ko wasa, kai wanan abu ya yi dad'i bari naje na had'a kayana, " ta juya da sauri ta shige cikin d'aki had'o kaya cike da murnar ta.
_wai wad'an nan ma'auratan kan su d'aya kuwaπ€π€π€_
Bayan suhailat ta gama had'o kayan ta sai ta fito cike da farin ciki, tace " to Honey na tafi sai wata rana."
Kallon ta ya yi shima yana dariya yace " to RAI NAH, ki gaishe da su ummie," ya bata kud'in mota, sukai sallama, ta fito ta tafi gida.
Tana doka sallama su ummie suka gan ta da wannan uban kayan sai da gaban su ya fad'i, ummie ta kalle ta tace " ke lafiya, ina mijin naki? "
Suhailat ta k'yalk'yace da dariya sannan tace " ummie sakina ya yi fa, kinbi duk kin d'aga hankalin ki," tazo ta wuce ta gaban su ta shige d'aki.
Ummie da su Aunty zainab sai suka tsaya sororo suna kallon kallo, suna kuma ko kwan to a kan abin da suhailat ta fad'a musu.
Ummie ta kalli zainab tace " kira min mahmud a wayar ki, kice ina neman shi."
Zainab tace " to ", sannan ta d'auko wayar ta ta kira mahmud ta shaida mishi sak'on hajiya, yace mata gashi nan zuwa.
Ba'a jima ba kuwa sai ga shi ya zo, abin mamaki yanda suka ga suhailat cike da farin ciki, haka shima suka gan shi, sam babu alamun damuwa ko b'acin rai tattare da shi.
Bayan mahmud ya gaishe da ummie sai ta kalle shi tace " mahmud suhailat ta zo min da wani labari wai ka sake ta, shine nake so in ji daga bakin ka. "
Mahmud ya kalli ummie yace " ummie gani nayi na tsane ta, itama ta tsane ni, shine nace mata kawai mu hak'ura da juna."
Ummie ta kalle shi tace " kunyi fad'a ne? "
Mahmud yace " A'a wallahi bamu tab'a yin fad'a ba ummie. "
Ummie tace " to bakomai tashi ka je."
Mahmud yace " to ummie, na gode.
Bayan Abba ya dawo da dare ummie ta fad'a mishi abin da ke faruwa, Abba ya kalle ta yace " dage wa zamu yi da Addu'a, babu abin da ya fi k'arfin ubangiji, koma waye yake son ganin k'arshen su Allah ya fi shi."
Sun dad'e suna tattauna wannan matsalar, har ya fad'a mata wayar da kamal ya yi wa aminin sa, daga k'arshe yace zai je wajen malam muhammad ya taya su da addu'a.
Tun daga lokacin suka dage da addu'a, har ita ma suhailat d'in.
Bayan kwana biyu sai ga mahmud yazo, akan yana bada hak'uri matar shi ta koma d'akin ta.
Bayan ya gama wannan rok'on sannan ya kalli ummie da abba yace " ni ina tunanin duk wad'an nan abubuwan da suke faruwa har da sa hannun kamal."
Abba yace " to tunda kasan da haka ai sai ku dage da addu'a ne, wani abokina ma yace ya ganshi yaje zaria cikin kusfa wajen wani malami amma malamin mushriki, saboda haka idan zaku dage ku dage da addu'a, muma muna taya ku, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu, dukkan su suka amsa da ameen.
A ranar aka ba mahmud matar shi, kafin su wuce gida sai da suka biya islamic kemis wajen malam sani, suka karb'o magun guna had'e da k'arin Addu'o i, wad'an da za su lazimci karanta wa kuma su yi amfani da su a koda yaushe.
BAYAN SATI D'AYA
Zaman su ya koma normal fiye da da, kuma tun daga lokacin suka k'ara kiyaye wa matuk'a wajen kula da ibadar su.
Bayan wata uku, suhailat ce kwance a kan jikin mijin ta, tana zuba mishi shagwab'a, ta kalli mahmud tace " HONEY! dan Allah ka barni in je in dubo zainab, kwanan nan ina yawan mafarkin ta. "
Mahmud yace " RAI NA! ai babu abin da zaki nema a gidan duniyar nan da zan kasa yi miki shi, saboda kema kina yi min duk abin da kika san zai faranta min, saboda haka ki shirya gobe in Allah ya kai mu, mu je mu dubo ta."
muje zuwa
urs π ±Kππ
Monday, July 23, 2018
Subscribe Our Channel
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write blogger