PDP Ta Kalubalanci Buhari Kan Ya Kori Ministar Kudi Kan Shaidar Yiwa Kasa Hidima Ta Bogi
__¥___
*
Jam'iyyar PDP ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan ya gaggauta korar Ministar Kudi, Kemi Adeosun tare kuma d hukunta ta bisa amfani da shaidar kammala bautar kasa (NYSC) ta bogi.
Sakataren Jam'iyyar na Kasa, Kola Ologbondiyan ya ce a halin yanzu ta tabbata cewa gwamnatin Buhari na cike da barayi, 'yan damfara da mutane marasa gaskiya inda ya jaddada cewa kada Buhari ya kuskura ya kyale Ministar wanda yin hakan zai nuna cewa ba da gaske yake yi ba game da shirin yaki da rashawa da ya kaddamar.
No comments:
Write blogger