A Najeriya a yau ake fara wani taron masana a kan rayuwar marigayi Dr Mamman Shata da basirarsa a fagen waka.
Masana daga kasashen duniya ne za su gabatar da makala a wajen taron, wanda Cibiyar nazarin harsunan Najeriya ta shirya, tare da hadin gwiwa da Sashen Nazarin harsunan Najeriya da kuma sashen Nazarin kimiyyar harshe na jami`ar Bayero ta Kano.
Taron dai yazo ne a daidai lokacin da wasu ma`abota tsofaffin wakoki irin na shata da dangoginsa ke kukan cewa kafafen yada labarai na mai da su saniyar-ware a filayen shakatawa da suke gabatarwa a cikin shirye-shiryensu.
Wannan na faruwa ne, kasancewar hankalinsu ya fi komawa kan mawakan nanaye, suna fargabar cewa irin hkima da azancin da ke cikin tsofaffin wakokin ka iya bacewa idan aka ci gaba da tafiya haka.
No comments:
Write blogger