Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun sanar da fara yajin aiki daga karfe 12 na daren Laraba 26 ga watan Satumba.
Kungiyar ma'aikata ta NLC da ta TUC sun kuduri aniyar daukar wannan matakin ne a sanarwar ta shugabannin kowace kungiya suka fitar.
Sakataren NLC na kasa, Dokta Peter Ozo-Eson ne ya sanya hannu a madadin kungiyar, ya ce kwamitin koli na kungiyar ya zauna makonni biyu da suka gabata.
Kungiyar ta amince da a sanar da gwamnatin Tarayyar Najeriya cewa ma'aikata za su fara yajin aiki, idan ba ta duba batun sabon albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar ba.
Ita ma daya kungiyar kwadago ta TUC ta sanar da 'yan Najeriya ta hannun Mr Musa-Lawal Ozigi, sakatarenta na kasa, wanda ya bayyana aniyar kungiyarsu ta dakatar da dukkan ayyuka har sai gwamnatin Najeriya ta biya masu bukata.
No comments:
Write blogger