spon

Saturday, September 29, 2018

Home RAHAMA SADAU TASAKE SAMU LAMBAR YABO

Subscribe Our Channel


Har yanzu tauraron fitacciyar jaruma Rahama Sadau na cigaba da haskawa inda ya samu wani sabon lambar yabo a karshen makon da ya shude.


Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya  a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar 22 ga watan Satumba a dakin taro na Transcorp hilton Hotel dake Abuja.
Rahama ta nuna farin cikin ta samun wannnan kyautar a shafin ta na kafafen sada zumunta.

Gasar Peace Achievers Awards biki ne wanda aka gudanar a ko wani shekara domin karrama fitattun hukumomi da yan kasar dake taka rawar gani wajen raya zaman lafiya a kasar.

Bikin gasar na bana shine karo na bakwai.
Kyautar da jarumar ta samu shine na uku da zata samu bana bayan na jaridar Leadership da gidauniyar Global Women Empowerment network

No comments:
Write blogger