spon

Sunday, September 2, 2018

Home YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI

Subscribe Our Channel


HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
 TITTLE YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI.

KAYAN HADI*
  • Kwai
  • Kifi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Fulawa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyada
 
*YADDA ZA KIYI*
Da farko ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki ďora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cicire 'kayar shi sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, ki fasa 'kwai kaďan ki zuba a ciki, ki ďauko fulawa ki zuba(hikimar sa fulawa dan ya haďe jiki ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe
 
SPINACH EGG SAUCE

INGREDIENTS:
1. Spinach (Alayyaho)
2. Eggs, oil
3. Tattasai, tarugu, albasa and garlic.
 
PROCEDURE: A wanke alayyaho a yayyanka qanana, sai a yayyanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko zaki samu tukunyar da babu komai a wuta ki juye alayyahon duka ki ďan turara sa. In kina da steamer zaki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.
Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in ya ďan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu ki juye alayyahon ki jujjuya su hade.
Ki kaďa eggs ki juye a ciki ki juya su haďe da kyau, in ya gama soyuwa sai ki sauke. Zaki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma doya da dankali.
Note: Zaki iya zuba isashen kwai ni nafi son shi a haka. Ba dole sai spinach ba zaki iya yi da sauran ganyayyaki. Kuma zaki iya yi babu kayan miya, idan kika yi steaming alayyahon tare da albasa sai ki kaďa kwai ki juye a ciki. A kula sosai idan kin yanka alayyaho ne kafin ki yanka to ki zuba ruwa isashe yanda zai taso sama sai ki kwashe zaki ga qasan ya koma qasa in ba haka ba zaki rinqa ci kina jin qasa. Yana da dadi in aka sanya a shinkafa. Ga kuma qara lfy.
 
Gashashen Kifi/ Grilled Fish
Kayan Hadi:
1. Kiyin Karfasa / Tilapia
2. Albasa, lemun Tsami, Citta, Kanunfari, Masoro, Tafarnuwa, Garin Yaji ko Tarugu.
3. Maggin Knorr, Gishiri, Kori, Thyme, da kayan Qamshi da Dandano
4. Myan Gyada.
Yadda Zaki Sarrafa: Ki wanke kifin ki ciki da bai, saka hannu har cikin bakin kifin ki wanke shi sosai. Bayan kin wanke sai ki tsane ruwan in sauri kike yi kisa towel ko tissue ki cire ruwan.
Daga nan sai ki daka ko kiyi blending kanunfari da masoro, citta, thyme, da sauran su. In kuma kina da garin su shikenan. Sai ki juye a mixing bowl.
Sannan ki dauko albasa kamar rabi haka ki saka, ki zuba tafarnuwa biyu manya, idan ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi blending ko daka yayi luqui luqui. Haka nan in tarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi.
Daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba curry kadan, ki zuba knorr da gishiri, sannan ki matse lemun tsami qaramin cokali daya ki zuba. Sai ki zuba oil yanda hadin zai kama jikin kifin.
Bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki. Sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a fridge yayi kamar minti 30 in a freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi qanqara ba.
Daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da oven ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin ki, kina yi kina jujjuya wa har ya gazu.
Hadin Sauce/Sauce
Kayan Hadi:
1. Albasa biyu ko uku
2. Tarugu, Tattasai da Green pepper
3. Tafarnuwa 1
4. Gishiri da Maggi knorr
Yadda Zaki Hada Sauce: Farko zaki yanka albasanki da tattasai da green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura mai a tukunya kamar quater qaramin ludayi, in yayi zafi ki zuba albasan da tattasan, ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba niqaqqen tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa tare da sinadarai, sai ki dan zuba ruwa kadan yanda zasu dahu. Zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida.
Daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din a sama. Ai haka zaki ji kawai yana shigewa cikin tumbin maigida yana santi.
Kada a manta a ajiye wa mai gida lemun tsami na wanke hannu bayan ya gama ci saboda qarni. Sannan a tabbata an saka ginger ko citta, tafarnuwa da kanunfari don suna da muhimmanci a gashi.

No comments:
Write blogger