'Yan Najeriya na ci gaba da jimamin kashe ma'aikaciyar kungiyar agaji ta Red Cross da kungiyar boko haram ta yi, bayan sun yi garkuwa da ita a watan Maris din shekarar nan.
Mayakan kungiyar sun kashe Hauwa Liman, wacce ungozoma ce, 'yan kawanaki bayan da su ka fitar da sanarwar cewa za su kashe daya daga cikin ma'aikatan nata.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce labarin kashe Hauwa ya daga musu hankali.
Gwamnatin Najeriya ta ce kisan ungozomar rashin imani ne.
- Buhari ya yi magana da mahaifiyar Leah Sharibu
- Red Cross: Wa'adin da Boko Haram ta bayar ya kusa cika
Latsa lamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar da Habiba Adamu ta yi da mahaifin Hauwa Liman:
An yi garkuwa da Hauwa da wasu sauran ma'aikatan agaji biyu a garin Rann da ke arewacin Njaeriya.
Daya daga cikinsu ita ce Saifura Ahmed Khorsa wacce kungiyar boko haram din ta kashe a watan da ya gabata.
Har yanzu dai, akwai wata daliba 'yar shekara 15 a hannun mayakan wadanda ke da alaka da kungiyar tada kayar baya ta IS.
Leah Sharibu na daya daga cikin 'yan makaranta 110 da aka yi garkuwa da su a garin Dapchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a watan fabrairun da ya gabata.
Hauwa Liman da Saifura Khorsa da Alice Loksha, da wata malamar jinya na aikin kula da mutanen da suka rasa gidajensu a garin Rann dake Jihar Borno, inda nan ne tashin hankali ya fi yawa lokacin da aka sace su a watan Maris.
A watan da ya gabata, ICRC ta sami bidiyon da ke nuna kisan Saifura Khorsa.
Wani dan jaridan Najeriya ya ce ya ga bidiyon da ke nuna lokacin da aka harbe Hauwa Liman.
Patricia Danzi, darektar yankin ta ICRC, ta ce babu wani dalilin kashe ma'aikatan kiwon lafiyar kuma ta na tsoron abun da ya faru a kansu na iya shafar ayyukan kungiyar a yankin.
Ta ce, "Wannan mummunan labari ne ga dukkanmu, ga iyalansu, ga ma'aikatan jin kai, ga ma'aikatan kiwon lafiya da kuma duka mata, 'ya'ya mata da kuma iyayen Arewacin Nigeria da ma duniya baki daya."
Ministan Harkokin Watsa labarai da Al'adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce gwamnati ta "raunata sosai" da labaran kisan, amma ya kara da cewa "za ta ci gaba da tattaunawa."
Ya ce kuma za ta ci gaba da aiki don 'yantar da Alice Loksha da Leah Sharibu.
No comments:
Write blogger